Showing 39001 words to 42000 words out of 109746 words

Chapter 14 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2927

k’araso cikin parlour…

Wani killer smile Auwal yayi kafin ya mik’e tsaye yace
“D’an halak! Maganar ka muke yi”

Cikin nutsuwa Arshaad d’in ya k’araso inda suke, kallon Jalila yayi yaga yanda take kuka, a ranshi yana mamakin ina Auwal ya samota haka, gashi sai kuka take yi…
Ganin ba wannan ne ya kawo shi ba yasa ya d’auke idonshi a kanta ya maida kan Auwal d’in sannan yace
“Daddy is waiting, infact everyone, for you, kayi sauri dan yace karka bari yazo ya sameka a nan!”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fara k’ok’arin fita.

Da mamaki Auwal yake kallonshi da Jalilan wadda tunda Arshaad d’in ya fara magana take kallonshi,
Ganin arshaad d’in na shirin fita ba tare da ya ma sake kallon Jalilan ba yasa Auwal yin ta maza ya zagaya ya tsaya a gaban shi sannan yace
“Saurin me kake yi? I’m just trying to clean up your mess here fa, amman kayi kamar ma baka santa ba, ko In barta ta tafi wajen su Abba ne?”

D’an dakatawa Arshaad yayi sai kuma ya juya yana kallon Jalilan..
Da ido Auwal yayi mata signal d’in da ta kasa ganewa, ita dai kawai sai ta mik’e, kamar an tsoma ta a ruwa jikinta na d’an rawa.

Murmushi Auwal d’in yayi sannan ya zagayo yace
“Talk mana Jalila, ko tsoronshi kike ji yau kuma?”

Kame kame Jalila ta fara yi, ta rasa ta Ina zata fara dan Bata san me zata ce ba, gashi duk da halin da take ciki tunda taji Auwal ya ambaci miliyan biyar ta rikice, hali zanen dutse!.
Don haka tace
“Daman nazo ne akan maganar mu”
Tayi maganar jikina na d’an karkarwa dan har yanxu k’irjinta bugawa yake yi…
yau ce rana ta farko data tsaya ta k’arewa Arshaad kallo!!
Ita dai tun lokacin da yake zuwa wajen Hudan ta san yana burgeta kuma yanayin shi, maganarsa, tsayi da k’amshin turarenshi suna mugun k’ara kid’imata!
Kawai dai ita ta san tana so Arshaad har cikin zuciyarta, amman yau data tsaya ta k’are mishi kallo ta sake rikicewa kuma ta tabbatar idan har bata sameshiba to ko dai ta mutu ko kuma ta shiga hauka…

K’irjinta in banda bugawa babu abinda yake yi, gashi ya tsareta da dogayen shanyayyun idanuwanshi, cikin tsare gida yace
“Wacce magana kenan??
Do i know you?”

Wata dariya Auwal ya saka kafin ya k’araso yana cewa “Okayy!! Bari in yi maka dalla dalla..
Maganar cikinka wanda ke a jikinta! Shi ta biyo ka ku k’arasa.”

Arshaad zuwa yanzu yazo wuya! Don haka ya yanke shawarar cin uban Auwal dan ya lura bayan rainin hankalin da yake yi mishi, harda hauka ma ya fara damunshi kwana biyu, gara a yita ta k’are ko zai dawo hankalin shi, in hauka ya za ayi ya d’auko Yarinyar da bai tab’a ganiba a rayuwarshi ya hau yi mishi wani maganan banza da wofi??!

A fusace ya juyo yana shirin yin kan Auwal, sukaji k’arar fad’uwar abu, da sauri duk suka juya suna kallon k’ofa..

Arshaad, ya san yana da gaskiya amman kalar kallon tuhumar da Hudan take yi mishi da kuma yanayin fuskantar, ne
ya sanya gabanshi yayi mugun fad’uwa sannan wata zazzafar zufa ta hau keto mishi, tabbas ya san taji shirmen da Auwal ya gama fad’a yanzu.
Auwal kam tsayawa yayi yana kallonta yana mamakin tsananin kamanninta da Abba da Aslam!
“Who’s she!?”
Ya fad’a a hankali ba tare da kowa ya jishi ba.
Chan kuma sai ya tuno da case din y’ar gidan Abba da har ta kaiga kulle su Mom d’inshi a cell!
Antake kwakwalwarshi ta d’au chaji, don haka a zafafe ya nufeta, daman neman ta yake yi ya kora mata warning!!
Jalila kuwa tsorone ya rufeta ganin Huda, a tunanin ta Umma ce ta fad’i inda take, su kuma suka zo har da su Kaka tafiya da ita, dan haka karkarwar jikinta ya tsananta ba abunda take tunawa irin auren ta da Mati mai wanki ta san yanzu kam babu fashi!.

