Showing 30001 words to 33000 words out of 109746 words

Chapter 11 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2923

Bashir za muje mu samu Abba, in shaa Allah, kinji ko??”
Da sauri Kaka yace
“Za muje a yau! Ki kwantar da hankalin ki kinji?”

A hankali taji kad’an daga cikin nauyin da zuciyarta tayi ya d’an sauk’a, dan haka ta d’aga musu kai alamar ‘to’ kawai,
tana sharar hawaye.


Ajiyar zuciya Baaba Talatu ta sauk’e, sannan ta nufi wajen kulolin da suka kawo ta zubowa Mama abinci ta kawo mata.
Sakina ce ta karb’a ta fara k’ok’arin bata, amma sai ta kauda kai gefe tace “ta k’oshi”
Cikin turo baki Sakina tace “haba Mama ki ce mana, kin ganki kuwa yadda kika koma? Gashi duk kin yi wata zuru zuru kamar…”
Dukan da Maman ta kawo mata tayi saurin kaucewa, duk kuwa sai suka hau murmushi….

Da naci da komai hakanan sai da Sakina ta d’urawa Mama abincin nan, ta kuwa ci sosai, dan sai da su Madu suka sa baki tukun Sakina ta hak’ura.

Sai wajen 11 na safe su Sakina suka fara shirin tafiya don suke suyi wanka suyi girki, ita da Ummu.

Baban su Sakina ne yazo d’aukar su!
Ya d’auka Mama ko wani zai yi mishi maganan Arshaad amman yaji shiru shiyasa shima yana yiwa Maman ‘ya jiki’ ya fita, dan baya so suyi mishi d’in, but ya tsara a ranshi zai gayawa matarshi, duk abinda ya sani, da kuma dalilin yin shirun da yai, saboda kar ayi mishi kallon munafuki.

Sai da suka biya duk wani bill sannan suka tafi
a lokacin an tafi da mama yi mata eco.
Su Kaka ma shirin tafiya gidan su Abba suka yi, aka bar Baaba Talatu. Sai a sannan ne Baba yazo, ganin Maman bata nan yasa suka gaisa da Baaba Talatu ya wuce kasuwa akan zai dawo da azahar in shaa Allah.

Su Kaka basu samu damar zuwa gidan su Abba ba, sai la’asar, a sakamokon kiran da aka yi musu akan results d’in da ya fito, dangane da case d’in Junaidu.........



Yadda Hudan taga rana haka taga dare, Gwaggo Asabe har mamakinta take yi dan duk juyi in tayi sai taga idonta biyu!
Gaba d’aya ta kasa bacci ta k’agu Safiya tayi taje taga jikin Maama, da taga safiya ta k’i yi k’arshe kawai mik’ewa tayi taje ta d’auro alwalla, tazo ta fara jero nafilfili.

Tana idar da sallar asuba kuwa bayan ta gama Azkar ta d’anyi karatu, ta shiga tayi wanka.
Tana fitowa ta tarar Gwaggo Asabe bata d’akin, hatta sallayar data barta akai ta nad’e.
Doguwar rigar da Gwaggo Asaben ta bata jiya had’e da Maclean da brush sabbi ta d’auka ta sanya, luckily ta samu comb a d’akin cikin drawer, dan haka ta goge shi da tissue sannan ta sa hannu ta zare ribbom d’inta ta hau ware tufkar da ta yiwa dogon gashinta wanda yanzu har ya kai tsakiyar bayanta….ita kanta tana mamakin yadda ya tofo a cikin shekara uku! Bayan askin dolen da Ya Jalila tayi mata…
Tunawa tayi da Jalila wadda Sakina tayi mata k’us k’us d’in Khadija tace mata ‘kamar ciki ne da ita( Jalilan)’ amman Umma tayi k’arya tace ‘ta tafi jinyar Hansai’.
A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya a ranta tana adduar ‘Allah yasa ba cikin ne da ita da gaske ba’
….abunka da zuciya mai kyau! gaba d’aya duk sai taji tausayin Yayar tata ya lullub’eta, don haka ta hau yi mata addua da fatan alkhairi, tanayi tana taje kanta.

Sai da ta gama tsaf, ta d’auko ribbon d’in ta tufke gashin a d’an k’asan tsakiyar kanta kad’an! Ganin yadda jelar take reto ne ya sanya ta kanannad’e gashin waje guda ta tura ta had’e da ribbon d’in,
d’ankwalin doguwar rigar ta d’auko tayi style d’in V da d’aurin very simple amman ba karamin kyau tayi ba, ga gashin data duk’unk’une ana iya hango santsi da kyallin shi da uban yawa dan d’ankwalin k’aramine sosai so bai gama rufewa ba.

