Showing 96001 words to 99000 words out of 100703 words

Chapter 33 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4484

juna, kamar ka sace su ka gudu.

Gidan da Arshaad ya siya zasu zauna da Huda nan ya mallakawa Auwal, hatta
lefe da kayan d’akin suma su Daddy duk suka bashi.

Sakina taso biyawa ta ga Huda amman jin yadda Daddy ya damu akan ta huta wai ‘ta hawo jirgi ta yi jigila jigila’ yasa kawai ta hak’ura suka wuce gidan ba dan ranta yaso ba.
A hakan ma kuma Daddyn ya ce “zuwa gobe su je asibiti a tabbatar da komai dai lafiya”

A chan suka tarar da Gwaggo Asabe tana gyaggyara musu gidan ita da wata mai aiki har girki sai da tayi
musu.
Suna gama oyoyo d’insu
ta sulale ta fice ko sallama bata yi musu ba
dan karma su rik’eta
saboda ita tun kwanakin baya da Mommy ta tilastamata zama a wajen su Hudan
ko kwana d’aya bata iya yi ba
ta gudu ta koma gidan Mommy a ranta kuwa ta raya ‘ta gama zama gidan sabbin Amaren nan gaskiya’..........

Aslam, yana tuk’i yana d’an satar kallonta.

Ganin tak’i ta yi shiru yasa ya sauk’e ajiyar zuciya ya yi parking a d’an gefen titi kad’an ya kashe motar ya juyo ya kamo hannunta.

Kamr za fashe da kuka ya ce
“Hudatie, kukan nan ya isa haka dan Allah.
Saboda ke fa na je wai dan ki d’an samu ki shiga mutane
amman ni kam na jima ma rabona da shi.
Da ace na san kuka za ki d’ebo Allah da ba za mu je ba gaskiya.
Ki share hawayenki…
Come here.” Ya fad’a hakan yana mai janyota izuwa jikinshi.

Da kyar ya samu ta d’an yi shiru kafin ya ce
“Ya Aslam matar nan ta bani tausayi..wallahi ba ita ta d’auka ba!
Sannan Yaron ina ganin lokacin da Maman shi ta bawa wannnan maid d’in shi a wani lungu wajen ba kowa time d’in ni kuma na fita yin waya da Sakina ne.”

Da sauri Aslam ya ce “are you sure?”

Cikin tabbatarwa ta d’aga mishi kai alamun ‘eh’.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce
“Tun farko daman maganar sark’ar nan na fahimci makircin mata ne.
Wannan maganar Babyn kuma da kika fad’a min
yanzu ya sake tabbatar min.
Zan je in samu Yash d’in
In fad’a masa sannan In tsaya har sai naga an fitar da ita tun kafin a shiga kotu ma.
Amman wacce iriyar dak’ik’iyar uwa ce zata yiwa d’an da ta haifa a cikinta haka?”

Cikin share hawayenta ta koma gefe ta zauna
ta ce “Nima dai abunda na ce kenan, amman wallah yadda naga ta bawa wannan maid d’in Yaron Allah yasa In ga Annabi.
Sannan jakar MANNUBIYAn a hannuna take!
Ta bani bayan ta d’auki abu a ciki ta ce ‘in rik’e mata bara ta je ta yi chanjin ta dawo’
A gabana ta bud’e ta d’auka abun da zata d’auka, ba komai a cikin jakar sai y’ar k’aramar fasashshiyar wayarta da abunda ta d’auka sai d’ari biyu
wallahi.
Tana dawowa ko tab’a jakar bata yi ba na ajjiye mata akan cinyarta. Kuma ko da ta dawo d’in babu komai a hannunta
haka nan
ta nemi waje ta zauna da jakar a gefenta.
Tana zama wayarta ta d’au ringin ta bud’e ta d’auka….
Tana gama wayar muka ci gaba da hira take ce min ‘Babanta ne
Za’a yi sadakar arbain d’in Mahaifiyarta jibi.’
Daman tun zama na na fahimci tana cikin damuwa, tun farko ita kad’ai a gefe na hango
shiyasanya ma na je na zauna kusa da ita
Ashe dalilin kenan.......”


