Showing 33001 words to 36000 words out of 109746 words

Chapter 12 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2945

irin kakannin nan masu shagwab’a jikokinsa ne, sai dai kuma shekarar Aslam biyar a duniya aka haifi Arshaad amman kwata kwata Granpa bai yi wani murna sosai ba ma balle aje ga maganar shagali da jan shi a jiki kamar yadda kowa ya d’auka…
Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi bai k’ara d’aukar sa ba, Aslam kuwa kullum suna tare, hatta abinci tare suke ci, takanas ya nemo wani bature yake yi mishi lesson a gida, da yamma kuma wani balarabe ne yake koyar da shi addini!
Sai da Granpa ya fahimci loneliness da rashin wasa da Yara agemate d’in Aslam d’in kan iya jawo mishi wani ci baya a rayuwarshi tukunna ya nemi makarantar da tafi ko wacce tsada a kaf Nigeria ya turashi a Abuja wajen mahaifinshi, tare da kwakkwaran warning a me makarantar na “kar a tab’a mishi jika ko me kuwa zaiyi! Kuma kar a bari aci zalinshi.” Duk da yana da wayo sosai dan, a lokacin shekararshi tara
Arshaad hud’u Auwal kuma uku wanda shima Granpa bai wani nuna farinciki ko tunanin janshi a jiki ba tun sanda aka haifeshi.

A lokacin ne kuma Yahaya ya sake tadawa Granpa maganar yana so ya tafi da Aisha Abuja , daman ya tab’a nunawa Granpa son yin hakan amman fur k’iri k’iri Granpa ya nuna mishi sai dai ya tafi da Mammy saboda itace tayi karatu bayan k’iri k’iri babu irin artabun da baayi da shi ba amman fur haka ya hana Aishan yin karatu acewarsa ‘irin su In suka yi karatu gagarar mutum suke yi!’.
A lokacin ya nace akan sai dai ya tafi da Mammy ita zata iya zaman Abuja wata k’ilan ma ta d’an dinga taimaka mishi ta fannin aiki, shi kuma Yahaya yace ‘ba zai tafi da ita ba!
Ko da ace Aisha bata kasance uwargidanshi ba tou tabbas da ita zai tafi’…..
Mistake d’aya wanda Yahaya yayi kuma yake kan yi har yanzu shine ‘k’iri k’iri yake nuna fifici a tsakanin matanshi’ (k’iri k’iri yake nunawa kowa ba tare da shakkar wani abu ba ‘ya fi son Aisha a kan Mammy’.

Da kyar a wannan lokacin dan sai dai Gramma ta shiga tsakani tukunna case ya mutu, dan daa Granpa cewa yayi sai ya tafi da Mammy dole! Shi kuma yak’i.

Tou kuma da Aslam ya koma chan ma da ya sake yin maganar Aisha ta bishi, still magana d’aya irinta farko shima Granpa ya maimaita mishi ‘sai dai ya tafi da Mammy’ shi kuma yak’i,
Shiyasa har yau shi kad’ai yake zaune a Abuja, yanzu haka shi da Aaima ne kawai a gidan.

K’in tafiya da Mammy da Yahaya yayi ata dalilin Aisha yasa Granpa ya rufe ido ya dinga keta mata ruwan rashin mutunci kala kala, ga Adama da Ummi suma basu barta ba, Mammyn ce ma ita bata shiri da ita kuma bata fad’a da ita.
A lokacin ne kuma Mahaifinta ya rasu, Allah yaso ni nayi aure don da ban san ya zan yi ba saboda shi kanshi Mahaifin namu su uku aka haifa biyun duk sun rasu, Mahaifiyar mu kuma daga gidan marayu ma aka aurota, balle inyi tunanin zuwa gidan y’an uwa!
Dan a lokacin halin da Aisha take ciki a gidannan, ko mage bata isa ta d’auko tace zata rik’e ba.

Aslam shekara biyu kawai ya iya yi a Abuja ya d’agawa kowa hankali Akan shi fa ‘Mahaifiyarshi yake buk’ata’ Dan ba kad’an ba suna mugun k’aunar juna, kuma yana da k’ulafucin uwa ba kad’an ba, itama kuma haka, komai Aslam, shima komai Mommy.

Saboda tsabar tsananin shak’uwar dake a tsakaninsu yasa har kusan zarewa tayi lokacin da aka kaishi Abuja,
Idan nace zan tsaya fasalta miki kalar soyayyar da sukewa junansu sai mu kai jibi anan..........

Ba yadda Granpa ya iya haka ya tarkatoshi ya dawo dashi kano gurin Mahaifiyarshi, akan dai ya bari a tafi da ita d’in.


Sai dai kuma daya dawo d’in
abun bai yi dad’i ba sam!
Dan k’iri k’iri Granpa ya dinga nuna banbanci k’arara ba tare da shakkar komai ba!
Abun mamaki hatta driver d’in da zai kai Aslam makaranta daban ne da nasu Arshaad.

Tun abun baya damun mutane har aka fara k’us k’us, su kansu Yaran suma suka fara fahimtar waensu abubuwan….dan shi Arshaad ma a tunaninshi Aslam d’in d’an Granpa ne shiyasa a lokacin yake kiranshi da ‘Uncle Aslam’ a lokacin.

