Showing 99001 words to 100703 words out of 100703 words
Chapter 34 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt
ta tukun ya ce “Baki je wajen Jalilan ba kenan”
Sai da tad’an kalli Arshaad da takwaranshi tukunna ta ce
Abhu,
Gaskiya ya kamata yau a saka Yaron nan a gaba a yi mishi fad’a sosai wallahi,
saboda shi na dawo, dambe har da almajirai a waje sabida Allah.”
A hankali Auwal wanda ya d’auka mai sunan Dad ya ce
“Mu je ciki yau inga har duka sai ya sha”
Ya fad’i hakan yana mai wucewa ciki.
Dariya Aslam ya yi ya ce
“Kiga yadda yake wani had’e rai kamar ba a wajen shi ya gado ba”
“Um um fa!
Yarintar shi kad’ai ka gani
baka san na mamansa ba”
Hudan ta bashi amsa.
Murmushi duk suka yi Huda ta wuce
shi kuma ya juya wajen su A’ish
waenda suka gama kwasar lunch box da jakankunan su.
Murmushi ya yi ya d’aga A’ish sama ya ce
“Mamana ya school ke ba kya fad’a ai ko?”
Sai kuma da sauri ya sauk’eta ya d’auki Anum yana cewa “sorry kakata
yi hak’uri na manta na yi alk’awarin yau ke zan fara kulawa.”
Da d’an k’arfi Huda ta ce
Kar ki yarda ya yi miki dad’in baki”
Tana mai wucewa
bayan ta kamo hannun Abbakar k’anin su Arshaad wanda yake a kindergarten suka shige ciki…
Sakina taso ta yi mishi shegen duka bayan ta gama jin bayanin abunda ya yi yau
dan ta zo wuya da halinshi
amman sai Aslam ya jata gefe ya yi mata Nasiha..
Nutsatsen fad’a sosai suka taru suka yi mishi
dan har Jihad Arshaad ya kira ta zo itama saboda Yaron yad’an shak’u da ita itama dan
tun yana zuwa hutu wajen Arshaad a Uk suke video call da ita, lokacin da su Sakina suka tafi course d’insu kuma
a gidansa ma ya zauna gaba d’aya ko da yayi aurenma tare suke har lokacin da suka dawo Nigeria tukun ya gudu gidan su Huda
dan sam baya san zama waje d’aya da Ammi
saboda ya san zai yi laifi itakuma zata dake shi ta yi fushi da shi
duk da yanayin rigimarshi
amman yana tsananin k’aunar iyayenshi shiyasa
baya son yaga tana fushi da shi. Sannan baya son fad’a da duka.
Haka nan suka had’u su shidda!
Da turanci da Hausa da larabci duk aka yi mishi fad’an.
Kuma da alamu fad’an ya shige shi sosai.
Tun daga ranar an d’an samu ya nutsu
amman ba a yi cikakken wata d’aya ba ya koma ruwa
dan haka kawai suka bishi da addua.....
Sai da bikin su Shuraim da Sumayya ya rage saura sati tukunna Aaima suka zo
dan a Abuja itama take tun aurenta. Ya’yanta uku biyu maza Farouk da Bashir sai auta Aisha.
Tun aurensu har kawo yanzu cikin kwanciyar hankali suke
sai dai y’ar rigimar Mata da Miji wanda wannan normal ne a ko wanne aure.
....
Sai da Ya Ja’afar ya yi shekara biyar tukunna aka samu ya dawo dai dai, idan ka ganshi yanzu ya nutsu sosai kamar ba shi ba.
Yana fitowa Junaidu ya bashi jari aka nema mishi mata ya yi aure shima y’ar bazawarar da Baba ya aura y’ar garin Katsina dutsanma bafulatana.
Umma har yau tana nan jiya i yau! A nan gidan Baba da Junaidu ya rushe ya sayi filin bayansu ya had’e ya yi musu ginin zamani take itama
amman b’angarenta daban
ita da masu aikin da Junaidu ya d’auko suke kula da ita.