Cikin jinjina kai Aslam ya ce “shikenan, zan je In samu Yash d’in.
I wonder why ya yi believing da sauri haka har ta kai shi ga yi mata wannan wulak’ancin!
Yanada zurfin tunani ban san me ya shiga kanshi ba…
Anyways zan je in sameshi.
Yanzu ki daina kuka share hawayenki kin ji honey…”

Cikin share hawaye Hudan ta ce “Ta bani tausayi ne sosai wallah, har da kukanta dama tana bani labarin Mahaifiyarta
sai kuma kawai muka ji sanarwa. Ni a ganina lokacin da wajen ya hargitsene aka saka mata sark’ar a cikin jaka
saboda tabbas a k’asa muka hango jakar a jefe
tana d’auka kuma aka k’araso kanta.”

“Hmmm,
makircin mata ne kawai.”
Cewar Aslam yana mai kunna motar.

A hankali Hudan ta ce
“D’an Indiya ne?
Friend d’in naka,
na ji sunansa ‘Yash’.”

Murmushi Aslam ya yi kafin ya ce “sunanshi Yashjub,
Itama MANNUBIYAn baki ji Manu ake ce mata ba.”

Cikin son faranta mata rai da kawar da zancen ya ce
“Good news
sannan surprise….
Bara dai mu je In munje za ki gani......”


Tunda suka shiga gidan suka zauna Aslam ya yi waya ya ce “suna parlour” ta kasa nutsuwa, in banda gyara zama da kalle kalle ba abunda take yi.
Ta so ta gane wasu items a cikin gidan kamar waenda suka zab’a ne ita da Sakina
lokacin bikinta da Arshaad.

Da sauri ta kalli Aslam ta ce “Laaa Ya Aslam
Sakina ce ta dawo ko?”
Dai dai nan suka k’arasa sauk’owa ita da Auwal.

Jikinta ne kawai ya bata tana bayanta
ga kuma Aslam yana kallon wajen yana murmushi.

Da sauri ta juya sai kuma ta mik’e da gudu ta zagaye kujerar ta tafi zata fad’a jikin Sakinar.
Da sauri Auwal ya shiga gaban Sakina tsakaninsu ya tsaya ya ce “a,a,a,a careful!!”
Yana d’an zaro ido da d’aga gira da d’an murmushi akan fuskarshi.

Da sauri Huda ta ce
“Au sorry na manta, Daddy ya Auwal” tana d’an dariya.

Dariyar shima ya yi yad’an matsa ai kuwa da sauri Sakina ta rungumeta ta na share hawayen murnar ganin y’ar uwartata.

Cikin farin ciki da k’aunar juna suka hau gaggaisawa da tambayar bayan rabuwa.

Sun jima suna hira kafin Sakina ta ja Huda suka yi sama.

Auwal kuma ya kira Arshaad suka hau video call su uku!
Ba k’aramin dad’i suka ji ba
da ganin yadda Arshaad d’in ya sake sakewa ya ware sosai kamar komai bai tab’a faruwa ba…..

Suna hawa saman Huda ta fara tab’a cikin Sakina tana murna har da kwallarta…
Nan suka zauna Huda ta fara zab’an sunayen da zxata sakawa Babyn In sakina ta haihu.
Ganin da tayi kamar Sakinar is moody ne yasa ta shiga tambayarta da damuwa akan fuskarta.
A hankali Sakina ta ce
“Ni inata mita mu ba a cikin estate za mu zauna kusa da ku ba, ashe ba ma a garin zamu zauna ba gaba d’aya.”

Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin ta ce
“Ai kin san Ya Auwal shi ke da MT d’in Abuja,
dole kinga a chan za ki zauna kusa da shi mana Sakina.
Za mu dinga zuwa ai
ku ma kuma na san za
ki dinga zuwa
sannan na san maybe ma ya dawo dashi Kano gaba d’aya ko?”

A hankali Sakina ta ce
“Ai cewa yayi wai a chan Cairo zan yi karatu
kuma de!
Ni duk kaina a d’aure yake ban ma san wajen zama d’aya tak’ameme ba, ya ce min dai wai zan ji dad’in karatun sosai.”

Dariya Huda ta yi kafin ta ce “ashe ya yarda kenan..
Ya Aslam ne ya sama mana karatun mu biyu ni da ke,
da yayi mishi maganar da farko sai kamar bai yarda ba
ya ce
‘shi yana Abuja family suna Kano ke d’in idan kika yi masa nesa aganinshi abun zai d’anyi wuya’
Shiyasa Ya Aslam ma ya ce min kar In gaya miki yet ki d’aga mishi hankali tunda bai riga ya amince ba.
Kinga yanzu kuma ashe ya amince…”

Da sauri Sakina ta rungume Huda ta ce
“Na ji dad’i da za
mu yi karatu tare”.
….
Sai da dare ya yi sosai tukunna su Huda suka kama hanyar estate.

