Showing 33001 words to 36000 words out of 100703 words

Chapter 12 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4376

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
63


Mikiya Writers Association.
Murmushi Arshaad ya yi
kafin a hankali yace
“Ummi, na same ku lafiya?”

Sai a lokacin Ummin ta yi laakari da yadda bashi da lakka a jikinsa da kuma tsananin ramar da yayi.

“Alhamdulillah” tace, sannan ta d’aura da cewa “where have you been?”.

Still yanzun ma murmushi ya sake yi, a hankali yace
“Bara in d’an huta”
Ya fad’i hakan yana mai wucewa ya shige cikin parlourn, wanda sai da ya zo wucewar ne tukunna Ummi ta lura da akwatin da yake tafe da shi!
Gabanta ne taji yad’an buga!
Gashi babu damar ta tsayar da shi ko ta hanashi wucewa, a k’asan ranta tace
“Anya kuwa zaman su Aslam da Arshaad zai yiu a waje d’aya?…”
Tana cikin wannan tunanin ta jiyo ihun Hudan!

Dakatawa Arshaad yayi ya juyo ya kalleta kafin yace
“Kamar muryar Huda..”

Shiruuu, Ummi ta d’anyi, chaan kuma ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya
tace
“Eh, suna nan, Granpa refuse to accept them”

Ya bud’e baki kenan
zai yi magana suka sake jiyo ihunta a karo na biyu..

Ita Ummi har ga Allah tayi tunanin wani abun ne ya sameta dan batayi zaton Aslam d’in ya dawo ba!
Shiyasa tayi saurin nufar d’akin, ba tare da b’ata lokaci ba shima Arshaad ya bi
bayanta da sauri….

NOW.
Wardrobe d’in a setin k’ofar yake a ta tsaye!
Shiyasa suna shiga suka gansu….

Da mugun sauri Arshaad ya juya Ummi kuwa da kyar kunya ta barta ta iya jan y’an k’afafunta ta bar wajen.
Ko kyallin Arshaad bata gani ba, ga de akwatinsa nan
a tsakar parlourn inda ya barshi…

Wucewa tayi sama da sauri dan ji tayi kamar za a bud’e k’ofar d’akin su Hudan a fito.

Achan d’akin kuwa
su Ummi suna fita Huda tasa kuka!
Ba abunda yafi d’aga mata hankali irin Ya Arshaad wanda suka had’a ido dashi! Shikenan ta san yanzu zai ce taci amanar sa ta gama!
Bayan ko sati uku ba ayi da yin bikin ba……

Shiruu, Aslam ya d’anyi
yana kallonta ta rufe idonta tana kuka ta duk’unk’une a tsaye waje d’aya, ajiyar zuciya ya sauk’e…..a hankali taji kamar ya bar wajen.
Addua take yi Allah yasa fita zai yi, ai kuwa a hankali
taji ya bud’e k’ofar ya fita.
Tana bud’e ido taga ita kad’ai,
ajiyar zuciya ta hau sauk’ewa a jejjere, da kyar ta samu ta d’an nutsu tukunna ta soma k’ok’arin barin wajen..
Poster da ta sub’uce a hannunta d’azu ta taka!
Kalla tayi ta sake kallo kamar tanason yin nazarin wani abun
chan kuma sai ta lumshe idonta ta bud’e kawai ta d’auka ta mayar inda ta ganta.

Jikinta duk a sanyaye hakan nan ta samu ta shirya da kyar
ta nemi waje ta zauna.


Aslam yana fita ya fara k’arewa falon kallo kamar akwai abunda yake nema. Yana cikin kallon parlourn Idanuwanshi suka sauk’a akan trolley madaidaici. Wani yawu ya had’iye mai d’an d’aci
tukunna ya furzar da iska ya nufi d’akin da yake da tabbacin Arshaad d’in yana a ciki.

Knocking ya tsaya ya d’anyi, jin shiru yasa ya tura k’ofar ya shiga…
Ganin ba kowa ya sanya yayi tunanin to ko dai ba nan d’in ya shigo ba, har zai juya sai ya jiyo motsin ruwa a toilet.
A hankali ya sauk’e wata siririyar ajiyar zuciya kafin ya koma ya nemi waje ya zauna a bakin gadon.


