Showing 93001 words to 96000 words out of 100703 words

Chapter 32 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4367

duben su suka tafi.

Su kuma Abokanan tafiyar tawa inaga tsorata suka yi dan ina shirin fitowa naga duk sun shige motar suna shirin tafiya.

Da sauri na yunk’ura zan tafi na ji an rik’e min k’afa!
Sai da gabana ya fad’i da na juya dan ni sam ban lura akwai tsoho ma a wajen ba a durkushe sai da ya rik’o nin.
Cikin kuka tsohon ya ce “bawan Allah ko baiwar Allah dan Allah taimakon musulunci zan mutu yunwa nake ji.”

Da sauri na ce “Baba dan Allah Abokanan tafiya ta za su tafi ka cikani In wuce.”

Cikin kuka tsohon ya ce “yunwa nake ji ka taimakeni dan Allah”

Haka nan inaji ina na gani na kama hannunshi ya mik’e su kuma Abokanayen tafiyar tawa suka wuce dan maybe sunga na dad’e su kuwa a tsorace suke.
Na ji takaici sosai
amman yadda tsohon nan yake karkawa da kuka yasa kawai na yanke shawarar In taimakeshi.

Sai da muka fara tafiya na fahimci ashe makaho ne!
Haka muka yi ta kutsawa dan hanyar ba jama’a sosai
har muka iske wata mai k’osai da kunu na siya da d’an kud’in da aka bani in yi na mota na bashi ya ci ya sha.
A hankali muna zaune a wajen ya ce “in bashi labarina”
Haka kurum ban sanshi ba amman na tsinci kaina da fad’a mishi komai na rayuwata
har kawo yanzu.

A hankali ya ce “kuma kana ganin ba kai ake nema ba kuwa!?.
Ka zo mu je Gidana ka d’an b’uya kafin kwana biyu sai ka wuce gudun kar ka je suna nan har yanzu ka fita a kamaka.”

Tsoro ya sanya ni na amincewa wannan tsohon, dan a yadda naga mutanen nan babu kalar imani a tattare da su.

Gidan nasa y’ar bukka ce
sai band’aki wanda aka yishi da langa langa a gefe
sai wani murhu da rijiya. Sam babu wani katanga ko wani abun da yake nuni da wajen keb’antacce ne.

Y’ar bukkartashi muka shiga muka zauna anan yake ce mini “Matarsa ta rasu watan da ya mutu,
Allah bai bashi d’a ba!
Danginsa kuma duk sun guje shi saboda basa son d’awainiya.”

Atake na ji tausayin bawan Allahn nan ya rufe ni, kuma a take muka saba shak’uwa ta shiga tsakaninmu…..
Kwana na biyu a wajensa,
na siya mishi abinci da d’an abun da ba a rasa ba duk a cikin kud’in da aka bani
a lissafina idan na tashi ni sai In d’auki drop har gidan Abokina ya biya.
Ban b’oyewa tsohon nan ba na ce masa “muma ba wasu masu arzik’i baneba, ba daban haka ba da na tafi da shi” dan na lura yana cikin kad’aici da buk’atar taimako “kuma akwai abubuwa da dama a kaina amman dai bara mugani in shaa Allah idan na koma gida na yi settling zan dawo in duba shi.
Dan nima a yanzu Ina matuk’ar buk’atar kud’i.”


Daga nan na nemo wata mata a gefe na rok’eta akan “dan Allah ta d’an dinga lek’ashi”
Ita kam Matar mamakima ta dinga yi dan a cewarta “duk zaman ta a k’auyen ita bata san da shi ba”.
Bayan Matar wuce ne muka yi sallama muna ji kamar kar mu rabu…
A bakin bukkar tashi Ina fitowa na ci karo da wani mutum cikin suite! Da akwati a hannunshi,
kamar yana cikin sauri, ya nuna min hotonshi da wannan tsohon kamar lokacin tun suna samari ya ce min “an ce yana nan! Da kyar da wuya ya samu location d’insa, dan Allah na san shi?”