Wani lokacin Huda idan ta je dubata har kuka take yi
saboda Umma ta zama abun tausayi. Duk k’asar da take ji da kwararrun likitoci Junaidu sai da ya kaita…an yi maganin Hausa da turanci amman har yau babu ci gaba
sai ma abun da ya k’aru
dan wasu lokutan har duka take yi.
Anty Zainab itama bata koma gidan Mijinta ba!
Ganin tana zaune haka ba wanda ya fito mata yasa itama Junaidun ya bata nata jarin
suke zaune ita da Baaba Talatu a gidan Kaka wanda nan ma ya gyara musu sosai.
Idan ka ga Jalila ba zaka ce ta tab’a yin rashin ji ba!
Ta nutsu sosai. Bayan aurenta sai da ta yi sauk’a yanzu haka a islamiyyar da Mijinta ya bud’e take koyarwa.
Ta rungumi Mama a matsayin Uwa
Sakina da Huda da Sumayya kuma a matsayin y’an uwa
sannan ta rik’e Mijinta wanda ta fahimci shine gatanta kuma shine masoyinta na gaskiya.
Tabbas Jalila tana cikin matan da za ace sun yi sa’ar samun Miji mai tsananin k’auna da tausayinsu tsakani da Allah.
Wani lokacin har ce mishi take yi ‘ya k’ara aure’ saboda duba da a yanda ya sameta ita!
Amman duk sanda ta yi mishi wannan zancen sai taga fushinshi
a cewarshi ‘shi ita yake so ba wani abun ba kuma
ya tabbatar ba zai tab’a iya had’ata da wata y’a mace a zuciyarshi ba.’
Ibraheem irin mazan nan ne masu zuciya
Mahaifiyarsa ta rasu itama two years back k’anwarsa ma ta dad’e da yin aure.
Dukda Ubangiji ya rubuta mishi rayuwar middle class zai yi
hakan bai hanashi siya mata y’ar k’aramar mota ta mata ba!
Sannan ya tashi daga gidan Junaidu ya yi gidansa
Ita ma kuma tana business d’in kaya daga India Dubai wanda Junaidu ne yake kawomata duk zuwanshi, itanma kuma ta tab’a zuwa sau d’aya da kanta ta je ta sari kayan ta dawo
bayan Hajji da Umara da Junaidun ya biya musu suka je ita da Mijinta tun farko farkon aurensu.
Ya’yan ta biyu mace da Namiji,
ta farkon sunanta Maryam mai sunan Huda tana ce mata didi
na biyun kuma
mai sunan Kaka, Bashir.
Sai kuma tsohon cikin jikinta maybe su haihu tare da Huda ko kuma Huda ta rigata.
Tsakaninta da Aaima akwai zaman lafiya da friendship da mutantanta juna ga zumunci......
Tunda aka fara bikin su Sumayya Hudan take nak’uda sama sama..
Sanin da ta yi lokacin haihuwar ta bai yi ba yasa kawai ta yi shiru a tunaninta juyi ne!
Sai dai ranar da za a kawo Amarya jikinta ya motsa sosai!
Dama Sakina ta fahimceta tun jiya dan haka ta yi rushing nata zuwa asibiti
ba tare da ta gayawa Aslam ba
dan ya ce ‘ba a nan yake so ta haihu ba, tunnda haihuwa ta uku tana zuwa da complications gara ya fita da ita waje’. Kuma ta san in dai ya ji Huda tana nak’uda ne amman ta yi shiru to zai ji haushi sosai.
Tun kafin su k’arasa asibitin faya ta fashe, ko minti talatin baayi da shigar da itaba ta haifo y’ay’anta biyu kyawawa maza masu kama da Aslam sak.....
Sai after one week tukunna Granpa ya had’a walima iya family kawai na welcoming Sumayya da twins waenda suka ci sunan Arshaad da Auwal
(Abhi da dada).
