Showing 90001 words to 93000 words out of 100703 words
Chapter 31 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt
ba
sai sake kiran Junaidu da tayi ta ce masa “sun iso yanzu ya zo” sannan ta je ta duba d’akin Amarya taga da sakata
tukunna ta dawo inda suke
ta tsugunna.
Daga K’asimu har Laraba babu wanda ya iya tab’a Sadiya
dan shima K’asimun zuwa yanzu ya fara tsurewa
sakamokon ganin da yayi ko motsi Sadiyar bata yi.
Tana tsugunnawa taji ana tab’a k’ofa dan haka ta je ta tambaya “waye?”
Ajiyar zuciya ta sauk’e jin Junaidu ya ce “ni ne”
A hankali ta bud’e mishi.
A hankali yad’an gaisheta
sannan ya hau tambayarta “mai ya faru?
Ina Umman nasu!?
Sun tafi tun jiya wayar su bata shiga. Mai ya faru ba dai hatsari suka yi ba ko?….”
Maganarsa ce ta katse sakamokon hango Sadiya a kwance a sank’ame!…….
Dakyar Junaidu wanda k’irjinsa ya hau dukan uku uku ya samu ya k’arasa wajen ya tsugunna ya yaye mata fuska!
Wani wawan tsalle K’asimu yayi had’e da ihu ya fad’a kan Laraba tsabar tsananin tsoro.
Da sauri shi kuma Junaidu ya kauda kanshi gefe ya runtse idanuwanshi wasu zafafan hawaye suna zubo mishi
dai dai nan Hansai ta k’araso wajen……
Cikin kuka Laraba wadda ta samu ta ture K’asimu daga kanta da kyar ta ce
“Hansai garin yaya haka ta faru?
Mai ya sameta haka ba ido?
Su waye suka kashe min Sadiya?”
Ta k’arashe maganar tana sake fashewa da wani matsanancin kuka.
Tiryaan tiryaan haka Hansai ta zayyano musu duk abunda ya faru bata b’oye komai ba
sannan ta ce “Tana da rai bata mutu ba, inaga yanzun
bacci tayi.”
Cikin tsanannin b’acin raii Junaidu ya rufe ta da fad’a kamar y’arsa…babu abunda ya fi b’ata mishi rai irin wai ‘wajen mayu da aljanu suka je’!
Ya jima yana bala’i yana hawaye kafin ya mik’e a mugun fusace ya fita.
Jalila kuwa in banda kiran sunanta tana tattab’ata ba abunda take yi.
Junaidu bai yi minti ashirin ba ya dawo gidan da wasu mutane kana gani kasan Likitocine.
Su suka d’auketa daga nan ya cewa Hansai ta biyo shi.
Bai dawo ba sai washe gari shi kad’ai ba Hansai.
Jalila da Laraba ya tarar a parlourn.
A hankali ya zauna yana kallonsu
Jalila ta rakub’e tanata faman kuka abun tausayi.
Da kyar ya kauda idonshi a kanta yana jin tsananin tausayin ta
dai dai nan K’asimu ya shigo
ya nemi waje ya zauna
sannan ya ce
“Gani dan albarka ya ake ciki?”
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce
“Umma bata mutu ba!
Amman halin da take ciki gara mutuwa…..
Ta samu tabun hankali
sannan idanuwanta babu
kuma k’afafuwanta sun shanye .
Yanzu dai na turasu Cairo ita da Hansai, za a yi mata aiki a chan daganan ta d’an dede ta kafin su dawo...”
Shiruuu, yayi yana jin zuciyarshi tana tafarfasa
kafin ya mik’e ya k’arasa wajen Jalila wadda take kuka wiwi ya zauna sosai a gabanta
A hankali ya kamo hannunta ya fara magana
“Jalila sai dai hak’uri,
kuka ba zai yi maganin komai ba, mu bita da addua kawai da fatan Allah ya bata lafiya.
Kuma inaso ki yi
hak’uri sannan
ki cire taurin kai
ki rungumi Mijin da aka zab’a miki!
Ki nutsu ki yi hankali Jalila dan girman Allah, Umma kad’ai ta isar miki ishara.
Ba komai kake sakawa a gaba ka samu ba.
Dan Allah dan Annabi Jalila ki koma kamar Jalilan ki ta daa yadda kike lokacin da muke a hannun Mama kafin dawowar Umma cikin rayuwarmu!
