Showing 75001 words to 78000 words out of 100703 words

Chapter 26 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4478

Yayartata ta ce “to yanzu wa zai lallashi wani?”

A hankali Huda wadda taga d’an rashin kyautawarta
ta juya ta yi hugging Khadijar
sannan ta kamo hannun Yayar khadijah daga inda take zaune ta ce “ina wuni”

A hankali tana murmushi dan itama yanzu duk ta sauk’o ta ce “Alhamdulillah, gida yayi kyau Huda Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya”

A hankali ta juya cikin d’an tsokana da dauriya ta yayewa Sakina fuskarta, dan har yanzu fuskar tata a rufe take cikin mayafin laffayar da aka nad’a mata.
Da kyar ta iya daurewa batayi kuka ba, fuskar nan tayi dagaje dagaje ta yi jajawur
kana gani ka san ta ci uban kuka bana wasa ba, daman tun shekaran jiya da suke waya take jin yanayin muryarta a dashe.

Cikin son sakata nishad’i
ta ce
“Haba mana Sakina, ki daina
kuka, kinga fuskarki kuwa?
Gashi duk kin yi wani laushi kamar ba ke ba.
Ai ba wai zama za ku yi achan d’in ba har abada, yana warkewa fa za ku dawo in sha Allah…Ni kumafaa daa? da zan tafi chan wani gari ba ke kika yi ta bani kwarin guiwa ba?”
Ta k’arashe a hankali daga nan ta yi shiru ta kasa ci gaba da magana.

Su Khadija ne suka saka baki, suka taru suka yi ta lallab’ata
har sai da ta d’an sake ta bar hawayen ta d’an kwantar da hankalinta tukunna
suka d’an shiga hira a hankali.
Khadijah ce ta ce
“Gaskiya Huda gidan ki ya had’u over!
Kalla kuma kaya koina duk girman gidan.
Bara mu lek’a mu kashe kwarkwatar idonmu”
Ta fad’i haka tana ajjiye mayafinta ta mik’e.
Itama yayartata mik’ewa ta yi.
Hudan har ta mik’e ta d’an fara takawa za ta bisu Khadija ta kamo hannunta ta zaunar da ita ta ce “zauna mai tafiyar ta’ta’taaa mun san hanya”

Duka Huda ta kai mata ta yi saurin gocewa tana dariya
suka nufi k’asa ita da yayar tata.

Banda dukan uku uku ba abunda k’irjin Sakina yake yi
daman tun d’azu ta d’an tsorata da yanayin tafiyar tata da ta gani.

Maganar da Huda ta fara yi mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunani da tsoron data tafi. A hankali ta juyo tana kallonta jin tana cewa
“Ya Arshaad ya sake guduwa..
Ba a san inda yake ba!
D’azu inaji Ya Aslam suna maganar shi da Dad a waya
da na tambayeshi kuma sai ya k’i gaya min komi, kamar ma haushi ya ji.”
Ta k’arashe maganar cikin karyewar zuciya.

A hankali Sakina ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ce
“Hudan
I can’t even begin to imagine what Ya Arshaad is goin through! Dauriya ce kawai yake yi dan haka idan ya ga ba zai iya zama ba ya nuna yanaso zai tafi
ya kamata ku bashi space
ku barshi ya tafin.
Kuma dan Allah ki daina nuna damuwarki over a kan Ya Arshaad a gaban Ya Aslam…Yes! Na san dole abun is somehow amman ki d’an dunga daurewa har Allah ya yaye miki son shi a zuciyarki
ki manta da shi ki rungumi Mijin da Allah ya zab’a miki ku zauna lafiya
dan na san Ya Aslam yana sonki wallahi tun a mansion d’in chan naso In fahimci wani abun
shiru kawai na yi miki.”

