Showing 30001 words to 33000 words out of 100703 words

Chapter 11 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4397

gaya mata kenan tun da hakan ne ra’ayi na, bana jin kuma
zai chanja ko da nan da shekaru nawa ne”

A hankali Shuwa tace
“Mai yasa?”

Da tsananin mamaki Mama ta d’ago tana kallonta kafin ta sake yin k’asa da kanta tace
“Hajiya dan girman Allah kar ki biyewa Baaba Talatu wannan karon…har yanzu wasu lokutan ina jin rad’ad’i a k’afata idan abun ya motsa, bayan k’afata har a cikin zuciyata ina jin tsananin rad’ad’in azabar da na sha a hannun Ya Usman.
Dan Allah Hajiya kar kice In koma gidansa”
Ta k’arashe maganar
tana me d’ago kanta ta kalli Shuwan da idanuwanta da suka fara zubar da hawaye.

Ahankali Shuwa tayi wani sassanyan murmushi
sannan ta kamo hannunta duka biyu a cikin nata
ta bata dukkannin attention d’inta tukunna tace
“Gidan Abba fa?”

A zabure Mama take kallonta
saboda bata tab’a yin tunanin jin wannan maganar daga gareta ba.
Kasa magana tayi bakinta ya hau rawa da alamun akwai abunda take son cewa amman ta kasa.

A hankali Shuwa tace
“Maryam, ko ni na kawo taurin zuciya duniya ba zan tab’a bari ki koma gidan Usman ba indai inada rai a doron k’asa”

Wani kuka ne ya tahowa Mama lokaci d’aya ta sakeshi! Tana sauraron Shuwa tana cigaba da magana
“A baya na yi kuskure, idanuwana sun rufe da takaici da kuma bak’in cikin ganin kina y’ata amman kin kasa yi mini biyayya! Wanda hakan ya kaini ga jefa rayuwarki cikin taskun da na kasa taimokonki kuma na kasa ganin hakan
har sai ranar da aka kawo min ke a karye.

Ban san da wannne baki zan baki hak’uri ba Maryam
ban san ta yaya sannan ta ina zan fara baki hak’uri ba dan laifukan da nayi miki sunada yawa…
Ina jin takaicin yadda na kasa fahimta da ganin laifi da badaidan da na ke ta faman aikatawa da wuri ba.
Ki yi hak’uri ki yafewa mahaifiyarki Maryam
dan Allah”

Da sauri Mama ta d’ago tasa hannu ta toshewa Shuwa baki tana kuka bilhakk’i da gaskiya.
Cikin kukan ta hau girgiza mata kai alamun ta daina rok’on ta.
Da kyar ta iya cewa
“Hajiya dan Allah ki daina rok’ona, ke fa Mahaifiyata ce,
tayaya za kiyi ta rok’ona haka.
Laifin in dai kece kikayi min
to na riga na saka a raina na yafe miki tun kafin ma ki aikata laifin.”

Kuka itama Shuwa ta fashe da shi, a hankali tasa hannu ta janyo Mama ta rungume ta suna kuka duk su biyun
gwanin burgewa gwanin ban tausayi.

Muryar Abba Madu wanda basu san da shigowarsa ba suka ji yace
“Ni fa? Za a iya yafe min nima?”

D’agowa suka yi duk su biyun suna kallonsa.
Murmushi yayi ya k’araso inda suke zaune ya zauna akan kujerar shima
A gefen Mama (ya zamana sun sakata a tsakiya shi da Shuwa)
A hankali yasa hannu ya dafa kafad’arta yace
“Za a iya yafewa Abba Madu shima?”

Da sauri ta fad’a jikinsa tana kuka at the same time tana d’aga masa kai alamun ‘eh’.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, wani hawaye mai cike da tarin k’aunar y’arsa da dana sani ya samu nasarar zubo masa ta ido d’aya!
Hannu yasa ya janyo Shuwa wadda itama take nata kukan ya had’asu guri d’aya da Maryam d’in ya rungume…….

Mama, ta manta rabon da taji kwatankwacin wannan farin cikin a rayuwarta
a ranta ta shiga aiyyana..
‘ashe zata ga wannan rana?
Ashe zata sake samun wannan opportunity d’in a rayuwarta?
Allahu akbar!
Ubangiji mai zamani
duniya juyi juyi
mahak’urci mawadaci
Tabbas komai in yayi zafi maganinsa Allah
sannan duk nisa jifa k’asa zai dawo!……’
Kuka take yi tana godewa Ubangiji tana sake godiya…..

