Showing 54001 words to 57000 words out of 100703 words
Chapter 19 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt
ta mik’e ta wuce d’akin.
Tana wucewa Umman ta juya ta ci gaba da abunda take yi, ba tare da ta kalli Anty Zainab d’inba tace
“Zainab y’ay’an yanzu fa sai hak’uri, in ba da Allah ka had’a su ba ba zuwar maka aike suke yi ba.”
Murmushin takaici Anty Zainab tayi kafin tace “Y’ay’an da aka b’ata dai!
Y’ay’an da son zuciyar iyayensu take kaisu ga halaka”
A zabure da mamaki Umma ta juyo tana kallonta sai kuma ta kwashe da dariya ta rangad’a gud’a! Kafin ta ajjiye brush da man hannunta ta juyo gaba d’ayanta ta gyara zamanta
ido cikin ido ta kalli Anty Zainab d’in kafin tace
“Kin san Allah! Bar ganin wai kin san cikina na san naki
Bar ganin mun yi Abotar sama da shekaru talatin da ke!
Billahil Azim kin ji rantsuwar y’ar musulmi ko?
Yanzun nan zan murzawa idanuna toka in gurza miki rashin mutunci,
har makofta sai an jiyomu.”
Ta k’arashe maganar tana d’aga murya.
Cikin tsananin b’acin rai Anty Zainab tace
“Murzawa ido toka kuma na nawa Sadiya?
Banda tsantsar son zuciya da son kai da rashin sanin ya kamata mai kuka sani?”
This time around mik’ewa tsaye Umma tayi cikin kad’a hannuwa tana gyara d’aurin zaninta tace
“Oya oya Zainba shiga d’aki yanzun nan ki d’auko kayanki ki yi waje! Tun kafin mu kasa sheda juna ni da ke.”
Dai dai nan Jalila ta k’araso wajen da gorar ruwan sanyi a hannunta, ba tare da ta san
dalilin hayaniyar da ta tarar ta d’an fara tasowa ba tace
“Ko baki ji abunda aka ce miki ba ne?
‘Out’ ta ce!!!!”
Anty Zainab d’in
bata kulata ba dan ba saar yin ta bace ba, ta kalli Umman tace
“Ko baki koreni ba Sadiya na gama zama da ke, dan ba zan
tab’a zama kina yi min zagon k’asa ba, amman kafin In tafi ina so ki san na san abunda kukayi ke da y’arki..
Yau naje wajen Malan yanzu haka ma daga chan na ke”
Bata damu da yadda maganar tata ta girgiza su ba taci gaba da magana
“Sadiya da kika san ba zaki bari ayi min abunda nace ba ai
da kin fito kin fad’amin na chanza shek’a, tunda
na san dalilinki na hana ayi aiki na
saboda kina gani ata dalilin aikin Jalila ne na samu matsala so kar azo a gyara nawa azo ita kuma Jalila ta rasa Arshaad ko? Haka ne ko ba haka ba?
Haba Sadiya!! Wacce irin zuciya ce da ce?
Wacece Ummul aba’isin fad’awata wannan matsalar tsofai tsofai da ni?
Ko kina tunanin ban san abunda nake yi ba?
Sarai fa na fahimci komai
kuma duk dan kar ku ji ba dad’i shiyasa na ja bakina na yi shiru.
Abun naki ma ni sai na ga kamar har da mugunta
saboda a ganina
Idan kin ce nace na hak’ura da Baban su Khadija bana son komawa gidansa a bar aikin
mene kuma
zaki d’aura da cewa
ayi abunda ba zan koma ba?
Haka muka yi da ke?
Haka alk’awari ya ce Sadiya saboda Allah?”
Anty Zainab ta k’arashe maganar tata tana fashewa da kuka
saboda wani takaici da dana sanin biyewa Sadiya da ta dinga yi tun Yarinta
da ya lullub’eta lokaci d’aya…..
Da kyar ta samu ta lallashi kanta ta share hawayenta sannan ta d’ago ta kallesu!
Su na nan a tsaye sun yi cirko cirko tace
“Bari ku ji in gaya muku..
Wutsiyar rak’umi ta yi nesa da k’asa! Ba na duba bana buga k’asa dan bin malaman ma ke kika saka ni
amman wallahi tallahi ku rubuta ku ajjiye in dai Arshaad kuke jira ya dawo ya auri Jalila to kuwa zata k’are ne a haka har abada babu Miji!