Ta d’auko wayarta kenan zata kira su Mama ta ganta a kashe, ba chargi.
Ajiyar zuciya ta sauk’e, daman ta san za ai haka, dan tun jiya chrgin ta yayi low sosai.

Zama tayintana jiran Gwaggwo Asabe ta dawo ta ari wayarta ta kira su Mama don duk ta haddace nambobin su.
Kusan minti arbain taji shiru..
ga anxiety yana neman kashe ta! Shiyasa ta yanke shawarar mik’ewa, ta hau nemanta.

Bata wani sha wahalan neman nata ba, dan tana fitowa daga d’akin taji k’amshi ya cika ko Ina a gidan wanda hakan ne
ya tabbatar mata da inda take(Gwaggwo Asaben), dan haka ta nufi k’asa.
A k’ofar kitchen d’in suka had’u da Gwaggon, da tray a hannun ta, da kuma tea flask da ta rik’e da kyar.
Sai da Hudan da d’an rissinar da kai tukunna ta gaisheta.

Da kulawa Gwaggo Asabe ta amsa…
Har ga Allah ta dad’e bata had’u da Yarinya mai hankali da nutsuwa irin Huda ba, ga kyau tubarkallah…shiyasa lokaci guda suka saba, taji ta shiga ranta sosai!
Har k’asan zuciyarta take yiwa Aslam d’insu kwad’ayin auren Yarinyar saboda ta had’a komai ga kyau ga hankali ga nutsuwa gata y’ar uwarshi!
Sai dai kuma yadda taga Arshaad yana shige mata sosai, watak’il shi ne zai fara cewa yana sonta, dan jiya ta lura har wata y’ar hira suka tsaya yi a parlour, sai wani nan nan yake yi da ita…..
Hannu Huda ta saka tana k’ok’arin karb’ar tea flask d’in dake hannunta wanda hakan ne ya katse mata tunanin ta!
Ba musu ta sakar mata , dan itama tana jin yadda ya kusan fad’uwa.
A tare suka nufi hanyar sama, tana gaba Hudan na biye mata baya, wata hanya suka kuma d’auka bayan sun shanye stairs d’in,
nan ta sake hango wani bene,
benen suka bi suka hau, suna kaiwa k’arshe suka tarar ta wata y’ar k’ofa
A bud’e k’ofar take hakan yasa suka shige, dogon corridor ne sosai, sai k’ofofi biyu, d’aya a farko farko hanyar dama, d’ayar kuma a kusan k’arshen dogon corridor d’in ta hannun hagu,
Wadda itan taga Gwaggwon ta nufa, sai da suka iso bakin k’ofar, tukun suka tsaya!
Rik’on tray d’in Gwaggwo Asabe ta gyara sosai a hannu d’aya sanna tasa hannu tayi knocking, tukun taja ta tsaya, ta gyara ruk’on tray d’in.
Kusan minti biyu tukunna suka ji ance “come in”
Hudan ta kalla tace “tayi amfani da empty hand d’inta ta bud’e musu.”
Hakan tayi, bayan ta murd’a handle d’in a hankali ta d’an tura sai kuma ta matsawa Gwaggo Asabe don ta fara shiga..
Murmushi Gwaggon Asabe tayi sannan ta shige
Itama Hudan ta bita a baya.
Sai da ta rufe k’ofar tukun ta juyo ta fara kallon d’akin….

“Ma shaa Allah” tace, a ranta.
Ba zaka kirashi d’aki ba kuma ba zaka kirashi da parlour ba, ga set d’in kujeru har da k’aramin dining, da makekiyar tv d’in da bata tab’a ganin irin ta ba, ga kuma set d’in gado shima komai akwai,
royal, light blue da fari haka colour d’in kujeru da gadon suke, hatta pentin d’akin haka yake. Ga kuma wani glass door, wanda kana iya hango swimming pool da shuke shuke da kujerun shak’atawa.
K’auyanci ta fara, don a ranta ta hau rayawa “daman ana pool a sama? saman ma ta biyu!
Ita tunda take bata tab’a ganin d’aki mai girma sosai da kyau irin wannan ba!”……

Tunanin ta ne ya katse jin Dad yana cewa “Hudan k’araso mana ya kika tsaya a k’ofa?”.

Sai a lokacin hankalin ta ya kai kan Dad, da wata mata a zaune a gefen shi yana rik’e da hannunta.

