Showing 63001 words to 66000 words out of 100703 words

Chapter 22 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4369

yiwa Sakina kwatankwacin son da Ya Auwal yake yi mata.”

Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin tace
“Kuma itama Ya Auwal d’in take so”

Da sauri Aaima ta juyo tana kallonta sosai.

Jinjina kai Huda tayi kafin tace
“Ni dama na dad’e da fahimtar hakan.
Tou kuma jiya Ashraff d’in ya sake tabbatar min…
Ya min complain akan
Ko kiranta idan yayi bata iya d’auka wani lokacin
sannan In zata kira sunanshi sometimes sai ta ce masa Ya Auwal!
Wani lokacin in ta fahimta ta yi saurin gyarawa.
Kwata kwata bata bashi time..
Shine ya kirani akan wai In na samu time yana son mu yi magana
face to face sannan kuma wai
waye Ya Auwal?!”.

Cikin rashin jin dad’i Aaima ta ce
“To ai za su cuci kansu ne daga ita har Ashraff d’in!
Kawai kamata yayi ta fito ta gaya mishi gaskiya shi kuma ya hak’ura.”

A hankali Huda ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce
“Bara in baki number tasa ku yi magana”

“Okay ba ni”
Aaiman tace tana mik’a mata wayarta.

A hankali Huda ta zaro wayarta wadda ke nan rik’e a hannunta daga cikin alkyabbar jikinta ta bud’e ta juye mata nambobin Ashraff a wayar ta mik’a mata.

Message ta tura mishi….
‘yau an kai Huda gidanta
so ba zata samu damar sauraronshi ba
amman ta fad’a mata komai game da issue d’in da yake facing ta b’angaren Sakina!
If he’s free ya zo su tattauna’.

A hankali Huda ta mik’e ta k’arasa k’ofar toilet d’in ta fara yi mata knocking..
Ta d’an jima kafin Sakinar ta bud’e k’ofar ta fito
a hankali tana tsane ruwan fuskarta da hannunta
alamun ta wanke fuskar ne.

Bata ce mata komai ba ta rab’a ta gefenta ta wuce..

Inda take zaune a kan gadon ta je ta gyara pillow ta koma chan k’arshe ta jingina da jikin gadon ta lumshe idanuwanta
bata ma bi ta kan Aaima da take cewa
“Yace gashi nan zuwa har ta bashi adreess”
ba.

Kamar minti talatin ya kira number Aaima ya ce “yana bakin estate d’in”.
……..
Aiima bata yi minti ashirinba
ta dawo.
Tun da ta shigo suka lura da yadda jikinta ya yi sanyi over.

A hankali ta nemi waje ta zauna a gefe ta yi shiruuu, ita kad’ai!
Sai ta d’an yunk’uro za tayi magana sai kuma ta koma ta yi shiru, dan ita ba ma ta san ta ina za ta fara ba.

Su dai su Hudan ido kawai suka dinga binta da shi
kafin Huda ta yi k’arfin halin cewa
“Aaima lafiya kuwa?”
Dan suma yanayin nata ya saka su a rud’ani.

Har ta yunk’uro za ta yi magana kamar farko
sai kuma ta sake yin shiru kafin tace “ina zuwa”
Ta fad’i hakan tana d’aukar wayarta.

Gallery ta shiga ta hau bincike har ta nemo hoton da take nema! Kamar za ta mik’a musu
sai kuma ta ce
“Bara in baku wani d’an tak’aitaccen labari……

Akwai wata k’awar mu
da muke department d’aya level d’aya d’aki d’aya da ita a Nile! Mu hud’u ne a group d’in mu, ni da ita da ragowar friends d’inmu su biyu
tun farkon zuwanmu tare muke har yanzu da muka zo k’arshe.”
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ci gaba
“Wadda muka fi shirin da ita
ita ce
‘Suhailat’
K’ut da k’ut muke ni da ita sosai.
Akwai wani saurayinta da suke tare tun farkon zuwanmu Nile
ta ce min tun a secondary school ta san Abokinsa
tare suka yi makaranta secondary
ajinsu d’aya!
To irin sun d’an shak’u d’innan kamar besties haka suke.

Wata rana Ina tunawa muna level 1 lokacin ya zo kawo mata ziyara (shi bestyn nata) sai suka zo shi da wani Abokinsa mai suna ‘Sageer’
Tun da Sageer ya kyalla ido ya ga Suhailat tashi d’aya ya ji yana sonta!
Kasa ma hak’ura yayi mu koma a lokacin dayake ni na rakata,
a take yake cewa Abokin nasa shifa ya ga mahad’in shi!
Bai bar wajen ba sai da number da address d’in gidansu Suhaila na nan Kano.

