Showing 21001 words to 24000 words out of 109746 words

Chapter 8 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2968

y’an sanda, kowa ya rud’e, duk an firfito, Sudais da Shuraim in banda kuka ba abunda suke yi!
Dai dai y’an sandan suna shirin tada motar Granpa ya fito Gramma na biye da shi a baya.

Daddy shima wanda shigowar shi yanzun kenan
Yayi saurin k’arasowa wajen, yana hango su kuwa da sauri ya k’arasa inda suke yafara kokarin fito da Matarsa, yana yiwa y’an sanda masifa!

Granpa wanda yanzu ya k’araso wajen ne ya dakatar da shi sannan ya kira babban d’an sandan…
Ko gaisuwar shi bai bari ya k’arasa ba ya d’auke shi da Mari, kafin ya fara magana cikin b’acin rai
“Ka san a ina kake!?
Ka san ko su waye waennan d’in)
Laifin me sukayi?
Who the hell ask you to arrest them?”.

“I did”
Yaji muryan Abba a bayanshi.

Da mamaki Granpa ya d’an juyo yana kallonshi..
Ba tare da Abb yace komai ba ya k’arasa cikin motar ya fito da Ummi ya kawota gaban Granpa sannan yace “ta fad’i abunda suka yi”.

Rarraba ido ta fara yi.
Cikin b’acin rai Granpa yace “a cire musu ankwar a fito dasu gaba d’aya.”
Bayan anyi hakan ne ya kalle ta sannan yace
“Mai ya faru?”

Da kyar ta iya d’agowa ta d’an saci kallon Mom, a take kuwa daman Mom d’in jira take, ta hau girgiza mata kai alamun kar ta fad’a.

Nan kuwa ta samu kwarin guiwa, cikin sheshshek’ar kuka tace
“Nima ban san abunda ya faru ba Granpa, kawai d’azu yana dawowa yace wai sun had’u da Maryam, in fad’a mishi me nayi ko kuma ya d’au mataki ban san me tace mishi ba amman kawai da nace ban san me nayi ba ya rufeni da dukaa.”
Tana kaiwa nan ta fashe da kuka sannan ta durk’usa a gaban Granpa.


Da k’arfi Abba ya runtse idanuwanshi…
Sai da yad’an seseta zuciyarshi da take ingiza shi a kan yaje ya rufe Ummu da duka, tukunna ya bud’e idanunshi ya sauk’e su akan Granpa…
Shima kuwa shi d’in ya zubawa ido.
Ganin kallon da Granpa yake yi mishi ne yasa kawai ya juya ya nufi side d’insu Aslam.

Ko minti uku ba a yi ba ya fito rik’e da hannun Huda.

Tunda suka tunkarosu Granpa ya kafe Yarinyar da ido!
Sai da yazo gabanshi sannan ya tsayar da Huda, da gaba d’aya kallo ya koma kanta.

Ummi ya kalla wadda ta rikice da ganin Yarinyar had’i da sake rud’ewa, sannan yace
“Baki santa ba ko?” Yayi maganar yana nuna Huda, kafin cikin d’acin zuciya yace
“Zaki fad’i gaskiya ko sai na yanke hukuncin da nayi miki alk’awarin d’auka???”

Gaba d’aya ilahirin jikinta karkarwa yake yi, tun ba ma da taga Gramma ta jawo Hudan kusa da ita tana d’an shafa fuskarta sannan ta k’ura mata ido ba!
Tabbas wannan itace y’ar Maryam da Abba, dan ga tsananin kamanni nan suna yi da Mijinta(Abba) ba kad’an ba, yanzu ya za tai mai zata ce??
Karaf!! suka kuma had’a ido da Mom, a take ta sake girgiza mata kai, wanda hakan ya sake rud’a ta dan bata san kuma abun yi ko cewa ba, ba daman tayi k’arya dan ga evidence, kuma ba daman fad’an gaskiya tunda bata san dalilin Mom na hanata fad’a ba.
Yanke shawarar sumewa tayi, dan haka ta fara k’ok’arin lumllumshe ido amma sai maganar da Abba ya fara tayi saurin watstsakar da ita daga suman k’aryar da tayi shirin yi jin yana cewa
“Granpa wannan y’a ta ce!”
Yai maganar yana nuna Huda
Sannan ya k’ara da cewa
“Those 3” ya nunata da Mom da Mammy, kafin ya cigaba
“Knew about everything all this while!!…
Ranar da Maryam zata haihu ta turo sister d’inta ta fad’a min, bayan sistern nata ta bawa Daniel sak’on, shi kuma munafuki sai ya fara zuwa wajen su da takardar saboda bakinsu d’aya tuntuni!
Bayan sun karance sak’on nata shine suka yi mata wannan reply d’in.”
Ya k’arashe maganar tare da zaro takardar gaban rigarshi ya mik’awa Granpa.