Ji tayi kamar ta rusa kuka!! Da ta san gurinshi Gwaggo Asabe zata zo da bata biyo ta ba, kenan ita duk b’uyab da takeyi ma a banza, tunda gashi a gidanshi ma ta kwana ba tare data sani ba,
kuma yadda ya nuna it’s like ya san tana nan d’in, shikenan ta san yanzu zai kira Abba shi kuma ya hanata zuwa taga Mama.

Gwaggo Asabe ce ta katsemata tunani jin ta sake cewa “Huda k’araso mana.”

A hankali take takawa izuwa bakin gadon inda suke…

Taji Dad yana cewa
“Ashe da gaskiyar Abba, daman ya ce tana wajensu Aslam ni ban yarda ba,
sune suka kawota jiyan ko?”

D’an murmushi Gwaggo Asabe tayi kafin tace
“Eh jiya lokacin da ka kira ni, Arshaad bai dad’e da kawota ba, shi ya rakota.”

Hudan dake jin su duk sai taji jikinta yayi sanyi, ashe ita kad’ai take ta shirmen ta.
A hankali ta k’arasa wajen, kanta a k’asa.
Har k’asa ta durk’usa ta gaida Dad, wanda cikin tsananin son yake yiwa y’ar d’anuwan nasa yayi saurin kamo ta ya zaunar da ita a kan d’an stool d’in da yake facing d’inshi,
cikin kulawa ya amsa kafin ya hau tambayarta “ya kwanan bak’unta?”
“Alhamdulillah” kawai ta iya cewa kafin ta juya ta hau gaida matar gefen shi har sau biyu amman ba alamun zata amsa kuma ta kafeta da idanuwa!
Tana shirin sake gaidata a karo na uku ne
Dad ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an dafa Huda tukun yace
“Karki damu ba zata iya amsawa bane, amman ta fahimceki, tunda gashi tanata kallonki.”

Yana gama fad’in haka ya juya ga Gwaggo Asabe jin tana cewa “ga breakfast, watak’il taci tunda naga yanzu jikin da d’an sauk’i, ko?”
Shiru ya d’anyi kafin ya sauk’e wata ajiyar zuciya tukunna yace
“Sai addua fa, amman Alhamdulillah, ni fa da Granpa zai yarda wallahi da an hak’ura da wannan theraphy d’in, saboda duk lokacin da akaje aka yi aka dawo ni sai inga kamar abun k’aruwa ma yake yi, kwanaki fa har hira tana yi, amman yanzu kiga gaba d’aya sai a hankali, danfa baki ganta last two weeks ba
(Tym d’in da suka dawo. A Abuja), shiyasa ai na hanata dawowa nan, da kyar fa da addu’o’i tukunna abun yayi sauk’i ta dawo hakan.”

Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e kafin tace “nima dai gaskiya na dad’e da lura, magana ce kawai banaso.”

Cikin d’an fad’a Dad yace “Ai kuwa ta gama theraphy!
Dan a gaskiya, ko ance za aje, sai dai In kaita Abuja kawai muyi sati mu dawo, abu ba fad’ar Allah ba amman an maidashi kamar dole!?”

Kwalla Gwaggo Asabe ta share sannan tace
“Ai shima Granpa d’in naji yana cewa ‘daga wannan an gama’.”Cikin katseta Dad yace “ai tun last year yake cewa ‘daga wannan an gama daga wannan an gama’! Amman an kasa gamawa da gasken.”

Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e ranta duk ba dad’i da yanayin y’ar uwarta ta….
A hankali ta durk’usa ta fara serving abincin cikin mutuwar jiki.
Hudan itama duk jikinta yayi sanyi dan haka tace
“Allah ya bata lafiya”.
A hankali Dad ya d’an juya ya kalle ta sai kuma yace
“Ameen” cike da jin dad’in adduar tata.

Juyawa yayi ya kalli Mommy, gani yayi har yanzu Hudan take kallo, kamar tanaso ta tuna wani abun..
Bai gama fahimtar yanayin ta ba yaga ta d’aga hannunta sannan tayi amfani da yatsar ta manuniya wajen sai da Huda!
Gaba d’aya hankulansu kanta ya koma,
cikin rawar murya kamar ta mai koyan magana sukaji tace
“Aaa-sllam, ttanna kama ddda Aasllm d’Ina”

Ba Dad ba hatta Gwaggo Asabe sai da
gabanta yayi wani irin mahaukacin fad’uwa!!!
Rabon da Mommy ta kira sunan Aslam, tun kafin ta fad’o daga bene!