Cikin zafin nama Auwal yana karasawa inda Huda take tsaye yace
“Hey! Couz…
You must be Huda right?
Inaso kije ki samu uban ki kice mishi......”

Cikin katseshi Arshaad wanda shima ya k’araso inda take yanzun yace
“Huda lets go don’t mind him, he’s crazy!!
Muje kawai za mu yi magana a waje.”
Ya k’arashe maganar yana durk’usawa don k’ok’arin d’aukar wayarshi data jifar a k’asa.

Hudan ita kanta bata san tana da kishi irin haka ba, sai yau. Wato ba zai ma iya fuskantanta a gaban Jalilan ba?!
Gashi yadda duk ya rikice jikinshi yana d’an karkarwa yasa ta d’aura ayar tambaya akanshi…
Ita Arshaad zai yiwa haka? Why? Of all people kuma yayarta!!!
Bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba!.

Ai kuwa a rikice, Arshaad yace
“Oh nooo, Huda dan Allah kar muyi haka dake mana, na rantse miki da girman Allah ban san wacece waccar ba!
Ban tab’a ganinta ba a rayuwata, wallahi!
Muje waje we ‘ll talk outside.”
Yai maganan yana k’ok’arin kama hannunta..

Da sauri ta fisge cikin kuka tace
“Don’t touch me! Ai dole kace baka santa ba mana, Ya Jalilan ce baka sani ba?
Daman Mama tace min rannan kaje kana nemanta, kuma nima naji Umma ma rannan suna wani magana da Anty Zainab dana kasa fahimta a kanka kaida Ya Jalila.
And if baka santa ba mai take yi a nan ya akayi ta san gidanku da ni kaina ban saniba?
Ana tunanin tana gidan Anty d’inta a gida ashe tana wajen ka!
I trusted you,I tot.....”

Arshaad kam zuwa yanzu ranshi yayi mugun b’aci dan a tunaninshi ko Sakina ce zata fad’awa Hudan wannan maganar a kanshi bai ci ache ta yarda ba, balle a bakin mutumin da bata tab’a gani ba sai yau!
Dan haka cikin katseta yace
“Ba kiyi trusting d’ina ba Huda! Tunda gashi har kin d’auki maganan da aka fad’a miki a kaina…
Rantsuwa ta k’arshe da zan yi miki shine ‘wallahi ban san Yarinyar nan ba!’ Mutum d’aya na sani a gidanku age mate d’inki itace Sakina. Kuma ban san wanne Arshaad d’inne yaje nemanta gida ba rannan d’in da kikace, amman bani bane ba!. Maganar su Umman shima i don’t know anything about it, wallahi!.
Anyways
Na gode da irin shaidar da kika yi mini..
Hudan aure za muyi ya kamata ace kinyi trusting d’ina tunda as far as i know inda ace ni d’an iskane da tuni ke zaki fara fad’a ba wai ita ko shi ba.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita dan in ya ci gaba da tsayawa a wajen zai iya yin abunda zai yi ending up yana regretting…

A hankali Hudan ta k’arasa ciki wajen Jalila ta kama hannun ta kafin tace
“Ya Jalila”
Cikin kukan makirci Jalila ta fashe da kuka ta rungune Hudan kafin tace “Hudan Allah da gaske ne abunda Auwal ya fad’a yanzu, gashi na kasa fad’awa kowa, ban san ya zanyi ba! Arshaad ya cuceni.”
Ta k’arashe maganar da wani mugun kuka, don ta lura Hudan ta yarda da ita,,dukda kuwa
har yanzu tana cikin rud’u akan ‘’me Hudan take yi a gidan’ Dan kalaman Auwal da yadda yace mata cousin ya sake dilmiyar da tunanin ta…
Amman yanzu ba wannan ne a gabantaba, raba Hudan da Arshaad shine first! Ga kuma zancen miliyan biyar! Don haka dole ta ajjiye komai a gefe ta duk’ufa ta cimma burinta.

