Showing 87001 words to 90000 words out of 100703 words
Chapter 30 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt
ta na Isa gareta ta sa hannu ta yi hugging d’inta ta ce “congratulations”.
Ajiyar zuciya kawai Mama ta sauk’e daga nan d’akin ya fara cika da jamaa..
Banda hayaniyar mata babu abunda ke tashi.
Suna cikin hira
suka ji d’aurin auren Jalila itama, nan take kowa ta hau tofa albarkacin bakinta
wasu su ce “Allah shi k’ara” wasu kuma su ce “Ai ta ma yi sa a data auri Abdullahin,
Mutum mai kirki da hankali da zuciyar nema
wallahi ta tsinci dami a kala...”.
Kowa idan ya ga Abba a wajen d’aurin auren nan tashi d’aya zai san yau d’in fa yana cikin farin ciki. Ba shi kad’ai ba hatta su Granpa idan ka gansu fuskokinsu tap! Cike da annuri.
Ba a jima ba suka shiga parlourn Madu aka yi musu hotuna suka wuce bayan sun ce “nan da anjima in an d’an watse Abba zai dawo ya d’auki Amaryar shi da kanshi.”
Madu ya ji dad’in hakan dan dama shima ya gama deciding
akan ‘ba sai an yi wani reton kai Amarya kamar wata Yarinya ba’.
Hakan kuwa aka yi,
Hudan ta so tsayawa amman awa uku kawai Aslam ya bata daga nann ya dawo ya d’auketa a cewarshi ‘gidan yayi mishi girma ya kasa shan ko ruwa tunda ya koma’…
Tunda ta ji haka dama ta b’aro jirginsa! Dan haka ta yi murmushi kawai ta girgiza kai tana mamakinsa.
Tunda aka idar da sallar Magrib Abba ya shirya tsaf!
Ana idar da sallar isha ya kama hanyar gandun albasa bayan ya samu Dad ya cika shi dakyar dan da farko rik’esa ya yi ya ce “akwai wani important aiki da zai tayashi
dan Allah”
Kamar Abba zai yi kuka haka ya yi mishi sai kuma ya ga Dad d’in yana dariya k’asa k’asa
dan haka ya gano tsokanace!
Amman dukda haka sai da ya yi da gaske tukunna Dad d’in ya cika mishi riga ya wuce mota Dad d’in kuma ya nufi gidanshi yana dariya……….
Yana zuwa ya tadda Madu zai shiga gida ya fito kenan daga masallaci dan haka suka shiga tare har parlourn Shuwa.
Nan Madu ya d’au waya ya kira Kaka da Baaba Talatu
suka zo suka had’u suka yi musu Nasiha!
Daganan suka sanya musu albarka….
Sai da suka zo tafiya ne Mama ta ji kuka ya taho mata.
Murmushi kawai Baaba Talatu da Shuwa suka yi
daga nan Baaba Talatu ta mik’e ta k’arasa ta mik’ar da ita suka yi gaba
Abba shima ya yi musu godiya da fatan alkhairi ya bi bayansu…..
Da shi da mai aikin ne suka ja akwatunan Mama guda biyu da ta had kayanta a ciki
suka kai mota suka sanya mata a booth...
Har k’ofar mota Baaba Talatu ta raka Mama ta bud’e ta saka ta a ciiki tukunna ta ce “Allah ya miki albarka”
Tana mai rufe mata motar ta koma ciki.
Dede nan Abba ya shigo ya rufe motar ya kunna ta,
a hankali ya sauk’e ajiyar zuciya sannan ya juyo ya sa hannu ya jawota ya yi hugging d’inta wasu hawaye suna zubowa daga idanunshi..
Da sauri ta ce
“Abba mutane fa suna wucewa”
Tana mai d’an k’ok’arin janyewa.
Bai cikata ba sai da ya yi niyya tukunna ya matsa amman still yana rik’e da hannunta yana kallonta ta cikin mayafin da ta d’an ja.
Murmushi kawai ya yi yana sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya koma ya zauna rik’e da hannunta ya tada motar suka wuce.
Sai a sannan tukunna Baba ya share hawayenshi ya juya ya nufi cikin gidan Kaka yana ganin uku uku......
Tunda suka isa bakin estate d’in ta lumshe idanuwanta.
A hankali ya yi horn aka zuge makeken gate d’in suka shige ciki.
Direct gidan Granpa Abba ya nufa da ita.