Ki duba dai ki gani
tsarin da kuke kai ke da Umma ba dai dai baneba sam!
Na fad’a muku na yi nasihar har na gaji daga ku
har Anty Zainab
wadda ita yanzu Allah ya taimaketa ta gane gaskiya.
Ki bud’e idonki da kyau ki duba ki gani
shin da ku da su Mama waye ya ci riba yanzu?
Kinga fa tun a duniya Ubangiji ya nuna muku iyakarku.
Ki hak’ura da Arshaad
ki hak’ura da So da Buri Jalila
ki hau matakin gaskiya za ki ji dad’i a yanzu da gaba.
Ki yi hak’uri ki tare a gidan Mijinki
Na so in bashi gida babba mai bene da komai amman furr ya k’i, haka dole na hak’ura na
bashi k’arami
mai d’akuna biyu da toilet d’aya da parlour har da tsakar gida saboda ya ce shi kad’ai zai iya affording dan ya tabbatar min ‘tabbas zai dinga biyana kud’in haya’
Jalila irin wannan Mijin mai wadatachchiyar zuciya shi a ke nema, ki duba fa kiga
ya san da zancen ki
ke da Auwal ya san komai amman ya ce ‘ya ji ya gani’
Mahaifiyarshi ma ta ce ‘ta ji ta gani’
What more could you ask for daga bawan Allah nan??.
Kar ki damu
na yi miki kayan d’aki da kayan kitchen na gani na fad’a, ki yi
hak’uri ki daure Jalila pls,
Mahaifiyarshi tana chan hankalin su duk a tashe!
Shiyasa na je na samesu na ce ‘anjima da yamma su zo a mik’a ki gidanki’.
Ki fad’amin ko nawa kike so
zan baki jari. Duk abunda kikeso don’t ever hesitate to ask me!
Dan Allah Jalila amman ki yi k’ok’ari ki gyara halayenki
dan zaman gidan aure daban yake da zaman gida
Baki da wanda zai gaya miki gaskiya sama da ni.....”
Nan ya yi mata Nasiha mai tsananin rashi jiki.
Ya k’arashe da “Allah yayi miki albarka.
Anjima kafin a kai ki
ki je gidan Kaka
Baba ya ce ‘ki je ki sameshi
suna son ganinki’.”
Cikin tsanannin kuka Jalila ta fad’a jikinsa
tana cewa
“Ka yi hak’uri Ya Junaidu.
Ka bawa su Mama hak’uri
In sha Allah zan chanja zan yarda….
Dan Allah ku tayani da addua
ni kaina bana son in sake komawa waccar Jalilar saboda in banda tsananin k’unci da tashin hankali da wulak’anci ba abunda na tsinta!
Hankalina yafi kwanciya a lokacin ina wajen Mama
babu kyashi ba hassada ba komai…
Dan Allah Ya Junaidu ka tayani bawa su Huda hak’uri wallahi na tuba.”
Hannu yasa ya rungume ta shima yana hawaye….
Sun jima a haka tukunna ya mik’e ya mik’ar da ita tsaye
ya kama hannunta ya ce mata “Ta shiga d’aki ta huta zuwa lokacin da Anty Zainab zata zo ta tafi da ita gurin su Baba”
dan sam baya son barinta da su Laraba gudun kar su sake hargitsa mata lissafi.
Da “to” ta amsa sannan ta shiga ciki
dan itama tana buk’atar Hutun.
Sai da ya ga ta kwanta tukunna ya juya ya fita ya yiwa su K’asimu sallama ya fice......
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
Final Episode.
Mikiya Writers Association.
Sai da aka yi sati d’aya tukunna Aslam ya bar Huda ta je wajen Mama da kyar,
dan sai da ta dinga yi masa kuka wiwi tukunna amma ya ce
“Daga ranar sai wata wata zata dinga zuwa”.
Tanata fushi haka suka nufi gidan da yamma bayan ce mishi ta yi wuni takeso ta yi.
Tana zuwa aka yi sa’a su Ummu suma sun zo ita da Sumayya da Khadija
dan haka farin cikin ya had’e mata biyu.
Gaisawa kawai Aslam ya yi da su da kyar
daga haka ya juya ya fita da sauri.
Dariya su Ummu suka yi suna mamakin irin tashi kalar kunyar.
