Showing 78001 words to 81000 words out of 100703 words

Chapter 27 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4372

still akwai good in you Arshaad
you felt guilty which is good.”

A hankali ya juyo ya kalleshi kafin ya ce
“For your information nine na janyo aka rufe maka company d’in takalman ka!
Is there any good in me left?”
Ya fad’i hakan yana kafeshi da dogayen idanuwanshi.

A hankali ya ji Aslam d’in ya ce
“I know Arshaad
na san komai!
Tun kafin In tafi a time d’in da aka kirani na fahimci kai ne
So
dan Allah maganar nan ya wuce
please”.

Cikin katseshi ya ce
“Na so In kashe ka!
Ka bar duniya
gaba d’aya
In auri matarka!
Is there any good in me?
Still kana da hope a kaina ........”

“Ina za ki je?”
D’in da Granpa ya ce ne yasa gaba d’ayansu suka juya suna kallon k’ofar da Mammy ta nufa sad’af sad’af zata fice.

A hankali Mom wadda tun d’azu take magana ba a jinta tace
“I have something to say”
Da d’an k’arfi.

Duk juyawa akayi aka zubawa screen d’in ido, suna kallonta
Idonta sharkaf da hawaye ta ce “Arshaad baka so kashe Aslam ba!
Ka dai yi yunk’urin yin hakan
amman kuma baka aikata ba
saboda baka so ba....……
A ranar birthday d’in su Shuraim!
Bayan Dad ya gama yi mana fad’a akan Sakina da abubuwan da muke yi..I was furious!
Sannan burin da na d’aura akan Auwal ya mallaki MT duk sai naga yana shirin tab’arb’arewa tunda na lura shi soyayya ce a gabanshi a yanzu!
Hankalina bai sake tashi ba
sai da Mammy ta sanar min da cewar ta ga copies d’in takardun MT da Granpa ya mallakawa Aslam a d’akin ka
a ranar
Lokacin da ta shiga
kai kuma ka fita ka barta a d’akin, wanda bamu san ma an mallakawa Aslam d’inba
kuma bamu san ya aka yi kai ka sani ba.

A take take ce min
‘Komai ya zo mana k’arshe ni da ita!
Amman ta samo mana solution
dan daman tun da taji labarin kyautar gidan da Granpa ya yiwa Aslam ta gama cire hope akan MT a Yaranmu muddin Aslam yana raye!..
Dan haka yanzu it’s either I’m with her
ko kuma I’m doomed’.

Sai da muka keb’e mu biyu tukun ta yi min bayanin
abunda za a yi shine…
‘Ga shinkafar b’era nan daman ita da shirin ta ta zo
gara kawai a yita ta k’are!’.

Dukda
a lokacin i was furious
amman ban yi amanna da shirin nata ba, sai da ta yi mini
cikakken bayani kuma na lura komai ya kusan zuwa mana k’arshe tukunna na yarda but still sai na ce mata ‘Gara mu zuba iyaka wadda zata la’antashi ko ta sakashi doguwar jinya
dan ni gaskiya ba zan iya kashe Aslam ba’.

D’ari bisa d’ari ta nuna min ta yarda, ban tashi sanin Mammy yaudarata ta yi ba
sai da na ga gawar Ummi a kan cinyata”.
Ta fad’i hakan tana fashewa da kuka.

Da sauri Mammy ta k’araso wajen ta ce “bana son munafurci!
Munafuka ai da ke aka yi....”
Wata mahaukaciyar tsawa Dad ya daka mata
ya ce
“wallahi idan kika sake yin magana sai na kasheki da hannuna kafin a tafi da ke gidan yari!”

In a serious tone Granpa shima ya ce mata
“Ki nutsu!
Ko In saka a fasa miki kai da bindiga”
Sannan ya juya ya cewa Mom
“Continue”

Cikin kuka Mom ta ci gaba da magana
“Muna tunanin ta yadda za mu shiga d’akin su Aslam mu zuba a lemon cikin fridge d’in da yake a d’akin nasu
ko mu zuba a ruwa ya sha
sai Allah ya kawo sauk’i
muka ji ya cewa Huda “ta had’a mishi coffe”

Hudan na shigewa kitchen aka fara watsewa, muma muka fita
Mammy ta cewa Dad ‘zata tafi tare da k’awarta ta ajjiyeta a bakin gate yanzu’. A gaban sa ta shiga motar kawar tata, motarsu shi da
Aisha tana fita ta fito ta yiwa k’awartata sallama muka zagaya baya ta ce min
‘in tsaya a nan baya in tabbatar babu wanda ya ganta
In yi keeping mata watch daga nan ita kuma zata shiga ta aiki Huda ko kuma dai ta d’an ja hankalinta ta watsa gudun kar idan zance ya fito Huda ta ce ita ce ta aiketa’.