Takanas Granpa ya aikawa su Shuwa nasu invitation d’in.
A compound d’in tsakar gidanshi aka yi decoration
manya manyan dining table masu seat 20 guda biyu aka k’awata
D’aya na manya d’ayan kuma na Yara jikokin gidan.
Wajen 5:00pm kowa ya hallara,
tun rasuwar Kaka Granpa ya zama shine Abokin Madu,
shiri suke yi sosai….Allah ya arawa Granpa tsahon rai tubarkallah, sai dai fa ya tsufa sosai dan baya ma iya takawa a kan wheelchair yake.
Haka aka fara gabatar da walimar bayan Madu ya bud’e taro da addua.
In ka gansu kowa cikin farin ciki da walwala da annashuwa
Mama na zaune kusa da Abba
Mom da Anty Kaulat sun saka Daddy a tsakiya
Mommy a kusa da Dad
Hudan kusa da Aslam sun d’au twins d’insu a hannu
Arshaad da Jihad
Sakina da Auwal Aaima da Junaidu
sai Jalila da Mijinta.
D’ayan dinning d’in kuma Yaran ne tun daga kan Arshaad har kan Abbakar Saddik.
Ana gama cin abincin Granpa ya yi gyaran murya
ya ce
“Hudan Maryam Aisha inaso in sake baku hak’uri”
Da sauri Madu ya ce
“Dan Allah ka yi shiru.
Yanzu haka kana ganin akwai grudges?
Komai ya wuce,
mu yafi juna
Allah ya yafe maana.”
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana kallonsu Mama one by one…
Cikin had’in baki Mama da Mommy suka ce
“Granpa iyaye basa laifi a wajen y’ay’ansu,
komai ya wuce.”
A hankali Huda itama ta ce
“Mune za mu nemi yafiya da albarkar ka. Komai ya wuce
ka manta komai kamar bai faru ba! Ka sanya mana albarka dan mu samu haske a rayuwarmu.”
Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e
sannan ya russunar da kanshi k’arasa
yana jin yadda hawaye suka fara taruwa a tsofaffin idanuwanshi da suka ga jiya suka ga yau.
Cikin zolaya Madu ya ce
“Stop being emotional mana old man!”
Da sauri Granpa ya d’ago ya ce
“Ai ka fini tsufa!”
Dariya aka saka saboda ansan dama sun saba, duk cikin su
biyun ba wanda yake so d’an uwanshi ya ce mishi tsoho!
Watarana ma Granpa cewa yake yi Madu ya girmeshi kuma ya tubure!
Dole a hak’ura a tafi akan an yarda Madun ya girmeshi…….
A hankali Huda da Mama suke kallon family d’in nasu..
Tun daga kan tebur d’in su har na su Arshaad
kowa kawai dariya da farin ciki yake yi.
A tare Mama da Huda suka share kwallar farin cikin da ta zubo musu
ba tare da kowa ya gani ba
sannan a tare a hankali suka ce
“ALHAMDULILLAH!”.
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!…
Na godewa Allah da ya bani ikon kammala littafina mai suna ‘So da Buri’.
Kuskuren da na yi a ciki Allah Ubangiji ka yafemin, darussan da suke a ciki kuma Ubangiji kasa mu amfana.
*Godiya ta musamman tare da fatan alkhairi ga
Anty Aisha Gadanya, Ina godiya kwarai Anty, alkhairin Allah ya Isar miki a duk inda kike*
*jinjina tare da godiya ta musamman ga y’an group d’in
So da Buri da H B’s palace masoyana bani da bakin gode muku sai dai Addu'a wallahi, na gode na gode sosai Allah bar zuminci ya kuma kare min ku kullum da koda yaushe na gode sosai*
*Godiya tare da fatan alkahairi ga duk wani member na Mikiya Writers Association, Ina godiya kwarai sisters Allah ya barmu tare ya ci gaba da kare min ku*
Taku har kullum
Humaira Bulama.
............