Aslam sarai ya lura da Huda,
yadda duk jikinta ya yi sanyi
kuma tabbas ya san damuwarta..
A hankali ya ce
“Hudatie kowa fa da lokacinshi, sannan ai lokacima bai wani ja ba, Manu fa matar Yash Indai zan iya tuna lokacin da ya turo min iv d’in bikinsa tou ina jin yanzu shekararta uku da aure!
Amman har yanzu bata haihu ba kuma kinga kishiyarta ita har ta haihu
Ita kuma tace me?
Ga Mommy itama sai da ta yi shekara kusan...”

Kukan da ta fashe masa da shi ne ya sanya shi sauk’e ajiyar zuciya yad’an kamo hannunta ya ce
“Gaskiya Hudatie zan fara miki bulala! Gaba d’aya kin zama shagwab’abb’iya,
abu kad’an kuka?”

Cikin kukan ta ce “tou Ya Aslam bakaga ita Manu d’in an yi mata kishiya ba?”

“Da sauri Aslam ya ce
“Woow!!
Good idea Huda, kai! Amma Allah ya yi miki albarka, kin kawo shawara kinga
nima sai in k’ara auren kenan!
Bara muga..daman ina son k’asar Egypt dan haka y’ar egypt zan fara aurowa
sai in auri y’ar indiya
sai in je garin Taraba In auro saboda Mommy
sai kuma In tafi Chad in auro
saboda inyiwa Dad shima kara.”

Cikin k’ara sautin kuka Huda ta ce “Ya Aslam ka fa lissafa hud’u kenan, ni kuma
a ina za ka saka ni?”
Tana tambayar tana sake fashewa da kuka.

Cikin dariya k’asa k’asa ya ce
“Au haba??
Ok tou bara in cire y’ar indiya
tunda kema ai kinada gashi sosai Irin nasu”

This time around duka ta fara kai masa……
Cikin tsananin dariya da nishad’in da yake ciki ya ce
“Haba mana
Hudatie Ubangijine fa ya ce
mu yi biyu uku har hud’u indai za mu yi adalci.”
Ya fad’i haka yana Parker motar a harabar gidansu dan har sun iso.

A hankali ya kamo
Hannunta cikin kulawa
ya ce “Kinga ni kuwa ba zan iya yin adalci
tsakaninki da ko wacce mace ba shiyasa na zab’i in zauna da guda d’aya!
Dan nasan muddin na k’ara aure to zan kasance cikin mazan da suke tashi da shanyeyyen b’arin jiki ranar gobe k’iyama.”

Kamar wata wawuya sai kuma ta fara murmushi kad’an kad’an tana kuka.
A hankali ta kwanta a jikinshi yasa hannu ya yi hugging d’inta.

Dariya ya yi kafin ya ce
“Irin wannan zafin kishi haka?
How much do you love me??”
Ya yi mata tambayar yana murza tafin hannunta.


A hankali ya ji ta ce
“Stars da ruwa kansu inda ace za a iya kirga su
tou baza su kai adadin yadda nake k’aunarka ba Ya Aslam..
I love you so much!!!
Till eternity
I’ll always love you...................”


..BAYAN SHEKARU GOMA!..
Abubuwa da dama sun faru..
An samu cigaba k’ari d’aukaka da farin ciki
sannan an samu rashi
na rasuwar Gramma Kaka da K’asimu.

Shekara biyu Mom ta yi a wajen Innaa, da kyar da fad’a da lallashi da shawarwari aka samu Daddy ya amince ta komo amman fa ya k’ara aure!
Dan tana tafiya ko shekara ba a yi ba ya auri wata k’anwar Abokinsa y’ar gayuu Budurwa amman zata kai 35 years
Ana kiranta da ‘Kaulat’.

Tabbas sai da Mom ta yi da gaske tukunna ta yi kokawa da zuciyarta
dan
Kaulat ta fita ta ko wacce hanya Kyau! Ilimi! Aji! Kud’i!
Gata!!
Sannan sai take gani kamar ma Daddyn ya fi son Kaulat d’in a kanta.
Amman kuma da ta yi hak’uri bata yi komai ba
sai abun ya zo mata da sauk’i
dan Kaulat sam babu ruwan ta
a waye take sosai
kowa nata ne
shiyasa ana aurota ma ta siye zuciyar kowa a cikin estate d’in.