Yana kashe motar ya d’an murza hannunta wanda tun d’azun da ya rik’e bai cika ba ya ce “Maryama”
Sai a sannan ta bud’e idon ta d’an juyo ta kalleshi.
Murmushi ya yi ya ce “mu je ko?”
Jinjina kai kawai ta yi daga nan ta fara k’ok’arin fita sai kuma ta juya ta ce “hannuna”
Sai a sannan ya d’anyi murmushi ya sakin mata hannun da kyar
ta fita da k’ofar dama shima ya fito…
Suna d’an yin gaba ta ga yana shirin kama mata hannu!
Bama ta san wajen su Granpa za su je ba
amman kawai ta yi gaba da sauri!
Murmushi kawai ya yi ya girgiza kai ya bi bayanta,
daga nan suka jera suka shiga a tare.
A parlourn su Granpa na biyu
suka samesu suna jiransu gaba d’ayansu har Mommy da Dad.
Tana shiga Mommy ta mik’e ta je ta yi hugging d’inta tana farin ciki…
A gaban Granpa ta fara durk’usawa suka gaisa ya yi welcoming d’inta
sannan ta k’arasa wajen Gramma itama ta yi welcoming d’inta ta saka mata albarka
tukunna Dad shima ya yi welcoming d’inta ya sanya mata albarka.
Daganan Granpa da Gramma suka bata gifts d’insu
Granpa ya bata fili a asokoro Grandma kuma ta bata sark’ar gold babba mai kyau da bangles d’inta da zobe.
Godiya sosai su Mama da Abba suka yi daga nan Dad shima ya bata nashi gift d’in kyautar mota har da Mommy aka hau godiya..
Sannan suka sake yiwa su Gramma godiya
daga nan suka yi musu sallama da Allah ya kiyaye hanya dan sun ce jirginsu 3:00am zai tashi......
A ranar dattijawan unguwa suka zo suka zo suka bawa Madu hak’uri sannan
da maganar ‘ya koma matsayinshi na mai unguwa’!
Da kyar kuwa da mugun kyar aka samu ya yarda ya karb’a
saboda shi a ganinshi komai ya wuce sannan yanzu tsufa ya kamashi amman sam suka k’i amincewa suka ce “Ai su basu da wani mai unguwa wanda ya chanchanta sama da shi”….
Tunda Abba yake bai tab’a ganin nisan dake a tsakanin gidan Granpa da Gidan da zai zauna ba sai yau!
Allah Allah kawai yake su k’arasa.
Suna shiga Mama taga abun mamaki..har da wata k’atuwar heart a tsakiyar falon an yi decoration, ita kam abunma ma sai ya bata kunya..kar wani ya shigo ya gani..
Ruwan furniture da electronics kuwa kamar ba a san zafin kud’in ba.
A chan sama ma d’akinsu Abba ya yi decorating sosai da red hearts
Ita dai Mama in banda murmushi ba abunda take yi
dan har ga Allah abun ya burgeta.
Idanuwanta suna kaiwa kan akwatuna dozen a take ta b’ata rai!
Da sauri ya kauda kai yana d’an murmushi.
Cikin rashin jin dad’i ta ce
“Abba cewa fa na yi ka barshi.
Ka san za ka yi shine mu kuma ka hana mu yin kayan d’aki?”.
Da sauri ya sa hannu ya toshe mata baki ya ce
“Maryam wallahi bani da energy d’in arguing yanzu, ba ri mu yi sallah ko? Mu ci abinci sai mu yi magana.”
Da “to” kawai ta bishi,
tana ta faman fushi suka yi sallar suka ci abinci.
Za ta ci gaba da mitar ya ce
“Bara inyi wanka sai ayi min mitar ko?”
Ya fad’i haka yana tattare wajen ya yi waje da sauri yana mamakin Mama da mitar ta har yanzu ashe tana nan.
Itama wankan ta yi ta nad’a laffayarta bayan ta chanza kayan da ta zo da su a cikin akwatinta.
Tana cikin nad’a laffayar ya shigo, ya tsaya a bayan ta.
Ko juyowa bata yi ba
ta ce
“Yanzu inda nice na nace sai na zo da kayan d’aki nasan ba zaka ji dad’i ba amman ni kalli ka yi lefe bayan an riga an gama magana,
sai kace wata Yarinya...”
A hankali ya juyo da ita ya ce
“Wallahi bana gane abubuwan da kike fad’a!
Na gaya miki bani da energy d’in arguing................”
EARLIER..
