Showing 99001 words to 102000 words out of 109746 words

Chapter 34 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2966

a tashe yake dauriya ce kawai take yi, tana kuma k’ok’arin taga ba wanda ta bari ya ma ji zancen har a samu a gyara lamarin in sha Allah.
Ganin arshaad d’in bashi da niyyar amsa ta ne
yasa kawai ta kira Auwal
dan taji me ke faruwa
a ina aka tsaya..

Shi sai a bakinta ma yake jin wai ‘Arshaad d’in bai je ba’
Saboda shi suna asibiti.

Ganin kamar bai san me yake faruwa ba ya sanya taja bakinta tayi shiru
saboda ance yawan yayata magana kan iya tabbatar da gasgatuwar ta. Dan haka kawai sai tace mishi
“ya duba musu Arshaad din pls”
Daga haka suka yi sallama.

Daman shima yana da shirinshi zai je wajen
So yanzu zai duba Arshaad d’in sai su wuce tare kawai
dan haka ya cewa Dad
“Bara yaje gida,
Sakina ta kirashi wai har yanzu Arshaad be k’arasa ba.”
“to” kawai Dad d’in yace masa.
Yana fita shima Dad din ya d’au waya ya kira Gwaggo Asabe yace
“Dan Allah tazo ta ji da Ummi.
Zai yiwa drivern da zai kawota kwatancen asibitin da suke....”

Drivern da ya kawota (Gwaggwo Asabe) shi ya maidashi mansion d’in.
Yana zuwa ya tarar da Daddy
ya shirya chap yana jiranshi
da akwatuna dozen biyu sun sha decoration
sai kuma basket na gift guda biyar, da akwatunan uwa uba gwaggwo da kawu..
Duk sun had’a. Tun sassafe Mommy ta aiko da kayan
shi kuma ya duba ya tabbatar komai dai dai.

Sai da aka gama loda kayayyakin a motoci wajen goma tukunna Abba ya fito da shirin shi shima da alama rakasu zai yi!

Dad, yana shirin shiga mota har driver ya bud’e mishi k’ofar motar ya hango tahowar Abba!
Wani takaici ne ya d’ebesa
bai san lokacin da ya daka masa tsawa ba! Yace
“Idan ka k’araso nan wallahi sai mun kwashi y’an kallo ni da kai!
Kaji dai na rantse
wallahi!!”
Ya k’arashe maganar yana mishi nuni da yatsar shi manuniya yana nuna sama.

Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e kafin yace
“Dad nimafa rakaku zan y....”

Cikin fushi Dad d’in yace
“Kaga mota nan, zo ka shiga!
Amman direct
Asibitin da aka kwantar da Ummi zaka je
Idan kuma ba haka ba to ka koma ka zauna a ciki.
Zab’i d’aya!”

idanuwa direbobin da masu aikin suka tsura musu..Ganin da Abba yayi har sun fara kwasar y’an kallon kamar yadda Dad d’in ya ambata ne yasa kawai ya juya ya koma ciki ranshi a mugun b’ace!.

Tsaki Dad yayi ya shige motar
yana mai cewa
“Ba za ku haukata ni ba,
wallahi!”.

Shi dai Daddy
shiga yayi ya zauna a kusa da shi, yana son tambayarshi
wata zuciyar kuma sai ta bashi shawarar ya bari ya Dad d’in ya d’an sauk’o tukunna sai suyi magana…
A haka drivern ya ja su suka nufi Gandun Albasa
Daddy yana mamakin meye haka yake damun Dad??
Dan tabbas ya san akwai abunda aka yi mishi......


GANDUN ALBASA.
Baaba Talatu tana fita harabar gidan ta tarar gurin har ya fara kachamewa!
Dan bayan Sakina ta bar wajen Umma da Anty Zainab kan Ummu suka dawo
wai “ai itace bata yi mata tarbiyya mai kyau ba shiyasa ta raina manya har haka...”
Ga kuma wannan tsohuwa ita ma ta kafa ta tsare tace
“Sai Ango ya fito tukunna za a fara gabatar da komai!”
Yayinda Ummu da wasu cousins d’inta suke ta k’ok’arin ganin sun yayyafa wa lamarin ruwa amman abun ya faskara!.