Hannu Granpa ya saka ya karb’a, sannan ya fara karantawa…..

Baya Daniel ya fara ja
dan daman, tun lokacin da aka fara zancen ya sha jikin jikinshi…

Karaf! idon Granpa ya sauk’a a kanshi, dan haka yace mishi “idan ya isa gate d’in daga nan yayi gaba kar ya sake ganinshi near his estate!!”

Ummi dajin haka ta san kashin ta ya gama bushewa don daga gani Granpa ya gama gasgata maganar Abba!
Don haka ta fara jiran jin sauk’ar mari ko duka, amman sai taji kawai ya dafa ta.

Tana d’agowa gabanta ya fad’i don gani tayi ya mugun had’e rai babu alamun wasa ko sassauchi akan fuskar shi.
Suna had’a ido ba tare da b’ata lokaci ba yace
“1 word from you!
Akwai gyara a cikin maganarshi?
Yes or no?”
Gabanta yana fad’uwa tana kuka tace
“No”
Da sauri Mom ta runtse idanuwanta gam!!!.

A hankali Granpa ya sauk’e ajiyar zuciya sannan ya zare hannunshi daga kanta, kafin ya kira d’an sandan daya mara d’azu!
Yana karasowa gareshi yace
“Arrest them!”

Da sauri Mom ta bud’e idanunta a firgice tana kallonshi, Daddy ma k’arasowa yayi wajen ya hau rok’on shi yana cewa
“Wannan family matter ne, a bari kawai za suyi settling a tsakaninsu dan Allah yayi hak’uri”.
Hatta Gramma sai da ta sa baki amman fur!!! Granpa yayi kunnen uwar shegu…

Banda kuka ba abunda Mammy da Ummi suke yi….

Sassauchi d’aya Granpa yayi musu shine
Bai bari an tafi dasu a motar y’an sanda ba kuma ba a saka musu handcuff ba.
Ya bada motar gida yasa drivernshi ya kaisu har cell, bayan ya tabbatar wa da y’an sandan “kar a bawa kowa bellin su sai nan da 2 months............”

Duk wannan bidirin da ake yi Aslam yana sama bolcony d’in parlourn Mammy yana kallon komai!

Motocin suna ficewa Gramma ta sake ruk’o Hudan da kyau sannan ta rungume ta, kafin tace
“Welcome to MT my granddaughter” har da d’an hawayenta. Sannan tace mata
“Zo muje ki huta ko?”

Ita dai Huda kawai binta take yi a haka ta jata tayi side d’insu da ita.
Har bedroom d’inta ta kaita, har ga Allah lokaci d’aya taji Hudan ta shiga ranta matuk’a!
Sai nan nan take yi da ita, cikin mintuna k’alilan aka cike gabanta da abinci kala kala.
Sai janta take yi da hira…
Da kyar Hudan ta samu ta d’an sake da ita, ganin da tayi matar tanada sauk’in kai ya sanya ta cewa “dan Allah tana so taje taga Mamanta!
Sun barta a asibiti tanata kuka, kuma bata da lafiya, gashi tanata kiranta amman bata d’auka.”

Gramma ta bud’e baki zata yi magana kenan Granpa ya shigo, kallonsu yayi kafin yace “ku biyo ni” sannan ya juya ya fita.

A zaune suka sameshi a parlourn da wani da suke da tabbacin Likita ne saboda ga lap coat a jikinshi.

A k’asa Hudan ta nemi waje ta zauna kan kafet, gramma kuma ta zauna a kan d’aya daga cikin kujerun parlourn.

Nuna mishi ita kawai taga Granpa yayi, daganan taga mutumin ya nufuto…..setin ta ya zauna sannan ya bud’e d’an k’aramin akwatin da ya shigo da shi.

Sirinji ya d’auko da wani abu kamar cutting bud sai reza guda d’aya!

Sai da aka sha fama sannan aka d’auki jikin, daganan ya bata rezar yace “ta yanko farcenta” cuttonbud d’in kuma a bakinta kawai ta saka ta cire ta bashi, daganan ya d’an sa hannu ya ciri gashinta dake kwance akan goshinta wanda har sai da tasa k’ara dan ba kad’an ba taji zafi!