A hankali Madu ya shiga lallashinsu yana cewa
“Su yi shiru”
Da kyar ya samu Shuwa tayi shiru saannan ta tayashi lallashin Mama
tukunna itama aka samu tayi shirun.

A hankali tasa hannayenta ta kamo nasu sanann tace
“Abba Hajiya
Dan Allah nima kuyi hak’uri akan yadda na gudu na bi Abba, ku yafe min dan...”

Da sauri Abba Madu ya d’aura yatsanshi akan bakinta yace
“Ba komai Maryam, komai ya wuce, Allah yayi miki albarka.”

Juyawa tayi ta kalli Shuwa,
a hankali tana murmushi
Itama ta d’aga mata kai tace “ya wuce!
Allah yayi miki albarka.
Sannan ina neman alfarma nima a wajen ki, kamar
yadda Ummi ta fad’a
nima In ba gani nayi kin koma gidan Abba ba
to ba zan samu peace of mind ba, Ina so in gyara abunda muka taru ni da dangisa da su Usman muka lalata.
In dai kin yafe min da gaske to inaso ki yi hak’uri ki koma gidan Abba, hakan shine abunda zai sanyani farin ciki
shine abunda nake so da burin gani a rayuwata”

Cikin sheshshek’ar sabon kukan da ya tahowa Maman tace
“Amman Hajiya..”

Da sauri Hajiya Shuwa
tace
“Ba zan miki dole ba, ba zan
tilastaki ba amman inaso ki sani
Hakan shine zai sanyani farin ciki
hakan shine abunda nake so
hakanne zai tabbatar min
na gyara abunda na b’ata
ya kuma taimakamin wajen sanyani in yafewa kaina.
Ki daure, ni Shuwa Ina rok’on ki
ki koma gidan Abba,
na san har yanzu kina k’aunar sa.”

Sunkuyar da kai Mama tayi tana wani gunjin kuka mai d’aci...

A hankali Shuwa ta share hawayenta sannan ta sa hannu ta shafa kumatun Mama kafin ta mik’e ta bar wajen da sauri.

Muryar Madu Maman taji yana cewa
“Kiyi hak’uri ki bi shawarar da duk wani masoyinki yake baki
Abba har yanzu yana k’aunarki
kema kuma na san kina sonshi.
Ki duba kiga
ko kwana biyun nan da suka wuce sai da suka zo nan shi da d’an uwansa akan maganarki
Maryama
a zamanin nan
ba lalle a samu mutumin da zai yiwa wata kwatan kwacin k’aunar da Abba yake yi miki ba.
Kamar yadda Mahaifiyarki tace to haka nima
ba zan yi miki dole ba
amman zan baki shawarar
ki bari ki yarda ki amince a maida aurenku da Abba,
hakan zai bashi nutsuwa da farin ciki na har abada
dan a yadda na ganshi ranar da suka zo na san ba abunda yake so da buri sama da a maida aurenku, nima kuma hakan nake so
Mahaifiyarki itama hakan takeso
Y’arki ma hakan take so
above all
na san kema hakan kikeso
achan k’asan ranki
kawai dai obstacles ne suke son tsaidake ga isa inda zuciyarki take so.”
A hankali ya shafa kanta yace
“Ki yi tunani mai kyau
amman ina so decision d’inki ya kasance abunda kike so ne kuma ki tabbatar zai sanyaki farin ciki har k’arshen rayuwarki.”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice dan lokacin sallah ya gabato….

A hankali Mama take sauk’e ajiyar zuciya, ta dad’e a zaune
sai da ta fara jin kiran sallah tukunna ta mik’e ta wuce d’akinta zuciyarta fal sak’e sak’e…..
Ta san cewa yanzu Abba baya tare da Granpa amman fa duk inda aka je aka dawo uba uba ne, ba a chanjawa tuwo suna kamar yadda take da tabbacin k’iyayyarta a zuciyar Granpa ba zata tab’a chanjuwa ba.....


Haka nan, har
dare Mama jikinta duk yayi sanyi kamar wata mara lafiya
Shuwa da Abba Madu basu sake yi mata maganarba
dan basa so suyi ta pressurizing d’inta..
haka nan suka yi dinner atare cike da da so da k’aunar juna suna hira gwanin ban sha’awa

Wani kalar farin ciki kawai Maama take ji wanda ta dad’e bata yi ba, yana ratsa zuciyarta.
A hankali from time to time take d’an fakar idonsu ta juya ta d’auke kwallar farin cikin da ta k’i daina taruwa a idanunta.

