Showing 75001 words to 78000 words out of 109746 words

Chapter 26 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2934

ta zama fiancé d’intasa ba amma ji yanda yake yi a kanta,
what if ta zama?”.

Murmushi yayi kafin yace
“Saura sati uku bikin.”

Da sauri Aaima ta kalle shi
sai kuma ta fashe da kuka tana cewa
“Kaga irin abunda rashin Mammy a kusa kan jawo ko?
Ni Ina ma na san da wani engagement balle maganar aure!
Kana gani fa Ya Aslam muna waya muna chattn kusan kullum amman no one even bothers to tell me…da ga zuwan Yarinya ta hargitsa gida yanzu tana shirin hargitsa zumunci sannan a haka kace ba bad luck bace ba?”

Lumshe idanunsa kawai Aslam yayi yana nan zaune a yanda ta barshi ya na jin ta.
Cinkin kuka tace
“Wallahi Ya Aslam kar ma ku bari In had’u da Yarinyar nan!
Bana jin akwai wanda yake jin tsanar d’anuwa kamar yanda nake jin tsanar Huda a raina a yanzu atake naji tsanar ta ta dabaibaye ni.
Ko da wasa muka had’u Allah sai na illatata!
Tayaya ma za a bar Ya Arshaad ya aureta bayan
na tabbatar da Mammy ba zata so ba.”
Cikin kukan ta sauk’o ta durk’usa a gaban Aslam sannan ta hau jijjigashi tana cewa
“Dan Allah in kowa yak’i fad’a mishi gaskiya Ya Aslam kai ka gaya mishi….in dai yana neman albarkar aure
tou kar ya kwaso ta!
Mammy ba zata saka ba na sani kuma ya kamata ya fahimci bad luck ce ita.”

Surutun Aaima ya isheshi har ga Allah, dan tun d’azu daurewa kawai yake yi, hakan yasa ya bud’e idanunsa da niyyar yi mata magana
ya ga ta zabura ta jaa baya a firgice.

Cikin tsananin mamaki take kallon yadda kwayar idanunsa suka yi wani irin jaaa lokaci guda.

A hankali ya mik’e sannan yace mata “Kiyi hak’uri Aaima, na san dole za kiji zafin rashin Mammy a kusa.
Bara inje in d’an huta, anjima kad’an zan dawo mu je dake kiga Mammyn.”
Yana gama fad’an haka yayi hanyar fita da sauri ya fice
dan so yake yayi nesa da Aaima a yanzu saboda
gudun aikata aikin da na sani...........

BULAMA ✍️


So da Buri
Free Book
49


An gama yi mata gyaran jiki kenan, Arshaad ya zo.

Dama tunda ya kira ta yace ‘gashi nan zuwa’, tayi sauri ta tashi akan turaren wutan da take a kai ta fad’a wanka.

Tana cikin d’aura d’ankwalinta ta fara jiyo hayaniyar shi da su Sudais! Kasancewar a d’akin k’asa suke yin gyaran jikin.

Loose gown ce a jikinta kalar kwanduwar kwai mai haske,
dan haka kawai ta d’an d’aura d’ankwalin ta zagayo da edges d’in ta bayan k’eyarta ta sake su suka zubo akan k’irjinta
wanda hakan yayi kamar mayafi saboda d’ankwalin yana da d’an girma.

Waya ya fara mata dan haka tayi sauri ta fita, ta bar Sakina wadda ake k’arasa mata nata yanzu.

Bai ga fitowarta ba, dan haka ya sake d’aga wayar yayi dialing numberta ya kara a kunnenshi…
Har ga Allah baya iya b’oye zalamarshi when it comes to Hudan! Y’ar tafiyar nan da yayi ya sanya ya sake fahimtar tsananin mugun k’aunarta da yake yi! Duk da cewa suna waya amman ji yake kamar yayi irin shekarar nan bai ganta ba! Ko dan tak’i yarda su yi video call ne may be shiyasa, he wonders why tak’i yarda suyi video call d’in
Sakina dai tace mishi gyara ake mata kuma in ya ganta idan ya zo ba lalle ya biya kud’in gyaran da kyau ba, ba yadda bai yi dasu ba amman fur itama Huda tak’i yadda ta bashi had’in kai ya gantan…
Yana cikin wannan tunanin ya fara jiyo wani k’amshi mai mugun fitinannen dad’i, a take yaji jikinshi ya mutu!

A hankali yake jin k’amshin na sake shigar mishi hanci yana sake karad’e ko ina yana sake kashe mishi jiki..