Morethan 10 minutes Arshaad ya d’auka a band’akin bayan shigowar Aslam.
Har Aslam d’in ya fara tunanin lek’awa a ransa yana tunanin ‘maybe ko baya ciki an yi mistake d’in barin fanfo a kunne ne’ sai kuma yaji an kashe tap d’in!
Still sai da ya k’ara 2 minute tukunna ya fito ya na tsane fuskarsa da towel….

A tunanin Aslam wanka Arshaad d’in yayi amman
fitowar da yayi sanye da kayan jikinshi ne ya sa ya fahimci ba wanka yayi ba sai dai
ko alwallah dan gashi ya nad’e dogon hannun white shirt d’in jikinsa gashin hannunsa a kwakkwance sajensa da sumarsa suka duk a jik’e.

Murmushin da Arshaad d’in yayi masa ne ya katseshi daga nazarin da ya fad’a.
A hankali ya mik’e tsaye yana kallonshi har ya k’araso inda yake tsaye.
Aslam yana shirin yi masa magana yaji yace
“Sorry..
Ban san kuna tare ba
Ummi and I
tot wani abun ne ya sameta
shiyasa mu....”

“Where have you been??”
Muryar Aslam d’in ta katseshi.


“Maldives”
Ya bashi amsa a tak’aice
sanann ya d’an wuce sa yayi hanyar fita yana ci gaba da cewa
“Already na riga na yi arranging komai for honeymoon”

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace
“Arshaad, i.......”

Da sauri Arshaad yace
“Let’s pray!
Naji har an kusan shiga masallaci.”
Yana gama fad’in haka ya bud’e k’ofar ya fice.

Aslam ya dad’e a tsaye kafin ya samu ya iya motsawa daga inda yake shima ya fice.

Bai sameshi a wajen ba sai a masallacin, a gefensa ya tsaya
suka yi sallar, sai da sukazo fita tukunna suka had’u da su Shuraim..

Suna ganin Arshaad d’in suka nufeshi suka yi hugging nashi
cikin tsananin farin ciki..Sudais yana dariya yace
“Ashe baka manta ba”

Murmushi yayi kafin yace mishi
“Ai na gaya maka last year daman ko Ina inane
zan dawo ayi celebrating this year da ni”

Murmushi dukkansu suka yi suka nufi gida.

Suna shiga su Shuraim suka yi sama shi kuma Arshaad ya jaa akwatin shi ya nufi d’akin da ya zab’awa kanshi.

Bai san Aslam yana tare da shi ba sai da ya shiga d’akin ya juyo zai rufe k’ofar! tukunna
suka yi ido biyu.
A bud’e kawai ya bar mishi k’ofar daga nan ya juya ya jaa trolley d’insa ya kai ya ajjiye.
Yana juyowa ya ga Aslam d’in still a tsaye, murmushi yayi kafin yace
“Ka k’araso ka zauna mana”

“Arshaad listen,
we have...”

Cikin katseshi Arshaad d’in yace “We have to talk ko?
About Huda!
Aure! And everything right?”
Numfashi ya fesar kafin ya cigaba
“Akan me to za muyi maganan abunda ya riga ya faru ya wuce?”

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace
“Ba abun magana kam gaskiya, i ust want to know how you feel about us, together, and everything
sannan kai!
Are you ok??”

Murmushi Arshaad yayi mai had’e da dariya kafin yace
“Aslam i feel fine!
Sannan I’m Ok.
Tunda har ka ga na dawo
Nigeria
Kano to
I’m Ok Aslam.
So kawai abunda zan gaya maka shine kar ka dubani kace zaka yi affecting relationship d’inku negatively, ni ban
ma san kuna gidan nan ba
da a hotel zan zauna zuwa
jibi inzo a yi birthday da ni
daga nan in nemi inda zan je saboda
I still can’t face Mammy!
Sannan ba zan iya zama a tsakiyarsu ita da Dad suna fad’a kamar Annabi da kafiri ba.
But still zuwa jibi
zan san yadda zan yi in sha Allah….”

