Showing 108001 words to 109746 words out of 109746 words

Chapter 37 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2958

yi, aikin rigar ciki da babbar rigarsu kuma na kalar kayan amman dark sosai
Sai hulunansu zannah bukar
d’in da suka amsa sunansu ZANNAH bukar! Amman kowa da design d’inshi, takalmansu
kuma na fata kalar ruwan goro masu mugun kyau da tsada iri d’aya.
Yayinda Auwal ke sanye da maroon shadda shima ya murza zannah bukar d’inshi mai asalin kyau da tsada.

Cikin girmamawa Aslam ya gaida su Abba
Daddy ne yayi dariya yace
“Kaga yau har da mu a y’an sneaking a shigo estate ko?”
Murmushi kawai Aslam d’in yayi. Kallonshi kawai Abba yake yi…
Ya manta when last da ya ganshi da manya kaya,
ba k’aramin kyau yayi ba,
har ga Allah Aslam ba wai favorite d’in Granpa bane kad’ai Har da shima Aslam ne favorite d’inshi!
Kawai dai shi d’in baya nunawa ne
Yaron akwai hankali da nutsuwa da sanin ya kamata
“Ina ma inama!
How i wish......”
Ya fad’i hakan a ranshi
sai kuma yayi saurin kawar da tunanin ya juya suka fara gaisawa da Dad.
Daga shi har Daddy ba wanda ya kalli ko inda Mammy take
Kuma sarai sun ganta dan har had’a ido suka yi da Abba!
Hakan kuwa ba k’aramin sake ingizata yayi ba
Tabbas yau sai ta nuna musu ta isa wallahi!

Chap!! Arshaad ya shirya dan haka suma duk suka mik’e
dan har an fara jera musu kira
Abokanan su sun fara zxuwa venue d’in..

Ba tare da Mammy ta motsa ba tace
“Arshaad!”

Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya juyo yace
“Na’am Mammy”

Mik’ewa tayi tsaye tace
“Koma ka zauna”

Sannan ta dubi su Dad waenda suke kallonta gaba d’ayansu tace
“Kuna iya wucewa
ku tafi!
D’a dai ni na haifa ko?
To wallahi tallahi ba wanda ya isa ya yi mini iko da shi!
Da kuka shigo kuka wani banzatar dani kamar baku ga mutum ba saboda ban kai ba
har kai Abba! Kalla Auwal shima
Aslam ne kawai ya gaidani ya kulani a kaff d’inku
saboda ka riga ka nuna musu bani da mutunci bani da daraja a idanunka!
To
Yanzu ni kuma zan nuna muku na isa dan wallahi ba za a d’aura auren nan ba kaji dai na rantse!”

Murmushin takaici Dad yayi
kafin yace
“Dole ba wanda zai kulaki mana Rukayya!
Saboda kema baki kula wanda ya kamata ki kula ba,
ko kin gaida ni tunda na shigo?”
Ganin ta kauda kanta gefe ya sanya kawai ya girgiza kai kafin yace
“Kaga Arshaad wuce mu tafi!
Zan ga wanda zai hanaka fita yau”

Mammy ya kalla, suna had’a ido tace
“In dai kana neman albarka a auren nan to ka sani ba zan tab’a saka maka ita ba!
Kuma wallahi Arshaad in dai ka fita a d’akin nan
to ban yafe maka ba!”

Da k’arfi ya runtse idanuwanshi yana ji kanshi na mugun sara mishi.

A zafafe
Dad ya yunk’ura zai yi magana

da sauri Daddy ya katseshi ta hanyar cewa
“Dan Allah dan Annabi ka kyaleta,
Uwa ba abar wasa bace ba!
Dole Arshaad da Huda suna buk’atar albarka ta
Dole.”
Yana gama fad’in haka ya juya ga Mammyn yace
“Mammy mu tsaya mu fahimci juna, wannan maganar bata tasoba.
Ki duba shi kanshi Yaron naki mana za fa ki cutar dashi saboda son zuciyarki
sannan da ita kanta Hudan,
babufa abu mafi gorantawa a rayuwar y’a mace
kamar azo aurenta a fasa!..”