Da kyar Hudan ta lallasheta, ta samu tayi shiru..
Rasa abunyi yasa Huda tace mata “bara taje ta dawo”
da taso ta tafi da ita, amman tak’i, dan haka ta mik’e tace “tana zuwa, tukunna sai su san me za suyi”

Cikin share ragowan hawayenta ta d’agawa Hudan kai, Hudan kuma ta fita a zuciyarta tana rayawa yanzu zata kira su Ummu dan ba zata iya wannan abun ita kad’ai ba! dole a kwatarma Jalila hakk’inta, tana tafe zuciyarta na tafarfasa, ita kawai idonta ya rufe da kishi har ya kaita ga kasa yin lisaafi mai kyau a kwakwalwarta.

Jalila na ganin fitar Huda ta share hawayenta ranta fess!
Sannan ta mik’e ta k’arasa inda Auwal ya daskare yake k’ok’arin hada 1+1 akan alamarin da ya gudana yanzun nan dan in dai shi ba dak’ik’i bane ba tou abu na farko daya fara fahimta shine ‘Arshaad Huda yake dating!’ And tabbas bai san Jalila ba, to who…..
Muryar Jalila wadda ta k’araso yanzu ne ta katseshi jin tana cewa
“Nayi duk abunda kace, yanzu abunda nakeso da kai shine ka kawo miliyan d’aya, ragowar kuma in aiki ya kusan kammaluwa, dan..”
Shak’ar!! Da yayi mata ce ta katse mata maganar tata, cikin d’acin zuciya da k’arfi yace
“Who are you?”.

BULAMA ✍️


So da Buri
Free Book
40


Sai da yaga numfashinta yana shirin d’aukewa tukunna yayi wurgi da ita sannan ya sake jeho mata tambayar
“who are you??”
Yana huci.

Cikin tsananin tsoro Jalila take kallonshi kafin ta ankara taga ya sake yiyowa kanta yana shirin damk’ar wuyanta a karo na biyu, yace
“Naga take taken baki da shirin fad’amin gaskiya ta cikin sauk’i!”

Da sauri cike da tsoro Jalila tace “me kakeso ka sani to?”
Tana mai ja da baya.

“Wacece ke!
Meye alak’ar ki da Arshaad sannan mecece alak’ar shi da wachchar Yarinyar??!”

Da sauri tace “wajenta yake zuwa a gidanmu! Ni ban tab’a ganinshi sosai bama sai yau, ban sanshi ba bai sanni ba!
Ai kaine kace ince na sanshi, amman ni bamu tab’a magana bama sai yau!!”

Takaici ne ya hana Auwal yin magana..

Chaan, kuma cikin tsananin b’acin rai yace “kin san da duk wannan amma shine baki tab’a gayamin ba sai yau?”
Ya k’arashe maganar cikin tsawa!.

Jalila gaba d’aya duk ta rud’e ta gaza fahimtar inda Auwal ya dosa.
Gashi yadda taga ranshi a b’ace tayi mugun tsorata
hakan yasa cikin rarrashi tace
“To ai naga nayi abunda ka fad’a ko?
Gashi har sunyi fad’a!
Menene kuma laifina a nan?”.

Da k’arfi yake sauk’e ajiyar zuciya!
Tabbas Micheal yayi masa shirme
to amman kuma ta bakin Jalilan ‘ai gashi sun yi fad’a!’
One of abunda yake so ya faru
ai farun ai at last!
But still ya zama dole ya koyawa Jalilan itama hankali..

Fuskar nan babu walwala ya kalle ta, kafin yace
“Mai yasa da na fara zuwa, baki fad’amin cewa baki da alak’a da shi ba?
Eh?
Kika barni a duhu?”

Cikin rashin fahimta tace
“Wallahi ni ban gane komai ba!
Dan Allah ka fahimci ni”.

Shiruuu, Auwal yayi yana d’an nazartarta yana kallonta..
Chaaan! Kuma yayi tsaki kafin yace “kije ki tattaro kayan ki,
ki wuce wajen Gwaggo Asabe, i’ll get back to you, idan kuma zaki zauna anan d’in ne to zan iya barinki but ki tuna abunda na fad’a miki d’azu!”.

Da sauri ta nufi d’akin ta na sama, kafin minti goma ta tattaro komai…


Auwal ji yake kamar ya shak’e ta yayi ta dukanta!
Kawai dai ya barta ne ya samu ta rabu dashi for now dan bayaso Daddy yazo kiranshi da kansa!
Amman tabbas sai ya koya mata hankali, dukda ya fahimci kamar jahilcinta da dak’ik’ancinta ne ya janyo komai..................