Da sauri Aslam ya matso inda yake yace
“No, you don’t have to. Kar ka je ko ina…”

Cikin katseshi Arshaad yace
“I’m sorry to say this
amman
after yadda kake feeling guilty right now akan halalin ka saboda ka san na ganku
i definitely need to go!
Kuna buk’atar air, in fact
your relationship is somehow complicated dan haka kuna buk’atar time da space
In other for you two to build a healthy and happy marriage..
If I can’t help banga dalilin da zai sa in zauna a tsakiyarku ba ina sakaku kuna feeling somehow.
Zan iya rantse maka akan cewa
I have moved on! And na manta da komai na cire Hudan a raina completely but na san ba lalle ka yarda ba, itama
ba lalle ta yarda ba, za ku
dinga gani kamar ko in kun yi abu zai sa inji ba dad’i ko wani abu makamancin haka
wanda hakan zai sa ku kasa sabawa da kuma sakewa da juna, ni kuma har ga Allah ba zan so hakan ba, therefore i think i need to stay away for some months ko a year haka..
Maybe nima idan na tashi dawowa In dawo da tawa bride d’in”
Ya k’arashe maganar da d’an murmushi a kan fuskarsa.

A hankali Aslam ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin yasa hannu ya janyoshi jikinshi yayi huggin nashi.....


K’arar wayarsa ce ta sanya shi cika Arshaad d’in yad’an matsa sannan ya zaro wayar ya d’auka yasa a kunnenshi yace “Auwal”
D’an jimm! Yayi, chan kuma yace “what for?”
A hankali kuma sai yayi murmushi yace
“Bara mu fito,
Arshaad is home
ma.”
Bai jira jin me Auwal d’in zai ce ba ya katse kiran ya d’ago yana kallon Arshaad kafin yace
“Mu je, Auwal ne”

Bai musa shi ba
ya bi bayanshi
suka fita……


A babban parlourn suka sameshi, zaune cikin d’aya daga cikin set d’in kujerun dake a parlourn.
Yana hango su ya taso,
duk da halinda yake ciki hakan bai hanashi k’arasawa yayi welcoming Arshaad warmly ba.

Aslam ne ya katse su ta hanyar cewa
“Mai ya faru ne?
You sound worried!
Yanzun ma kuma you look worried”

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Tana Ina please?
Bani da energy…..”

Gaba kawai Aslam d’in yayi
shi kuma ya bishi a baya.
Suna zuwa k’ofar d’akin nasu ya murza ya shiga Auwal d’in kuma ya tsaya a waje.

A zaune ya sameta, ta rafka uban tagumi…sanye cikin doguwar rigar da ta fitar d’azun zata saka.

A rayuwarshi blue is one of his favorite colours, gashi blue d’in mai d’an duhu wanda ya taimaka wajen fito da ainahin kyawun farar fatarta..Yanayin dim light d’in dake kunne a d’akin ne ya taimakawa stones d’in jikin rigar tata wajen yin kyalkyali na musamman mai d’aukar ido da hankali…
Normal d’aurin d’ankwali tayi irin na ture ka ga tsiya
wanda ya fitar da uban tulin gashinta da ta tufke ta nannad’eshi a k’eyarta.
Ba komai a fuskarta ko mai bata shafa ba amman kalar kyan da tayi masa yau dole ya bada tukuici!.

A hankali k’asa k’asa yadda ta tabbatar ba zai ji ba tace
“Ni fa bana son kallo”
Tana mai d’auke kanta daga gareshi had’i da d’an turo baki.

Murmushi kawai yayi sannan ya tako gabanta ya tsaya yace
“Saboda me yasa bakya son kallon?”

Runtse idanuwanta tayi, a ranta tace
“Wannan ko maciji albarka”

Batai auni ba taji yasa hannunshi a nata ya mik’ar da ita tsaye yana kallon rigar jikinta kafin ya maida idanunsa a kan d’ankwalin, murmushi yayi yace
“D’aurin masifaffu dama yafi yiwa masu tsiwa kyau.”

Haka kawai sai ta tsinci kanta da kasa d’agowa da kuma kasa cewa komai, still bata san daliliba amman maganar tasa ba k’aramin dad’i tayi mata ba!
A take taji haushin shi da fushin da take yi da shi suna d’an raguwa…


Ya jima yana kallonta kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace
“Ki je Auwal yana parlour yana jiranki, muryarsa har rawa take yi, da alama emergency ne.”

Ahankali ta sauk’e ajiyar zuciya dan ta san me ya kawo shi.

Sai da ya sake cewa
“Ki je”
Tukunna ta iya jan k’afafuwanta ta d’anyi baya kad’an ta yadda ta tabbatar ba zata gogeshi in ta zo wucewa ba sannan ta wuce.

Har ta kusan k’ofa taji yace “ungo”
Tana juyowa ta ganshi a kusa da ita yana bata hijab d’inta.