Ku d’auki maganata as curse a matsayina na k’anwar Mahaifinta, bi’ma’ana baki ne na yi mata….”
Wani wawan tsalle Umma tayi ta dira kan Anty Zainab ta shak’o wuyanta wanda sai da ta kaita k’asa
Ba su yi wata wata ba suka rufeta da duka ita da Jalila….
Tun Anty Zainab tun tana daurewa har ta ware murya ta hau zunduma ihun neman agaji….
Da kyar mak’ofta suka kwaceta a hannunsu bayan sun shishshigo..
Still inbanda zage zage da tujara ba abunda Umma da Jalila suke zubawa.
Wata mata ce tace mata
“Ta zo su wuce ta kaita wajen Talatu ta d’an kimtsa daga nan sai ta wuce gidanta
saboda gaba d’aya jikinta sun yi mata jjina jina.”
Ba wanda ya iya tanka musu dan an san halinsu,
haka nan matar ta kama Anty Zainab wadda take tafiya da kyar ta jata sukai waje
Mutane ma aka fara watsewa.
Wani tsohone ya kasa hak’ura ya juyo ya kalli Umma
yace
“K’anwar Mijinki ce fa!
Kuma k’awarki tun kuna Yara saboda Allah idan ke kin daketa ai bai kamata ki bar y’arki ta d’aura ko da yatsa a jikinta ba.
Wannan rashin sanin ya kamata har Ina?
Ki bi duniya a sannu fa, Sadiya.”
Yunk’urowa ta yi zata yiwa tsohon rashin mutunci
wasu samari biyu da suma basu kai ga fitaba suka yo kansu d’ayan ya ce
“Kun san Allah In rashin d’a’a ne mu har certificate muke bayarwa!
In kuma kanku na hayak’i to ku tanka mu gani”
Shiruuu, suka yi
ba wadda tace uffan.
Girgiza kai kawai tsohon yayi ya juya ya fita.
“K’ananan marasa kunya kawai”
Samarin suka ce kafin su juya su fita, daga nan aka watse aka barsu su biyu suna huci.
Su Baaba Talatu suna tsakar gidansu na ciki wajen d’akinta a kan darduma gaba d’ayansu
hankalinsu a mugun tashe dan yanzun nan aka shigo da results d’in tests d’in da aka yi wa Baba!
Suna a haka
aka shigo da Anty Zainab.
Da sauri Ya Jamilu ya mik’e ya k’arasa kusa da matar yana tanbayarta “lafiya?”
Dan su da farko ma basu gane Anty Zainba d’in ba
saboda gaba d’aya fuskarta jini ne.
Tiryan tiryan matar ta koro musu bayani tun daga kan ihunta da ta jiyo da yanda idanuwanta suka gane mata Sadiya da Jalila a kanta suna jibgar ta.
A hankali Shuwa ta mik’e ta k’arasa ta kamo hannun Anty Zainab ta cewa matar “an gode”
Matar tana fita Baaba Talatu ta rarumi mayafinta!
Da sauri Kaka ya mik’e yace
“ina za ki je”
Fashewa ta yi da kuka cikin kukan tace
“Kar ka hanani.
Na rok’eka da girman Allah kar ka hanani ci ma Sadiya yau!
Duk abubuwan da take yi bana magana yau kam ta kaini bango wallahi.”
Kallonta kawai Kaka yake yi kafin cikin b’acin rai yace
“Laifin waye Zainab taje gidanta ta zauna?”
Ta bud’e baki kenan zata yi magana ya d’aga mata hannu yace
“Dan Allah ki barmu mu ji da Usman yanzu!
Shuwa ku wuce ciki ki taimaka mata ta gyara jikinta
ku kyale Sadiya kawai!
Kuna ganin halin da Mijinta yake ciki ai amman wani lokacin sai ta yi kwana biyu ma bata lek’o shi ba!
Ku zuba mata ido ita da y’arta zan samu lokacinsu kwanan nan.”
A hankali Shuwa ta jaa Anty Zainab suka shiga ciki
Baaba Talatu ma tabi bayansu tana sharar kwalla.
Kaka kuma da Ya Jamilu suka koma inda Baba yake zaune yanata faman zubar da hawaye.
Sai da aka had’a da allurai da magungunan bacci tukunna Anty Zainab ta samu ta iya runtsawa a ranar.
Washegari kuwa sai da Shuwa ta yiwa su Khadija da gaske tukunna suka hak’ura amman da cewa suka yi sai sun je sun samu Sadiya da Jalila sai dai a tashi gidan wallahi!
