Showing 63001 words to 66000 words out of 109746 words

Chapter 22 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2963


“Ku taso muje,
Kaka yana kira.”

Hijabansu suma suka sanya, suka fito, gaba d’ayansu.

A tsakar gidan suka tarar da Umma tana bawa Ya Ja’afar koka a baki!
Ya dalalar da wani ya zxubar da wani….
Da tsoro Hudan ta kallesu, sai kuma ta k’arasa! Sai da ta d’an rissina tukun ta gaida Umma.

Da kyar Umman ta iya amsawa
Ya jafar d’in kuwa da ta gaidashi, kallonta kawai yake tayi bakinshi na zubar da yawu da d’an ragowa ragowar kunun, ya kasa cewa komai.
Daga d’an nesa Sakina tace “ina kwana” bata jira jin amsawar su ba ta wuce tayi waje abunta.
Itama Mama d’an matsawa kad’an tayi suka gaisa sama sama kafin tace
“Ya jikin nashi?”
“Da sauk’i” Umma tace, tana wani b’ata rai irin ita an dameta d’innan…
Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace
“Bara muje Kaka yana kiranmu.”

Wannan karon banza Umman tayi da it.

Guiwa a sace suka fice daga gidan ita da Huda Umma tana jin kamar ta bisu ta shak’e su!
K’arshe dai haushin akan Ya Ja’afar aka sauk’e, dan kokon da bai sha ba kenan tace wai “yana ta b’ata mata lokaci”.
Jikinshi ta bashi tsumma ya goge, da kyar! Daganan ta mik’e ta fice ko wanka bata yi ba.

Su Mama kuma bayan sun fita ne, Hudan take tambayar “mai ya samu Ya Ja’afar?”
Sakina ce ta iya amsa mata da
“Fad’a suka yi! Nasu na y’an shaye shaye
Wani ya d’au makeken dutse ya buga mishi a kai. A haka ma ya d’anji sauk’i….”

A babban parlourn Madu suka same su dukkansu, Shuwa Baaba Talatu Madu da Kaka!
Kana ganin fuskokinsu ka san ba lafiya ba!
Dan haka su Mama suka sha jinin jikinsu suka gaidasu suka nema waje suka zazzauna.

Baaba Talatu ce tace
“Maryam yaushe Yaran nan suka zo?”

A hankali Mama tace
“Jiya da daddare”

Jingina kai tayi tukunna tace ,
“Shi Abban ne yace su kwana?”

A hankali ta girgiza kai.

D’an shiruu ne ya biyo baya kafin Kaka yace
“Maryam mun yi miki magana akan ‘ki d’in jira tukunna’ amma ko? Mai yasa kike da taurin kai ne?
Kinsan me taurin kan naki ya haifar yanzu?”
Bai jira amsar taba ya d’aura da cewa
“Kinga na farko yanzu haka Usman yana hannun hukuma!
Yanzun nan aka kamashi bayan ya wanke k’afa yaje ya kwashi y’an sanda ya kaisu wai su d’aure Abba saboda yana bin matar aure!!
Ban san dai ya aka yi ba amman reshe ya juye da mujiya, yanzu haka yana d’aure a station!

Sannan kema Abban yace ya baki minti 40 ki maida masa Yarinyar shi da hannun ki, in ba hakaba kuma to duk abunda ya biyo baya ke kika ja!
Kuma yace gaishe kin ma ta daina zuwa yi daga yau!.

Cikin kuka Mama tace
“Kaka dan Allah kar ku ce in yi abunda yake so..
Wannan wanne irin son kai ne Abba yake gwadawa?
Na ji na yarda da maganar ku da kuka ce bai san da itaba tun farko na yafe mishi wannan amman dan Allah kar ku bari ya raba mu! Kawai ni ya fita a harkar mu gaba d’aya, bama buk’atar shi.”

Murmushi Madu yayi kafin yace “Hudan kema ba kya buk’atar Mahaifinki??”
Sai da ya sake maimaita tambayar tukunna ta d’aga kanta alamar ‘eh’ sannan tace
“Zan zauna a wajen Mama”

A hankali, Madu yazo ya zauna a gefen su da kyau kafin ya fara magana
“Shikenan zamu gwada mu gani, amman idan mun yi nasara kin dawo wajen Maman naki to inaso kisan cewa
Ba a inda take zaki zauna ba sai dai ki zauna a gidana! Saboda Usman ba zai tab’a bari ki ci gaba da zama nasa a gida ba sannan na san ba zai dinga barin itama Maman naki tana zuwa inda kike ba
kwata kwata kinga kenan baki zauna da Abba ba kuma baki zauna da Mama ba!”