Daga nan ya mik’e ya cewa Granpa “nanda 24 hours in shaa Allah zai dawo”
Sannan yasa kai ya fice.

Gramma taso tayi mishi magana amman ganin yadda ya had’e rai ne yasa kawai ta kyaleshi suka koma d’aki ita da Hudan bayan ya sallamesu.

Iya gata Huda taga gata a wajen Gramma, amman dukda hakka Hudan zancenta d’aya ne “zata je wajen Mama”

Da kyar ta samu ta lallab’ata akan zuwa gobe za suje su duba Maman nata, sannan ta yarda tayi bacci mai cike da mafarkin Mama kala kala.....

Sai bayan isha tukunna Auwal ya dawo, daman saboda aikin da ya d’orawa kanshi kwana biyun nan sometimes har kusan kwana yake yi a office.
Aikin da ba nashi ba da wanda yake nashi duk yi yake…ya kuwa ci sa’a dan Granpa har ya d’an fara sauk’owa da kuma tunanin maidashi kujerarshi.

Bai tashi fahimtar babu Mom a gidan ba sai da safe da ya fito zai tafi office!!
Cikin nutsuwa yake break fast d’inshi, tun sauk’owarshi Jalila dake kitchen ta had’a uban milo da mdara tana sha ta jiyoshi, tana lek’awa kuwa ta ganshi..
Don haka da sauri ta koma ta hau danna kwab’etar a bakinta har tana kwarewa, cikin minti kad’an ta shanye sannan ta goge bakinta ta nufi k’ofa dan bata so ya fita ba tare data karbi uban kud’ad’en data k’udira a ranta zata amsa ba!
Dan bazata iya jira sati biyu ya cika ba kamar yadda Umma ta fad’a ba..
Sannan inta karb’i kud’in ma ba bata zata ke yi ba
Dan ita ba sakarya bace ba
tana gani sati hudu da suka wuce
Kaff kud’in hannunsu sai da suka Kare aka dinga cewa ‘Auwal zai dawo gareta a rikice kuma da maganar auren ganga ganga!’
Ga shi har ita tazo gidan shi bai je ba
k’arshentama da tazo d’in da mari yayi mata sannu da zuwa…
Sannan bataga alamar rabuwa tsakanin Huda da Arshaad ba dan haka
kud’inta kawai zata amsa taje ta yi fafa na kwana biyu ta sayi kayan kwalliya da turarurruka tazo ta yak’i Arshaad tunda gasu a gida d’aya!…..
Da wannan tunanin ta fice daga kitchen d’in

Ya gama breakfast ya mik’e kenan ita kuma tana fitowa.
Sarai ya ganta amman sai ya basar kawai, ya juya ya d’auka jakar shi kafin ya fara k’ok’arin barin wajen, dasauri ta shiga gabanshi ta tsaya sannan tasa hannu ta rik’e jakar, bata damu ta gaisheshi ko ta tambayi ya yake ba tace
“Muna biki, inaso zan je, kuma ni wannan mai girkin gaskiya bana iya cin abincin ta tayar min da zuciya yake yi, tun jiya da Adama ta tafi nake fama da yunwa, so anjima ka taho da wata sabuwar mai abincin ta gwada inga ko zan iya ci!”

Yayi mamaki da yaji tace ‘Mom bata nan’, a ransa yace “to Ina ta tafi kenan??” Sai kuma ya raya “anyways zai kira ta yana fita yaji mai ya faru!
Dan kwata kwata he can’t stand Jalila, shiyasa cikin k’aguwa da son ta rabu da shi yace mata “tou” kawai, sannan ya fara k’ok’arin barin wajen.
Da mamaki yake kallon ta ganin tak’i sakin mishi jaka, da d’an fad’a yace “dalla Malama cikani kar In yin latti!”

Itama cikin tsantsar rashin kunya tace “sai aikin zuwa office kullum amman kwakwalwa kamar ta kifi, simple abu idan an fad’a maka ba zaka d’auka ba ni ina mamakin ma ta yadda kake yin aikin wallahi!!
Da kaji nace maka za muyi biki Ina so zan je kenan! sannan
ina nufin yau nake son zuwa maybe kuma kwana zan yi maybe ko kwana biyu
dan an riga an fara bikin!
Dan haka ka saka driver ya kaini idan na gama kuma yaje ya d’auko ni, in kuma ka bari na dawo da kaina to ka san mai zai faru ba sai na tsaya yi maka bayani ba!.
Sannan kuma inaso a cika min jaka ta!”
Ta k’arashe maganar tana hard’e hannayenta a kan k’irji, sannan ta fara jijjiga irin ina sauraronka d’innan.