Har zata juya na rik’o hannunta na ce mata ‘ta zuba d’an mitsitsi kawai dan Allah’
A gabana ta nuna min d’an k’aramin da zata zuba
wanda na tabbar ko b’era ba lallae ya iya kashewa ba!
Na so ta bani ragowar amman sai ta ce ‘ko dai ban yarda da ita bane ba?’
Shiyasa kawai na yi trusting d’inta na barta ta wuce.

Kafin Mammy ta zagaya
ina zuwa bakin k’ofar kitchen d’in ta baya sai na ga
Hudan ta fita!
Ina shirin kiran Mammy a waya naga an shigo..
Wallahi Arshaad fuskarka da jikin ka a rufe suke ko’ina
amman tashi d’aya na gane ka.

A tunanina bakin ku d’aya kaida Mammmy sai da na ga
ka zaro allurar da bata cikin tsarin mu tukunna gabana ya fara fad’uwa.

Ba k’aramin sanyi na ji ba da naga har ka bud’e allurar zaka zuba kuma sai naga ka yi tsaki ka rufe ka mayar ka ajjiye
alamun ka fasa”.

A take gaba d’aya kowa a falon aka ce
“Alhamdulillah”

Cikin kuka ta ce
“Garin lek’en ka da nake ta yi yasa har ka gannni
ka fito ba tare da ka d’auke allurar ba.
A cikin filawowi na b’uya kana wucewa na zagaya
ta k’ofar parlour
zan shiga kitchen d’in
tun a bakin main door na parlourn na hango Huda
tana shirin shiga kithchen d’in
amman ban hango Mammy a kitchen d’inba
wadda na tabbatar ita ce ta had’a da allurar da ba lalle ta gama sanin ta mecece ba ma da shinkafar b’erar ta matse gaba d’aya a cikin coffee d’in wanda sanadiyyar hakan ne na rasa y’ar uwa ta d’aya tilo
a duniya.

Da sauri na fita na zagaya baya. Ina zuwa bayan kitchen d’in na ga Mammy a wajen tanata gumi, ta ce min ‘ta zuba amma fa saura kad’an Huda ta kamata’.
Jin kamar tahowar mutum ta bayan mu ne
ya sanya kawai muka yi sauri muka bi ta gaba muka bar wajen. Na saka driver ya mik’a Mammy estate
ni kuma na koma part d’ina.”
Cikin kuka ta ce
“Arshaad ba kai za a kama ba
Mu za a kama…baka da laifin komai”.

Da sauri Mammy ta ce
“Ke dai za a kama munafuka!!
K’arya take yi min, duk abunda ta fad’a k’arya ne wallahi.”

A hankali Arshaad ya lumshe idanuwanshi wasu zafafan hawaye suna zubo masa.

Mom bata damu ba ta ce
“Another things…
Although ban san waye ya turo Mommy daga bene ba but Mammy nake zargi dan na ji tana waya rannan kamar da malaminta ne tana cewa ‘a sake toshe mata baki a goge mata tunani kar ta tona mata asiri kafin ta san abun yi next da ita’ da kuma na tambayeta sai ta k’i gaya min komai dan haka bani da tabbas
amman tabbas na san wanenen musabbabin ciwon nata tun farko
Mammmy ce ta yi mata asiri!
Har wajen bokan da yayi aikin idan kuna so zan kaiku.
Shiyasa tun a cell Mommy tana warkewa mu bama ma saniba
Ita kuma Mammy ta fara mugayen mafarkai
Inaga sauk’ar da akeyi a gidan nan kullum ne ya sanya
abun bai koma kanta ba
ta samu mafarkan suka barta.”

A hankali Aslam ya ce
“Ita ta turo ta daga bene”
Kafin ya kalli Mommy ya ce
“Mommy ranar da naje zan ce miki Ina son tafiya Uk
ana i jibi auren su Arshaad…
Pretending kawai na yi dan ban san ta Ina zan fara ba
sannan naji kin ce peace da kwanciyar hankali kawai kike buk’ata a yanzu
Amman tabbas na ji conversation d’inku ke da Dad.”