Shiruuu, Hudan ta yi kamar tana tunanin wani abu
kafin chan ta ce
“Yauwa Sakina, kin san
wani abun mamaki?
Ashe Ya Aslam ya sanni tun kafin yazo gidanmu shi da Ya Arshaad............”
Nan ta zaiyyane mata labarin da ya bata da
kuma yadda yake nanata mata yana ‘tsananin k’aunarta’
yake kuma gwada mata.
Da zaman da suka yi a chan gidan da komai……

Murmushi kawai Sakina ta yi
kafin ta ce
“Hudan you are lucky, Very lucky!
Ban yiwa Ya Arshaad adalci ba
amman inaso ki rubuta ki ajjiye
ni Sakina na ce
‘Ya Aslam ya fi k’aunarki
Akan Ya Arshaad’
Sannan Huda dan Allah
ki daina pushing d’insa away
ki janyo abunki ku rungumi juna, Allah ya bawa Ya Arshaad shima tashi wadda zai so.
Ki nutsu, ki fahimci karatun soyayyarsu su biyun
duk true love suke yi miki
that I’m sure of
amman ko waye yaji labarinku ya san Ya Aslam ya fi k’aunarki
although Ya Arshaad shima has sacrificed a lot for you sannan shine ya reneki kika zama mutum therefore na san ba lalle ki iya mantawa da halaccinsa ba wanda ni kaina ba zan tab’a mantawa ba
amman Huda soyayyarki da Ya Aslam daban take a cikin labarin soyayya!
Ki nutsu kar ki cuci kanki
dan kema kina son abunki
fahimta ne kawai baki yi ba.”

Hudan na shirin yin magana Aaima ta hawo.

A kan 3 seater da suke zaune ta zauna kafin ta ce
“Anty Huda da Anty Sakina,
kinga na kasa hak’ura sai da na sake biyoki ko?”
Ta fad’i maganar tana kallon Sakina.

Murmushi kawai Sakina ta yi ta kamo hannunta.

“Crying bride”
Aaiman ta ce tana d’an lakatar hancinta, sannan ta d’aura da cewa
“Amarefa sun daina kuka yanzu”

A hankali Sakina ta d’an kwanta a jikinta ta ce
“Thank you Aaima.
A lot!”

Murmushi Aaiman ta yi kafin ta ce “Ba komai Sakina,
Allah yasa mu dace.
Ni dai yanzu matsalata shine wannan kukan da kike yi, ki daina pls, ko kun zo tafiya kar ki sake yin wani kuka
Ya Auwal raina ki zai yi!
Bar ganin bashi da lafiya
Allah idan ya tusoki gaba ko hmm..
Gara ki nuna mishi kema Amaryar zamani ce”

Duk murmushi suka yi kafin Huda ta ce
“Aaima Allah duk ranar da za a kaiiki gidanki idan kika yi kuka
ni kad’ai na san me zan yi miki”

Murmushi ta yi ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce
“Speaking of which..Ina son tambayarku wani abu amman kunyar ku nake ji”
Ta fad’i hakan tana rufe fuskarta da tafukan hannunta.

Dariya duk sukayi dan yadda ta yi d’in dole ka yi dariya.

Cikin dariyar Hudan ta ce
“Mene pls?”

Sai da ta d’an dara itama kafin ta ce “Sakina wanda ya maidaki gida
shekaran jiya wachchar
Brothern ku ne?”

“Woow!!”
Sakina ta ce da d’an k’arfi tana d’an zaro idanu waje kafin ta ce “An gama!
Ai harma na hango ranar d’aurin auren ku.
Kin san shima sai da ya ce min
he felt something..”

Wani ihu Aaima ta yi a hankali sosai irin na jin dad’in nan
kafin ta ce “Shikenan…”
sai kuma ta sunkuyar da kanta ita ala dole ta ji kunya, k’arshe ma tashi ta yi ta tafi bayan ta yi hugging Sakina ta ce mata
“A kula da Ya Auwal plss
Allah ya bar k’auna sai kun dawo”

Tana fita Sakina ta zaro waya zata kira Junaidu
Hudan ta rik’e mata hannu.

Da d’an mamaki ta juya tana kallonta kafin ta ce “mai ya faru?”

A hankali Huda ta ce
“Sakina Aaima bata yi deserving suruka da k’anwar Miji irin Umma da Jalila ba.

Shiruuu Sakina ta yi itama duk sai jikinta ya yi sanyi, a hankali ta ce “Tabbas”

Dede nan su Khadija suka hawo suna haki
Yayar Khadijan ce ta ce
“Hudan wannan tour a gidanki ai aiki ne!”
Sai kuma ta ce
“Na ga d’akin da zan zauna idan na zo yi miki wankan jego
a chan ma muka shantake
Gadon laushi Allah yasa dai idan nazo kar in yi ta bacci dan gadon nan duniya ne.”

Dariya Khadija ta yi kafin ta ce
“Ai kuwa ki shirya dan alamu sun nuna nan da wata tara cif za ki dawo zaman jegon.