Tsayawa tayi bata matso ba balle yayi tunanin zata saka…

A hankali ya matsa inda take yana kallonta itan ma shi take kallokafin ta yi k’asa da kanta kamar d’azu.
Yanayin yadda ta yi d’aurin tabbas in ya saka mata a haka zai iya shak’eta shiyasa yasa hannu ya zare d’ankwalin ya rik’e a hannunsa

So yake ya saka mata hijabin amman kyau da shek’in da gashin yayi da kuma yanayin parking d’in da tayi ne ya yi mugun tafiya da imaninshi dan haka ya tsaya ya shagalta da kallo….

A hankali yaji tace
“Bara in je, ka ce ce emergency ne”
Ba tare da ta d’ago kanta ba.

Wata nannauyar ajiyar zuciya taji ya sauk’e kafin a hankali ya ware hijabin kamar baya so..sai da ya nemo fuskar hijab d’in tukunna ya ajjiye d’an kwalin nata a gefe ya sa hannuwanshi duka biyu ya bud’a ya kawo dede setin fuskarta yace
“Raise your face”
Tana d’agowa suka had’a ido yana kallonta itan ma shi take kallo ta cikin hijabin.
A hankali ya matsar da hijabin yasa mata a fuska sannan ya d’an jashi ya zauna dede kafin ya ida warewa ya sakar mata shi ya rufe ilahirin jikinta.
Tana shirin wucewa taji yayi cupping fuskarta yad’an matso kusa da ita.
A zabure ta d’ago tana kallonshi shima ita d’in yake kallo kafin ya lumshe idanunsa a hankali ya kai lips d’insa dede goshinta ya sakar mata light peck d’in da ya sanya ilahirin jikinta d’aukar rawa!
A hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya matsar da bakinsa a dede setin kunnenta yace
“You look beautiful tonight”
Yana gama fad’in haka ya cikata ya wuce toilet
dan yana buk’atar yad’an watsa ruwa kafin lokacin dinner, garin yau akwai zafi
sannan shi kanshi kwana biyun nan yana saurin jin zafin yanayin dauriyace kawai yake yi.


Da kyar ta samu k’irjinta ya d’an ragu da bugawa
sannan ta d’an dedeta kanta ta fita wajen Auwal.

Tare ta tadda su a parlourn shi da Arshaad.
Gaba d’aya sai ta tsinci kanta da diriricewa kamar mara gaskiya, ta tsaya.

Tun sanda ta fito
Arshaad ya ganta, ganin duk ta rikice ta kasa k’arasowa ne yasa yace
“ko In baku guri ne?”
Ya fad’i hakan da d’an k’arfi ta yadda ya san za ta jiyo sa.
Da sauri ta d’ago ta kalli inda suke, suna had’a ido ya sakar mata lallausan murmushi sannan ya sake maimaita tambayar tasa.

A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta fara takawa ta isa inda suke ba tare da ta sake yarda sun had’a ido da Arshaad d’in ba.

Murmushi kawai yayi ya zaro wayarsa a aljihu ya shiga daddanawa….,

Tana zama Auwal ya juyo gaba d’ayanshi gareta ko gaisawa bai iya tsayawa sun yi ba yace
“Dan Allah da gaske gobe za a kawo kud’in auren Sakina?”

Ba k’aramin tausayi ya bata ba dan har wata kwalla taga ta taru a idanuwanshi..

A hankali tace
“Ya Auwal duk abunda kaga Allah bai yi ba muddin ka yi addu’a to ba alkhairi bane, ka kwantar da hankalinka zaka samu wadda ta fita in sha Allah.”

Cikin katseta yace
“Da gaske ne kenan”
A hankali muryarshi na d’an rawa.

D’agowa tayi da niyyar sake bashi hak’urin ya rungumi k’addara
kawai
taga hawaye bibbiyu suna zubo masa!
Da sauri ta runtse idonta tace
“Ya Auwal dan Allah ka daina mana, ka rungumi k’addara kayi adduar Allah yasa hakan shine mafi alkhairi”

Bud’e baki yayi da niyyar yin magana sai kuma ya kasa,
da sauri ya tashi ya fita a side d’in gaba d’aya ba
tare da ya sake waiwayon su ba.

Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali tana jin tsananin tausayin Auwal a ranta.
Kamar ance ta d’ago, tana d’agowa suka had’a ido da Arshaad, murmushi
ya sake sakar mata
kafin yace
“Abun tausayi, ko?”