A gate d’in estate ta had’u da su duk sun fito har Gramma wadda ta kawo su Shuraim
don tun jiya da suka k’i bacci
da safe kuma suka dinga yiwa Abba kuka akan suna son Ummi ta dawo, ya kaisu wajenta.
Da kyar ta lallab’asu
bayan tace musu “Ummin tayi y’ar tafiya ne
amman soon za su dawo, suyi hak’uri.”

Hudan tana k’arasowa Gramma ta kamo ta, tace
“Ki kwantar da hankalinki
Ki bisu kinji, na san kina kewar Maman ki, amman na san Abba da kansa zai kaiki idan komai ya gama daidaituwa, kinji y’ar albarka?”.

Anhankali ta d’aga mata kai tanajin k’aunar matar da girman ta suna ratsa zuciyarta.
Dad shima abunda ya fad’a mata kenan sannan yace “duk abinda take buk’ata idan sunje ta rubuta ta bawa Arshaad ya kawo mishi,,already anyi mata d’an siyayyan abubuwan da zata buk’ata for now suna cikin mota.”
Da “to” da kuma godiya shima ta amsa mishi.

Auwal yana fitowa daga mik’a Jalila wajen Gwaggo Asabe suka fara shirin tafiya…
Abba ne ya bud’e mata gaban wata mota yace ta shiga, tana shirin shiga dai dai nan Gwaggo Asabe wadda ta fito yanzu ta k’araso taja Hudan tayi hugging d’inta, ji suke kamar kar su rabu dan har sun saba a cikin y’an wuni biyun da suka yi tare.

Auwal yana gefe in banda tab’e baki babu abunda yake yi, ji yake kamar yaje ya shak’e ta! Shi fa ya tsani yaga ana fifita wani, kuma ya lura kamar hakan a jinin y’an gidan yake! k’iri k’iri sun iya nuna banbanci…..gashi yanzu ma akan y’ar k’ank’anuwar Yarinya an kwashe Surukan gida kaf! An kai cell, an bar mahaukaciya!….
Ya ja tsaki yafi a k’irga k’arshema mota ya shige yana ta mita a ranshi yana cewa
“Kamar duk ba a tsatso d’aya muka fito ba!”
Mu an maida mu kamar wani bole especially ma ni….kowa idan ya tashi k’orafi sai kaji yace ‘Auwal’.”
Shi kad’ai haka yayi ta mita yana ta faman kumbure kumbure..


Su kam bama su san yana yi ba. Sallama suka yiwa juna
kafin Gramma ta ruk’o hannunta (Hudan) da kanta ta saka ta a mota ta juyo.

Daurewa kawai take yi, amman Abba yana zuwa da yayi hugging d’inta sai ta kasa ci gaba da daurewa ta fara hawaye.
Da kyar suka lallasheta sannan suka maidata gida,
suka fito, suka kama hanya ba dan ransu yanaso ba, suka
fice a estate d’in suna masu jin dumbin kewar gida cike a zuk’atansu.

Suna fita suka had’u da motar Kaka da Madu, horn suka d’anyi musu don haka suka dakata!
Dan shi Abba bai ma gane su ba.

A D’an gaba kad’an suka yi parkin, dan haka suma su Kaka suka juyo da akalar motar tasu suka isa inda suke suka yi parking….

Suna fitowa Abba ya ganesu dan haka ya k’arasa ya cewa su Aslam su zauna a motar,
shi da Dad kuma suka fita suka samesu.

Suna wucewa itama Hudan ta fara k’ok’arin bud’e k’ofar amman sai ta jita a rufe!
Cikin d’an tsare gida tace “zan je wajen Kakannina!”

A k’ufule yace
“Baza ki ba!”

Wani takaicine ya rufe ta taji kamar ta rufeshi da duka, taya ga su Kaka tana kallo suna kallonta, amman ace ba zata je wajensu ba? Inaaa, ba zai yiu ba!
Dan haka ta fara k’ok’arin bud’e k’ofar ta k’arfi! Tun k’arfinta.

Ta gefen ido yake kallonta,
tanata dambe da handle d’in motar, tun k’arfin ta.

Ta fi minti biyar tana fama ganin ta kasa yasa ta juyo da d’an ladabi tace
“Ya Aslam dan Allah ka bud’e inje wajen su mana.”

Ta bashi dariya sosai amman ya danne, still amsar d’azu ya sake maimaita mata babu alamun wasa a fuskarshi
“Baza ki ba!”