Duk dariya suka yi
banda Huda wadda hankalinta ya fara tashi dan ta ga yamma ta fara yi.

Sai da suka huta tukunna suka mik’e suka dudduba saman
chan sama kuwa suka ce basu isa su shiga turakar sabbin maaurata ba
haka kurum su ganewa kansu.

Haka nan
Khadijah ta tisa Hudan a gaba sai shak’iyanci take yi mata
Hudan kuwa kamar ta yi kuka dan ita kad’ai ta san halin da take ciki.

Suna a haka Gwaggo Asabe ta shigo, abun dariya suna had’a ido da Sakina kawai sa Sakinar ta saka kuka….
Dakyar aka lallab’ata aka rarrasheta suka yi sallama da Huda tana kuka itama tana kuka
Gwaggo Asabe da su Khadija suka yi mata rakiya har bakin mota su kuma su Khadijan aka saka driver ya maidasu gida
daman sun yiwa Huda sallama, ta so ta basu ko d’an inner wears ne na sa rana da ake rabawa, ganin a yanda suka tafi yasa ta yanke shawarar kai musu har gida in shaa Allah.

Aslam, ne ya kai su Sakina har airport, ita da Daddy za su yi
tafiyar wanda yaketa janta da hira da barkwanci ba ruwanshi da wani batun surukantaka,
sai da ya ga ta d’an sake tukunna ya ji dad’i…
Haka har jirginsu yayi taking off. Duk dauriyar Sakina sai da idonta ya cicciko sanann ta k’ank’ame kujerar da take kai,
sai da jirginsu ya dedeta ya lula sararin samaniya tukunna ta samu nutsuwa Daddy yana ta tsokanarta.



Washegari da daddare Granpa ya nemi ganin kowa!
A lokacn jikin Huda ya d’an yi sauk’i tafiyar ma ba laifi dan k’afar tata ma da sauk’i
dan haka suka tafi tare ita da Aslam.

A chan suka tarar da kowa.
Suna zuwa Huda jikin Mommy wadda ta fara mik’o mata hannu taje ta fad’a.
Sai da suka gaisa cikin so da tattali tukunna ta mik’e ta nufi inda Aslam yake a gaban Granpa.

“Hmm” kawai Mammmy ta ce
ta yi d’an mitsitsin tsaki sannan ta kauda kai.

Cikin kulawa Granpa ya amsa gaisuwar tata ya na mai tambayarta “ya sabon guri?”

“Alhamdulillah” ta ce ba tare da ta iya d’agowa ba
dan gaba d’ayansu kunyarsu take ji.

Sai da kowa ya zauna tukunna Granpa ya kalli
Dad ya ce masa “Ina Muhammad?”
Cikin tsananin tashin hankali da rashin jin dad’i dan su already sun san case d’in tun 3 days ago shi da su
A hankali Dad d’in ya ce
“Bamu gansa ba since”

Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e, shi kansa bai san ta Ina ma zai fara ba. A hankali ya ce
“Yi musu waya su shigo
za a nemoshi.........”


Mutanen nan da suka zo suka d’auki sample na tomb print d’insu sukayi musu tambayoyi sune suka shigo.
Dukkan su waje suka nema suka zazzauna bayan sun kai wani file gaban Granpa sun ajjiye.

A hankali Granpa ya kalli Dad ya ce “Kirawo Yusuf!
Duk da ya san komai
ya kamata a yi komai da su
har Auwal da Adama”

Computer d’in parlourn ya yi using ya kira Daddy..,,
Mom na gefensa a lokacin suna cin abinci, yana
ganin kiran ya ji gabnsa ya yanke ya fad’i!
Dan haka ya ture abincin
ya d’auka ya ajjiye wayar a gabansu shi da mom.

Bayan y’an gaishe gaishe Granpa ya ce
“Ina Auwal?”

Suka ce “su suna hotel su Auwal kuma suna asibiti”
Kamar zai ce ‘a kirashi shima’ sai kuma kawai ya ce ‘a barsu kawai’
Daga nan ya yi gyaran murya ya fara magana…..
“Last week waennan mutane sunzo sun karb’a tombprint d’in kowa!
Na san ba lalle kun san dalilin d’aukar tombprint d’inba dan haka bara in yi muku bayani.”

A hankali Aslam ya mik’e ya ce “Granpa, please excuse me”
Kana ganin fuskarsa ka san yana cikin tsananin tashin hankali.