Cikin kuka Mama tace
“Abba dan Allah ka dai na, za ka karya mata guiwa”

Murmushi ya sake yi kafin yace
“Maryam hakan shine gaskiya!
Kuyi hak’uri, for the first time nayi miki alk’awari ban cika ba!

In dai zan fad’a miki ki ji, tou inaso dan Allah ki bar Yarinyar nan ta koma wajen Mahaifinta
kamar yadda ya buk’ata, ko munje kotu ya fimu gaskiya, kuma rashin hankalin da Usman ya sake yi yau d’innan ma wata shaida da point ne Abba ya sake samu.
Ki barta ta tafi, za ku dinga waya sannan yace anytime kike son ganinta kije ki ganta, idan ma bakya son zuwa gidan nasa to zai saka ko driver ne ya kaita ko wani park ko restaurant, ku had’u achan amman yace ba zai sake barinta tazo inda kike ba!
Har ga Allah Maryam, Abba is trying to be just here.”
Da sauri ta d’ago tana kallonshi da jajayen idanunta.
D’aga mata kai yayi alamar gasgata mganar shi,
kafin Baba Bashir ya d’aura da cewa
“Maryam har yanzu zuciyar ki a k’ulle take da zafin abunda Abbas ya aikata miki, shiyasa ba za kiga abinda mu muka ganiba, wanda muma a da bamu ganshiba sai bayan da muka yi k’ok’ari muka goge takaicin shi daga idanuwanmu.”

“Mune muka haifeki, baki da masu fad’a miki gaskiya sama da mu, ki tashi ku tafi suyi miki kwatance ki kaisu ki dawo, dama haka rayuwar take, ba komai kake kwallafawa rai kuma ka samu ba, ki bari ko nan da wata biyu ne haka, sai a san abun yi kinji? Yanzu kuje kawai.”
Hudan ke kuma idan kin koma, ki san yanda za kiyi mishi magana a samu ya saki Babanku Usman kinji?”
Cewar Shuwa.
A hankali Mama ta rintse idanuwanta wasu zafafan hawaye suna zubo mata!
Ta manta rabon da Shuwa tayi mata magana mai tsayi haka.
Bata dawo daga duniyar tunanin da ta tafi ba, taji Sakina ta furta wasu maganganu da suka girgizata matuk’a! Wai “An saka ranar Huda nan da wata biyu da Arshaad!!”

Ba Mama kad’ai ba, gaba d’aya parlourn shiru ya d’auka!
Chaaan! Shuwa tace
“Allah ya sanya albarka”
Da sauri Mama ta kalle ta da idanunta hawaye shab’e shab’e!
Kasa jurewa Shuwan tayi kawai ta mik’e ta kama hanya ta fice…

Baba Bashir ne yace “ku tashi kuje Maryam, za muyi wannan maganar wata rana!”
Cikin kuka Mama tace
“Kaka, Abba
Naji zan barta ta koma
amman dan Allah kar ku saka na maida ita, ba zan...”
Kukan da ya kufce mata ne yasa ta kasa ci gaba da magana ta mik’e ta fice tayi cikin gidan…
Baaba Talatu ce ta bita domin lallashin ta.

Wannan shi ake kira isa da mallaka!!! Tayaya zaka
sa ranar Yarinya ba tare da tuntub’ar Mahaifiyarta ba? Saboda Allah fa!.

Shiruuu, parlourn ya d’auka, chaan Kaka yace “su mik’e su kai su”
Ita Sakina tausayi ma y’an tsofaffin suke bata, sun tsufa amman har yau basu huta ba, bayan jigilar case d’in y’an unguwa ga na family…ta tabbatar yanzu suna maida su, police station zasu wuce, akan case d’in Baba………..


A k’ofar tafkeken mansion d’in da suka isa da taimakon kwatancen Sakina suka yi parking, daganan suka yi musu sallama, da d’an Guntun maganganu tukunna suka wuce, su kuma suka shige ciki.

A parlourn suka tarar da Abba, Daddy har Dad da Arshaad! Da alamun maganganu suke yi masu mahimmanci.

Yadda Hudan ta baro Mama tana kuka yasa ta d’an ji zafin Abba!