Shiru Auwal yayi, ji yake kamar ya shak’eta ta mutu kowa ma ya huta!
Cike da gajiya da ita yace
“Nawa kike buk’ata??”
Ba tare da b’ata lokaci ba tace
“Dubu d’ari shidda!!”.
kallon tsana ya fara jifanta da shi, chaan! Kuma sai ya d’an yi murmushi kana ya matso kusa da ita
ya mik’o mata hannunshi kamar wanda zai karb’i wani abun, cikin yin k’asa da murya ahankali yace
“Ban gishiri in baki manda!”
Yana murmushi tare da d’age mata girarshi d’aya.

Tsaki Jalila taja, Dan sarai ta fahimci me yake nufi hakan yasa ta fara k’ok’arin barin wajen….

Zagayeshi tayi da sauri ganin yana shirin ruk’ota, amman bata tsira ba dan tana wuce shi shima ya juyo kafin ta ankara taji ya ruk’o hannunta sannan cikin sanyin jiki yace
“Ko har kin hak’ura da kud’in yanzu kuma bakya so? Na San fa kema kinyi missin….”
Maganarshi ce ta mak’ale sakamokon idanuwanshi da suka sauk’a a kan Daddy wanda ya hard’e hannuwanshi kawai ya zuba musu ido, kana ganin fuskarshi ka san yana cikin tsananin b’acin rai!.

Da sauri Auwal ya cika hannun Jalila sannan yayi saurin yin k’asa da kanshi..
Daddy yana k’arasowa ya jaa hannunshi kawai ba tare da ya ce mishi k’ala ba suka fice.
Mukullin mota ya bashi sannan ya fad’a mishi inda zai kai su.

Auwal yana son tambayarshi ‘me zai kai su police station’ amman sai kawai yaja bakinshi yayi shiru sakamokon ganin yadda Daddyn ya had’e fuskarsa tamau!!

Suna shiga ciki Auwal ya fara yatsina yana toshe hanci sannan a hankali ya cewa Daddyn “pls, zan jira ka a waje.”

Banza Daddy yayi da shi bai ce mishi komai ba..
Suna a haka dpo d’in ya fito, yana ganin Daddy ya ganeshi
dan haka ya shiga gaidashi cikin girmamawa..
Amsawa Daddy yayi sannan yace mishi “yana son ganin su Mom”
Sai a lokacin Auwal ya d’ago a razane yana kallonshi fuskarsa na nuna buk’atar son jin k’arin bayani.

Babu wanda yace mishi komai, dpo d’inne yace “To dan Allah yaje office d’inshi zai kawo mishi su”
Daddy bai so hakan ba amman yadda dpo d’in ya nace ne yasa kawai suka nufi office d’in nashi shi da Auwal.

Ko minti biyar ba a yi ba aka shigo da su!
Dakyar Auwal da Daddy suka iya gane Ummi, Mom itama ta wujigatu ba k’arya!
Duk cikin su Mammy ce mai d’an kyan gani.

Mom tanaganinsu ta fashe da kuka, da sauri Daddy yaje ya rumgume yayi ta lallashinta tukunna ta zauna.
Ummi ma kukan take yi, Mammy kuwa suna gaisawa ta nemi waje ta zauna, dama tsaftataccen wuri take ta adduar samu don ta samu damar baje hanci ta shak’i tsaftatacciyar iska.

Auwal gaba d’aya kanshi ya d’aure, dan haka yaje wajen Mammy ya hau tambayarta ba’asi, dan ya lura ita kad’ai ce ke a cikin hankalinta.
Tiryan tiryan haka Mamyn ta zaiyyano mishi komai, tana gamawa ta fashe da kuka kafin tace
“Na san mun yi laifi, amman wallahi hukuncin nan yayi mana tsauri! Ka ga inda aka ajjiye mu kuwa!
Wallahi ko wajen tumaki ya fishi daraja,tsafta da kyan gani
A wajen fa ake kashi ake fitsari, gashi ka san Adama da Zainab suna da allergy..kalli jikinsu kaga gaba d’aya borin jini ne,jiya ba wanda ya runtsa a cikinmu!!
Ban san tayaya za muyi wata biyu a irin wajen nan ba, dan wallahi Auwal na tabbatar muna yin sati a nan to sai dai a kwashi gawarwakinmu.......”
Tana gama fad’an haka ta sake rushewa da wani irin kuka mai cin rai.