Cikin no nonsense face
Granpa ya yi amfani da kakkausar muryar wajen ce masa
“Koma ka zauna!”
Babu alamun wasa a tattare da shi.

A hankali Aslam ya koma ya zauna yana sauk’e ajiyar zuciya a jejjere jijiyoyin kansa duk sun baiyyana…Ya rasa wanne irin taurin kai ne Granpa yake da shi! Shi sam bai yi tunanin wannan maganar za ayi ba da wallahi ba zai zo ba!
Shi a tunanin sa sun riga sun gama kashe case shi da su granpa d’in da su Abba
har abada…….

Muryar Granpa d’in ce ta katseshi jin ya ci gaba da magana yana cewa
“Dalilin da ya sanya aka d’auki tombprint d’inku ba komai bane ba illa…
A lokacin da ake bincike
an yi nasarar samun yatsun mutum biyu da palm
a jikin tukunyar da Huda ta dafa coffee wanda
kamata yayi a samu tombprint d’inta ita kad’ai
tunda hatta Ummi
ta ce bata tab’a tukunyar ba ma
Ita ta zuba mata da kanta.”

Kwarewa Mammy ta yi da k’arfi
wanda duk ya janyo hankalin jama’a kanta.
Da sauri Aaima ta je ta matso ruwa a dispenser ta kai mata
suka shiga shafa mata baya ita da Mommy
tana sha
tukunna
ta d’an dawo dede.

Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin ya ci gaba da cewa
“Bincike yana tafiya
bayan an yi testing tukunyar an tabbatar da poison mai k’arfi ne a ciki sannan har da shinkafar b’era. Sai kuma still
aka samu gidan allura a cikin dustbin d’in kitchen d’in
wanda ba komai ne a cikin wannan allura ba
face poison d’in da aka yi amfani da shi aka zuba a cikin coffe d’in. Tou a jikin syringe d’inma kuma sai aka sake samun wani sabon tombprint d’in wan..........”

Shigowar Arshaad ce ta katse Granpa da kowa na wajen
gaba d’aya sai kallo ya koma kansa.

Shiruu parlourn ya d’auka na y’an mintuna kafin ya ce
“Assalam alaikom, sorry I’m late”
Bai jira jin me za su ce ba ya k’arasa gaban officer d’in kawai ya mik’a mishi hannayensa duka biyu.

Kuka Dad ya saka kawai ya mik’e ya fita.
A hankali Granpa ya sunkuyar da kanshi k’asa
wasu zafafan hawaye suka zubo masa.

Da mamaki Mommy ta mik’e ta k’arasa wajen ta kamo hannun Arshaad cikin zaro ido ta ce
“Arshaad me ye haka ?”

Da kyar ya samu hawaye ya zubo masa a ido d’aya! A hankali yana kallonta ya ce
“Mommy ni ne!
Duk wannan bayanin da Granpa yake yi muku a k’arshe suna na za ku ji a matsayin mai laifi!
Ni na yi poisoning Ummi wanda Aslam naso kashewa tashi d’aya abun ya fad’a kan Ummi
dan haka
dan Allah taron nan ya watse haka, ku daina kwana kwana
kowa ya tafi
officer please arrest me”
Ya k’arashe maganar yana sake juyawa ya mik’awa officern hannuwanshi duka biyu kamar farko.

Mik’ewa kawai officer d’in ya yi ya zaro ankwa.

Ba k’aramin tashin hankali Mommy ta shiga ba
bata san lokacin da ta shiga tsakaninshi da officer d’inba cikin fushi ta cewa officer
“meyene haka yake faruwa?”
Kafin ta juya ga Arshaad ta ce
“Arshaad ba zan bari ka tafi gidan yari ba!”
Ta fad’i haka tana nunashi da yatsanta dede fuskarshi alamun warning
tana hawaye sannan ta ci gaba da cewa
“Ko meye ka aikata ba zan bari ka tafi gidan yari ba wallahi!
Na san ba halin ka baneba
pushing d’inka aka yi
kayi hak’uri ka dawo Arshaad d’in da muka sani”

Cikin kukan ta k’arasa gaban Granpa ta ce
“Granpa Ummi kanta na san ba zata so haka ba!
Dan Allah in domin ita kake yi to ka yafewa Arshaad
ransa ne ya b’aci zuciya ce ta kaishi
ba laifinsa bane ba.”