A hankali suka gaidasu, bayan sun amsa bata tsaya ba kawai ta haye sama! Har sai da Sakina ta d’an yi mata magana bayan sun hau, dan taga kamar basu ji dad’in yadda tayi musu d’in ba.

Ko lunch k’in sauk’a tayi, ba yanda Sakina batayi da ita ba amman tak’i sauk’a, gashi Abba sai kira yake a waya tana amsawa tana cewa “Huda sallah take”

Kamar minti ashirin haka, suka ji knocking. Sakina ce tace
“Come in”
A tunanin ta ko maid aka turo ta kawo musu abincin.
Turo k’ofar yayi ya shigo,
Sakina bata san lokacin da ta fara dariya ba ganin Abba ya shigo har da hular kuku a kanshi da basket d’in abinci a hannunshi.
Harararta yayi, ya d’aura yatsanshi akan lips d’inshi alamun tayi shiru!
D’aga hannuwanta sama tayi
tana gimtse dariyar tata, sannan ta mik’e ta fice da sauri.

Sai da ya ajjiye kular, sannan yace “princess”
Shiru tayi still tana kwance ta bawa k’ofar baya.
Chan taji yace
“Hudan”
A hankali ta mik’e ta zauna ta juyo tana goge
hawayenta, fuskarta tayi jaaa alamun taci kuka, over!!

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya zauna a bakin gadon, yayi hugging d’inta ya fara lallashinta ai kuwa kamar jira take ta saki kukan babu control.

Bai hana ta ba, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru tukunna
a hankali yace “sorry dota, i’m really sorry, ok?”

Cikin sheshshek’a tace
“Abba Mama na da bp, yanda na baro ta tana kuka, Allah zai iya tashi?”
Murmushi yayi yana sakinta kafin ya gyara zamanshi yana kallon k’ofar fita tukun yace
“Hudan, na fiki jin zafin kukan da Maman ki take, please don’t question my decision, it’s the right thing.”
Ahankali tace
“Amman Abba pls...”
“Shhhhhhh”
Yace ba tare daya kalleta ba, kafin ya juyo ya fara k’ok’arin zuba mata abinci.
Omelet d’in da ya soya mata ya saka a gefe, da pizza slice uku da ya d’auko.
Da farko k’in ci tayi sai da yayi dagaske, tukun ta d’an karb’a.
Bayan ta gama ta sha ruwa, ya d’an dunga janta da magana yana ta faman lallashinta.
Hudan bata iya dogon fushi da mutum ba, don haka ta d’an sauk’o, hakan kuwa yayi matuk’ar ragewa Abba kusan 20% na damuwar da yake ciki
shiyasa da ta rok’esa akan ya saki Baba ba don halinsa ba sai dam kakanninta da hankalin su yake a tashe!
Abban ya amince, a take ma a gabanta yayi waya yace a sake shi.
Ta ji dad’i sosai kuwa.
Daganan suka d’an ci gaba da maganarsu.

Hammar da yaga tanayi ne
ya sanya ya fahimci bacci take ji, dan haka yace mata “ta kwanta”
Bata yi 10 minutes da kwanciyar ba ta fara bacci….
Ahankali yake kallonta yana tunani kala kala…
Sai bayan kusan 1 hour tukun ya rage mata k’arfin ac ya lullub’eta da bargo, sannan ya fita da kayan abincin...............


A chan parlourn k’asa kuwa, sam Sakina bata lura da Auwal wanda ya daya dawo break ba, sai da ta kusan k’arasawa dining d’in!
Tun kusan sauk’owarta yaji a jikinshi!
Addua yake Allah yasa itance, don haka ya k’urawa stairs d’in ido…
Ba a hankali take tafiyarta ba ba kuma da sauri ba! Da d’an
murmushi a kan fuskarta.

Gaba d’aya ya shagala da kallonta, har wani lumshe ido yake yi yana bud’ewa.

Jikinta ne ya bata kamar ana kallonta, sai kuma mayen k’amshin turarenshi da ta fara ji a jikin shi tun ranar farko ya daki hancinta!
Dan haka da sauri ta d’ago ta kalli dining d’in..
Suna had’a ido yayi saurin rintse idanuwanshi kafin a hankali ya bud’e su a kanta!
Doguwar riga ce a jikinta Ashape y’ar kanti bak’a mai ratsi ratsin sky blue sai d’ankwalinta wanda tayi simple d’auri da shi..
Rigar bata wani kamata ba,
amman kasancewarta mai garin jiki yasa ta d’an fiddo mata surar jikinta kad’an!.