Da daddare tana shirin kwanciya Huda ta kirata,
kamar had’in baki itama maganar Abba ce take so suyi,
bayan sun gaisa ta gama y’an kame kamen ta kafin ta rok’eta
Allah da Annabi ta dawo gidan Mahaifinta.

Cikin son kawar da zancen Mama ta sako wata hirar
ganin da Hudan tayi kamar bata son zancen ne ya sanya bata sake mata maganar ba har sai da suka zo sallama,
nan d’in ma d’an shiru Mama kawai tayi, chan kuka tace mata “ta gaida Ummi da Aslam tayi mishi godiya”
sannan ta katse kiran.
A hankali Hudan ta gyara kwanciyar ta akan gadonta ta kwanta rigingine tana mai kallon sama ...........


AFTER TWO WEEKS.
A zaune Ummi ta shigo ta tarar da Hudan ta rafka uban tagumi.
Murmushi tayi ta k’araso inda take ta zauna kafin ta dafa ta.

A hankali Huda ta d’ago tana kallonta wanda hakan ya sanya Ummin ta fahimci kuka tayi.

Karkatar da kai Ummin tayi kafin tace
“Huda ko nice Aslam fa
ba kawo kud’i ba ko
bikin Sakina za ayi ba zan barki ki je ba, wallahi.
Ke kika jawowa kanki
dan haka kar ki zauna kina wani kuka, ai baki ma yi kuka ba ki jira sai Abban ku ya dawo gobe, na tabbatar in dai yaji labari wallahi da ni da ke kashinmu ya bushe!
Bar ganin yana lallab’a ki in dai yaji wannan zance to fa ba zaku kwasheta da kyau ke da shi ba. Kuma yana zuwa zan gaya masa tunda ni kin raina ni

Da sauri Huda tace “wallahi Ummi ba rainaki nayi ba.”

Cikin katseta Ummi tace
“Raini ne mana Huda!
K’iri k’iri fa kika hanani number Mama saboda kin san in na kirata na fad’a mata
zata yi miki fada kuma dole ki yi abunda bakya so d’in
so bama kya so taji
ballantana har a kai ga tayi miki magana amma
ni Ina kallon ki kina kallona a cikin gidannan yau sati biyu
kina wasar y’ar b’uya da Mijinki kuma ban isa in hana ki ki hanu ba tunda ban Isa da ke ba”

Cikin kuka Huda tace “Allah Ummi kin isa”

Mik’ewa tsaye Ummin tayi kafin tace
“Idan har na isa to
ki tattara kayan ki da kika kwaso da hannunki ki maida
ki gyara d’akin
ki wanke toilet kafin ya dawo.
Wallahi na manta yaushe zan ce na tab’a ganin Aslam yana gyaran d’aki
amman jiya dakanshi har mopping naga yanayi
kuma ba yadda ban yi da shi akan ya bari a gyara ba amma ya k’i yarda saboda ya san nan d’in turakarku ce bai kamata a shiga ba.
Dan maiyasa shi yana mutuntaki amma ke ba zaki kwatanta ba?.
Ki tashi kije ki koma
sannan idan ya dawo ki bashi hak’uri tare da alk’awarin ba zaki sake ba…
In dai har na isa da ke kenan, kamar yadda kika fad’a.”
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga d’akin.


Sai da Hudan taci kukan ta
ta godewa Allah
tukunna ta tashi ta sauk’a k’asan…
Ta yarda zata zauna a d’akin
amman tabbas zata cire tsoro kunya da kawaici su yi agreement ita da Aslam!
Auren su ba na soyayya bane ba Infact k’ok’arin kawo karshenshi ma ya kamata suyi a yanzu so
ba zai yiu ya hautsina mata kwakwalwa da zuciya ba
bayan ba son juna suke yi ba
so gara su san inda suka dosa kowa ya tsaya a iya limit d’insa…….

Tana shiga d’akin k’amshin turarensa ya mata sallama,
a hankali ta shak’a ta lumshe idanunta! A take wata nutsuwa da kasala suka dirar mata
sannan taji zuciyarta tana yin sanyi b’acin ran da take ciki kuma yana d’an raguwa.