Mammy kuwa hukuncin life inprisonment aka yanke mata na kisan Ummi
dan k’iri k’iri Mommy ta kafa ta tsare tak’i yarda a yi shari’ar case d’inta da Mammy.

Mammy ta yi nadama
a gaske a prison…
Sukan je su ganta dan ba a chanjawa tuwo suna she’s still part of the family.
Banda sauk’a da haddar Alqurani, nafila da neman yafiyar Ubangiji ba abunda ta saka a gaba.....


Yanayin karatun su Huda wanda Aslam ya tsara akan za su yi a Cairo hakan bai faru ba
saboda Mama da Daddy cewa suka yi ‘Huda ta yi BUK tunda a kano Aslam yake
Sakina kuma ta yi gwagwalada.’

Mazajen nasu sam! Basu so hakan ba amman ba yadda suka iya haka nan suka amince domin sun san duk abunda babba ya hango Yaro ba zai iya hangowa ba.

Cikin sa a suka fara karatun nasu
Allah ya taimake su ba a samu strike da delay ba ko sau d’aya har suka kammala karatunsu da first class ba tare da sun samu delay ko tangarda ba.
Hudan ta zab’i fannin Paediatric
Sakina kuma Gynecologists.
Suna kammala karatunsu suka tafi course na k’aro Ilimin sani a fannukansu na shekara bibbuyu a UK.

A lokacin both Aslam da Auwal kowa ya bud’e sabbin
company d’insa a chan uk d’in dan haka kusan tare
suka tafi da mazajensu da ‘ya’yan su
har suka kammala!
Sai a wannan lokacin ne kuma Arshaad ya yanke shawarar dawowa gida tare da Amaryarsa mai suna ‘Jahad’ y’ar k’asar Saudi Arabiya
wadda ya aura last year!
Kaff familyn MT babu wanda bai je bikin Arshaad ba har su Ummu, tun a lokacin suka so ya koma gida yak’i
yanzu kuma shi da kanshi ya yanke shawarar komawa gida dan he’s pretty sure baya yiwa Huda zazzafar soyayyar da yake yi mata a baya.

A ranar da suka dawo Huda da Sakina suka tarar da babbar kyauta daga Granpa
wanda ya bud’e musu tangamemen asibiti
mai hawa wajen biyar!
Ya basu ya ce “su zab’i suna su saka”
Da farko sunan Madu suka so su saka amman sai Mama da Ummu suka basu shawarar su saka
‘Mai Turare’

A ranar Granpa ya had’a walimar welcoming Arshaad da Amaryarsa
Bud’ewar Asibitin su Huda
da kuma saka ranar Sumayya da Shuraim
wadda Sumayya ta amince da auren da kyar!
Bawai don bata son Shuraim ba sai dan ita a ganinta bai kamata ta auri age mate d’in ta ba......
......Yau da kanta take so ta je ta d’auko Yaran
saboda tana son zuwa wajen Jalila da su, duk da cikin wajen wata bakwai d’in dake a jikinta hakan bai hanata driving da kanta ba.
Tunda wuri dama ta kira driver ta ce masa ‘kar ya je, da kanta zata je ta kwaso su’.

Tana zuwa tun a bakin gate mai gadin da ya bud’e mata ya ce “ta je da wurwuri office d’in principal yana ta fad’a!
Tun d’azu ake kiran layin office d’insu ita da Maman Arshaad amma duk su biyun basa d’auka.”

Da sauri ta k’arasa office d’in, tana shiga ta sauk’e ajiyar zuciya ta girgiza kanta
a ranta ta ce
“Dama na sani”

Tana k’arasawa ta kamo
kunnen Arshaad ta jaaa da k’arfi ta d’aga shi ya mik’e
cikin fushi ta ce
“yau ma ko?
Wai mai yasa baka jin magana ne?”

Da sauri principal d’in ya ce
“Mrs Aslam
This boy must leave this school gaskiya!
We can’t tolerate him anymore!!
Wallahi saboda share d’in Dad d’insa a makarantar nan ne yasa muka barshi
amman yanzu kam mun gama yanke shawarar sallamarshi.
Zamu fitar wa da Dad d’in nasa share d’insa idan yak’i amincewa.”

Hudan na shirin fara lallab’asa principal d’in ya katseta ta hanyar cewa
“Mun rigafa mun gama magana!
Saboda Allah ko malamai bama bari su daki Yaro saboda iyaye basa so
amman bamu huta da case ba kullum
duk akan Arshaad.
Fad’a da zuciyar shi yayi yawa gaskiya.”

Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e
sannan ta cikawa Arshaad wanda yake ta faman kumbure kumbure kunne
ta mik’awa
Anum key d’in motar ta ce
“Na san ya girmeku
amman kun fishi hankali!
Gashi ke da A’ish
Ku ja Yaran ku je ku jirani a mota gani nan zuwa.”

Har suka fice yana nan a tsaye bai motsa ba dan haka ta daka mishi tsawa ta ce
“Bisu kaima ka je ka jirani!
Saura kuma idan na fito in ji sabon labari”.

Yana fita ta nemi guri ta zauna..
Da kyar da sid’in goshi ta lallab’a principal d’in,
dan zuciyarshi ta zo wuya game da lamarin Muhammad Arshaad....

Wani abun mamakin tana fita ta tarar da wani sabon damben!
Ko ba a fad’a mata ba ta san waye..
Tun kafin ta k’arasa ta hangoshi akan ruwan cikin wani almajiri yanata kimarshi
d’ayan almajirin kuma yana kanshi yana dukan shi amman ko a jikin sa.

Da kyar da taimakon wasu samari aka janyeshi daga kan almajirin da ya danne dan shi d’ayan almajirin yana hangota ya matsa gefe.
Sosai kuwa ya yiwa almajirin jina jina dan dama a fusace ya ke su kuma suka tab’osa.

Sai da ta d’an duddubashi ta ga ba wata matsala tukunna ta basu kud’i ta had’asu da samarin da suka raba damben ta ce ‘su taimaka su kaisu chemist tana da Yara k’ananu a mota’ daga nan ta basu hak’uri ta ce “su bisu su tafi chemist
aje ayi masa dressing.”
Daga nan Arshaad ya shiga motar
ta ja suka wuce
daman su Anum ana fara fad’an suka tura su Abbakar suka hana su fita suka rufe motar ba wanda ya fito a cikin su balle a had’a da shi.

Gidan Jalilan da bata je ba kenan, haka ta kama hanyar estate da su tana mamakin Arshaad, chan wani murmushi ya sub’uce mata
a hankali ta girgiza kanta
a ranta ta ce
“Sai dai ba d’an Sakina da Auwal ba”.

K’ala! Ba ta ce mishi ba.
Driving d’inta kawai take yi dan a mugun takure
take jinta.

Tun da Yaron ya ga an zo gidansu ta lura da yadda yad’an tsorata, aikuwa tana gama parking a compound jikinshi ya fara karkarwa ya ce
“Ummi dan Allah kar ki gayawa Ammi komai.”

Ko kallonshi Huda bata yi ba
ta ce “Ai naga ni ka rainani!
Jiyan nan ka gama yi min alk’awari amman fad’a har biyu yau kad’ai?
Haba Arshaad!”
Shiruu ta yi kamar mai tunanin wani abu kafin ta ce “Ka san wani abu?” Bata jira ya Bata amsa ba ta ce “Na ma daina kiran ka da ‘Arshaad’ daga yau dan baka yi halin mai sunan ka ba wallahi, dan haka chanja
maka suna zan yi
In maidaka mai sunan me gadi! za ka sha mamaki.”

Takaici da zafin zuciya dan har yanzu fushi yake da waenda sukai fad’a yau bai gama hucewa ba
yasa ya fashe da kuka.

Dai dai nan
Auwal Aslam da Arshaad suka shigo compound d’in
suna hira suna raha da dariya…
Arshaad, yad’an yi k’iba kad’an
Auwal kuma ya tara k’asumba da gemu kamu d’aya
Aslam kam ba abunda ya k’ara ba abunda ya rage.

Tun kafin su k’araso Yaron ya tafi wajen Arshaad da gudu ya fad’a jikinshi ya ce
“Uncle kaga wai Ummi za ta maidani mai sunan me gadi!”
Sai da sukayi dariya k’asa k’asa tukunna Arshaad d’in ya d’an b’ata rai ya d’auke shi ya ce “Eh to…
Ni na bata shawara
saboda naga ka cika fad’a sosai.”

Ai kuwa nan ya rikice da kuka.

Dariya kawai Aslam da Auwal suka yi sukai gaba suka barsu.

Sai da Aslam ya k’arasa wajen Huda ya d’an shafa fuskarta da tirtsetsen cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login