Gaba d’aya rawa jikin Dad ya d’auka, a hankali ya sa hannu ya juyo da fuskarta, ya kalli cikin idanunta sannan yace
“Kina so kiga Aslam d’in naki?”
Da sauri ta hau d’aga mishi kai, sai kuma hawaye, shaaarrrr suka zubo mata.

“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!”
Shine abunda Dad ya dinga maimaitawa, cikin kid’ima ya mik’e ya fita yana cewa “su Gwaggwon su tsaya gashi nan zuwa, kar kowa yaje koina.”

Ba ayi minti goma ba sai gashi ya turo k’ofa, rik’e da hannun Aslam Abba yana binsu a baya!
Cikin zumud’i yace “Ga Aslam d’in naki” ya fad’a yana tunkarar ta, yana cewa su Abba “komai yazo k’arshe in shaa Allah, Aslam yau da kanta ta kira sunank.........”
Razananniyar k’arar da ta fasa ce ta hanashi k’arasa maganar tashi, ta kuma rud’a duk wani wanda ke a cikin d’akin!!
Basu ida dawowa haiyyacinsu ba ta kuma sakin wata k’arar! Wadda kusan rabin estate d’in sai da aka ji!.
Cikin tsananin tashin hankali firgici kid’ima da tsoron da ya baiyyana k’arara a kwayar idanunta take nuna Aslam d’in tana kururuwa!

A kid’ime Dad wanda duk ya rud’e ya sake nufota still yana rik’e da hannun Aslam wanda ya sake shiga tsananin tashin hankali da rud’ani don shi Dad ce mishi yayi “yazo Mahaifiyarsa tana nemanshi yau da kanta!” Gashi yanzu kuma ya tarar da haka!….
K’arar da ta sake saki ne ya kid’ima su dan tafi ta ko yaushe! Sai kuma ta saki jiki rigif ta fad’i sumammiya akan gadon…..
Da sauri Aslam wanda idanuwanshi suka kad’a sukai jaa over, ya k’arasa inda take ya hau jijjigata yana kiranta amman bata motsi…….d’ago jajayen idanuwanshi yayi yana kallon Dad.
Gaba d’aya sai Dad d’in yaji tausayin su, su duka ukun ya lullub’e shi..

Abba ne yayi k’arfin halin zuwa inda suke, yad’an kura mata ido kafin ya cewa Gwaggo Asabe “ta mik’o mishi ruwa!”

A hankali yake yayyafa mata ruwan, har sun cire ran zata farka sai kuma sukaga tana motsi da idanunta alamun zata farfad’o….
A hankali Abba yad’an kalli Aslam wanda ke zaune a gefenta ya rankwafa kanta sannan ya kama hannunta gam!! Yana kallon idon da take k’ok’arin bud’ewa, alamun a kag’e yake yaga ta bud’e idanun nata!

Da kyar Abba ya tattaro courage d’in da ya iya cewa Aslam
“Aslam, ko zaka d’an je waje ko? Kar ta farka kuma ya zamana kai d’in zata fara gani.”

Da sauri yace
“No Abba, I think bata gane ni bane ba.”
Sai kuma ya kalli Dad yace “Dad da kanta ai kace ta kirani ko?”

Ganin da Dad yayi Aslam d’in na neman koma musu wani firgitachche ne ya sanya shi kawai cewa
“Kaje wajen tukunna mu gani.”
Jikinshi har wani karkarwa yake yi, sai da Dad ya sake cewa
“I’m so sorry Aslam, ita tace a kiraka but ban san me ya sake faruwa ba kuma, for now just, ka d’an jira a waje ko?”

A hankali ya cika hannun ya mik’e ba tare da ya yarda ya had’a ido da kowa ba ya fice,
Dede nan Dad ya fashe da kuka, gaba d’aya sai hankalin su Abba ya sake tashi, saboda abune wanda basu saba gani ba!
Don haka duk sai suka hau bashi hak’uri suna tausar shi, tare da adduar in shaa Allah Allah zai bata lafiya soon…


A b’angaren Dad shi kuma Aslam yake ji, da ya sani da bai yi saurin kiranshiba, gaba d’aya duk sai yaji ya tsani kanshi…..
Da kyar suka samu ya tsaida kukan ya k’arasa gurin Mommy wadda ta farka yanzun tanata faman dube dube a mugun tsorace alamun neman tsari take daga sake ganin Aslam d’in.

Sai da komai ya lafa sannan Gwaggo Asabe suka fito ita da Hudan daga d’akin….