Ba tare da b’ata lokaci ba na ce masa “eh”

Dan haka mutumin ya ce mini
“sun tab’a yin businesses da tsohon ne, tsohon ya aminta da shi amman shi sai
ya gudar masa da kud’insa
so tun daga lokacin abubuwa basu yi mishi kyau ba!
Shiyasa ya yanke shawarar dawo mishi da dukiyarsa.”
Ya d’aura da cewa
“Dan Allah in bashi in ce masa
ya ce sunanshi Kabir,
Alhaji Kabir.
Ya taimaka ya yafe masa”

Yana min maganar ne
shi duk a tunaninsa ma ni d’an tsohon ne.
Jin muryar tsohon ya fito yasa ya yi sauri ya yi min sallama a cewarsa ‘ba zai iya facing d’insa ba dan
kunyarshi yake ji.’

Duk da nace ya d’an tsaya ko ruwa ne ya sha
saboda naga inba magana ya yi ba tsohon ba zai gane shi ba dan ba gani yake yi ba, amma sam yak’i yarda, ya damk’a min akwatin yana d’an waiwayowa yana kallon tsohon har ya shige motarshi driver ya ja suka tafi.

Akwatin na ja na kai d’aki na fito na kama hannun tsohon muka shiga ciki na zauna.
Na zuge akwatin ba tare da na ce komai ba.

Sai da gabana ya yanke ya fad’i dan gabaki d’aya akwatin cike yake da mak’udan kud’ad’e dollars!

A hankali na ji tsohon ya ce
“Kai da waye d’azu a waje?”

Cikin In inaa na ce
“wani mutum ne ya zo neman ka! Ya ce kun tab’a yin buisiness kai da shi ya gudar maka da kud’i.”

Shirruuu tsohon nan ya yi kafin chaan! Ya yi murmushi ya ce
“na kasa tunawa”
Kafin ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya ce
“Akwai abunda ban gaya maka ba…
Inada sabara a kwakwalwata
shiyasa ma kaga wasu lokutan Ina zama ina yin kuka ni kad’ai.
Wani makwafcina anan ya d’auke ni satin baya ya kaini asibiti aka tabbatar da cewa ‘ba zan k’ara sati uku a duniya ba!’.”

A take wani tsananin tausayinshi ya lullub’e ni!
Ga dai kud’ad’e nan ya samu
bayan
ya sha wahalar rayuwa amman a lokacin da kud’ad’en suka riskeshi
sai ya zamana ba za su yi mishi amfanin komai ba.
Ban san lokacin da kuka ya kufce mini ba!.

Jin ina kuka yasa tshon ya hau tambayata “menene? Mai ya faru?
Me ye a cikin jakar? Ko wani abun tsoron na gani?”

Shiru na d’anyi kafin ince mishi
“Kud’i ne a ciki,
Dollars.”

Shiruuu na ji ya yi…
Ya jima tukunna ya ce
“Ka taimakeni ko masallatai ne in gina dan Allah.
Saboda kaga ni ba ido da lafiya gare ni ba.
Bana bukatar ka gina min gida ko wani abu daga kud’in tunda kaga ba lallae inga k’arshen aikin bama
kawai dai ka rik’e Allah ka tayani gyara lahirata ta hanyar gina masallatai da islamiyoyi a k’auyukan nan.”

A lokacin tabbas ina son komawa gida
amman kuma
wannan tsohon yana buk’atar taimakona a yanzu
sannan inaso a ida auren Huda da Arshaad kafin In koma dan tabbas na kasa cire ta a cikin zuciyata
kuma na riga na d’auki alk’awarin ba zan aureta ba!
Tunda na lura sam bana cikin zuciyarta tun ranar da ta ce min Arshaad zata aura
k’ok’ari kawai nake yi inga na fitar da ita a raina
saboda no matter how much I love her ba zan tab’a iya zama da ita idan bata ra’ayi na ba!
Amman kuma
bana buk’atar a aurar da ita a gaban Idona
sannan still ina jin fargabar fitowata
duba da sharrin da aka yi min
da kuma waenda nake tunanin ni suke nema..A ganina gara In d’an fahimci abubuwa daga b’oye kafin a kaini lahira
tun da ban san waye yake farautata ba!
Sannan aikin da zan yiwa wannan tsoho tabbas lada zan samu…
Shiyasa a take na yanke shawarar jifan tsuntsu biyu da dutse daya....

...Haka nan na tsaya tsayin daka wajen taimaka masa kamar yadda ya buk’ata aka shiga gina masallatai a duk k’auyukan da makarantun islamiyya
gini mai kyau da had’uwa, na ban mamaki.