Ranta ne ya b’aci ganin yanda yake wani rufe ido yana sake bud’ewa yana k’are mata kallo! Da sauri ta sa hannu ta warware d’ankwalinta ta yafa a jikinta sannan ta doka wani uban tsaki, wanda yayi sanadiyyar dawo dashi cikin parlourn.

Har ga Allah abinda take tunani ma shi Allah bai bashi ikon lura da nan d’in ba, kawai shi dai yasan ya tsinci kanshi cikin tsananin farin ciki da shauk’i na daban, sannan yanda ta yi d’aurin ya sake fito da ainahin kyauwun fuskarta
dan yawanci cikin hijabi yake ganinta, ga wani lallausan saje dake shirin had’ewa da gashin girarta, na gefen kunnenta ma ya sauk’a sosai kamar zai had’e da gashin k’eyarta, sannan tunda yake bai tab’a ganinta tana murmushi irin yau ba!

Bai ida dawowa dede ba yaga ta juya da sauri zata bar wajen.
Da sauri ya mik’e ya k’arasa ya sha gabanta kafin yace
“Sakina, please, listen to me dan Allah.”

Wani kallon tsana tayi masa kafin tace
“mallan dalla matsa In wuce”
Tayi maganar babu alamun wasa a tare da ita….


Zagayeshi take k’ok’arin yi amman yak’i ya bata damar yin hakan, da alamun ma in ta biyeshi to a yadda yakesa hannayenshi wajen k’ok’arin kareta daga wucewa tsaf zai tab’ata!
Don haka ta tsaya ta fara aika mishi da harara kafin tace
“Malan ni ba Jalila bace ba!
Ka bar ganin wai a gidanku nake wallahi
Idan baka bani hanya na wuce ba, zan zabga maka mari!”

Ga mamakinta sai taga yana dariya, sai da yayi mai isarshi sannan yace
“Na yarda!
But duk mari d’aya zaki bani 10 minutes d’inki, kawai ko d’an hira ne muyi…..tbh i can do anything to get your attention”
Ya k’are maganan yana kallonta da murmushi akan fuskanshi sannan ya d’anyi k’asa da kanshi…..
Yanayin zanen flower d’in da aka yi na sky blue akan kayan jikinta yayi mishi kyau sosai!
Zanen ya bi da kallo, har ya sauk’e idanunsa akan yatsun k’afarta! ,
Gaba d’aya ya shagala da kallo yaga ta janye da sauri cikin b’acin rai tace
“D’an iska kawai!!” k’asa k’asa, ita kanta bata yi tunanin zai ji ba, sannan tayi sauri ta nufi d’akin da ke kusa kusa, tana shiga ta datse k’ofar ganin yana shirin biyo ta.

Tunda Auwal yake a rayuwar shi, har snake friends d’insa wani lokacin suke kiranshi da shi, ko master, ko danger sunaye dai na rashin d’a’a kala kala but bai tab’a jin ba dad’i ba!
Amman yau da Sakina tayi mishi wannan kallon har ta furta, gaba d’aya duk sai yaji babu dad’i! He hates it.

Kasa ci gaba da lunch d’inma yayi don haka ya mi’ke ya fita ya koma office da tunani barkatai a ranshi!
He just wants to talk to her, yana so ya sake ganin smile d’in nan nata!
D’an 5 minutes d’in da suka yi shi da ita d’azu tare zai iya cewa
‘it one of the best moment of his life.......’

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
46


BAYAN WASU Y’AN KWANAKI.
Tun ranar da su Hudan suka koma Nasarawa gra, malaria da mura suka yi mata ram!Bata iya komai hatta karatunta ma Sakina ce ta karb’a take yi.
Gaba d’aya hankalin Abba a tashe yake, kwananta d’aya a asibiti aka sallamosu aka had’o su da nurse wadda zata dinga yi mata allurai da chanjin drip.
Shi da kansa (Abba) yake jinyar ta, da kyar yake yarda yaje yayi bacci amman da sassafe shi da Arshaad ne suke tashinsu a bacci.
Babu abunda yafi d’aga musu hankali irin yanda bata iya cin abinci dan ta samu lost of appetite! A rana sai a girka abinci kala nawa amman da kyar zata iya tsakular d’aya, gaba daya duk ta zabge ta rame tayi wani irin fariii!
Sai dogon hanci wanda ya sake fitowa tubarkalla, idanuwan nan daman ya lafiyar kura sun sake lumshewa kamar na mashaya.