Baaba Talatu ce ta k’arasa ta ja wannan tsohuwar gefe suka had’u ita da Shuwa suna mata magana k’asa k’asa…
Ganin kamar ana shirin fara traditional event d’in
cikin kwanciyar hankali ne yasanya Umma ta sake cewa
“Nima fa kamar uwa nake a wajen Hudan!
Dan haka ba zan bari kowa ya tab’a ta ba har sai Angon nata ya k’araso..
idam kuma fasawa yayi ne to kawai a fito a fad’a wa mutane sai a fasa sakata a lallen,
dan ba girman mu bane mu tsaya muna yiwa mutane wasa da hankali!
Ko ya kuka gani?”
Ta k’arashe maganar tana kallon cousins d’in Ummu waenda suke gefen ta! Ba su kad’ai ba kusan kaff wajen babu wanda bai ji abinda tace ba hatta su Shuwa.

“Ga Angon nan”
Muryar Mommy wadda suka fito su uku yanzu ta daki dodon kunnuwansu!
Da sauri Mama da Aslam suka kalleta!
Ba tare da ta kallesu ba ta
kama hannun Aslam ta fara janshi
Mama na binsu a baya kamar rak’umi da akala shi kuma yana binta!..
Bata cikashi ba sai da ta kaishi gefen Hudan sannan ta zaunar da shi.

Da sauri Ummu ta matso k’asa k’asa tace
“Mommy a Al’ada fa dole sai Angon zai....
Cikin katseta Mommy tace
“A addini fa?”
Bata jira Ummu ta bata amsa ba ta sake ce mata
“Kalla nan kinga”
Tayi maganar tana
nuna mata Huda wadda sai a lokacin Ummu ta lura da yanda mayafinta ya jik’e sharkaf!
Wanda kana gani ka san ruwan hawaye ne…
Mommy bata jira jin me zata ce ba ta ci gaba da yi mata magana k’asa k’asa irin na masu hankali,
tace
“Saboda ita kawai ki bari ayi a gama!
Na tabbatar ba wai rashin zuwan Arshaad kad’ai bane ya saka ta kuka ba! Har da maganganun matar nan! Tun muna parlourn bayankun nan muke juyo komai.
Dan Allah kar kice a’a!
Kalla kiga mutane kowa ya zuba ido an fara k’ananun maganganu, na tabbatar in dai ba Angon suka gani ba to haka za a tashi ana gulmace gulmace shima kuma sai idan an samu waenchan matan sun bari anyi d’in kenan.
Na tabbatar mutane k’alilan ne kuma na jikinku sosai suka san ba Arshaad bane wannan, ba kowa ne zai gane ba
so dan Allah ki kwantar da hankalinki ayi abun nan a gama without any more dramas.
Saka lalle ai ba d’aurin aure bane ba, ba komai kawai bidi’a ce so mu bisu kawai ayi a gama.”
Tana gama fad’an haka ta juya ga jamaar wajen tace
“Kuyi hak’uri mun yi latti wani d’an uzuri ne ya tsaida mu!
Sunana Hajiya Aisha
Maman Ango, mun gode kwarai da zuwanku dan taya mu farin ciki.”
Daga nan ta juya ta cewa
Ummu
“Ni zan fara ko ke?”
Da murmushi kwance akan fuskarta.

Kallonta kawai suke yi
daga Ummu har Mama.....……


Mama da Ummu sun so hana mai video coverage da pics d’auka amman ganin yanda hankalin kowa yake a kansu
da kuma Mommy wadda tace ‘su bari kawai tunda ga wasu ma a gefe suna ta d’auka da waya’ ne ya sanya
kawai suka hak’ura.
K’awayen su Huda kuwa abun ba k’aramin d’aure musu kai yayi ba dan tabbas sun san wannan ba da shi akayi cocktail jiya ba, kuma ba shine a pre wedding ba!
A haka dai suka bar maganar akan in an tashi za suni komai a bakin Sakina....


Aslam kuwa so yake ya mik’e amman sam ya kasa!
Ya rasa dalili..tun da yake bai tab’a jin fargaba irin wadda yake ciki a halin yanzu ba!
Ana cewa k’afafuwa da gangar jikin mutun suna sagewa ya koma kamar gunki bai tab’a yarda da hakan ba sai yau da ya faru a kansa dan hatta kwayar idanunsa ya kasa juyawa, so yake ya runtse idanuwanshi ya samu ya dedeta zuciyar shi amman sam ya kasa!
Yana nan a haka yaji Ummu na rufa mishi wata jibgegiyar alkyabba akan jamfar jikinshi
Akan hular kanshi
Ummu ta d’aura mishi wani jan kyalle mai tambarin moon a gaba golden colour
(Allah yaso suna da extra)
Daga nan ta mik’a mishi wata sanda wadda ta ci ado! Tace masa “ungo, rik’e”
Mommy ce ta kama hannunshi ta sanya mishi
sandar sannan ta had’a da nata hannun ta maste!
Sai a lokacin ya samu nasarar lumshe idanuwanshi
sannan ya d’an bud’e su kad’an yana kallon k’asa....