Cikin tsananin farin ciki suka zauna anata hira
har su Shuraim waenda Mama ta damu Abba har sai da ya kwaso mata su yau da safe tukunna hankalinta ya kwanta…tun suna nuk’u nuk’u har suka ware
aka shiga tab’a hirar da su abun gwanin ban sha’awa.
Hudan ce ta ce “bara ta kira Sakina itama ayi da ita”
Dan haka ta kirata video call…
Mura take yi sosai
dan hatta muryarta ma ta d’an disashe sannan sai goge hanci take yi ya yi jaaa sosai har ma da fuskar tata gaba d’aya.
A haka sukai mata sannu sukai mata sallama a cewar su “ta je ta huta”
Ba dan taso ba ta ce “tou” ta yi musu sallamar itama ta kashe.
…..BAYAN SATI BIYU…..
Duk yadda Aslam ya so ya hana ta fita haka yanaji yana gani yau ma ya barta ta fita gidansu Mama bayan doguwar magiyar da su Sudais suka yi ta jera masa.
Kasancewar yau birthday d’in Mama yasa suke son had’a mata surprise birthday kafin ta dawo…
Tun Safe Abba ya d’auketa suka fita daga gidan,
ya kaita spa suka je shopping
daga nan suka biya park!
Sai da Sudais ya tura mishi ‘we are done’ Tukunna ya ce mata “ta taso su koma gida”.
Ba wani hayaniya ballons d’inma ba wasu masu yawa ba ne sai k’atoton cake d’inta mai hotanta a jiki
da drinks kala kala..
Haka suka shirya surprise d’in.
Tana shiga ta gansu har Mommy da Aaima duk sun zo suma….
Ta yi tsananin farin ciki kuwa
harda y’ar kwallar ta…ba abunda yafi mata dad’i irin yadda Shuraim da Sudais suka maida ta uwa
suke ji da ita kamar yanda itama take ji da su.........
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, Mama bata bawa Sudais da Shuraim single reason d’in su yi kukan rashin uwa ba!
Daman tun ranar farko a bikin su Huda da ta gansu Yaran suka shiga ranta matuk’a.
Yadda take yi musu ko Ummin iyakar abunda zata yi musu ne.
Tarbiyya kam da gaske take basu ita, idan lokacin raha yazo ayi in sun yi kuskure kuma ta nuna musu kuskurensu ta yi musu gyara.....
Suma su Shuraim d’in
tun basu sake da ita ba har suka sake, ko shawara suke nema wajenta
komai wajenta
dan tabbas yadda take jinsu a cikin ranta haka nan suma suke jinta
suke kuma tsananin girmamata...
Tsakaninta ita da Abba kam tabbas Mama zata iya cewa tana cikin mata first class a sa’ar miji a duniya, ko kuma ma ta ce ita kam ta fi kowa sa’ar Miji a duniya…...Tsantsar zallar k’auna da kulawa had’e da tattali yake bata
baya duba shekarunsu
sam dan shi
idan ya tashi gwada mata soyayya kamar wasu teenagers haka yake ganinsu shi da ita........
A b’angaren Mommy itama bata bawa Aaima reason d’in da zatayi missing Mammy ba,
kulawa da shak’uwa ce a tsakaninsu ta musamman
dan ita Mommy ce mata ta yi ta d’auketa a matsayin best friend d’inta.........
........
Kamar kullum yadda suka saba yau ma Sakina ta kirata suka shiga hirarsu gwanin ban sha’awa duk da kuwa Sakinar ba wani dad’i take ji ba saboda murar da take ta faman mata on and off!
Ta rasa sukuni gaba d’aya sanyin garin ya isheta.
Jin yanayinta da muryarta
da kuma rashin lafiyar da take ta yi kwana biyu
ya sanya Hudan ta ce
“Maman baby je ki kwanta ki huta
Allah ya sauwake.”
Ta k’arashe maganar da d’an dariya k’asa k’asa sannan tana addu’ar Allah yasa harsashenta akan Sakinar ya zamo gaskiya ne.
“Ok na gode
sai da safe” Sakinan ta ce..Ba ta kashe wayar ba
ta d’an yi shiruu kamar mai tunani sai kuma ta kwashe da dariya kafin ta ce
“Ai ni sai yanzu ma na fahimceki!
Tab! Inaaa ba wannan tukunna
wallahi iyaka mura ce kawai take damu na.”
Cikin rashin fahimta Huda ta ce “Ba kince an sallameku ba?”
Dariya Sakina ta yi ta ce “to
kuma daga an sallamemu sai me?”