A cikin kwana biyun nan ba Hudan ce kad’ai ta rame ba har Auwal!! Dan kwata kwata Sakina ko a waje ta ganshi to ta bar wajen kenan sai in ya tafi tukun zata koma, k’iyayyar k’iri k’iri take nuna masa babu ji babu gani.
Ranar da aka kwantar da Hudan a asibiti kuwa, da Auwal d’in yaje dubota akai rashin sa’a Sakinar ce a wajen Abba ya d’an fita ita kuma Huda tana bacci dan haka ya samu chance!
Ganin da Sakina tayi abun nashi ba na k’are bane yasa ta fito mishi a Sakinar ta ta wankeshi tass!! Sannan tace
“Ta tsaneshi, ba zata tab’a iya yin rayuwa da mazinaci mak’aryaci kuma mayaudari ba!
Ya fita a harkar ta tun kafin ta sauya mishi….”

To dai tun daga ranar ta samu ya d’an sakar mata mara, dan ita yau kusan sati d’aya ma amman bata saka shi a idontaba.
Abunda bata sani ba ashe rashin lafiya shima yayi na kwana biyu..gaba d’aya duk
ya rame, office kawai yake iya zuwa, Daddy yayi tambayar duniya har ya gaji ya kyaleshi…..


Yau Hudan ta d’an tashi jikin da sauk’i tun safe, dan yau
through out batayi amai ba kuma ta d’an ci abinci ba laifi
Abba sai murna yake yi, don haka yace “idan zata iya tazo suje k’asa suyi dinner da kowa (cikin mutane)”.

Sudais ne ya ruk’o hannunta na dama Abba kuma na hagu, Sakina sai murmushi take yi,
dan ba k’aramin burgeta suke yi ba sai wani lallab’a ta ake yi kamar kwai!
A haka suka sauk’o gwanin ban sha’awa.
Tayi tunanin a nan za suyi dinner d’in
amma sai taga sun nufi side d’in Daddy, Sakina ba dan taso ba ta bisu dan kwata kwata bata son abunda zai had’ata da Auwal, sam!.

A chan suka tarar da Aslam da Arshaad…
Basu samu Daddy a wajen dining d’inba amman an kammala jera komai.

Ba suyi 5 minutes da zama ba, su Daddy suka sauk’o shi da Auwal! Bai yi wata wata ba ya nemi kujerar dake gefen Sakina ya zauna Allah ya taimakeshi babu kowa a wajen.
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana jin wata nutsuwa ta musamman….

Sakina kuwa kamar ta tashi haka taji, kawai dai ta san su Abba za su d’an iya fahimtar wani abun shiyasa ta zauna saboda itafa ko a labari bata k’aunar a sako sunanta kusa da na Auwal!

Cikin kulawa aka shiga exchanging greetings..
Sai da aka gama gaggaisawa tukun Daddy yace “sorry i kept you waiting, Auwal ke hunger strike kamar wani baby abincin ma wai sai naje na lallab’ashi tukunna zai yarda yazo yaci”
Murmushi Aslam yayi, Abba kuma yace
“gashi kuwa duk ka rame, what’s wrong with you?”
Yayi maganar referring to Auwal d’in.

“Nothing”
kawai ya iya cewa yana sunkuyar da kanshi k’asa.

Murmushi Abban yayi, dan kamar yad’an gano Auwal d’in amman sai ya basar kawai aka fara cin abinci.

Arshaad ke zaune a kusa da Aslam Abba kuma na ata gefenshi (sun saka shi a tsakiya) Duk su biyun suna lura da yanda yake kallon Hudan wadda ke opposite d’insu akai akai!
Gaba d’aya Arshaad sai yaji ya damu sannan bai ji dad’in hakan da Aslam d’in yake yi ba kwata kwata!
Amman sai yayi ta k’ok’arin kawar da duk wani negative thinking a kanshi.
Ita kanta (Hudan) a takure take, gashi zuciyarta ta hanata sukuni.

Loma biyu kawai Sakina ta iya yi cikin kwanciyar hankali dan tunda Auwal ya fara mata
‘Hi’
‘How are you?’
D’insa taji wani malolo ya tokare mata mak’oshi!
Bata san lokacin da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login