Cikin katseshi Mammy
tace
“Yi mini shiru Yusuf!”
Sai da Daddy da Auwal suka d’an zabura jin yanda ta kirashi .
Bata damuba taci gaba
“Babu maganar sulhu fa a tsakaninmu!
Maganace na riga na yita na gama, babu kuma uban wanda ya isa ya sanya ni in chanja wallahi!”
Cikin tsiwa da masifa tace
“Kuma kar ka wani ce mini In duba rayuwar wata Huda dan babu abunda ya shafeni da ita!
Allah Ubangiji yasa a yi ta mata gori a had’a har da kyama da hantara daganan har k’arshen rayuwarta wannan ba damuwa ta bace ba.”

A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi.
Ba tare da Abba ya kula kowa a cikin su ba kawai ya juya ya fita, da sauri Aslam ya bi bayanshi.

Takawa Dad yayi ya tsaya a gabanta sannan yace
“Rukayya bani da ishashshen lokaci!
Ki nutsu ki shiga hankalinki kiyi abunda ya dace, for the last time ina mai shawartarki
ki ajjiye wannan haukar ki bari a d’aurawa Yaron nan aure.”

Cikin katseshi ido cikin ido ta kalleshi kafin tace
“Yahaya! Ko da ace ka bar nan ka tafi kai kad’ai ba tare da Arshaad ba
Wallahi muddin ka d’aura mishi aure da Huda wallahi tallahi billahilazim sai na tsine mishi!”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kawai ba tare da yace mata uffan ba ya juya, har ya kai bakin k’ofa
sai kuma ya juyo yana kallon Arshaad wanda shima shi d’in yake kallo
Wani mugun tausayinshi ne ya lullub’e shi lokaci guda, a hankali yace masa
“ka zauna, kar kaje koina bara muje mu dawo .”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita, su Daddy ma suka bishi a baya.
Abba ko Aslam bai tsaya jira ba ya shiga motarshi suka yi gaba tare da su Shuraim, dama suna ciki anan suka barsu.
Aslam na shrin shiga motar shi shima yabi bayan Abba su Dad suka fito
“Wuce mu tafi masallacin”
Haka kawai Dad yace mishi daganan kowa ya shiga motarshi sukai gaba.

Aslam ya dad’e a tsaye so yayi ace ya bi bayan Abba
dan ya san definately gida ya koma, saboda yaga yadda ranshi yake a b’ace!
Ga shi daman shima so yake ya zille maybe he can use this as an opportunity.

Har zai bishi sai kuma kawai ya yanke shawarar bin bayan su Dad d’in.
Da kyar ya iya tada motar dan yafi minti goma a ciki a zaune bayan ya shiga d’in, daga
k’arshe dai ya tada motar ya fice daga estate d’in…..
A hankali yake driving, babu
nisa sosai dan haka mintuna k’alilan ne suka kaishi masallacin.

Da mamaki yake kallon motar Abba a parke a harabar masallacin!
Kokwanto ya hau yi akan anya kuwa motar tashi ce?
Sudais da ya gani ya nufo shi ne ya tabbatar mishi da Abban nan ya yo..
Chan kuma ya hango suna gaisawa shi da su Madu
cikin tsananin farin ciki da nishad’i.
Auwal ne ya dafa shi dan haka yayi saurin juyowa
Kwata kwata in banda k’unci da firgici ba abunda ya hango a shimfid’e kan fuskar Auwal d’in!
Yana mamakin abunda ya sanyashi a wannan yanayin yaji yace
“Aslam dan Allah idan sun zo kace......”
“Ku wuce muje mana!
Ya naga kun tsaya anan?”
Muryar Dad ta katsesu.

Kallon Auwal d’in yayi ya kalli Dad sannan yace
“Ok”
Kawai, ya juya ya yi gaba….
Duk taku d’aya ji yake kamar yana kusanta kanshi da kabarinshine!
Tabbas badaban Mommy ta rok’e shi akan ya zauna a garin nan ba to da tuni baya nan!
Babu yadda bai yi da ita ba d’azu amman nan ma
furr! Ta ki yarda, ta nace
ta tilastamishi dole sai da yazo wajen nan!
He might look calm
but tabbas ya san ba lalle k’afafuwan shi su iya fitar dashi daga masallacin nan ba!
Wannan wacce iriyar k’addara ce?
Mai yasa yake jin hakan har yanzu?
Mai yasa yake jin haka?
Garin yaya ya bari hakan take faruwa da shi…..?
A hankali yaji Abba yace
“Aslam”
Firgigit! Haka yayi
hankalinshi ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, sai
a sannan ne ya ga yana daff da yin karo da bango ashe,
da sauri ya ja burki!
Sannan ya juyo da kanshi yana kallon Abba wanda yake matsowa daff da shi sosai.