Daman chan ita Khadija basa shiri da Jalila kwata kwata.
Da yamma bayan su Khadija sun wuce, Mama da Shuwa suna zaune suna kallo Baaba Talatu ta shigo. Yanayin ta kad’ai yasa Shuwa ta fahimci abunda ya kawota a hankali ta lumshe idanuwanta ta bud’e sai kuma kawai ta mik’e ta bar wajen.
A hankali Baaba Talatu ta k’arasa inda Mama take ta zauna sannan ta amsa gaisuwar da Maman take yi mata da fara’a, sai da
suka gama gaisawa tukunna ta mik’a mata takardun hannunta da ta shigo da su.
Kallonta Maman tayi kafin ta kalli takardun sai kuma tasa hannu ta karb’a ta fara karantawa.....
Tabbas ta sha wahala a hannun Baba
amman ba k’aramin tausayinsa ta ji ba. A hankali tace
“Allah sarki Ya Usman” wasu hawaye suna zubo mata.
Hannayen ta duka biyu Baaba Talatu ta kamo
kafin tace
“Dan Allah dan Annabi Maryam Ina neman alfarma a wajenki…
Usman bashi da lafiya
dududu sauran mishi bai kai shekara ba!
Ya nemi a maida aurenku
dan yanaso ya mace a matsayin Mijinki..
Na san Usman bai kyauta miki ba!
Na’am ya yi laifi
amman a halin yanzu bashi da maraba da babu.
D’an lokacine wanda ba zai ma kai shekara ba
kawai za ku yi tare.
Dan Allah Maryam.”
Kasa magana Mama tayi
Sai da Baaba Talatu ta sake cewa
“Maryam”
Tukunna ta juyo a hankali tace
“Baaba dan Allah dan Annabi kar ki rok’eki abunda ba zan iya ba!
Ki yi hak’uri amman a gaskiya wannan alfarmar taki ta yi tsauri da yawa.”
Bayan kwana biyu,
Baaba Talatu ta sake dawowa.
Sun dad’e suna magana da Mama…
Haka kurum kamar almara Mama ta samu su Madu tace “ta amince da auren Baba!
Tunda ya rok’i yana neman alfarmar ya mace a matsayin Mijinta to zata yi mishi hakan
a matsayinshi na wanda take kallo kamar d’an uwa”
Ba yadda ba su yi da ita ba amman fur!! Tace
“Ya Usman kamar d’an uwa yake a wajenta
dan haka zaata zauna da shi na shekara d’ayan ba komai.”
Ba dan sunso ba suka amince saboda sun riga sun yi alk’awarin ba za su sake tilastamata ko su sakata tayi abunda bata so ba.
Sai dare Shuwa taje ta sameta,
cikin son fahimtar da ita ta shiga yi mata nuni da yadda Abba yake ta faman zirya….
A hankali Mama ta yi murmushi kafin tace
“Hajiya ni fa dama na gama yanke shawarar ba zan koma gidan Abba ba”
Da mamamki Shuwa take kallonta.
A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“Jin ku kawai nake yi Hajiya,
amman yanzu tashi d’aya in na koma cewa za ai kamar Ina jira matarshi ta mutu ne.
Sanann ko bayaga hakama
na riga na gama deciding in dai ba Mahaifinsa bane ya amince da ni to ba zan tab’a komawa ba, ina so Mahaifinsa ya nema mishi aurena kamar yadda ko wanne uba yake yi wa d’ansa
sannan ya yi welcoming d’ina cikin zuri’arshi, ya karb’eni
a matsayin surukarshi kamar yadda ko wanne uban Miji yake yi wa matar d’ansa...
....na san hakan ba zata tab’a kasancewaba
ni kuma In ba hakan yayi ba to ba zan koma ba!
Kinga kuwa babu batun maida auren mu ni da Abba dan na san Mahaifinsa ba zai tab’a amincewa ba
sannan ba zai yi waennan abubuwan da nake kwad’ayin inga yayi min ba.
Shuwa za tayi magana Mama tayi saurin d’aura hannunta a kan bakinta
ta ce ‘dan Allah ta yi shiru, a bar maganar’
Saboda
ita kanta daurewa kawai take yi.
CONTINUATION!.
Driving Aslam yake yi cikin nutsuwa, har suka isa MT estate ba wanda yace k’ala!