Sai da ta kusan k’arasowa inda yake tukunna ya samu k’arfin jikin juyawa sakamokon jin takun tafiyarta wanda flat shoe d’in k’afarta ke badawa…

Yana juyowa suka had’a ido!
Tsayawa kawai yayi ya kasa ci gaba da motsi, kamar wani statue.

“Ya Arshaad wayarka”
D’in da Sudais (waenda suke tare dashi a parlourn, d’an gefe kad’an da shi) yace masa ne ya d’an dawo dashi daga duniyar da ya lula.
A hankali ya rik’o wayar wadda ta kusan zamewa daga hannunshi kafin ya iya
cewa
“Lafiya, ya gida?”
Still yana kallonta.

Hudan ita kuwa kunyar kallon take ji, dan haka ta fara kame kame ta kasa cewa komai bayan gaisuwar da tayi masa.
Sun yi kusan minti biyu a haka!
Ganin bashi da niyyar d’auke idanunsa daga kanta yasa ta sake cewa ”Ya hanya?
Ka dawo lafiya?”

“Alhamdulillah”
Ya ce kawai ya ci gaba da abinda yasa a gaba…

Wani irin kallo yake yi mata, tun daga kan y’an yatsun k’afarta har kan d’ankwalinta idan ya dire sai ya sake komawa daga inda ya faro kamar ya samu tv.

Ganin abun nashi ba na k’are bane ba yasa tace
“Ya Arshaad dan Allah ka daina kallona”
Tana rufe fuskarta da tafin hannunta, a shagwab’a.
Hakan da tayi kuwa ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Sorry na daina.
Ina Sakina? Kice tazo ta karb’i tukuici mai tsoka.”
Ya fadi hakan a kasalance
still bai daina kallon nata ba sai dai yanzu ya fara motsi ba kamar d’azu da ya k’ame ba.

Cikin son kawo k’arshen kallon tace “Ana yi mata gyaran jiki, in ta gama zata fito.
Ka je kaci abinci yanzu, da kaina na yi maka girkin.”
Ta fad’a tana sunkuyar da kanta k’asa.

Wani sassanyan murmushi Arshaad yayi, yana mai jinsa a sama! Farin cikin da yake ciki yau anya zai iya misaltuwa kuwa? Cikin murmushin yace
“Anya Huda ranar da aka ce an d’aura mana aure ba zan mutu dan dad’i ba kuwa?”.
Da sauri ta d’ago ta kalleshi, sai kuma ta tura baki ta kauda kai ta d’an b’ata rai.
Dariya yayi this time around kafin yace “Sorry tou, ba zan suma dan dad’i ba kuwa?
Just looking at you fa da kuma jin wai kin yi min girki da waennan kyawawan hannayen naki! Wallahi ji nake kamar in yi ihu dan murna, Ina kuma ga in akace kin zama mallakina gaba d’aya?”

Dariya ta d’anyi tana me sunkuyar da kanta k’asa, kafin tace “To muje kaci kar ya huce”.

Ya lura ta gaji da kallon shiyasa take ta so su bar wajen ta samu su daina facing d’in juna, dan haka yayi murmushi kawai kafin yace
“Mu je tou”
A ranshi ya raya
‘I can’t help it, ni kaina inaso In d’an janye idon but na kasa.’

Ita tayi serving nashi bayan sun isa dining d’in, kamar yanda yayi zato kuwa, tana gamawa ta nemi kujera ta hud’un wadda yake kai a side d’inshi ta zauna.

Dariya ta bashi dan haka sai da ya d’anyi dariyarshi tukun ya mik’e yaje inda take yace
“Tashi ki ga”
Rau rau tayi da ido
za tayi magana yace
“Shiiii, taso”

A hankali ta mik’e ta bishi.
Sai da ya zagaya d’ayan side d’in tukunna ya zaunar da ita a kujerar da take setin tashi
Kamar za tayi kuka tace
“Ya Arshaad to kar ka kalleni”

Dariya yayi yace
“Tou” kawai, ya zagaya ya zauna ya fara cin abincin shi
yana santi yana kallon nata da bata so.

Ko plate d’in abincin baya kalla, kawai spoon yake sakawa ya d’ebo ya kai baki, dad’i har kwanyarshi.

Suna a haka Sakina ta fito,
jin an bud’e k’ofa kuma an nufo dining d’in ne ya sanya ya d’an
juya.
Murmushi yayi kafin yace
“Ta hannun dama! Kina da babbar kyauta yau.”