Bata jira amsar ta ba tana dariya ta ce
“Eh, an sallamemu
dan jikin nashi ya yi kyau
amman muna lek’awa, kullum,
check up”.
Shiruuu, Huda ta yi kafin ta ce
“Anya kuwa Sakina?”
Sai da Sakina ta yi dariya sosai tukunna ta ce mata
“Allah da gaske,
babu komai ma fa tsakaninmu har yanzu
sai dai hira kawai da tsantsar kulawa da soyayyyar da yake gwada min.
Da sauri Hudan ta ce
“Kai!”
Cikin murmushi Sakina ta ce
“Kin san Allah nima kaina ina mamakin shi, ba daban ina fahimtar yanayin sa ba
tou da sai in iya cewa ma bashi da lafiya…Ban san dalilinsa ba kinga ni kuwa ai bazan ce gani ba!
Besides ni nama fi son haka.”
Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin ta ce
“Kuma bai chanja miki ba? As in ba ya wani fushi da ke”
“Ko d’aya, wallahi
kulawar ma da yake bani ni kaina banyi tunanin ta ba
kawai dai maybe shi tsarinshine haka ko kuma dai wani abun
besides ai bamu fa wani dad’e ba so it’s not an issue.”
“Shikenan tou, ki gaidashi”
Shine abunda Huda ta ce. Daga nan suka yi sallama suka kashe wayar.
Murmushi kawai ta yi tana duba wayar, a hankali ta sauk’e ajiyar zuciya
ta shiga tunani
....Kullum tare suke kwana, a jikinsa take yin bacci, tana jin yanayin bugun zuciyarshi da yadda yanayinsa yake alamun lafiyarsa k’alau kuma a k’age yake amman in banda hug ba abunda ya tab’a shiga tsakaninsu……
Sam bata san ya shigo d’akin ba dan yaje siyo musu milkshake a chan k’asan hotel d’in da akeyi wani mai dad’i!
Sai da ta ji ya kwanta a bayanta tukunna ta yunk’ura da sauri tana shirin yin magana shi ya rigata ta hanyar cewa
“Sakina I love you fisabilillah
Ba wai wani abu daban ba!
Shiyasa kika ga ban yi yunk’urin komai ba saboda
Ina so ne har sai kin fahimci hakan, kin yarda dani, kin saki jiki dani tukunna.
Na san zan takura amman yadda nake jin ki a raina
tsaf zan iya rayuwa dake a haka muddin baki gama fahimtar kalar k’aunar da nake yi miki ba……..”
A hankali ta juyo sosai tana kallonshi suka yi facing juna a kwancen!
Kasa cewa komai ta yi kawai sai ta sunkuyar da kanta k’asa kafin chaan! Ta ce
“Ya Auwal na yarda da kai na yarda da chanjin da na gani a tattare da kai.
Tunda har kaga na aureka tou yarda da k’auna ce ta kawo hakan.
Sannan zan rayu da kai a ko wanne hali.…..”
Yadda ta ga yana kallonta ne ya sanya ta yi saurin b’oye fuskarta a k’irjin shi
dan tashi d’aya sai ta ji duk kunya ta lullub’eta.
Murmushi ya yi yad’an shafa kanta, a hankali ya yi kissing kan nata yana mai shak’ar k’amshin da yake fitarwa kafin ya shiga binta da wani mayen kallo k’irjinsa yana bugawa da masifar gudu….
Sannu a hankali yanayinsa yana k’arasa sauyawa ya sa hannu ya janyota ya saka ta a jikinsa sosai!.
Sai da numfashinta ya kusan d’aukewa sakamokon wasu sak’onnin da ya shiga aika mata waenda suka girmi hankali da wayonta.
Da sauri cike da tsoro da fargaba muryarta na rawa ta ce “Dan Allah!!!
Ni fa da nace haka bawai ina nufin yanzu ba.”
Ko sauraronta Auwal bashi da niyyar yi, dan tun kafin a je ko’ina notikan kansa suka kwance hankali ya fara barin gangar jikinsa…
Tabbas ya yarda kuma ya sake tabbatarwa ‘kamilalliyar mace daban ta ke! Sannan matar sunna sinadarinta na musamman ne’ Gashi kuma abun sai ya taru ya had’e masa da giyar zazzafan feelings da soyayyar da yake yi mata, shi yasa ya manta kowa ya manta komai hatta shi da karankansa ya manta kansa.