Mom ce ta sake cewa
“Sannan mammy.....”

Da sauri Mommy ta k’arasa gaban screen d’in ta had’e hannuwanta biyu ta ce
“Dan Allah dan Annabi Adama ki yi shiru”
Sai kuma ta fashe da wani sabon kuka.

A hankali Granpa ya ce “kowa ya zauna”

Ba ayi minti uku ba duk suka zazzauna har Arshaad da Granpa ya sake ce mishi
“Muhammad zauna kaima”

Da kyar Granpa ya samu ya ci gaba da magana….
“daZa mu yi amfani da tombprint mu hukunta mai laifi…
Second hannun da ya fito a jikin tukunya apart from na Huda hannun Rukayya ne!
Sannan ya sake fitowa a jikin syrinji tare da na Arshaad
wanda na tabbatar kafin ya saka safar da Adama ta fad’a ne ya yi mistake ya rik’e
dan bai fito a jikin tukunya ko murfin ta ba.
Ya fahimci hakan inaga
tun a ranar da aka d’auka samples d’in shiyasa ya yanke shawarar ya gudu!
Ban kuma san me ya dawo da shi ba dan haka yanzu inaso ka fad’i gaskiya da gaskiya tun da an san komai
kuma muma mun fahimci komai.
Kaga waennan manyan y’an sanda da ss ne
kar ka cuci kanka
ka yi bayanin da zasu d’auki rahoto dan na yi alk’awari sai na hukunta duk wani mai hannu a kisan Ummi!.
Shin maganar da Adama ta fad’a gaskiya ce?”

A hankali Arshaad ya girgiza kanshi kafin ya ce
“Ba haka bane ba!
Ni ne na zuba!
Ni na yi hacking wayar Sakina na kira Huda waje tana fita ni kuma na je na zuba!
Dama inada wannan plan d’in a raina tun dawowata saboda na fahimci Aslam yana son auren shima.
Granpa na rok’eka da girman Allah ka barsu su tafi da ni.”

Tsabar takaici Aslam bai san lokacin da ya shak’o sa ba ya ce
“Meyene ribar ka Idan an tafi da kai?
Me za ka ji a jail!?
Arshaad ka san inane jail kuwa?”

Sai yanzu Gramma wadda tunda aka fara case d’in ta sunkuyar da kanta tana salati
ta samu ta fashe da kuka…
A hankali ta d’ago kanta ta taso ta iso inda suke
ta kama Arshaad ta mik’ar da shi tana kuka ta ce
“Aslam ka manta waye Arshaad ne?
Tun kuna Yara
Idan ya yiwa mutum laifi b’uya fa yake yi ko da ace mutumin ya yafe masa sai yayi kusan wata yana wasan y’ar b’uya da shi. Ka san Arshaad yana da kunya yana da kawaici kuma yana k’aunarka!
Na tabbatar laifin da ya aikata ne ya saka shi yake jin ba lalle a yafe mishi ba sanann shi kanshi ba zai iya fuskantar kowa ba shiyasa ya gwammaci zaman jail a kan zama da mu
sannan kuma ka tuna Arshaad
yana iya sacrificing komai saboda Mahaifiyarsa
unlike her! I’m pretty sure ita yake ta k’ok’arin rufawaa asiri
wanda hakan ya had’u da
Guilt shiyasa yake k’ok’arin tura kanshi jail!
Haka ne ko ba haka ba! Arshaad?”
Gramma ta k’arashe maganar tana sake fashewa da wani sabon kukan.

Gaba d’aya kuka suka saka
Aiima Huda Dad Sudais Shuraim Mammy Daddy Mommy hatta Granpa da Abba wanda yake chan a zaune ya kasa motsi
kowa kawai hawaye yake yi.

Hannuwan Gramma ya rik’e gamm! A cikin nasa ya ce
“Gramma dole Ina da laifi one way or the other..
Ga Junaidu sannan ga successful company d’in da na tarwatsa na lalatawa Aslam…
Na biyewa son zuciya Gramma!
Na biyewa
So da buri, ki kyaleni dan Allah ki rabu da ni
I need time alone away from all of you!
Besides Ina jin tsoron kaina
a duk lokacin da na ga Huda da Aslam na kan ji tsananin kishi!
Ba zan iya ba!
This is torture!
Ni kad’ai na san abunda nake going through”
Ya k’arashe maganar yana fashewa da kuka.