Dan kowa akwai abunda yake tunani…
A cikin gidan Granpa ya yi parking, da sauri driver d’inshi ya k’araso ya bud’e mishi motar ya fito cikin kamala
suka nufi cikin gidan direct.
Ba kowa as usual,
har chan sama suka wuce tare..
A hankali Granpa ya d’an kalleshi ya ce “ka fad’awa su Yusuf Ina buk’atar ganin kowa da kowa anan after isha”
“Okay Granpa” Aslam d’in yace daga nan Granpa ya nufi personal parlourn shi wanda zai sadashi da bedroom d’insa.
Da mugun sauri Aslam wanda yake ta faman kame kame ya na rarraba ido ya fad’a d’akin Gramma.....
A zaune ya tadda su suna hira su biyu.
Da sauri duk suka d’ago suna kallon k’ofar ganin yadda ya afko.
Dariya Gramma ta yi kafin tace
“K’araso mana”
Sannan ta mik’e tace
“Granpa ya dawo ko?
Arshaad yace tare kuka fita”
“Eh yana d’akinsa” ya bata amsa sannan yad’an russuna ya gaida ta cike da ladabi.
Sai da ta k’arasa bakin k’ofar tukunna ta d’ago kansa ta amsa sannan tace
“Sannu da zuwa,
ya hanya?”
A hankali yace “Alhamdulillah”
Yana d’an satar kallon inda Huda take zaune ta sunkuyar da kanta.
Murmushi Gramma tayi sannan ta sa kai ta fice ta ja musu k’ofar dan ta lura idan ta ci gaba da zama a d’akin Aslam na iya zuwa ya rungumo matarshi a gabanta.
A hankali ya ke takawa har ya k’arasa inda take ya tsugunna a gabanta.
Da sauri ta lumshe idanunta ta fara k’ok’arin nemo nutsuwa da lakkar jikinta dan ta gaza samunsu.
A hankali ya kamo hab’arta ya d’ago da fuskarta
yana kallon yadda ta runtse idon da k’arfi!.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “I miss you..
Sosai!!!”
Bata bud’e ba kuma bata yi magana ba,
tana nan a yadda take.
A hankali ya fesar da numfashi yace
“Ko you still need more time?”
Sai a lokacin ta bud’e idanunta da suka d’an tara hawaye tace
“Moree time for?”
Ba tare da ya bari ta jaa numfashi ba yace
“Us!
More time for us..
ranakun da na baki sun yi miki kad’an ko?.
I was so eager to see you
amman ke naga ko murna ma ba ki yi da ganina ba”
A hankali yana kallonta yace “ko arzik’in sannu da zuwa ma ban samu ba.
Ya fad’i hakan yana d’an cika hab’arta sannan ya gyara zaman shi yana fuskantar ta.
Da sauri ta yi k’asa da kanta tana jin yadda k’irjinta yake dukan uku uku.
A hankali ta ji ya ce “Umm??”
Cikin wani kalar yanayi da siga.
Sai da ta sake yin k’asa da kanta tukunna tace
“Ina wuni, ya hanya? Ya aiki?”
Ajiyar zuciya ya fesar kafin yace
“Lafiya,
hanya Alhamdulillah
Aiki kuma, was terrible!
Na d’an samu matsala
har ya kai ga an rufe company d’ina na chan.”
Da sauri ta d’ago ta kalleshi
kafin tace “Subhanallah.
Garin yaya?”
Ya ji dad’in yadda ta damu da alamarin ba kad’an ba. A hankali ya d’anyi murmushi
cikin son kawar da zancen company d’in yace
“Don’t worry,
ba komai.
Ai inada wani ni da Abba..
Daman bawa ya kan samu abu
at any time kuma ya kan rasa,
wannan yana daga cikin k’addarar bawa,
fata kawai shine ya zamo mai yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau”
A hankali ya sa hannu ya kamo nata yace
“wata biyu baya!,
Ubangiji yayi mini kyautar da sai da na suma tsabar farin ciki!
Ya bani abunda na riga na fidda rai da samu,
Amma yanzu ace dan na rasa company sai in damu?”
Yayi mata tambayar yana wani sassanyan murmushi.
A hankali k’irjinta yana wani mahaukacin racing tun da ta fara jin bayaninsa, ta d’ago tana kallonshi.
Har yanzu murmushi yake mata.
Wasu hawaye ne suka zubo mata dan ta so ta fahimci inda ya dosa!