A fusace Auwal ya mik’e a wajen yayi hanyar fita, Daddy yana ganin yanayin mik’ewar tashi shima yayi saurin mik’ewa ya sha gabanshi yana cewa “ina zaka je?”

Cikin d’acin zuciya yace “ba ruwan ka Daddy, this is between me and Abba!!”
Yana gama fad’an haka ya sake yunk’urin fita, da sauri Mom wadda itama ta k’araso wajen tayi hanzarin rik’o hannunshi, yana juyowa yace
“Mom dan Allah ki barni kawai, i need to teach him a lesson!! In banda tsabar rainin wayo a kan y’arsa zai yi muku haka? Y’ar gwal ce ita?”

Cikin fad’a Daddy yace
“Tou sannu sarkin marasa kunya!! Uncle d’in naka zaka koyawa hankali? Haukan naka ya tashi daga tsakaninku yana shirin haurawa kan y’an uwana kenan?? To wallahi a kul d’inka Auwal!!
Raina a b’ace yake da kai tun d’azu shiru kawai nayi maka, kar ka yarda ka kaini mak’ura!!”
Yana gama fad’an hakan ya koma wajen dpo ranshi a mugun b’ace…

Da sauri Mom ta sake rik’o hannunshi duka biyun ta matse gagam sannan ta fara magana
“Kayi hak’uri ka sauk’a daga kan wannan dokin zuciyar Auwal, dan babu inda zai kaimu, idan ma za a hukuntasu to bata haka za a yi ba, kaji??
Yanzu na tabbatar kana yin wani abun laifin ka za a gani, kuma nima kaga dai gani da nawa issue d’in, sannan ga matsalar ka da Granpa abun zai yi mana yawa.”
Cikin yin k’asa da murya tace
“Kana gani ai Arshaad da ya fika wayo tun jiya bai zo ba, kuma na tabbatar yana cikin gidan, shi kuma Aslam dayake babu uwar shi a ciki ta sama ya mak’ale yanata kallonmu bai ce ko yayi komaiba, bai san ba ganshiba.
Don haka inaso kayi hak’uri ka danne zuciyar ka, tukunna sai mu san abun yi, kaji ko?”.

Da k’arfi ya sauk’e ajiyar zuciya yana bin hannun Mahaifiyar tashi da yayi jajur ya kumbura ga borin jini kala kala, da ido. A haka har gara ita nata da d’an sauk’i akan Ummi, dan ita nata har fuska…

“Kaji ko?”
d’in da tace mishi ne ya sanya yayi mata nodding kai kawai sannan ya koma ya zauna, itama ta dawo ta zauna.


A Chan teburin dpo kuwa
Babu yadda Daddy bai yi da shi ba akan “zai biya ko nawa ne a ware musu office d’in wani d’an sandan a gyara musu toilet su dinga amfani da shi su uku kawai zuwa nan da 2 months d’in”!
Amman furr!! Dpo d’in yak’i, yace
“Jiya bayan na dawo sojoji Mahaifinta ya aiko suka kaini har gabanshi da daddare
ya ja mini warning akan in tabbatar na basu horo mai tsanani, kuma ya shaidamin yana da cid’s da yawa, muddin na k’etare umarnin shi to a bakin aikina.
Tsabar yanaso ya tabbatar min idanunsa suna kaina, yau da safe ya kirani, duk wani abinda ya faru a nan daga dawowata zuwa tafiya ta gida da zuwana nan yau da safen kaff! Babu abinda bai gayamin ba, har na cikin dare wanda bananan a bakin shi na ji.
Hatta abinci yace sau biyu kawai za a dinga basu…

So, dan haka dan Allah ka rufamin asiri ina son taimakonku tabbas amman ina jin tsoron rasa aiki na. Da kuma hukunci da yayi alk’awarin yanke min, wanda ban san meneneba.”

Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, sannan ya juyo ga su Ummi….
Idanuwa yaga sun zuba mishi alamun suna sauraron komaai.
Tausayin su ne ya kamashi, hakan yaasa yayi saurin d’auke kanshi yana shirin yiwa dpo d’in magana Mom ta matso ta katsesu ta hanyar cewa
“Tou dan Allah idan ba zaka iya komaiba, ka raba mana d’aki da matan nan, basu da mutunci kwata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login