Bud’e idanuwanta tayi ta shiga k’arewa d’akin kallo
tana ganin fuskarsa a idonta, murmushi ne ya sub’uce mata da ta tuna irin uwar hararar da ya zabga mata sannan yace
“Ba zaki je ba!” ya juya ya fice.
A hankali tace
“Dama maza ma sun iya harara?”

Tana murmushin tana tunani ta shiga gyara d’akin cikin nutsawa kwarewa da iyawa.
Tana gamawa ta shige toilet ta wankeshi tsaf tsaf.

A wajen Ummi taje ta karb’o kasko da turaren wuta ta saka a d’akin sannan ta shiga kitchen ta had’a masa spring rolls da tea, duk dan a barta ta fita.
Tana gamawa ta fito ta kai dining ta jera a inda taga yana yawan zama.

Tana cikin jerawa Ummi ta sauk’o, dariya tayi kafin tace
“Fad’a na ne?
Ko kuma biyayyar aure?
Ko dai bribe d’in a barki ki fita gobe??”

Turo baki Hudan tayi sannan ta d’anyi murmushi.
A hankali Ummi ta k’araso inda take ta dafa kafad’arta sannan tace
“Na gode Huda.
Kin nunamin nima na isa da ke”
Ta yi maganar tana murmushi.

Murmushi mai had’e da dariya tayi sannan ta fad’a jikinta tayi hugging nata
tace
“Ummina kin isa mana”

A haka su Shuraim suka shigo suka samesu, hakan ba k’aramin burgesu yayi ba kuwa, dan haka Shuraim ya k’araso ya yi joining hug d’in Sudais kuma ya tsaya ya fara bubbuga k’afa shi ala dole sai dai a cika su a yi mishi nashi special…
Cika su Ummi tayi yana ganin haka ya k’araso yayi hugging d’inta.
Ahankali ta zaroshi daga jikinta ta kama hannun Shuraim ta rik’e da nashi a waje guda sannan ta kamo hannun Huda ta saka mata hannayensu a cikin nata
kafin ta fara magana
“Na san ba wani girman su Shuraim kika yi sosai ba
amman dan Allah Huda ko bayan raina
ki zame musu uwa ki yi musu dukkkannin abunda zan yi, ba su da kamarki a duk fad’in duniyar nan.”

Da sauri Huda ta toshe mata baki da hannunta
Idonta ya cicciko da kwalla
tace
“Ummi ki daina dan Allah kar ki d’agamin hankali da yammar nan!
Bana son irin wannan maganar in sha Allah babu inda zaki je ki barmu muna tare...”
Kukan da ya kufce mata ne ya hanata kasa k’arasa maganar tata.
A hankali Shuraim ya yi hugging d’inta sannan ya d’ago idanuwanshi da suka taru da kwalla ya kalli Ummi yace
“Ummi
Ki daina irin wannan maganar please, muna tare happy family together forever in sha Allah”
Ya fad’i hakan yana murmushi.

Murmushi Sudais yayi
sannan yace
“Group hug!”
Ya had’asu duka yayi hugging
yana dariyar
son ganin ya kawar da sad moment d’in.

Suma duk dariyar suka saka suna sharar kwalla.

Sun d’an jima a haka tukunna Shuraim ya jaa kujerar ya zauna yana cewa
“Let me eat small..
Yau haddar pages biyu nayi, tunda muka tashi a English section nake abu d’aya
amman dukda haka sai da Mu’allim ya rankwasheni,
duk cikina ya zuge….”

Tray d’in Aslam ya shiga k’ok’arin janyowa,
nan Ummi ta hanashi ta hanyar buge masa hannu.

Hudan na dariya ta shiga ta d’auko musu nasu wanda ta saka a cooler.
Nan kuwa suka hau ci suna santi dan ana bud’e cooler Sudais ma ya dawo yace “ya fasa tafiya saman”

Dariya kawai suka yi musu daga nan Ummi ta d’an jaa ta
gefe tace
“One last thing
Taje ta yi wanka ta shirya..
Yana zuwa idan ya ga ta yi miishi kwalliya nan da nan zai barta maybe ma ya barta ta kwana, haka ake yiwa maza….tayi sauri maza maza taje ta shirya yana..”

Tun kafin Ummi ta gama magana Huda ta wuce sama d’auko kayanta…kunya
da kuma son aikata abunda Ummin tace ne ya sanya ta kasa tsayawa taji k’arshen maganar.