Gani tayi kawai mutumin yana k’ok’arin sakawa Arshaad wanda ya tsaya kawai yana hawaye ankwar, da sauri ta mik’e ta koma wajen ta fincike ankwar ta yar sannan cikin fad’a ta cewa mutumin
“Wallahi bar ganin aikinka kake yi, na rantse da Allah idan ka saka mishi ankwa sai na tsinka maka mari!”

Runtse ido Arshaad ya yi da k’arfi kafin ya samu ya bud’e ya juyo da Mommy ya ya kama kafad’unta duka biyu ya fara magana cikin d’aci
Idanuwanshi jajawur
“Mommy ba laifi d’aya bane a kaina okay?!
Ko kin kawar da wannan dole zan tafi jail saboda Junaidu ya yi filing complaint a kaina and all evidences are against me so just let it go this is wat i deserve.
Dan Allah.”

K’amewa kawai ta yi tana kallonshi.

A hankali Aslam ya k’araso wajen ya dafa shi ya ce
Arshaad!
Ka juya ka fita a parlourn nan
zan san abun yi please.
Dan Allah ka tafi kawai!
Meye ma ya kawo ka nan in the first place?!”
Ya fad’i hakan cikin d’an d’aga murya.

A hankali Huda wadda ta k’araso wajen yanzu itama tare da Aaima ta ce
“Ya Arshaad me ya had’aka da Ya Junaidu?”

Lumshe idanuwansa ya yi a hankali ya juyo yana kallonta ya ce “Kin tuna sharrin da aka yi masa akan case d’in Chief Justice!?
Sannan akaso a sake d’auke shi bayan an sakeshi?
Those that ring a bell??”

A firgice wani kalan kuka yana taho mata ta ce
“Ya Arshaad dan Allah kar ka ce min kaiine!
Dan Allah Ya Arshaad”

Sai da ya matsa dede setin fuskarta tukunna yana kallon cikin idonta ya ce
“It was all me!”

Wani irin kuka ta fashe da shi
ta durk’ushe a wajen cikin kukan ta ce
“How??
Why???”

Ranshi a tsananin b’ace ya ce
Why?
Tambayata ma kike yi ‘why’!?
Bara ki ji dalili
‘It was all because of you’
And bari ki ji abunda ya faru…
Naga take taken Junaidu
At that very day
kuma kema naga kamar kina k’aunar sa, nuna miki ne ban yi ba amman
hankalina a matuk’ar tashe na bar wajen ki. Na biya ta wajen friend d’ina Jamil! Sai na samu suna tattaunawa akan wata magana…Yanayi na yasa ya tambayeni dan haka ban b’oye mishi komai ba
na fad’a mishi damuwa ta.
Ya san ki ya san yadda nake sonki shiyasa ya ce ‘in bashi number da information d’in Junaidun kawai’.

Abun ya zo mana da sauk’i saboda already best friend d’in Junaidun Yaron Abokin nawa ne Jamil.
A time d’in ban san me za su yi ba kawai ni dai nace ‘a san yadda za a yi min da Junaidu’
Sai da aka kashe mutumin tukunna na fahimci me sukayi.”
Cikin d’aci ya ce
“Kinsan wani abu?”
Be jira jin me zata ce ba ya ce
“Ban damu ba!
Kwata kwata ban damu da kisan kan da aka yi ba saboda
Idanuwana sun rufe
I was just selfish and bad!
And happy tunda Junaidu ya b’ace kenan babu abunda zai sake shiga tsakaninmu ko ya yi
yunk’urin raba mu.
Ban damu da yadda ya sha wahala a Prision ba
bayan an sake shi na sa a d’auko mini shi.”
Yana kallonta ya sake cewa
“Kinsan wani abu?”
Nan ma be jira amsa ba ya d’aura da cewa
“Ko da aka ce motar su ta kama da wuta
Hudan ban ji haushi ba ban ji babu dad’i ba
ban kuma fad’awa kowa na san wani abu ba!
Na take komai
na rufe idona duk dan inga na mallakeki!
I was bad!
Ban yi deserving freedom ba so pls dan Allah ku bari kawai su tafi da ni.”

Cikin fushi Aslam ya ce
“Ba za a bari ba!
Da kasa aka kama Junaidun ai kuma still kai kasa aka dinga bashi shelter da abinci mai kyau
Kaga hakan yana nuni da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login