Ba tare da b’ata lokaci ba aka fara gudanar da alada……..
Bayan uwar Amarya da uwar Ango sun yi, ragowar jama a suma suka zo suka sanya musu suka basu gift
daga nan aka fara serving abinci.

Sai a lokacin Anty Zainab da Umma suka samu suka iya zama…Umma so take yi ta sake mik’ewa tsaye tace
“To Ina y’an unwan Ango!?” ta sake creating scene amman sam ta kaasa dan in banda
dishi dishi babu abunda take gani! A ranta ta shiga aiyyana
…..Tabbas sai taci uwar malan ado! Wallahi sai ta saka an yi mishi yasin mai walk’iya!
Ba Malami ba ko uban waye shi. Kuma sai ya bata kud’inta.
Jiya jiyan nan fa ta sake komawa wajenshi dan ta sake nanata mishi, shi kuma ya
tabbatar mata da “babu aure tsakanin Hudan da Arshaad
ya riga ya gama aiki
kuma ya buga k’asa ya tabbatar ba Mijin ta bane ba
sannan
ya ingiza zuciyar iyayen shi (Arshaad) ya rura wutar k’iyayyar Hudan a cikinta
ta yanda ba zasu tab’a bari ayi auren ba musamman ma Mahaifiyarshi (Arshaad)…”
Amman kalli yadda Maman nasa taketa jan Hudan a jiki,
anyi musu hoto yafi kala nawa tare sai faman fara’a take yi tana washe baki kana ganinta ka san tana cikin tsantsar farin ciki….Inaaaaa!!!!!
Taya ma zata tsaya ta yarda Hudan ta auri wannan
No1 kyakkyawan da ita tunda take a rayuwarta ko a telebijin bata tab’a ganin mai kyawunsa ba! Ga uban kud’i ga kyau kamar aljani
Allah sarki Jalilan ta
dole ta mutu akan soyayyar Arshaad, ai kuwa idan zata yi yawo tsirara wallahi sai ta raba auren Huda da Arshaad ko sama da k’asa zasu had’e
Wallahi sai dai in rabo ya kasheta akan dai ta zauna ta nad’i wannan abun takaicin da ta san k’arshe in dai bata d’auki mataki ba to shine ajalinta!
Kuma ko yana so ko baya so sai ya auri Jalila!
Wannan alkawari ne ta d’aukarwa Jalila da ita kanta!
D’an halal ka fasa……..

Anty Zainab ce ta tab’o ta
wanda hakan ne ya katse mata tunani.
Da kyar ta iya motsa wuyanta dan ji take kamar ba jini da rai a dukkannin ilahirin jikinta
Suna had’a ido taga itama Anty Zainab d’in idanuwanta sun kad’a sun yi jazir!
Kafin Umman tace wani abu
taji tace
“Sadiya taso mu tafi,
kai na ciwo yake yi min”

Suna shirin mik’ewa
suka fara jiyo gud’a daga parlourn Madu sai a sannan ma suka lura Shuwa da Baaba Talatu da wasu y’an tsirrun mutane basa wajen
A bakin matan wajen sukaji an fara k’us k’us d’in
“Ashe tun d’azu mazan gidan Ango suka zo sun kawo lefe yanzu suka wuce
da yake falon Madu yana da k’ofar shiga da fita ta waje, shiyasa har suka zo suka tafi ba wanda ya sani
Sai da suka tafi yanzu akace aje a fito da shi” Sunaji anata k’usk’us d’in “ai motocin da suka zo da su ma kansu abun kallo ne!
Gasu kana ganinsu kaga manyan mutanen da kud’i ya zaunamawa”

Da kyar Umma take iya jan numfashi, dan ji take yi gaba d’aya iskar wajen bata isarta!.
Ummu ce ta d’an matsosu kafin tace
“Umma kuzo muje a fito da lefen nan kowa ya gani ko?”

Anty Zainab ce ta iya ce mata “eh”
Itanma da kyar,
daga haka ta mik’e ta d’an dafa Umma kana tace
“Muje Sadiya”
Da kyar ta iya mik’ewa k’afafun ta suna rawa suka jera ita da Anty Zainab suka bi bayan Ummu suka yi parlourn b’aki.