Cikin dariya Sakina ta k’araso suka gaisa tayi mishi sannu da zuwa.

Fitowar Abba wanda zai fita ne
yasa tace musu “tana zuwa” tabi bayan Abban wanda ya nufi waje bayan sun gama gaisawa da su Arshaad d’in.

Ganin ta biyo shi ne yasa ya d’an tsaya a y’ar varendar bakin main door d’in,
tana k’arasowa Auwal shima yana isowa wajen!
Ai kuwa ta had’e rai ta cuno baki ta d’auke kai. Shi kuwa Auwal gaba d’aya numfashinsa sama yaji yayi, da kyar ya samu ya seseta kanshi, ya shiga gaida Abba cikin nutsuwar da Abban bai tab’a saninshi da ita ba.

Murmushi Abban yayi bayan sun gaisa yace “wuta da auduga” yana kallon Sakinar da ta d’an kalleshi kad’an,
kunya ce ta rufeta dan haka tace “Ya auwal Ina wuni”
Murmushi yayi wanda ya baiiyyana dimple da tsantsar kyawun fuskarshi, kafin yace
“Lafiya, ya gida? Kwana biyu”
Cikin takaici tace
“Alhamdulillah”

Abba ne ya katsesu ta hanyar cewa
“You were saying?” yana kallon Sakina had’e da kallon agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunshi.

Bataso yin maganar a gaban Auwal ba amman ba yadda ta iya, hakan yasa tace
“Um daman Abba, wai pre wedding picture nake so inyi surprising su Hudan da shi, In ba damuwa, please.”

Dan k’uraa mata ido yayi, kafin yace
“Okay, banda shirme.”
Sannan ya juya har zai wuce sai kuma ya juyo yace
“Kina buk’atar cash ko?”
Yayi maganar yana mai zura hannunshi a aljihu.

Dasauri Auwal yace
“No. Abba I’ll take care of it.”

“Okay” kawai Abban yace, dan sauri yake yi, yayi gaba ya bar su a wajen.

Murmushi Auwal yayi kafin ya dawo dai dai setin Sakina inda ta kawar da kai ta mayar da fuskarta ta, yace
“For this surprises sake za a d’an kula ni ko?
Na wuni d’aya tak dai?”
Ya k’arashe maganar yana karyar da wuyanshi sannan ya maida fuskarshi kalar tausayi.

Kallonshi tayi, bakinta na d’an motsi, tana son yin magana amman yanda idanuwanshi ya sarke da nata ne, ya sanya ta kasa cewa komai.

A hankali ya lumshe idanunsa ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciyar da har sai da ta jiyo hucin numfashinsa mai d’umi wanda ya had’e da wani calm scent da kuma k’amshin turarenshi…
tana shirin d’auke idanunta daga kan kyakkyawar fuskarshi, ya bud’e idanunshi
cikin hikima ya sake yin nasarar sark’e kwayar idanuwan nasu waje d’aya, a hankali taji yace
“I love you!”.

Gabanta ne ya bada wani ‘Dumm!! Da masifar k’arfin da bata san dalili ba....

Da kyar ta aro jarumta ta yafa, da mugun k’ok’ari tayi nasarar zare kwayar idanunta a nashi k’irjinta na ci gaba da dukan uku uku.
Harara ta zabga masa, ba tare da ta yarda ta sake kallon cikin idanunshiba had’e da yin tsaki sannan ta juya da mugun sauri zata shiga ciki..a ranta tana aiyyana
‘Tabbas Auwal tantirin shed’an ne!’ Dan gashi yana k’ok’arin rusa mata tsari cikin mintunan da basu gaza ashirin ba…


Da kyar ya iya had’a kuzarin da ya bashi nasarar shan gabanta, ya tsaya a bakin k’ofar, dan ba k’adan ba jikinshi yayi mugun yin weak!
Da sauri ya had’a hannuwanshi biyu waje d’aya kafin yace
“I’m sorry? so sorry ba zan k’ara ba.
Please lets just..
Bari in kira wanda na san zai yi, a Kano yake yanzu nan zai zo, professional ne, okay?”
Ya k’arashe maganar da alamun serious a kan fuskanshi, yana mai d’aga mata gira duka biyu da d’an ware ido.

“Unhm”
Kawai tace sannan ta koma gefe tayi folding hannayenta tana kallon wani waje.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, ya fara k’ok’arin dialing number mai hoton….