Wanann karon hatta Abba kuka ya saka.

Da sauri Huda ta mik’e ta fita da sauri
Aaima kuma ta bi bayanta.

Bata tashi sanin Aaiima na bayan nata ba sai da suka shiga cikin parlourn gidanta.
Jin mutum a bayanta yasa ta juyo suna had’a ido kawai sai suka fashe da kuka a tare gaba d’ayansu….
Da kyar Huda ta iya d’akko wayarta ta kira Junaidu yana d’auka ta ce
“Dan girman Allah ya zo tana son ganinshi
a kan case d’in Ya Arshaad!
Ya dubi girman Allah
ya taimaketa
idan wannan ce alfarma d’aya tak da zai yi mata a duniya ya zo ya yi withdrawing complaints d’inshi dan ya rasulillahi...........”



“Za mu yi arresting Rukayya Yusuf za mu tafi da ita! Za a sake bincikar ta sannan
a kotu za ta ji hukuncinta”
Daya a cikin y’an sandan ya fad’a…….....

Anfi 20 minutes ana fama da Mammy dan hauka tayi musu tuburan da kyar sai da aka nuna mata bindiga tukunna ta tsaya aka datsa mata ankwa.

Kukan da Arshaad yake yi sai da ya saka kowa kuka.
A hankali ya durk’ushe a wajen.

Mommy ma ta so hanawa amman Dad ya rik’eta
haka aka fita da Mammmy tanata kuka tana tonawa kanta asiri dan sai faman jerowa Dad Granpa da Mommy Allah ya isa take yi
a cewarta su ne suka tunzurata ta yi komai
sannan in da Granpa bai bawa Aslam gida
sannan ya bashi Mt a b’oye a munafurceba to da bata yi abunda ta yi ranar birthday d’in su Shuraim ba.

Ana fita da Mammy bayan d’akin ya d’auki shiru
na kusan 7 minutes.
Babban y’an sandan ya yi gyaran murya ya sake cewa
“Unfortunately za mu tafi da Arshaad shima..
Bashi da laifi a case d’in Ummi
amman yana a case d’in Junaidu!
Kuma Junaidu a sama shima ya kai k’arar shi
dan direct case d’in daman hannuna ya fad’o.

Sannan Aslam ma idan yanaso zai iya filing complaint ya yi shara’a da shi
akan tarwatsa mishi company da ya yi.”

Cikin tsananin b’acin rai Asalm ya k’arasa inda mutumin yake tsaye ya ce
“Who the hell do you think you are?
Ni zaka gayawa abunda zan yi da brother d’ina!?
Idan na sake ji kace zan yi shari’a da shi I ‘ll make sure ka yi regretting kasancewarka d’an sanda!
Off you go..
Just leave!
Za mu k’arasa issue d’in mu mun gode.”

A hankali cikin d’an b’acin rai mutumin ya ce
“Mr Aslam watch you words!
Kuma let me assure you
Idan ba Junaidu ne yazo nan ya ce ya yi withdrawing complaints d’inshi a Arshaad ba to dole za mu tafi da shi!
And idan ka yi interfering to
za mu had’a da kai”

A hankali Arshaad ya mik’e ya k’arasa ya dafa kafad’un Aslam ya ce
“Let it go..
It’s fine i’m fine.”

Yana shirin yin magana
Junaidu ya shigo shi da Aaima…………………
Tabbas!
Ya so ya hukunta Arshaad,
yaso ya hukuntashi akan irin abunda ya yi masa amma
ta dalilin Hudan sannan tsakanin shi da Aaima tabbas ya san watak’il wani abun ya k’ullu dan tunda ya ganta ya rasa sukuni sam!
Waennan dalilai biyu suka sanya kawai
ya k’arasa inda mutumin yake tsaye ya ce
“Na yi withdrawing complaint d’ina! Arshaad can go free.
Allah ya sa mu fi k’arfin zuciyoyinmu.”

Wata nannauyar ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e
kafin ya juya inda Junaidun ya ke ya yi hugging d’inshi sannan ya d’ago yad’an yi tapping shoulder d’inshi ya ce
“Thank you Junaidu,
thank you so much.”