Mutane kam wasu basu ma samu damar shiga ba
dan akwatunan sun cike parlourn tap!
Ganin kowa cirko cirko a tsaye iya y’an k’alilan kuma na a ciki suna mik’owa ana fitowa da shi ne yasa suma suka ja suka tsaya a gefe
kai kana ganinsu ka san basa cikin hayyacin su..

Ta gabansu aka fara wucewa da akwatuna
nan kuwa suka maida hankali suka hau k’irgawa!
Ana wucewa da goma
Umma ta nemi d’an dakalin slop ta zauna dan jiri ne taji yaana d’ibarta ba na wasaba!
A tunaninta su kenan
amman ga mamakinta sai taga ana ta sake fito da wasu!
Ganin ta k’irga ashirin da d’aya basu k’are ba ya sanya
ta janyo Anty Zainab wadda itama tayi mutuwar tsaye kafin tace
“Zainab zo mu bar wajen nan,
tabbas kwakwalwa ta ta d’an samu matsala sannan bana gani sosai!
Gani nake yi anata wucewa da akwatuna fa har yanzu basu k’are ba.”
Da sauri Anty Zainab d’in tad’an dafa ta
dan yanda take magana da sauri kuma da k’arfi kamar wata zararra ya sanya mutane har sun fara d’an juyowa ana kallonsu. A hankali tace mata
“Ba idonki bane!
Ashirin da hud’u ne cass! Gasu chan ragowar ukun
Sai kuma waenchan baskets d’in da ban san na menene ba”
Bata ida rufe bakinta ba aka fara fito da na Gwaggo da Kawu.
Ai kuwa
Umma bata san lokacin da ta mik’e tsaye ba tace
“Amman dai Maryam sayar da y’ar nan tata tayi ko!?
Haba mana wannan abu kuma ai ya zama hauka!
Meye hakan? Me sukeso su nuna?”

Cikin takaici Anty Zainab tace
“Wallahi Sadiya za kiyi hanyarki nima inyi tawa har a tashi daga bikin nan gaskiya!
Maganar Allah kenan, haba mana! So kika mu zama abun kwatance?
Sai wasu abubuwa kike yi kamar tab’abb’iya?
Kiyi controlling kanki mana
Haba?”
Ta fad’i hakan tana mai wucewa ta barta a tsaye nan dan a yanda take jin zuciyarta yanzu, tsaf zata iya sauk’e ruwan bala’i da fushinta akan matan dake k’ok’arin maidasu telebijin….

Sai da Umma taga an gama fito da kayan an watse daga wajen sannan ta samu da kyar taja y’an k’afafuwanta ta isa harabar tsakar gidan.


Banda gud’a da hayaniyar mata ba abunda yake tashi
A lokacin har an bud’e akwatunan farko an fara dubawa….

Sai a sannan ne Aslam ya samu ya tatttaro nutsuwar shi da d’an ragowar kuzarinsa ya mik’e tsaye!
Yana mik’ewa Ummu da Mommy suka k’arasa wajensu..
D’an b’ata rai yayi kafin yace “Mommy zan wuce
wannan bidi’ar bada ni ba gaskiya”
Murmushi Mommy tayi ta shafa kanshi kafin
ta juyo ta cewa Ummu
“Zai iya tafiya?”

Murmushi Ummun tayi kafin tace “eh, zai iya ai an gama komai”
A hankali yace mata
“Sai anjima”
Cikin kulawa tace
“Mun gode kwarai Aslam,
mun gode.”

Ajiyar zuciya kawai ya sauk’e
daga nan ya ajjiye sandar hannunshi a gefe ya juya
dai dai nan su Sudais suma suka mik’e
Shuraim yana ta b’ata rai shi ala dole ya gaji..

Ummu da Mommy ne suka yi musu rakiya har waje, shi da Sudais da Shuraim bayan ya kira drivern da zai maida Mommy gida yace masa ya taho yanzun…
Mutane in banda kallonsu ba abunda suke yi sunata yaba kyawun Angon
Gashi bai wani zak’e ba irin yanda Angwayen yanzu suke yi! Instead shi ya kama kanshi matuk’a, hakan kuwa ba k’aramin burge jamaar wajen yayi ba.