A ranar Huda ta sha Allah ya isa dan ita ce ta kirata a waya har ta janyo mata wannan jalalar.
Sam bata tab’a tunnanin zatayi rai ba
dan Mr Auwal sai da ya yi mata dalla dalla……..
Tun daga ranar kuwa ta rasa nutsuwa da sukuni. Daga nan ma Las Vegas suka wuce Honeey moon…
Auwal shi kad’ai yake k’ibarsa yana enjoyment d’inshi
Ita kam in banda rama ba abunda take yi
dan
kwata kwata ba enjoying garin take yi ba
dan ita gani take ma kamar su suke tunzurashi yin wasu abubuwan.........
Da kyar Aaiima ta iya samun Abba ta yi masa maganar Junaidu dan zuwa wannan lokacin kam soyayya mai k’arfin gaske ta k’ullu a tsakaninsu.
Abba ne ya samu su Dad ya yi musu bayani su kuma suka ce a tambayi su Mama indai har ba shi da wani mugun hali sai a shirya komai
dan
kasancewarsa d’a ga Usman hakan ba shi zai sanya su shiga tsakanin Aaima da farin cikin ta ba dan k’iri k’iri ta nuna shi take matuk’ar so!.
Sannan su a ganinsu yanzu Aaiman abar tausayi ce
duk da kuwa sun san idan suka ce rashin Mammy yana a cikin matsallolin Aaima ba su yiwa Mommy adalci ba
duba da yadda take iyakar k’arshen k’ok’arinta wajen ganin Aaiman bata rasa komaiba
amman kuma uwa dole daban take.
Dan haka za su yi k’ok’ari wajen ganin sun taimaka farin ciki ya wanzu a rayuwarta na dindindin......
Tabbas Mama ta ji dad’in wannan had’in
dan haka tashi d’aya
ta faiyyacewa Abba halayen Junaidu wanda tun tasowarta dashi bata tab’a ganin shi da wani mummunan hali ba
sai dai mai kyau
sannan yanada zuciyar nema da amana
ga sanin ya kamata…..
Abba ma ya ji dad’in jin haka
dan haka ya ce “bara ya je kawai ya samu su Dad ayi komai a gama. Kafin Aaiima ta tafi rubuta finals d’inta a saka rana, tana dawowa a d’aura aure in shaa Allah.”
A hankali Mama ta ce
“Amman fa Abba akwai wani abu guda d’aya!
Kasan case d’in Junaidu na zaman jail
wanda tunda ya je ya dawo ya kud’ance! Kud’i na ban mamaki….
Last week ma sai da aka sake gano Gidaje da kadarorinsa
dan shi b’oyewa yake yi..a iyaka Kano fa Gidajensa masu matuk’ar kyau da tsada sun fi ashirin
ga kadarori ga filaye
wanda bamu san source of income d’inshi ba!
Inda hali gaskiya a d’an yi mishi tambayoyi akan wannan lamari a bincika.
Naji dai kwanaki su Abba Madu sun ce sun yi mishi tambaya
amman banji sun ce ga amsar da ya bayar ba.”
Jinjina kai Abba ya yi daga nan ya ce ‘zai nemi zama da Junaidun ko zuwa gobene in shaa Allah, su tattauna.”
.....Har gida kuwa Junaidun ya zo ya sameshi bayan ya ce masa ‘ya zo yana son ganinsa’
Shi da Daddy ya tarar
dan haka ya gaidasu cikin girmamawa
suka amsa masa da kulawa.
Ba tare da b’oye b’oye ba Abba ya ce “sun san bashi da wani mummunan hali amman kuma suna buk’atar sanin kwakkwaran source of income d’inshi”
A hankali Junaidu ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya fara basu labari....
“A lokacin da aka sallame ni daga prision…………
Mun fito mun kama hanya,
bamu kai ga zuwa inda za mu je ba cikina ya b’aci!
Dan haka na nemi alfarmar su tsaya in d’an yi uzuri.
Suna tsayawa na fita…
Ina kutsa kai cikin d’ajin kamar an ce in juyo nan na ga wasu maza da mask su uku sun nufi motar.
Duk sai da suka fito da y’an motar suka dubasu amman sam babu abunda suke nema wanda sai daga baya na gane waenda Arshaad ya tura ne
kuma ni suke nema.
Kamar na sani a lokacin sai na b’oye kaina. Bayan na b’oye kaina su kuma suka gama dube