Wata razananniyar k’ara Umma ta saka mai had’e da ashar kamar wata mahaukaciya!
Jalila kuwa
gefe guda kawai ta koma ta zauna dab’ass!! Ta k’ame a waje guda sai kuma hawaye suka hau zirya wani na korar wani ba k’akk’autawa…..
Tabbas ko jiya sai da Abdullahi ya kirata, da ta k’i d’auka ya yi mata message yana cewa
“Gobe in shaa Allah zai yi mata kyauta surprise
na ban mamaki.”
Tsananin tashin hankali da bak’in ciki suka sanya kawai ta tafi ta sulale ta sume a wajen.
Da gudu Umma ta k’arasa kanta ta hau jijjigata
amman sam bata motsa ba!
Sai da Hansai ta d’ebo ruwa aka shek’a mata
tukunna ta farfad’o,
suna had’a ido da Umma ta fashe da kuka:
Kasa cigaba da kallon idon nata Umma ta yi, ta mik’e kawai ta ja hannun Hansai suka shige chan k’uryar d’aki.
Jakarta kawai ta d’auka ta cewa Hansai “yi mini kwatancen Dajinma!”.
A zabure Hansai ta ce
“Ke!!! Sadiya? Dajinma??
Gaskiya ni kam ba da ni ba!
Har me ya yi zafi haka?”.
Cikin katseta da sauri Umma ta ce “komai ma ya yi zafi!!!
Haba Hansai!
Sai kace ba kya gani?
Ki duba kiga Maryam da Huda sun fini ta ko wacce hanya
sannan tsabar Bashir d’an kutumar bura uba ne
Kalli a yadda ya aurar da Jalila
kuma auren ma da talakan tukuf!!
Dan nasan had’in sa ne wanan, shegen tsoho ya tsaneni ya tsane y’aata!
Tun da ya kafa mata k’ahon zuk’a sai da ya yi mata auren dolen tukunna hankalinsa ya kwanta!
Ai kuwa wallahi ba zata sab’u ba! Ko sadakin ba za mu karb’a ba wallahi sai ya sakar mini y’ata, ban haifeta dan ta je ta auri talaka ba wallahi..
Ki yi min kwatance ko kuma In tafi in nema. In ba haka ba mutuwa zan yi
kin san Allah takaice da bak’in ciki sai sun kasheni!!!!…..”
Cikin son fahimtar da ita Hansai ta ce
“Sadiya wajen nan ban da mayu da aljanu ba abunda suka cikashi!
Kumafa sai kin yi tsirara tukunna zasu saurareki!
Ke kad’ai a tsakiyar daji.”
Da sauri Umma ta ce “zan iya!!
Kwatance kawai nake buk’ata
ki yi mini
idan na je
ko me akace min inyi zan iya
muddin zan ga Maryam da Huda a k’ark’ashina
sannan basu fini da komai ba!
Haba mana!
sun fi kowa ne?
Kalli mazajen fa da suka aura
Hansai zuciyata zata buga ki yi min kwatance in wuce da wuri tun kafin Maryam ta tare a lalata auren sannan a sauwwak’ewa y’ata wannan auren talakan tukuf d’in ta auri Arshaad.”
Ajiyar zuciya Hansai ta sauk’e kafin ta ce
“Sadiya ni a ganina
gara dai aje wajen y’an saffa saffa da aka saba
susan abun yi, Dajinm......”
Wani uban ashar Umma ta k’unduma kafin ta ce
“Hansai kar ki kashe ni!
Malaman Ina ce sune suka bamu wannan hayak’in muka yi muka turnuk’e ko Ina?
Na tabbatar ya shiga gidan Madu ta shak’a kowa ya shak’a
ke har kwandila na tabbatar ya zagaya amman kinga an fasa auren Maryam da Abba?
Sannan
malaman ba su ne suka yi ta amshe kud’ad’en mu akan batun Jalila da Arshaad ba?
Kin tab’a ganin Arshaad ya yiwa Jalilan koda message ta waya?
Dan haka kawai ni kinga ki rabani da zancen malaman nan
ba zan iya ci gaba da kwasar takaicinsu ba duk y’an damfara ne!
Gara kawai ki had’ani da Aljani ko Maye wanda na san ba cuta ba cutarwa!!!…
Yi min kwatance maza maza inje ayi a gama kafin Maryam ta tare”.
Ta k’arashe maganar rai a masifar b’ace a gaggauce tana gyara ruk’on jalarta da mayafinta.