Su Mommy suna komawa
suka tarar anata ware lefe an yi filla filla ana gani…

Tun daga kan atamfofi Umma ta raina kanta…
Zata iya cewa tunda Laraba ta kawota duniya bata taba shiga tashin hankali irin na wannan lokacin ba!
Hankalinta bai gama tashi ba sai da aka zo kan akwatunan jewelry’s
kit kit
waenda aka ware guda biyu aka shak’e taff da sark’a da y’an kunne
Na farkon fashion ne
Na biyun kuwa gold ne zalla!
Matar dake gefen ta ce taji tana cewa
“Ai dama su family d’in MT haka suke lefe duk matan gidan da aka tashi aurar su ko wacce sai da aka yi mata kit d’in gold!
Yanzu kuma wannan kinga shine jika na farko da yayi aure.
Kaii ammanfa wannan Yarinyar ta tako, gaskiya tayi goshi
Allah yasa y’ay’anmu a danshinta. Zata sha gata ba kad’an ba!
Naji ma kamar ance wai k’asar zai bari ma da ita gaba d’aya!”.

Tabbas zuwa wannan lokacin Umma ta daina ganin komai in banda duhu! Maganar ma sama sama ta dawo ji
daga nan kuma jinta da ganinta suka d’auke d’iff!!

Mutanen wajen kowa hankalinshi yana kan kallon lefe mai abun mamaki da alaajabi
Saboda kaff cikin su babu wadda zata ce ta tab’a ganin lefe kwatan kwacin wannan....


Dimmm!!!
K’arar fad’uwar Umma ta sa jamar dake kurkusa da ita zabura suka jujjuyo…..

“Subahanallah!
Mai ya sameta!!
D’in da aketa maimaitawa ne
ya janyo hankalin mutanen gurin kaff kowa akayi kanta akai mata rumfa......




A zaune Auwal ya tadda shi,
a d’akinsa. Ya jinginar da kanshi a jikin gadon ya lumshe idanuwanshi fuskar shi tayi jajawur! Kana ganinshi ka san yana cikin tashin hankali.

Auwal bai damu da yanayinshi ba dan shi ganinsa ma da yayi a zaune ko shirin tafiya bayayi shi yafi komai b’ata masa rai!
Cikin muryar b’acin rai yace
“Haba Arshaad!
Ka sa mutane sun tara jama’a kai kawai ake jira kazo ka wani zauna anan, me kake jira?
Gaka nan dai a shirye tsaf!
Mai kuma ya hana ka tafiya tun d’azun?
Nace maka ina zan taho karka jira ni.
Ka san yanda hankalinsu ya tashi kuwa?
Dagajin muryar Sakina ka san ba lafiya ba!
Taso mu tafi da sauri dallah”

Wata nannauyar ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin a hankali ya samu ya d’an bud’e lumsassun dogayen idanuwanshi, sai da Auwal ya d’an zabura
sakamokon had’a ido da suka yi da Arshaad d’in!
Da kyar ake iya hango maroon eye balls d’inshi da suka b’uya cikin jajawur d’in idanun nasa.
Sai a lokacin Auwal ya lura da yanda jijiyoyin kanshi suka fito sukai rud’u rud’u!
Da sauri ya k’arasa ya zxauna a gefen shi kafin yace
“Lafiya kake??
Me ya sameka haka?”
Ya jera mishi tambayoyin
duk ya rikice.

Banda ajiyar zuciya ba abunda Arshaad yake ta faman sauk’ewa yama kasa yi mishi magana
Da kyar ya samu yace
“Mammy ce ta….”
Sai kuma yayi shiru.
Cikin firgici da tsoro
Auwal yace
“Ta hana ka zuwa??
Lumshe ido Arshaad yayi kafin a hankali yace
“Har ma auren! Tace idan aka d’aura sai ta tsine min!”

A zabure Auwal ya mik’e
kafin yace
“Innalillahi wa innailaihirrajiun!
Shine kuma ka zauna za ka kashe kanka haka?
Zama ai bai ganmu ba!
Bara in je in samu su Dad in yi musu bayani, idan ta kama har Granpa sai a sa a case d’in.
Mai yasa Mammy zata yi mana haka?”
Ya k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka.

A hankali Arshaad d’in yace
“Ba wanda bai sani ba.
Kowa ya san da case d’innan.
Har mamanta da sisters d’inta duk an bata hak’uri amman tak’i hak’ura.”

Wata kakkausar ajiyar zuciya Auwal d’in ya sauk’e kafin yace
“Ya aka yi Mammyn ta sani?
Last time da naje na dubasu naga kamar duk basu san da zancen ba..
Na san dama suna iya causing problems shiyasa nima ban yi gigin fad’a musu komai ba!
Ko maybe Ummi da aka kawo ce ta kirasu ta gaya musu?”

Da d’an mamaki Arshaad d’in yake kallon shi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace
“Baka had’u da Mom ba hala?
Sun dawo jiya.
All of them”

Da mamamki shima Auwal d’in yake kallonshi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login