To ashe itama Suhailan duk kanwar ja ce
dan muna komawa d’aki itama ta haukace mun haka nan
ta dinga yabon kyawun Sageer d’in da had’uwar shi
sanann ta sanar da ni yanda ya samu kyakkyawan gurbi a cikin zuciyarta.

Kafin wata d’aya
Soyayya da shak’uwa mai zafi ta shiga tsakanin Suhaila da Sageer...

A Dawowar da nayi kafin exams lokacin bikinku da Ya Arshaad, kafin In koma wani mumunnan alamari ya afku ata dalilin rashin wayon Suhaila!
Ta biyewa soyayya
ta mallakawa Sageer kanta
gaba d’aya bayan ya
d’auketa sun je sun yi court marriage sai kace wasu marasa mafad’i!
A cewar sa hakan zai sanya ta yarda da shi ta aminta ita zai rayu da har abada tunda ita a tsarin gidansu
Mace sai tayi phd tukunna take yin aure!
Haka nan Babansu yake da wannan muguwar ak’idar,
shi kuma Sageer ya ce ‘in dai ita kad’ai zai so kuma ita kad’ai zai aura zai kula
to ya kamata ta fahimci a yanayin tsarin halittarshi ta d’a Namiji ba zai iya yi mata wanann dogon jiran ba’.

In tak’aice muku labari dai
ciki yana yin wata d’aya ya baiyyana kanshi a jikin Suhaila!
Dan tsananin laulayin da take yi ya sanya hatta
matan dake gefen d’akin mu sai da suka
soma fahimtar wani abu
game da wannan
k’addarerren cikin!
Dan ta ce babu kalar protection d’in da ba suyi using ba.

Ba yadda muka iya haka muka rufa mata asiri mu uku
muka nufi asibiti da ita
dan tace idan Baban ta ya san labarin wallahi na lahira sai ya fita jin dad’i!
Yadda kika ga Granpa to haka itama Babanta yake da mugun tsauri! Kuma ita abun nata ma duka biyu za a iya cewa
dan Mahaifiyarta itama hakan take da tsauri.

Muna zuwa muka zubewa Likitan kud’i muka gaya mishi flushing muke so a yi mata duk da tanata ce mana ance ‘tana da matsala cikin ba zai fita ba’ Amman still muka zab’i mu gwada sa’ar mu..
Bayan y’an gwaje gwaje
unfortunately
Likitan ya zaunar da mu yayi mana cikakken bayani akan cikin nan ba zai fita ba!
Saboda tanada matsala
kuma in dai ance za a cire d’in tou it’s either ta mutu
ko kuma ta samu uterus failure.

Bamu da wani zab’in da ya wuce mu nemi Sageer duk da kuwa ta ce mana ‘tun last zuwanshi da ta ce mishi tana da ciki
ya d’auke ta ya kaita asibiti aka gaya mishi abunda aka gaya mana!
Kwana d’aya kawai yayi mata a gidan da suke had’uwa
daga nan ya k’ara gaba
kuma tun daga ranar ko wayarshi ta kira a kashe take jin ta. Although bai nuna mata komai ba
dan faram faram ma suka rabu
ko amai idan ta yi shi yake kwashewa ya gyara gurin
yanata faman jera mata sannu’.

Wani babban tashin hankali da abun al’ajabin da muka fuskanta shine
Hatta gidansu Sageer da address d’insu da ya bayar a garin Gombe gaba d’aya fake ne!
Hatta sunan Babanshi
Alhaji Bashir mai galon da ya fad’a mana gaba d’aya k’arya ne. Har Gombe
d’aya a cikinmu ta rok’i saurayinta ya je
ya bincika mana
amman babu abu d’aya da yake gaskiya a cikin labarin Sageer!
Komai fabricating kawai yayi.