Wani k’ululun takaici ne ya tokare mak’ogwaronta, dama ga haushin Arshaad da take ji tun d’azu!
(Don Abba har yana shirin shiga motar da take amman ya janyeshi yace “yazo zai tuk’a shi”)
Yanzu gashi ya had’ata da wannan boss d’in!
Shi bai bari ta tafi da Abba ba kuma shi ma ya kasa shigowa su tafi tare ko dayake ta san
saboda yana jin kunyar had’a ido da ita ne shiyasa!
Kuma ya san koda ya shigo d’in ma fita zata yi ta bar mishi motar dan haka d’in ta gama shiryawa a ranta.
Amman kuma at least ai da ya gwada
Insted
yana kallonta amman ya shige motar Abba yaja suka tafi da shi da su Shuraim..
.....Abunda Huda bata sani ba shi kuwa Arshaad fushi ya d’auka da ita bana wasa ba ata dalilin zargin da tayi mishi!.


Bata iya rashin kunya ba amman bata san lokacin data tak’ark’are ta zabgawa Aslam wata uwar harara sannan ta murguda mishi baki ba!
A tunanin ta su Abba yake kallo dan direction d’insu taga yana kalla
amma abunda bata sani ba shine duk abunda take yi yana kallonta ta gefen idonshi.
Tunda yake a rayuwarshi bai tab’a ganin harara da murgud’a bakin da yayi matuk’ar burgeshi da bashi dariya irin wannan ba, hakan ya sanya wani sassanyan murmushin da ya dad’e bai yi ba wanzuwa akan kyakkyawar fuskarshi, wanda har sai da Hudan taji sautin murmushin tayi saurin juyowa tana kallonshi amman ga mamakinta sai taga still su Abba yaketa kallo waenda suka tsaye a setin su..
Gani tayi kamar Madu yana magana da fad’a fad’a!
Cikin takaici ta juyo tana kallon Aslam a ranta tana aiyyana “wato dan yaga ana fad’a shine yake murmushi, lallema wannan mutumin!.”

A chan wajen su Madu kuwa abu bai yi dad’i ba!
Dan tun farko da Madu ya tambayi Abba “dalilin da yasa ya d’auko Hudan lokaci guda haka?”
Abba ya k’ule!
A ganinsa dan mai yasa Madu zai yi mishi tambayar ‘dalilin d’aukar y’ar sa da yayi’ bayan shekaru da dama da yayi ba tare da ita ba!.

Daga k’arshe dai, Abba tafiya yayi ya bar wajen dan bayason yayi musu rashin kunya.

Daddy ne ya tabbatar musu da “sunje har unguwar da Hudan ta taso kuma sunji irin zaman da Huda tayi a gidan Baba, wajen mutane bakwai suka tambaya amman duk maganarsu d’aya ce! Ba abunda basu saniba a halin yanzu na irin zaman da Hudan tayi na azaba a hannun mutumin nan, har k’usar da Ja’afar ya buga mata a ciki suna da labari!”

Yace musu
“Tun jiya suke ta faman lallab’a Abba, da kyar suka samu ya hak’ura amma daa cewa yayi sai ya kulle Usman kuma yayi shariah da su!”

Daga k’arshe yace musu
“Dan haka, ko kotun da Madu yake ik’irarin zai je sai dai ya kulle kanshi da kanshi dan wannan dalili kad’ai ya isa a barma Abba custody d’in Huda!.”
Yana gama fadin haka shima yayi musu sallama cikin girmamawa ya wuce ya koma mota Auwal ya ja suka yi gaba suka barsu a wajen, daman su su Abba sun dad’e da wucewa.


Tunda suka shigo gidan Huda take bin had’add’en mansion d’in mai hawa biyu da kallo!
Har Aslam ya gama parking bata sani ba, sai da yace
“Na bud’e lock d’in, ki fita sai kin fi jin dad’in kallon!”

Tukunna ta dawo hankalinta, gaba d’aya kuma sai kunya ta lullub’eta.

A hankali tasa hannu ta bud’e ta fito, still mutane waenda suka kwashe kaya daga chan gidan sunata kai kawo, da alamun basu gama jeran ba, dan gashi har sets d’in kujeru wasu ba a shishshigar ba.
K’ofar shiga gidan biyu ne manya manya!
Kamar yadda Dad ya fad’a gidan wajen zaman mutum uku ne ma amma k’ofar farko ta gefen dama yafi girma dan wajen d’akuna sha biyar ne da faluka bakwai (shine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login