Ajiyar zuciya Hansai ta sauk’e sannan ta kalleta ta ce
“Zan iya kaiki wajen dan ba lallai ki gane ba, nima k’awarnan tawa
na tab’a rakawa
kuma zan gane..Ni na yiwa Mijina ita kuma kishiyarta
wadda ta b’ace b’at!! Har yau babu ita ba labarinta kamar yadda ta buk’ata.”
Wani shu’umin murmushi na tsantsar jin dad’i Umma ta yi.
A hankali Hansai ta ce
“Muje in rakaki,
sai ke ki shiga jejin ni kuma in jiraki a bakin kogin.”
“Na gode Hansai”
Umman ta ce
fuskarta tana baiyyana tsananin farin cikin da take ciki.
Laraba da Jalila suna parlourn a yanda suka barsu
suka zo suka wuce su.
Ce musu kawai sukayi “bara su je su dawo”
Ko Laraban basu gayawa inda suka nufa ba suka fice
suka kama hanya………
Sai da sukayi mota uku
da mashin biyu
tukunna suka isa bakin kogin dede ana kiran sallar Magrib.
Naira hamsin suka biya mai kwale kwalen
ya tura su ya kaisu bakin dajin
Umma ta shiga cikin dajin
Hansai kuma ta zauna a wajen itada mai kwalekwalen zaman jiran fitowarta
da alk’awarin zasu bashi naira d’ari biyu idan ya jira ya
fitar dasu.
Sauri sauri Umma take tafiya ita kad’ai a cikin dajin
dan tana so su yi su gama su koma koda wani d’an k’auye ne su kwana a hanya
saboda tasan tabbas komawarsu a yau ba zata yiu ba.
Wani kalan murmushi ta yi sakamakon hango dakali a zagaye mai kewaye da ruwa
a tsakiyar wasu dogayen bishiyu guda bakwai.
Already Hansai ta fad’a mata yadda zata yi dan haka ta kwab’e tik! Hatta zoben hannunta da y’an kunne sai da ta cire ta ajjiye ta cire takalminta ta nufi dakalin tsirara haihuwar Laraba.
Tana zuwa ta d’auki itace mai d’an tsini ta chaka a tsakiyar hannunta sannan ta bi
ta zagaye wannan ruwan da yake kewaye da dakalin tana mai d’iga jininta a cikin ruwan!
Tana gama zagayewa ta tsallake ruwan ta hau ta d’ale kan dakalin ta zauna.
Wata firgitatciyar k’ara aka yi da ta sanya jinta ya d’auke d’iff gaba d’aya!
Hatta Hansai da mai kwalekwalen sai da suka ji
dan haka a firgice mutumin ya ce “Kai! Kai!! Kai!!!
Maza mu bar nan basa k’aunar jininta!! Kar mu je abun ya shafemu, bara mu juya da sauri.”
Da sauri Hansai wadda itama k’arar ta mugun firgitata ta ce
“Ban gane basa k’aunar jininta ba?
Kamar ya?”
Kallon ta mutumin ya yi kafin cikin b’acin rai ya ce
“Au ku baku san sharud’an wajen ba kuka kwaso k’afa kuka taho?
To ni kam bada ni ba gaskiya!
Ba zaki sa a had’a da ni ba.”
Yana gama fad’in haka ya fara k’ok’arin juya kwalekwalensa.
Kuka Hansai ta saka kafin ta ce “Malan y’ar uwa ta fa?
Ya za ai In tafi In bar y’aruwata??”
Tsaki kawai ya yi kafin ya ce
“Kin san Allah in kika b’ata min rai kika yi min taurin kai har wani abun ya shafeni sai na kasheki!!!
In kuma kina son tsira tou
ki ja bakin ki ki yi shiru mubar nan tun kafin a jiyo mu!!
Idan Allah ya kaimu gobe da sassafe na san basa nan sai mu zo mu d’auki gawarta!”
Hansai na shirin yin magana cikin kuka wata mahaukaciyar iska ta hankad’o su dagasu har kwalekwalen nasu!
Da kyar ta tsayar da su a tsakiyar kogin ai kuwa da
mugun sauri mutumin ya cika inda suka kakkama saboda kar su zube ya hau tuk’a kwalekwalen ya kaisu bakin rafin…
Ko tsayawa k’ullewa bai yi ba
ya fita da guda
ganin haka yasa itama Hansai ta raka shi da nata gudun
dan ba k’aramin tsorata tayi ba.