Tabbas Ina da buk’atar kud’i
amman ban tab’a yunk’urin d’aukar ko naira biyar ba!
Apart from kud’in motar da yace In dinga d’auka a ciki dana abinci da shelter.

Akwai kud’i sannan na samu maaikata masu yawa sosai
dan ko wanne k’auye masu ginin daban suke
shiyasa kafin wata uku aka fara shirin kammalawa.

Ba abunda yafi sakani farin ciki irin yadda Allah ya arawa wannan tsohon tsawon rai har na tsawon lokacin da aka zo kammalawa duk da dai jikin nashi sai a hankali.

Ranar da na kammala aikin da
washegari ya tashi da tsananin ciwo wanda kana gani ka san sai a hankali kawai.
A wannan bukkar tashi muke har kawo wannan lokacin
amman fa muna cin mai kyau mu sha mai kyau.

Ina ganin yana yin jikin nashi na ce “bara inje In nemo mai abun hawa a kaishi asibiti cikin gaggawa”
Amman sai ya rik’eni ya rok’eni akan in tsaya akwai maganar da yake so ya yi da ni.

Abu na farko da ya fara tambayata shine sunana!
Duk tsawon lokutan nan Yaro yake kirana da shi ni kuma in kirashi da Baba.
Sai da mutanen last k’auyen da aka yiwa masallaci suka tambayeni ‘suna son
rubuta sunanshi’
Tukunna da kyar ya ce min sunanshi
‘Alhaji Kabir mai fetur’

....Ahankali na ce mishi “sunanan ‘Junaidu’.”

Da kyar cikin tsananin ciwon da yake ciki ya iya ce min “in d’auko masa wata y’ar jaka”
Ya yi maganar yana mai yi min nuni da wajen da jakar take!
Tabbas na shiga rud’ani
saboda yadda ya juya ya nuna min jakar yasa na fahimci yana gani.....

Ina d’aukowa ya ce “In bud’e”
Ko da na bud’e d’in wasu takardu ne a ciki da waya
had’ad’d’iya mai kyau da tsada.

Wayar ya umarceni da in d’auko, in yi dialing number
dana ga an yi saving da ‘barrister’.
Haka akayi, tana shiga bugu d’aya ana biyu aka d’aga!
Cikin girmamawa na ji ance “sir”
Da mamaki na kalli tsohon wanda shi kuma yake mik’a min hannu alamun in bashi wayar…
Kaina bai gama d’aurewa ba sai da na ji kalar turancin da tsohon yake yi inda cikin harshen turanci na ji yana cewa wannan wanda suke waya
“Suna kusa ko?
To su yi sauri suzo yanzu.”

Tsoro da firgici suka sanya na mik’e da sauri na fara ja da baya.

A hankali tsohon nan ya ce
“Dan Allah kada ka ji tsoron komai.
Matso kusa in baka wani d’an tak’aitaccen labari.”

Da farko k’in yarda na yi in matsa d’in dan ni a tunanina ko d’an shan jini ne ko kuma d’an 419 bare ma da na tuno da mak’udan kud’ad’en da aka kawo mishi gaba d’aya sai na sake duburbucewa.

Da kyar da sid’in goshi ya lallab’ani na matsa kusa da shi.
Ina zama ya ce min
“Kar ka ji tsorona d’ana,
Ni ba macuci bane ba”
Bai bani damar yin magana ba ya cigaba da cewa
“Kamar yadda na fad’a maka da farko Allah bai bani haihu wa ba.
Na kasance attajiri na gaske dan a k’asar nan
idan akwai waenda suka fini kud’i tou bana jin
za su fi mutum biyu!
Arzik’i na ya samo asali ne
daga sana’ar man fetur,
da na samu Ubangiji ya sanya mini albarka harkar tawa ta bud’e sai na fad’a sana’a
Business ko wanne iri ne zan yishi kuma da ikon Allah Ina farawa sai ya habb’aka ya yi albarka ta ban mamaki.

Ni asalina maraya ne,
tun Ina gidan marayu muke soyayya da matata da na ce maka ta rasu watan baya.

Ina matuk’ar k’aunarta
sai dai kuma kishiyoyinta suka zamo silar da ya sanya bata ji dad’i a rayuwarta ba!
Ta rayu cikin tsananin k’unci da azabar rayuwa.