A gabanta suka yi waya sukai fixing time @5:00 pm
Zai k’araso, nan da 2 hours kenan.

Suna gama wayar tace “thankyou” kawai sannan ta fara k’ok’arin wucewa.

A hankali yace
“Am, Sakina… i”.

Da sauri ta d’aga mishi hannu d’aya, alamar (stop)
Kafin tace
“Ya Auwal please..
Ka kyale ni!
Bana so!.
I’m in a very serious relationship, besides ko ma bana dating d’in kowa I will never ever choose you! After what you did to Jalila kuma still ka ke dodging..
Kullum ko sunan ka naji an kira abunda nake tunowa kenan!.
Ban shirya auren bazawari ba, ko da ace maza sun k’are ina rok’on Allah kar ya d’aura min k’addarar auren bazawari second hand.”

Auwal bai san san ya akai ba, amman tabbas kamar hawaye yake ji suna shirin zubo mishi.

Ita kanta Sakinar ta lura da yanda idanunshi suke kyallin hawaye. Jikinta ne ya d’anyi sanyi dan haka
ta yi k’ok’ari ta danne ragowar maganganun da take ji suna taso mata.

A hankali yace
“Sakina na rantse miki da Allah a yanda nake jin ki a cikin zuciyata, ba abunda ba zan iya sacrificing akan ki ba, kuma babu abunda ba zan iya yi a kanki ba, zan iya chanja kaina in koma yadda kike so na zama, muddin zaki yarda da ni.
I don’t know how why but ni kaina ina jin tsoron kalar k’aunar da nake yi miki! I just knew you but i have fallen head over heels…
Na tabbatar ba wanda ya tab’a yiwa wata kalar pure love d’in da nake yi miki..
Ba wai wani abu daban ba
kawai k’aunarki, yardarki, soul d’inki shi nake muradi.”
Ya k’arashe maganar cikin karyewar zuciya.

Shiruu, tayi kawai tayi k’asa da kanta, bata k’aunar abunda zai sa ta sake had’a ido da shi.
A hankali tace
“Ka rabu da ni!
Dan Allah.”

Yana shirin yin magana Arshaad ya bud’e k’ofa
Hudan na a bayan sa.

Juyawa Auwal d’in yayi
aka hau kallon kallo..,,

Arshaad ne ya katse shirun ta hanyar mik’awa Auwal hannu suka yi musabaha, a hankali Hudan ita kuma ta gaidashi.
Yana amsawa ya wuce ya nufi part d’insu yana ji kamar zuciyarshi zata fashe! Tabbas ya san ba komai ke binshi ba sai hakki..Hakkin y’an matan da ya yaudara, da waenda ya wulak’anta, da waenda yayi mocking soyayyar da suke yi mishi! Duk hakkin su ne yake binshi. Yayi mocking soyayya, ya yaudari dayawa ta hanyar kalmar soyayya, ya wulak’anta dayawa dan sun nuna mishi zallar soyayya, shiyasa shi kuma yanzu Allah ya d’aura mishi tsantsar so mai mugun zafi da azabtar da zuciya
wanda ya san wadda yake yi wa ba lalle ta soshi ba,
gashi yanzu ma direct ta fad’a mishi ‘she’s in a very serious relationship’ wanda hakan sai da ya kusan kasheshi ba tare da ta lura ba.
Daman haka so yake?
Dama haka mutum yake ji?
Tabbas shi kam ya san ajalinshi..dan muddin Sakina bata yarda dashi ba akwai matsala! Ranar kuwa da akace ta auri wanda take ik’irarin suna tare d’in ya san a ranar zai bar duniya……
Yana wannan lissafin da tunanin ya k’arasa b’angarensu, direct side nasa ya nufa, yana zuwa ya rufe ko Ina ya k’ara k’arfin ac ya zxube a kan kujera, ko d’aki kasa k’arasawa yayi..........



Hudan ta bud’e baki kenan zata yi magana Sakina tayi sauri ta wucesu ta shige ciki.
Direct sama d’akin Hudan ta nufa, ta dad’e ta kusan awa d’aya tana juyi a kan gado ita kad’ai, daga baya ta hak’ura ta sauk’o.
Suna zaune suna hira su Sudais suna gefe suna chess,
tun da suka dawo daga karb’o gown d’in ta (Hudan) wadda delivery man ya kawo suke zuba idon ganinta amman bata sauk’o ba, Hudan taso zuwa amman Arshaad ya hanata…
.....Sakina bata dace da Auwal ba at all, amman in haka Allah ya tsara basu da damar shiga tsakani, besides yayi mamakin changes d’in da yake gani a Auwal those days, maybe in ya samu wadda yake so ya aura a samu ya nutsu!
Ko a office yanzu ya daina biye biyen matan da a daa yake yi kamar bunsuru....
Arshaad, yana wannan tunanin yaji sauk’owarta dan haka ya juyo yana kallon yanda take tafiya a hankali kamar ba Sakina ba.