Murmushi kawai ya yi
Arshaad yana shirin yi mishi magana ya juya ya fita.

Da sauri Aaima ta bi bayansa dan yi mishi godiya.

Bata samu ta cimmasa ba
sai a compound d’in Granpa dan sauri yake yi sosai.
Da d’an k’arfi ta ce
“Hey”

Ajiyar zuciya ya sauk’e ya lumshe manyan idanuwanshi tukunna ya juyo.

Gaba d’aya jikinta a sanyaye yake a haka ma bata ga sanda aka tafi da Mammy ba.

Tana zuwa ta ce
“Thank you. Mun gode kwarai!
Allah Ubangiji ya taimakeka kaima a lokacin da kake buk’atar taimakon gaggawa”

A hankali ya d’an sunkuyar da kanshi, har ya d’ago zai yi magana sai kuma ya lura da yanayinta..
Ganin da yayi bai kamata su yi wannan maganar yanzu ba yasa ya ce
“Ba komai.
Amman akwai alfarmar da nake nema a wajenki!
Naga yanzu
you are not in a good shape idan ba damuwa
zan iya zuwa nan da 1 week
da laasar
around 5 haka!
I need to talk to you.”

A hankali ta ce
“Allah ya kaimu”

Daga nan suka yi sallama ta sake yi mishi godiya
ta koma ciki. Tana tafe tana matsar hawaye.

Abakin kofar shiga taga mutumin ya fito da ragowar mutane biyu

Haka kawai jikinta ya bata
an tafi da Mammy dan daman bata ganta ba d’azu da ta dawo parlourn...
Anan wajen kawai ta durk’ushe ta sa kuka.


Aslam yana ganin mutumin ya fita ya sauk’e ajiyar zuciya ya kalli Gramma ya ce
“Gramma Ina takardun dana baki d’azu da safe?”

A hankali Gramma tana matsar hawaye
ta juya ta nufi hanyar d’akinta.

Bata yi 4 minutes ba ta fito rik’e da wasu takardu masu yawa file file wajen uku.
Bai bari ta k’araso ba ya k’arasa ya karb’a sannan ya zaunar da ita a kan kujera ya ce “thank you”

A hankali ya k’arasa ya d’an rissina ya mik’awa Granpa ya ce
‘ya duba,
yana zuwa
bara ya d’anyi magana da Arshaad.’

A hankali ya k’arasa inda Arshaad yake ya ce
“Arshaad you are my brother and best friend.
Bani da d’an uwa kuma Aboki kamar ka
amman ka yi hak’uri ba
laifina bane
Allah ne ya d’aura mana son mace d’aya!
Ba zan iya b’oye maka ba
I loved Huda tun kafin ka kaini wajen ta mu gaisa
i knew her tun ina Uk....”
Nan ya bashi brief labarin da ya gayawa Huda. A hankali ya ce “Da na dawo naga yadda kake k’aunarta
shiyasa kawai na yi deciding
In bar maka ita! Which almost kill me shiyasa yanzu nake mai baka hak’uri..
Da ace inada iko da zuciyata
to da na hak’ura na bar maka ita amman ba zan iya ba!
I’m sorry to say this to your face wallahi ban san irin k’aunar da nake yi mata ba
ban san ma kalar wannan son nake yi mata ba sai da na mallaketa a matsayin matata!
Dan Allah ka yi hak’uri ka fahimceni......”

Hugging d’inshi kawai Arshaad ya yi yana hawaye.

Dakyar suka cika juna
Arshaad d’in ya ce
“You have sacrificed a lot for me ka gaya min dalilin da zai sa ba zan hak’ura In cire matarka a raina ba?
Kar ka damu
you have tried
Aslam
for my happines
kanaji kana gani ka danne farin cikin ka saboda ni in yi farin ciki.
You are the best brother and the best friend in the world..
Komai ya wuce
Ina so ka saka a ranka kamar ban tab’a had’uwa da Huda ba
amma dan Allah please inaso zan bar k’asar nan!
For some years
Ina son in yi healing daga Mammy da kuma everythin..
Don’t stop me please......”

Murmushi Aslam ya yi kafin ya ce “ba zan barka ka tafi haka ba”
Ya fad’i haka yana mai juyawa ya isa inda Granpa ya ke yad’an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login