Ni mutum ne
wanda yake son mutane masu amana, bayan son da nake yi wa uwar gidanaa
tsoron Allah da amanarta ne suka k’ara min tsananin k’aunarta.

Apart from her bana jin akwai wanda ya tab’a rik’e mun amana yayi mun abu tsakaninshi da Allah
sai kai Junaidu.

Na sha adopting Yara in rik’esu tsakani da Allah
amman kowa idan ya lek’a ya hango tarin dukiyata sai ya nemi cutar da ni!
Rabinsu ma buri suke kawai suga sun halaka ni.
Da taimakon Allah da taimakon uwar gidana nake tsere wasu tarkunan wanda
fahimtar da aka yi tana taimaka min ne yasa
aka shiga tsakaninmu
na juya mata baya.”
Cikin kuka ya ce
“Ban tashi gane gaskiya ba
sai a ranar da zata bar duniya
tukunna
aka samu asirce asircen suka bar jikina na ganta a matsayin masoyiyata instead of da da nake ganinta as my enemy.
Na yi kuka ma yi takaici!
Saboda ita take d’awainiya da ni idan ciwona ya motsa Ina kyararta Ina komai
ashe itama bata da lafiya.

Duk da na saki ragowar mata na biyun da na fahimci laifin su ne
sannan
na bata hak’uri ta ce ta yafe min amman na kasa yafewa kaina!
A ranar da zata bar duniya
maimakon ni in lallasheta
A dead bed d’inta
sai ya samana ita take lallashina.
Na yi rashi tabbas sannan na san na rasa mutum d’aya tak da ya tab’a rik’e mun amana.
Ita ce ta ce min ‘In kwantar da hankalina zan samu wanda zai rik’en amana kamar ita
I should mark her words.’

Bayan ta rasu da kwana biyu..
daman tun kafin a shiga tsakanin mu
na yanke shawarar ‘zan damk’awa mutum mai amana guda d’aya rabin dukiya ta
idan na samu kenan,
rabi kuma in rarraba a gidan marayu, ba wai kuma masu
kula da gidan marayun zan bawa in ce su raba musu ba
A’a
Yaran gidan marayun zan bud’ewa account each
In saka musu kud’insu a ciki
saboda yadda duniya ta lalace
tsaf mutane za su iya danne kud’in dan na ga yadda mutum yake komawa akan dukiya…..
Saboda haka na fara
searching…..
A yadda na je maka a haka nake zuwama mutane
amman har da waenda suka mareni!
Mutum d’aya na samu kafin kai ya taimaka min kamar yanda ka yi sai dai shi ana kawo kud’i kamar yanda aka kawo aka baka ya gudu!
Ko lek’e na bai sake yi ba.......”
.......
Muna cikin wannan zancen
Mutannen da ya kira suka k’araso.
Manyan lauyoyine
da kuma wani babba a efcc.
Da mamaki nake kallonsu.
Ban san sanda hawaye suka zubo mini ba!
Jin yana musu bayani
akan yadda ya yi alk’awarin bawa mai kyakkaywar zuciya dukiyarsa. Hope takardun sun zama ready? Saboda gani nan”
Ya yi maganar yana nuna ni
ya ce
“Nine successor d’insa”

A take suka ce “eh,
komai is ready”
Sannan suka mik’o min takardu suka ce “in yi signing.”

Da farko kasawa na yi
saboda yadda mamaki aljabi da tsoron Allah ya lullubeni,
sai da tsohon ya rik’e mun hannu tukunna na dawo dede
na shiga signing takardun
da kwakwalwa ta ta kasa d’aukar d’umbin kud’ad’en da idanuwa na suke gane min!.

Ina gama cike wadannan
tsohon ya ce “yaso ya rabawa marayun kud’ad’en da kanshi
amman kuma
bashi da isheshen lokaci
so zai d’aura wannan nauyin a kaina”

Nan ma wasu takardun na cike na kud’i shima dede adadin wanda aka gama mallakamin
wanda zan rabawa marayun nan.

Jakar da d’azu ya ce ‘In d’auko in bashi waya a ciki’
Ita kuma filayene da gidaje
da gidajen man fetur d’insa, ya ce min “I should consider it shikuma as thankyou from him,
dan bai san ta Ina zai fara yi min godiya ba!
Na tabbatar da maganar matarshi sannan na bashi hope na cika mishi burinshi.”