Da muka fahimci haka
sai muka koma wajen Bestien ta, to shima dai ta wajen na sa duk sammakal dan ce mana ya yi
shima Iyakar wannan information d’in da muka sani akan Sageer shima shi kad’ai ya sani, ya ce
a wajen ball suka had’u suka fara shiri
suka d’anyi business tare
ranar kuma suna tare ya ce masa zai je wajen k’awar shi shine yace zai rakashi.
Shi bestyn nata ma
cewa yayi
wai ‘mu yi ta addua gaba d’ayan mu
maybe aljani ko maye muka had’u da
Allah ya tak’aita’.”
Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e sannan ta ci gaba da cewa
“To yau dai Allah ya had’ani da Sageer!”
Bata gama rufe bakinta ba ta mik’a musu hoton data nemo a wayar tata tun d’azu………

Sakina ce ta fara karb’ar wayar
tana kallonta kafin ta sauk’e idonta a kan wayar.

A hankali Huda ta ce
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Bayan itama ta l’eka ta gani.

Sakina kuwa lumshe idonta kawai ta yi ta bud’e
ta kalli Aaima idonta jazir tap kwalla ta ce
“Aaima are you sure??”

“Very sure Sakina!
Ki yi ta sliding za ki ga pictures da videos d’insu kala kala irin wannnan shi da Suhaila.

Daga nan ki gaya min Idan wannan bawan Allahn ba Ashraff bane ba.”

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
69

Mikiya Writers Association.
Kai kana ganin fuskokinsu ka san suna cikin tashin hankali ba na wasa ba.

Kallo suke suna sake kallan pictures d’in amman ba ta inda za su ce ba Ashraff bane ba.

A hankali Sakina ta mik’a mata wayarta sannan ta ce “yana Ina?”
Ta yi mata tambayar tana k’ok’arin mik’ewa tsaye.

Cikin ruk’o hannunta Aaima ta ce
“Ya tafi”
Sannan ta d’aura da cewa
“Mai aiki nasa taje har chan waje ta shigo da shi parlourn Mammy.
Abunda ya bani mamaki ya kuma d’aure min kai
shine
yadda ya nuna kamar irin kwata kwata babu alamun yama tab’a ganina d’in nan
sannan kuma he looks calm and innocent!

Kasa hak’ura na yi bayan mun gaisa na ce mishi
“Sageer”
Amman sai na ga yana kallona da mamaki!
Ganin da nayi ban ma san abunyi next ba yasa kawai na ce masa ‘ya tafi, dan Allah yayi hak’uri wani abun ya taso min urgent!’
Cikin fahimta ya nuna min ba damuwa ya mik’e ya tafi.
Sakina kaina ya d’aure saboda a ganina inda ace Sageer d’in ne to da ko a idanunsa zan fahimci firgici! Da d’an alamun wani abun dole zai nuna amman kuma
ko twins banajin za su iya zama super identical haka kamar shi da sageer..
Hatta fa yanayin magana kallo tafiya komai nasu iri d’aya ne..”

Cikin katseta Sakina ta ce
“Kar ki damu Aaima, ba wani
Sageer
sunanshi Ashraff!
Shine!
Raina miki hankali kawai yayi.
Ga Abokin sa nan ma Abbakar a wanann hoton.”

Da sauri Aaima ta karb’i wayar ta kalla sai kuma ta ce
“Ai shine Saddik d’in”

“Hmm”
Kawai Sakina ta ce tana
mai dialing numbershi a wayarta.

Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e kafin tace
“Kuma kin san abunda zai sa ma mu sake gasgata shi d’in ne…
Ranar farko da suka fara zuwa
a ranar da ya had’u da Suhaila
da ya ce mata
‘I’m Sageer by name’
Sai da Abokin nashi ya juya a zabure yana kallonshi
sai kuma na ga ya fara murmushi yana girgiza kai.”

Dede nan Ashraff ya amsa call d’in Sakina…
Daman a handsfree ta saka
“Hello baby”
Suka ji ya fad’a.

Sai da Sakina ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ta ce
“Ashraff ko Sageer?”

“My god!!
Waye ne Sageer d’innan ne?
Kin san i was just about to call you sai kika kira…
That cousin of yours
she looks confuse!
Tana ganina ta ce min Sageer itama.
Ask her ta yi miki bayani please dan i d.........”

Cikin katseshi ta ce
“Dakata Ashraff!
Ba ita bace confused, ni ce!
Bayani kuma ba ita za ta yi min ba kaine!.
So I’m all ears
Ina so inji
ta yadda ka chanja sunan ka
da kuma yanda kake planing zaka yi da mu
Ni da Suhaila da kuma d’an cikinta”

“Oh Noooo!
Innalillahi wa innailaihirrajiun
Sakina haba mana.
Tana ina ita cousin d’in taku?
Bata wayar please…
Wallahi daman yadda na ga tayi na san akwai matsala,
waye Sageer? Wacece Suhaila? Ciki kuma a Ina?.
Sakina na riga na gaya miki y’an mata biyu kawai na yi dating b4 you
and duk na nuna miki pictures d’insu, please Sakina
kar ki biye mata
i think akwai confusion a lamarinta
amman wallahi ni ban san wani Sageer ba,
bata wayar please”.