A gidansa inda ya nufa ta kwana bayan sun sha artabu saboda da cewa yayi ba zata bishi ta ja mishi jalala ba dan ya lura dak’ik’iya ce......
Kamar yadda ya yi mata alk’awari
washegari da sassafe ya nemo mutane suka nufi wajen!
Har ita suka shiga wajen.
Anan kan dakalin suka hango Umma kwace k’afafuwanta a cikin ruwan ta gaba
Hannayenta ta gefe da gefe duk a cikin ruwan da yake zagaye da d’an dakalin
Gashin kanta kuma yana tab’a ruwan ta baya.
Da sauri suka k’arasa inda take suna isa Hansai ta fashe da kuka a mugun tsorace
ganin an kwakule mata idanuwa.
A cikin
Mutannen ne wani ya cire y’ar sharar jikinsa suka rufa mata suka yi waje da ita.
Har aka isa gidan Mutumin in banda kuka ba abunda Hansai take yi
duk a tunanin ta mutu
amman ana zuwa gidan da aka kawo ruwa matar mutumin tana wanke mata fuska sai sukaji tana magana k’asa k’asa.
Da sauri Hansai ta matsa sosai ta fara yi mata magana
tana cewa
“Sadiya me kike cewa?? Sannu sannu Sadiya, mai ya faru dake haka?”
Sam amsar da take bata babu kai!
Ita kuma Hansai ta dage sai magana take yi
tana d’an murna ganin y’ar uwar tata nada sauran rai.
Matar ce ta ce mata
“Bafa zata fahimceki ba.
Babban abun mamaki ne ma da aka sameta da rai, sai dai kuma ina yi mata takaicin a haka zata k’are rayuwarta
dan sam ba zata tab’a yin hankaliba.
Allah kad’ai ya san me da me ta gani
sannan
kin san suna d’auke hankali da kwakwalwa bayan sun cire ido.”
Cikin tsananin fashewa da kuka Hansai ta ce
“Na shiga uku!!!
Dan Allah idan akwai mai Magani duk inda yake ki yi min kwatance In kaita wallahi k’anwata ce.”
Sai da matar ta d’an k’ura mata ido tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce
“K’anwar ki ce amman kika kawota ga halaka?
Wacce iriyar yaya ce ke?
To bari kiji in gaya miki
tunda muke a k’auyen nan
kafuwar shekaru kusan d’ari!
Ba a tab’a yin wanda ya shiga wajen nan basu k’aunaci jininshi ba ya fito da rai!
Wasu kuma da aka k’aunaci jinin nasu ma za su je su dawo k’alau daga baya kuma kiga hankalin ya tab‘u!
Balle ita da basu k’aunace ta ba tunda gashi har idanuwan sun cire
ai kawai
ku rungumi k’addara dan ni bansan wani me magani ba gaskiya.
Ku samu ta warke daga wannan radd’ad’in kwakulewar idon, ku yi jinyar haukarta
Idan iyakar abunda ya sameta kenan.”
Tana gama fad’in haka ta mik’e ta yi gaba.
Hansai ta yi kuka ta yi kuka kafin daga baya
kawai ta sa aka taya ta ta kinkimi Sadiya bayan an sanya mata kayanta ta d’aura akan mashin.......
Suna isa wani k’auye ta ci sa’a ta samu motar kano direct!
Shata ma tayi
ta ce in sukaje gidan zata shiga ta d’auko masa kud’insa
saboda Sadiyar ta samu ta mik’e.
Har k’ofar gida ya kaisu.
Sai da ta rufe mata fuska da d’ankwali tukunna ta shiga ta kira K’asimu da Laraba.
Da taimakon drivern aka shigar da ita
K’asimu sai faman sababin tambayarta yake yi…..
Laraba kuwa tun daga yadda taga fuskar Hansai da kuma Sadiyar gabanta ya fad’i!
Shiyasa ta ma kasa maganar ko iya kama Sadiyar ma bata yi ba, yadda take a sandare ne ya sanya ta yi tunanin ko mutuwa ta yi shiyasa ana shiga gidan tun kafin a gama kwantar da ita akan tabarma ta fashe da kuka.
Jin kuka yasa Jalila wadda tun jiya Laraban ta b’oye ta a d’aki ta cewa su Baaba Talatu ‘ta gudune itada Sadiya’ ta fito!
Tana hango Sadiyar a kwance ta tafi jikinta ta fad’a ta fashe da wani matsanancin kuka.
Hansai bata tanka su