Ita dai Huda gaba d’aya kanta ya kulle, hakan yasa ta kasa hak’uri ta hau tambayar Gwaggo “meke faruwa? Mai ya sameta take haka? Tun yaushe? An yi mata sauka?”

Dan ita Huda har ga Allah kawai ta fi jirkita akan lamarin na iska ne, tunda gashi dai ita da kanta ta tambayeshi but yana shigowa gaba d’aya ta firgice! Tayaya uwa zata dinga gudun d’anta haka?? Don ko ba a gaya mata ba ta gane itace Mahaifiyar Aslam ko dan yanayin kamar da suke yi da juna! But why him? Him alone?”

Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan tace “bani minti talatin, inje inyi wanka, Ina dawowa za kiji komai in shaa Allah.”

Kamar yadda Gwaggo Asabe tace
Sai da tayi wanka ta dawo ta zauna sannan ta fara bata labari…………
Asalin sunan Mommy, Aisha ana kiranta da Humaira, k’anwarta d’ayar duniya Khadijah wadda ake kira da Asabe.
Aisha da Asabe sun taso cikin yanayin k’unci na rayuwa ata dalilin babu..
Yahaya ya had’u da Aisha ne lokacin da ya kai ziyara Taraba, jalingo a wani d’an k’aramin k’auye.
Ata dalilin, masallaci da makarantun addinin daya d’auki nauyin ginawa.
A rafii yana zagaye ita kuma taje d’ebo ruwa suka had’u.
Tunda ya kyalla ido ya ganta ya rikice, a lokacin Mahaifiyarsu ta rasu Mahaifinta kawai ya rage musu.
Tun Aisha tana kauce mishi har itama ta fara kulashi sama sama.
Tashi d’aya ba kwana kwana ya nuna mata yana k’aunarta kuma yana son aurenta,
Bata bashi amsa ba tace “yaje ya samu Mahaifinta”.
Yahaya bai yi wani jinkiriba
yaje ya samu Mahaifinta da maganar
sannan yayi mishi alk’awarin ‘bayan auren zai barta tayi karatu har sai tace bataso’,
dan ya lura burin Mahaifin nasu kenan.

D’an guntun bincike akayi akan Yahaya, a lokacin, daga nan Mahaifinta ya bashi aurenta yace masa “duk lokacin daya shirya yazo da iyayenshi a d’aura”
To fa!! anan ake yinta, dan k’iri k’iri Granpa ya nuna k’iyayyar shi muraran akan Aisha da inda ta fito, acewarshi “sam ba a jin auren d’ansa bace ita d’in!!!”.
Buwayar Ubangiji, rabon Aslam, da soyayyar Granpa a matarshi ne
suka tabbatar da auren Yahaya da Aisha wanda aka d’aura a k’auyen Jalingo ba tare da halartar Granpa ba.
Tabbas anyi rigima ba k’arama ba, kafin, da kuma bayan auren!.
Zan iya cewa ban taba ganin macen da ta sha wahala a hannun suruki kamar Aisha ba!
Sauk’in ta d’aya Gramma tana mugun sonta ba kad’an ba, dan tun lokacin da Yahaya yaje mata da labarin Aisha farat d’aya taji Yarinyar ta kwanta mata, ita ta dinga lallab’a Granpa har aka yi auren.

To bayan auren ma haka tayi ta fama, in tak’aice miki labari
hankalin Granpa bai kwanta da Aisha ba har sai da ya aurawa Yahaya ajin nashi da yake ik’irari! Wanda ranar d’aurin auren ana d’aurawa Yahaya yana hawaye kamar k’aramin Yaro, dan zan iya cewa ban tab’a ganin Mijin da yake matuk’ar so da gudun b’acin ran matarshiba kamar Yahaya ba.

Sauk’i d’aya da Aisha ta samu a gurin Granpa shine haihuwar Aslam da tayi, zan iya ce miki ko y’ay’an da Granpa ya haifa a cikinshi bayayi musu kalar son da yake yiwa Aslam, ko dan ya kasance jikansa na farko ne? Allah kad’ai ya sani.
Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi aka tabbatar da hakan, domin kuwa kalar farin cikin da yayi kowa sai da ya gani ya tabbatar da ‘Granpa na cikin farin ciki’!.
Zakkah da sadakar da ya bayar kuwa bana jin har yau a tarihin kaf garin Kano an tab’a bada irinta.

Aslam ya taso cikin gata, duk wani abu da kika sani Granpa ne yake yi mishi…
A tunanin kowa, Granpa zai kasance

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login