Cikin kulawa yace
“Sai yanzu?”

Murmushi tayi tace
“Bacci ne ya kwashe ni”

Shima murmushin kawai yayi
Hudan kuwa bata ce mata uffan ba…
So take sai sun keb’e tukunna
dan tabbas In tunanin ta ya bata dai dai to Sakina tana k’ok’arin rufta kanta inda dai dace ba.

Suna zaune Auwal ya shigo,
kujerar da Sakina ke kai 2 seater yaje ya zauna ya fara yi mata magana k’asa k’asa..
Ga mamakin Hudan sai taga Sakinar ta biyeshi, suna ta
k’us k’us daga baya kuma ta mik’e ta cewa Hudan “ta zo taji”, shi kuma ya mik’e ya juya ya nufi hanyar fita.

Binta Hudan tayi, suna kaiwa hanyar bene ta rik’o hannun Sakinar wadda ta fara taka stairs.. Juyowa tayi tana kallon ta, k’asa k’asa Huda tace
“Sakina kar fa ki biyewa Ya Auwal!
Naga kamar ya fara cin galaba a kanki. Kin san Allah kuwa dan iska ne!
Ranar da muka je Munjibir park baki ga y.....”

Da sauri Sakina ta matsa kusa da ita ta sa hannuta ta toshe mata baki!
Tun lokacin da Hudan ta fara magana taga tahowarshi, tana so ta hanata taga ya sa hannu ya d’aura akan lips d’inshi alamun tayi shiru yana d’an murmushi
Bama jin Hudan take yi sosai ba saboda gaba d’aya hankalinta ya tafi wajenshi sai da taji tana neman b’aro musu aiki tukunna...


Kallonta Hudan take,
tana “hum um hum um”
Alamun ta saki mata baki.
Ganin tak’i barinta
ya sa ta sa hannu ta janye hannun Sakinar akan bakinta
kafin tace
“Dan na fad’a miki gaskiya shine kike k’ok’arin kasheni? Har da hancina fa kika toshe.
Kin san Allah, tou su Ummu zan gayawa dan ba zai yiu inaji ina gani ki kula d’a is....”
Da sauri Sakina tace
“Shhh, behind u.”

Tsit! Hudan tayi kamar ruwa ya cinye ta, a hankali kuma ta juya…
Karaff! Suka had’a ido da Auwal, yana d’an murmushi yana kallonsu.

Hudan ta san gaskiya ta fad’a, amman sai ta tsinci kanta da jin mugun kunyar shi…
Juyawa kawai tayi ta haye sama, Sakina kuma ta tsaya, ta fad’a mishi amsar abinda ya manta bai tambayeta ba, har ta kaishi ga dawowa.

Bata dad’e da shiga ba Sakina itama ta shigo.
A parlournta ta sameta, dan haka ta zauna akan hannun kujerar da take kai kafin tace
“Hudan, dan Allah ki daina had’a ni da wannan mutumin, na fad’a miki ba zan tab’a sauraron sa ba, infact kin san ina da wanda zan aura ko?.
Kinaso ki san maganar me muke yi?”

Sai da ta d’an k’uraa mata ido, tukun tace
“Eh”

Murmushi Sakina tayi kafin tace “Zo muje d’aki to ki shirya, in yaso muna sauk’a k’asa zaki gani.
Kamar tayi mata musu, sai kuma ta mik’e ta bita.

Suna shiga taga Sakina tanata fito da kayan kwalliya, aikuwa tace bata san zance ba!
Dan in akwai abinda Hudan ta tsana to a shafa mata foundation da concealer, ji takeyi kamar anyi mata suminti a fuska, sometimes har numfashin ta take ji yana d’an yin sama sama, bata tab’a jin iskar gari sai ta wanke.”

Ba kalar rok’on da Sakina bata yi mata ba, amman furr tace “wallahi ba da itaba, ko me za ai sai dai ayi a haka” ita a tunanin ta ma ko wani get together su Sakinar suka had’a, dan tace mata surprise ne suka had’a musu ita da Auwal.

Abunda kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login