Cikin son fahimtar da shi da kuma kawo k’arshen bagwaren relationship d’in nasu
a hankali tace
“Ya Aslam shike nan yanzu Granpa zai sake cewa ni bad luck ce kenan”
Sai kuma ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara share hawayenta.
Shi da farko ma bai fahimceta ba saboda yadda ya shagala da kallon lips d’inta, sai da
yaga ta fara kuka tukunna yad’an dawo dede sannan ya fahimceta!
Dariya ma shi ta basa
dan haka a hankali yayi y’ar dariya kafin yad’an matse hannunta wanda yake a cikin nashi yace
“In ya fad’i hakan, sai yaya?”
Da sauri ta d’ago tana kallon yadda yake mata wani murmushi mai tsada!
Cikin zubar hawaye tace
“Masoya ma wasu in sun lura zaman su tare zai na causing problem hak’ura suke yi da juna, ballantana kuma mu.
Tun kafin abu yayi nisa
azo tun Granpa yana magana shi kad’ai har kowa ya fara gara kawai mu rabu da juna Ya Aslam ka samu wadda kake so ka aura
nima in........”
Da sauri ya d’aura d’ayan hannunshi akan lips d’inta yace “shhh…”
Bai jira jan lokaci ba
yace
“Ni already na samu wadda nake so
Hudatie
bana jin kuma zan sake son wata a gaba sai dai wani ikon Allahn.
Tunda Allah ya bani ke ya gama mini komai.”
A hankali ya cire hannunsa a lips d’inta ya yi cupping fuskarta a cikin palms d’insa biyu ya d’ago da kan da take ta k’ok’arin b’oyewa
yace “open your eyes”.
Gam!! Haka ta sake runtse idanuwan nata
k’irjinta na dukan uku uku da wani kalar mahaukacin sauri.
Cikin matso da fuskarsa daff da tata ta ji yace
“Open your eyes before i kiss you!”
Da sauri ta ware idanuwan nata tarr! Ta zuba su a cikin nasa…..
Kallonta yake yi itanma shi take kallo ta ji yace
“I love you”
Da sauri ta runtse idanunta sai kuma hawaye sharr! Kamar an bud’e fanfo..
A hankali cikin kuka still yana rik’e da face d’inta tace
“Ya Aslam dan Allah kar ka yi haka. Za aga kamar daman chan muna son juna.
Za a ganmu kamar butulu.
Ba sona kake yi ba,
idan muka rabu ka had’u da true love d’inka zaka fahimci hakan. For now dan Allah let’s just end this relationship............”
Muryartace ta mak’ale sakamokon had’e bakinsu da yayi waje d’aya!….
Wani Irin salo ya shiga aika mata da shi wanda ya kusan tarwatse kwakwalwarta.
Sai da ya ji tana shirin sume masa tukunna ya janye a hankali ya bud’e rinannun idanuwanshi, yana maida numfashi, a hankali yace
“Those this feel fake?”
Fashewa tayi da kuka ta fara k’ok’arin kwace fuskarta amman yak’i bata dama
Instead ma kawai sai ya janyo ta izuwa jikinshi yayi hugging d’inta ya shiga shafa bayanta alamun rarrashi
yayinda zuciyoyinsu suke bugawa a tare da mugun k’arfi......
Jin yanda take kuka sannan ta ma k’i ta saurareshi
yasa ya cikata a hankali yace “ki gayawa su Shuraim
Granpa yana son ganin kowa
after sallar isha.”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice dan yaga kamar tana buk’atar fitar tasa......
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
67
Mikiya Writers Association.
Tunda Baba Bashir ya shiga gida yake ta faman kai kawo,
ba wai tunani yake akan wa Mama zata aura tsakanin Baba da Abba ba
a’a
tunani yake yi ta yadda zai fahimtar da Baaba Talatu
dan already ya gama deciding
tunda dama Mama tace ‘saboda Granpa yasa ba zata koma ba’ Gashi kuma yanzu Granpa d’in ya zo da kansa
to kuwa in sha Allah ba zai yi k’asa a guiwa ba sai yaga an d’aura auren Mama da Abba.
Kawai shi yanzu damuwar shi Baaba Talatu ce dan ko
jiya da kyar tayi bacci!
Halin da Baba yake ciki ya tada mata hankali ba kad’an ba
so take kawai taga farin cikin shi ta ko wacce hanya
tsananin tausayinsa take yi.
Ya dad’e yana nazari kafin ya d’au hanyar d’akin da Baba yake jinya dan yana ganin gara su fara maganar da shi tukunna.
Yana zuwa