Kamar yadda ta had’a akwatinta ta hau da shi saman hakanan ta had’oshi harda kayayyakinta waenda ta d’an d’auraye ta shanya, ta kwaso ta sauk’o da su.

Ba iya d’akin ba
Hatta parlourn zuwa yanzu ya d’auki k’amshin turaren wuta.

Tana shiga ta ajjiye akwatin ta fad’a tayi wanka tayi brush ta d’auro alwallar Magrib dan ta gabato, ta fito d’aure da d’an guntun towel
saboda bathrobe d’in da ya had’a ya wanke a washinne machine ya shanya tare da inner wears d’insa har
yanzu bata gama bushewa ba.


Wani had’add’en d’inkin doguwar riga A shape ta fitar,
kalar atamfar royal blue an yi mata d’inki irin mai stones d’innan…

A hankali ta ware bra da pant sannan ta kinkimi akwatin nata ta nufi wardrobe

Bud’ewa tayi ta sa akwatin nata a chan k’asa
sakamokon kayansa da ta gani a jere a side har biyu! A ranta tace
“Wato har wasu kayanma ya sake kwasowa
Ummi tana chan tanata cewa In dawo d’akin bayan shi gashi partyn shi ma yake yi ya samu freedom”
Kamar tana ganinshi haka ta ke kallon kayan tana zabga musu harara…
Idanunta ne suka sauk’a abkan wata takarda kamar poster haka a ta chan k’asan takardar taga an rubuta
‘2021 tournament mathematics competition
Winner
NTIC’

Da k’arfi taji gabanta ya buga!
Da sauri tasa hannu ta zaro sticker……..tun bata kai ga k’arasa zarowa ba ta fahimci ita d’in ce da gaske!

A hankali ta cirota daga k’asan kayan nasa tana kallo tana sake kallon hotonta da sunanta b’aro b’aro a sama ‘Maryam Huda Muhammad’
Ga award d’inta a hannunta da medal d’inta tana murmushi…
Kanta ne ya d’aure ta fara k’ok’arin juya takardar
dan kamar da tana zarowa taga rubutu a bayan da biro.

“Bincike fa babu kyau”
Taji muryarsa a bayanta daff da ita!.

Bata san lokacin da ya shigo ba amman ta d’anji k’amshin turaren da yake tashi ata jikin kayanshi ya k’aru a d’akin.

Kwakwalwar ta already a cunkushe take ga tarin mamaki gashi dama duhu ya d’an farayi bata kunna globe ba tana d’anjin tsoro
hakan ya sanya da taji mutum da murya a bayanta
ta kwala ihun da ita kanta sai da ta d’an tsorota….
Da sauri ya juyo da ita ya sa tafin hannunshi akan bakinta yace “Shiiii.”

Da sauri itama ta sanya dukkanin k’arfinta ta b’intike hannunshi daga bakinta
kafin tace
“Ya Aslam banaso Allah ka daina”
Ta fad’i hakan tana k’ok’arin kare jikinta a rikice
dan ba k’aramin kunyar towel d’in take yi ba.

Dariya ma shi ta basa
Yarinyar da ya gama k’arewa kallo ba tare da ta san ya shigo ba itace take wani kakkare jikinta…
Wani d’an guntun murmushin gefen baki yayi
sannan ya kama towel d’in ta sama yace
“Idan ban daina ba fa?
What will you do?
Yaji za ki sake yi min ki gudu sama , ko me?”
Ya fad’i hakan yana d’an jan towel d’in kad’an kamar zai fisge.

Cikin tsananin tashin hankali ta sake kurma wani ihun a karo na biyu….

Ido cikin cikin suke kallon juna,
so take ta d’auke idanunta a cikin nashi amman ta kasa
sakamokon sak’onnin da yake aika mata daga kwayar idanuwan nasa.

A hankali ya bud’e baki zai yi magana yaji an turo k’ofar d’akin da d’an k’arfi an shigo.....................


5 MINUTES BEFORE NOW.
Ummi, sauk’owarta kenan daga sama zata d’auki abu a kitchen, sam bata san Aslam ya dawo ba.
Tana shiga kitchen d’in taji kamar an shigo
dan haka ta d’au abunda take buk’ata ta fito tana kallon k’ofa…

Sakin lemon hannun nata tayi ya fad’i k’asa cike da mamaki da murna
tace
“Arshaad!!
Sai kuma ta k’arasa da sauri bakin k’ofar inda yake tsaye ta hau dudduba shi tana murmushi fuskarta cike da murna da farin ciki.


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login