Fashewa kawai ya ji Sakinar ta yi da kuka, cikin kukan ta ce
“Haba Ashraff!
Despite abunda ka yi da k’aryar da ka yi
still kana so ka ci gaba da b’oye b’oye?
Wat have i ever done to you to deserve this?”

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” kawai ta ji yanata maimaitawa kafin ya ce
“Shikenan Sakina,
na gane! Yanzu na fahimci komai…
Kina neman hanyar da za ki zillemun ki auri Auwal d’in da kike ta tunani kullum ko?
Ko kina tunanin ban saniba ne?
Idan ba kya sona ki fito fili kawai ki gaya min ki daina yi min kwana kwana!
Bawai ku had’a baki ba
ku k’ulla min sharrin abu mai muni haka ba.
Wallahi tallahi kin ji de na rantse miki
ni ban san wani Sageer ba
ban san wacece Suhaila ba
sanann wallahi Sakina da gaske nake sonki ba yaudara a ciki! Ke kad’ai ce a cikin zuciyata”
Ya fad’i haka yana me fashewa da kuka kamar k’aramin Yaro
sai kuma ta ji ya kashe wayar, kiit!.


Ashraff, yana kashe wayar ya kira Saddik yana d’auka bai jira jin me zai ce ba
ya ce
“Saddik, I’m doomed….”
Sanann ya hau koro mishi bayani hankalinshi a mugun tashe.

Shiruu Saddik d’in yayi
bayan ya gama ji
kafin ya ce
“Listen closely Ashraff..................”


Gaba d’ayansu hankalinsu a tashe yake, bama su san ta Ina za su fara ba.
Aaima ce ta yanke shawarar kiran Suhailar dan haka ta d’au waya ta shiga sunanta ta danna call……

An fi thirty minutes tukunna aka samu layinta ya fita daga busy ta amsa kiran Aaiman.

Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e kafin ta ce
“Da wa kike waya haka?”

Sai da ta d’anyi jimm! Tukunna ta ce
“Wata friend d’ita ce”

Shiruu, Aaiman ta yi tana tunanin wacece k’awar Suhaila haka da bata san ta ba…
Sanin ba wannan ne a gabansu ba
ya sa kawai ta kawar da zancen ta hanyar bata labarin Sageer Ashraff from A -Z kafin ta ce
“Yanzu ko gidan su idan kinaso zamu iya zuwa dan Sakina ta ce ta san gidan
kuma zata bamu adress har number Mamansa.”

Cikin katseta Suhailan ta ce
“Mun gama case d’in Sageer fa!
Ki manta kawai please, kar ki
sake yi min maganarsa”

A rikice Aaiman ta ce
“Kin gama case d’insa da cikinsa a jikinki??”

“Please Aaima”
Shine kawai abunda Suhaila ta ce.

Aaima za ta yi magana kawai ta ji ta katse kiran.

Kasa cire wayar daga kunnenta Aaiman ta yi,
da kyar ta d’ago tana kallonsu still da wayar kare a kunnenta.

Kirane ya shigo wayartata
dan haka ta d’an zabura saboda a kunnenta wayar take har yanzu…
Tana ganin mai kiran nata ta d’auka da sauri ta ce “yauwa Khadija kin san me yake faruwa?
Yanzun nan....”

Cikin katseta Khadijar ta ce
“Sageer, yanzun nan ya kira Suhaila….
Suna fara magana ta tashi ta shiga bathroom, haka
kawai na ji inaso in yi mata lab’e saboda na san kusan wata nawa ana neman shi
sai yau kawai muga ya kirata.

A yadda na fahimta
Its like akwai wadda zai aura a yanzu! Wai family d’insu
sun zab’a masa
shiyasa ma ya d’auke k’afa
amman yayi mata alk’awarin aure nan da wata biyar
muddin ta yi shiru.

Ban gama dawowa daga mamaki ba
na ji conversation d’in ku a waya yanzu.
Meyene yake faruwa?”.

Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e rai a b’ace ta ce
“Wato shine Ashraff d’in ta tabbata kenan!…”
Nan ta d’an yi briefing Khadija a kan case d’in sannan ta ce
“Khadija Suhaila tana son
Ashraff
ba zata tab’a iya k’etare umarninshi ba!
Dan haka yanzu aiki yana a hannunki..
Ki taimaki y’ar uwar ki
tunda ni dai kinji yadda muka yi da ita.
Zan turo miki number Mamansa yanzu
daga nan ki kirata ki yi mata bayanin komai!
Lokacin b’oye b’oye ya wuce
dole iyaye su shiga case d’innan.
Mugun tantiri ne Ashraff d’innan wallahi! Kin san yadda ya nuna kuwa kamar bai sanni ba amman kalli har ya kirawota munafuki d’an iska!
Kuma wallahi k’arya yake yi
shi ya ga Sakina ya ce yana sonta ba wani had’asu da akayi
Infact
Families d’insu ma basu san juna ba sai ata dalilin ita Sakinar da shi Ashraff d’in.

Wanne irin rashin wayone haka Suhaila take yi!
Dan bayan soyayya tabbas akwai dak’ik’anci a cikin lamarinta, saboda Allah ace wai Mutumin da yayi maka wannan abun
tashi d’aya ya dawo ya kalallame ka kuma ka yarda?
Duk da ban san me ya ce mata ba amman ai ya kamata ta tambayeshi dalilin da ya sa ya bamu fake adress ko?”

A hankali Khadija ta ce
“Tabbas”
Sannan ta ce
‘Ta tura mata number Maman ashraff d’in ta kirata yanzu ba sai anjima ba
kafin Suhaila ta dawo d’akin.”

Da “to” ta amsa sannan ta katse kiran
kafin ta kallesu ta ce
“Yayar Suhailan ce,
Itama ta san da zancen.
Ina number Maman nashi?”

Kamar yadda Sakina ta fad’a haka ta bada number Maman Ashraff bayan sun kwantar mata da hankali da kyar! Dan da cewa ta yi sai ta je ta sameshi a duk inda yake!
Hudan ma harda y’ar kwallarta ganin yadda Sakinar duk ta firgice ta fita haiyyacinta tana ta kuka wiwi.
Gaba d’aya sun gigita da lamarin Ashraff. ..........


Suna zaune a d’akin wata maid ta shigo musu da abinci kala kala..
Aaima da Huda ne suka d’an ci
Sakina kam har yanzu hankalinta a tashe yake,
ashe ita ta yi gudun gara ne ta tadda zago
ba tare da ta sani ba…


Sai bayan sallar Magrib tukunna Junaidu ya kirata ya ce “taje yana waje, su wuce.”

Aaima ce ta rakata har bakin mota bayan sun sha kukan su ita da Huda
sannan sun d’an yi mata y’ar guntuwar Nasiha suma, dan itama Aaiman ba komawa za ta yi ba sunyi sallama kenan
saboda
ta san Huda tsaf sai ta rik’eta kamar yadda ta kanainaye Sakina.

Duk da halinda Sakina take ciki
sai da ta fahimci kallon da Aaima da Junaidu suke yiwa juna!
Tun d’azu dama da za a kawo Huda ta d’an lura
yanzu kuma ta sake tabbatarwa
dan har tana yiwa Junaidun magana ma bai sani ba.

Kasa hak’ura tayi bayan sun d’au hanya ta ce
“Ya Junaidu ko dai In had’aku ne?”

Wani lallausan murmushi ta ga ya yi kafin ya ce
“A’a fa Sakina,
tuwon girma ai miyarsa nama!
Idan na d’auko wannan ina da wajen ajjiyeta ne?”

Da sauri Sakina ta ce
“Ya Junaidu
ranar nan fa na ji Kaka yana cewa Gidajen ka wajen biyar a Kano kawai ga motoci
ga filaye.”

Dariya ya yi this time around
sanann ya ce
“Ki bar maganar nan..
Although har ga Allah i felt something
towards her
very strong
amman tunda na rasa Huda
i don’t think zan yi aure
idan ma zan yi d’in to
gaskiya ba nan kusa ba.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e
tana kallon yadda fuskarsa ta chanja
lokaci guda.
Daga haka motar ta d’auki shiruuu
kowa da abunda yake sak’awa a ranshi, har ya kaita k’ofar gidan nasu ya ajjiyeta.

Tana sauk’a yayi reverse ya juya dan akwai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login