Daga nan
duk ya saka na yi signing
Ina kuka yana kuka.

Sannan ya bada will d’in nine d’ansa sannan ya rok’eni
‘ko bayan ranshi in dinga yi mishi addua dan Allah.’

Ganin numfashinshi yana d’aukewa yasa na kinkimeshi muka kai shi motar da mutanen nan suka zo a ciki
amman Ina kwantar da shi a seat d’in baya na ji yayi kalmar shahada a hankali
sannan jikinshi ya sake......

Na yi kuka matuk’a.....

Ban yi k’asa a guiwa ba,
tundaga Adamawa har Abuja sai da na je da kaina na fara rarrabawa marayun nan rabin kud’ad’en shi da na yi alk’awari
wanda har yau ina kan aikin.”

A hankali Junaidu ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce
“Wannan shine sanadin arzik’i na.
Babu k’arya k’ari ko ragi a cikin labarina.”
......
A hankali su Abba suka sauk’e ajiyar zuciya
bayan sun gama saurarenshi
kafin Abba ya ce
“Tabbas Junaidu samun irinka a zamanin yanzu sai an tona.
Allah ya yi maka albarka.
Ka cigaba da rik’e amana da alk’awari
Allah yasa ka gama da duniya lafiya.

Idan mun gana magana za ka ji sak’on mu daga wajen Aaima in sha Allah.”

Cikin girmamawa ya yi musu godiya
daga nan suka yi sallama ya wuce.........


Bayan sati d’aya Aaima ta ce masa “su Daddy sun ce yana iya turowa anytime idan sun shirya”
Tsakanin Aaima da Junaidu ba zaka iya tantance wanda yafi wani farin ciki ba.

Su Kaka da Ya Jamilu ne suka zo suka nemawa Junaidu auren Aaima.
A parlourn Daddy aka tarbesu
tarba ta mutunci!
Cikin mutunta juna suka yad’a manufarsu suka nema aka basu.
Wata biyar ciff! Aka saka ranar auren
daga nan suka bayar da goronsu da alawa da kud’i nera miliyan d’aya!
Aka watse cikin farin ciki barkwanci mutunta juna da nishad’i.
……………..
Sai da Sakina ta fara kukan gida tukunna Auwal ya yarda suka dawo a lokacin watansu biyar a k’asashen waje.
Ya so ta tsaya su biya Paris dan nan ne kad’ai basu je ba a cikin k’asashen da ake yawan zuwa a d’an shak’ata
(Har Hajji da Umaara sun yi)
Amman ganin yadda ta d’aga hankalinta sannan ga yanayin condition d’inta yasa kawai ya hak’ura suka dawo.

Direct gidansu,
Daddy ya ce su wuce dan ta samu ta d’an huta.

Tabbas Daddy ya san in ba da kyar ba
to kuwa
za a yi irinta Granpa da Aslam
A
shi da d’an cikin jikin Sakina
saboda yanda
yake jin son jika ko jikar tashi tun kafin su zo duniya a ransa Allah kad’ai ya sani.

Ita Sakina har mamaki da kunya ma take yi, haka nan fa takanas! Zai kirata
ya yi ta jero mata adduo i ita da babyn
sannan ya yi ta turo mata important things akan condition d’inta
abunda ya kamata ta ci da wanda bai kamata ta ci ba saboda lafiyarta da babyn…

Wasu lokutan ita kam har kukan farin ciki take yi
dan gata da soyayyar da Auwal
yake nuna mata bata jin she could ever ask for more.

Tunda ta lura yana d’an wasa da sallah ta kafa ta tsare sannan ta nuna mishi b’acin ranta!
Yanzu sam Auwal ya manta rabon da ya bari lokacin sallah ya wuceshi.

Zaman lafiya da k’aunar juna
shine definition d’in rayuwar su
ga families d’inshi suma hatta Granpa da Mom kiranta suke yi su ji ya lafiyarta da babyn
dan Auwal a ranar da ya sani washegari ya kasa rufewa
farin ciki yasa sai da ya fad’awa su Mom da Gramma har su Abba tukunna hankalin shi ya kwanta,
sai da ya gama sanarwa kuma sai ya d’anji kunya.

Idan ka gansu tsaf da su sun yi k’iba sun yi fresh in banda glowing ba abunda suke yi!
Gashi sun yi mugun dacewa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login