Sunkuyar da kanta tayi
a hankali ta d’aga kan alamar
“Eh”

Yana shirin yin magana Ummi ta sauk’o! Har ga Allah haka kurum sai ta tsinci kanta da rashin jin dad’in ganinsu a zaune su biyu.
Tana zuwa ta nemi guri ta zauna kusada Huda ta kamo hannunta k’asa k’asa tace
“Huda tunda ba ku kad’ai bane a gidan, ku dinga saka key a k’ofar ku mana.
Wallahi ban san ta ina zan fara kallon Aslam ba”

Da sauri Huda ta sunkuyar da kanta k’asa sosai
wanda hakan har sai da ya sanya Ummi ta d’anyi murmushi.

Sarai Arshaad ya ji abunda suka ce amman bai nuna musu ba! Hasalima chatting d’insa kawai yake yi yana murmushi.

Ganin hirar tata ba zata yiu da Hudan ba yasa ta juyo ga Arshaad tace
“Ka je wajen Mammy?”

Sai da yad’an k’ura mata ido, kamar ma bai ji abinda tace ba
tukunna yad’an gyara zaman shi ya maida wayar aljihu kafin yace
“A’a,
direct daga airport nan nayo”

A hankali tace
“Bata da lafiya”

Bata ida rufe bakinta ba yace
“I know!”

Ta lura da yadda yanayinsa ya chanja amman hakan ba zai hanata yi masa nuni da gaskiya ba dan
haka tace
“Arshaad no matter what, ko me tayi maka
Mahaifiyarta ce!
She’s sick!
Very sick!
She needs you!
Aiima bata nan ita kad’aice.

Ajiyar zuciya ya sauk’e yana kallon Ummin ido cikin ido yace
“Abba baya nan ne?”

“Eh, yayi tafiya
shi da Daddy
business trip
sannan za su bud’e
branch d’in construction company d’insu shi da Aslam a UK sun ma bud’e
It was successful sannan trip din nasu was also successful
shiyasa jibi za mu yi double celebration in sha Allah.”
Ummin ta zayyano mishi
dan so take su yi magana kar
ya samu question d’in da zai sake jifanta da shi as an excuse.

“Ma sha Allah
Allah ya k’ara d’aukaka”
Yace, daga nan ya mik’e.

Itan ma mik’ewa tayi
tace “We are not done”

Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e kafin ya kalleta yace
“Ummi ko In koma inda na fito ne?
Although i came for Shuraim and Sudais but it’s like bakya murna da ganina!”

Da sauri tace
“Arshaad ba haka ba...”

Cikin katseta da d’an b’acin rai yace
“To na rok’eki da girman Allah ki daina yi min maganar Mammy
Ummi kina so inje In zauna Ina ganin suna fad’a kullum ita da Dad ko yaya?”

Tausayin sa ne ya fara rufeta dan haka ta k’arasa inda yake ta kamo hannunshi ta rik’e a nata tace
“Ba haka bane son, ka
fahimceni”

Kamar zai yi kuka yace
“Me kike so inyi yanzu?”

Har ta bud’e baki za tayi magana sai kuma tace
“Ba komai,
nothing”

A hankali ya zame hannunsa a cikin nata ya juya ya shige dakinsa.

Ta d’an jima a tsaye
kafin ta sauk’e ajiyar zuciya ta juya ta nufi kitchen ta fara setting dining table.

A hankali itama Huda ta mik’e ta k’arasa ta shiga tayata.

Sai da suka gama tukunna Huda ta wuce d’aki, ita kuma
Ummi ta zauna anan kan dining d’in ta rafka tagumi.


A gaban dressing mirrow ta sameshi yana taje gashinsa..
Sanye cikin pyjams dark ash da suka yi mishi kyau matuk’a!.

A hankali ta k’arasa bakin gado ta zauna ta d’auki wayarta da ta mak’ala a charge ta danna kiran Sakina
Bayan ta zare wayar a charging.

Tana d’auka tace
“Yanzu Ya Auwal ya tafi”

“Um”
Kawai Sakinar tace, a hankali.

Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin tace
“Yayi matuk’ar bani tausayi, har da kuka fa yayi.
Da kin sani baki gaya mishi yanzu ba”

Shiruu, ta ji Sakinar tayi
kafin chan tace
“Ya dameni da kira da massages!
At least yanzu zan huta
sannan i don’t want him to have any false hope.”
Cikin son kawo k’arshen maganar Auwal d’in tace
“Za ki zo goben?”

Sai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login