A hankali ya kama hannunshi ya d’an jashi gefe..

Da d’an murmushi akan fuskarshi yana mai kallonshi sannan ya fara magana
“Watak’il yau in yi maka laifi!
Amman dan Allah Aslam ko menene ya faru karka bad’a mini k’asa a ido”

Da mamaki yake kallonshi
zuciyarshi tana dukan uku uku!
Dan a take a yanzun tunani d’aya ne kawai ya fad’o mishi
daga jin furucin Abba na yanzun!
Da mugun sauri ya fara kokawa da zuciyar shi yana k’ok’arin kawar da tunanin
dan jiya ma ba k’aramin artabu ya sha ba! Ko rintsawa bai yi ba
ata dalilin false hope d’in da Mommy ta sa ya d’aurawa kanshi.

Dafa shi Abba yayi sannan yace “mu shiga”
Yana gama fad’in haka ya wuce ciki.
Da kyar Aslam ya iya jan k’afafuwan shi, ya shiga ya nemi waje ya zauna kusa da Abba daff da liman da su Daddy Opposite Auwal.

Kana ganin Auwal tashi d’aya zaka gane bashi da nutsuwa kwata kwata!
Ko zaman kirki ya kasa yi a wajen, sai zaro waya yake da alamun kira yake yi
amman kuma ba a d’auka!
A fili sannan da k’arfi
yace “damn it!!”
Sannan yayi jifa da wayar tashi
wanda hakan ya janyo hankulan mutane kanshi….
Suna had’a ido da Daddy ya zabga mishi harara.
A hankali ya sunkuyar da kanshi ya d’au wayar sannan yace
“Sorry”.
Hannu Dad ya mik’a mishi alamun ya bashi wayar!.
Ba musu ya mik’a mishi
shi kuma ya sa hannun ya karb’a ya saka ta a aljihu
daga nan aka fara gabatar da d’aurin aure……..

Auwal k’ok’ari yake yi su had’a ido da Aslam sai dai kuma Aslam d’in yak’i d’ago da kanshi kuma kamar ma idanuwanshi a rufe suke.

A bangaren Aslam kuwa
zai iya cewa ya jima bai shiga irin wannan tashin hankalin a rayuwarshi ba!
Mai yasa ya yarda yazo nan?
Wanne irin heartbreak zai yi facin?
Yanzu kenan a gaban idanunsa yana ji yana gani za ayi komai....
“Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun....”
Ya furta a hankali sosai!
Baya ganin komai zuwa yanzu
shiyasa ya runtse idanuwanshi kawai yana jiran lokacin
da zai farka ya ganshi a gadon asibiti ko kuma yaji
ance mishi
Man rabbuka?!…..

Yana jin su sama sama
Daddy ya gabatar da kanshi a matsayin waliyyin Amarya
Dad kuma a matsayin waliyyin Ango!

Da k’arfi zuciyarshi ta buga jin limamin yace
“Waliyyin Ango yana nemawa Yakubu Aslam auren
Maryam Huda!”

Bud’e idanuwansa yayi tarr!!! Ya fara ganin komai.
Kaii inaa bai ji da kyau ba!
Ko kuma dai
sunan waliyyin Amarya aka ambata dai ko wani abun daban….

Da sauri ya d’ago jajayen idanuwanshi yana kallon Daddy jin yace
“Mun bayar”

Limamin kuma yana cewa “sun yarda cinta shanta suturarta komai ya koma hannunsu?
Hannun Yakubu Aslam.”

Bai gama fita daga shock ba
Yaji Dad yace
“Mun yarda!
Mun karb’a!”

Zuwa yanzu gaba d’aya jikin Aslam in banda karkarwa ba abunda yake yi gashi ya had’a wata uwar zufa! Tashi d’aya.

Tun daga nan kanshi ya kulle
jinsa ya d’auke!
Binsu kawai yake yi da ido
suna gudanar da d’aurin auren!.
Yana kallo Dad ya zaro kud’i ya mik’awa Daddy!
Limami ya sanar shedu suka shaida…

Jin shi bai tashi dawowa ba sai da muryar limami ta fara tashin amo a cikin masallacin
“Alhamdulillah!!!
An d’aura auren
Yakubu Yahaya Umar Faruku MT Aslam
Da
Amaryarsa
Maryam Yakubu Huda
akan sadaki naira dubu d’ari biyu!
Lakadan ba ajalan ba.

BULAMA ✍️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login