Ranar 12th birthday d’in Aslam ne Granpa yayi wani abun da ya girgiza mutane!
Gida guda ya d’auka ya bawa Aslam as birthday gift, a Dubai!
Wanda su kansu y’ay’ansa basu ma san yana da shi ba, kar ki ce k’aramin gida fa mansion ne mai zaman kanshi! Dan ko a jikin takardar wajen d’akuna ashirin ne suka fito a cikin gidan, iya d’akuna kawai!.

Mutane basu dawo daga shock ba ya cewa Yahaya “ya yiwa lawyer d’inshi magana a fara had’a takardun MT! yana so zai mallakawa Aslam su tun yanzu, in yaso shi (Yahayan)sai ya rik’e mishi idan ya kai 18 years ya bashi abunshi.”

Cikin nuna k’in amincewa Dad ya d’an fara k’ok’arin fahimtar da shi akan shekarun Aslam d’in da kuma gudun abunda hakan ka iya janyowa
K’asa k’asa ba tare da ya bari kowa yaji ba.

Amman Granpa maimakon ya fahimceshi sai ya birkice mishi, ya fara magana yana fad’a kowa yana ji!
Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba!
Fad’a a ranar ba kalar wanda bai yi mishi ba a gaban taron y’an birthday…
Sai da Aslam d’in yayi kamar zai yi kuka yana bashi hak’uri tukunna aka samu ya hak’ura.
Jiki a mace haka Dad ya fita ya kira lawyer ya hau kora mishi bayani……

Kusan minti talatin tukunna ya dawo ya sanar mishi lawyer d’in yace zuwa nan da jibi in shaa Allah komai zai kammala.
Kaf a wajen!
Y’an tsirarrun mutane da Granpa ne kawai suke farin ciki
amman kowa a family d’in in ka kalli fuskarshi ba zaka iya tantance me ke wakana a cikin zuciyarshi ba, sai dai tabbas tashi d’aya zaka hango damuwa binne a k’ark’ashin komai.

Ana i gobe takardun zasu iso, wato washegarin birthday!
Wani mummunan al’amari ya afku.”

Ajiyar zuciya Gwoggwo Asabe ta sauk’e kafin ta kalli sama hanyar staircase
( parlourn k’asan da yake da matattakalr staircase d’in biyu anyi tsarin wajen ne irin me high ceiling dinnan, mutumin da yake falon sama wanda ya had’a staircase d’in dama da hagu yana iya hango komai na k’asa, shima na k’asan haka, sai kuma hanyoyin dogon corridor biyu da suke kallon juna, d’aya yana a right staircase d’ayan yana kusa da left one.
Sai d’akin special guest guda biyu da yake a main parlourn sama da kuma hanyar da zata had’a ka da benen da zai kaika chan sama).
Sannan ta cewa Huda “kinga chan wajen?”
Tayi maganar tana kallon falon saman, kafin taci gaba da cewa
“Mommy tana tsaye tana waya a jikin k’arafunanan taba d’ab lek’o k’asa……
Ganin shigowar Dad Aslam da Arshaad a tare yasa gaba d’aya hankalinta ya dawo kansu tana yi musu murmushi,
Arshaad ne ya hau kawo mata k’arar Auwal tun daga k’asan yana yi yana hawa benen, dan haka ta mayar da hankalinta a kanshi tana ce masa ‘ya taho a hankali kar ya fad’i..’ bata ida rufe bakinta ba dai dai Arshaad ya kusan k’arasawa inda take kawai kamar wadda aka turo sai k’ara akaji timm!!!A take kuma ihun Aslam ya karad’e gidan gaba d’aya…
Da gudu ya k’arasa inda take kwance dukda cewa ta fad’o ne bisa wasu tumtum da suke kan kafet d’in k’asan, hakan bai hana kanta zubar da jini ba! Saboda ba duk jikinta ne yayi nasarar sauk’a a kan cuision d’inba!.

Da kyar Dad ya iya k’arasawa wajen ganin yadda take kallon sama tana karkarwa yasa kawai ya yanke jiki a take ya fad’i sumamme dan shi a tunaninshi ma mutuwace zata yi.

Banda ihun kiran Mommy ba abunda Aslam yake yi, wanda hakan ne ya jawo hankalin mai gadi ya iso..
Ya dad’e ya na knocking yaji shiru ga Aslam yanata rad’a ihu dan ita Mommy a lokacin mai aikin ta zuwa takeyi tana tafiya, kuma lokacin har ta tafi , so ita kad’ai ce sai su Dad da suka shigo wanda yake a sume!
Kuma akai rashin sa a suka tura k’ofar bayan sun shigo
ta shiga lock!.
Arshaad kuwa, mutuwar tsaye yayi, ya k’ame k’am! In banda kallon wajen da take a tsaye kafin ta fad’o d’in ba abunda yake yi, dan har lokacin da mai gadi ya nemo mutane aka b’alla k’ofar aka shigo, Arshaad yana nan a yanda yake, dakyar aka iya janyeshi a wajen aka kaishi wajen Mammy, dan kurma ya koma musu, sai da yayi kwana biyu baya magana…..

A asibiti kuwa da kyar aka dedeta numfashin Dad, bayan awa biyar Allah ya bashi ikon farfad’owa, garau ya tashi dan haka hankalin mutane ya d’an kwanta, saboda a yanda jinin shi yayi mugun hawa ba wanda bai yi mishi zaton stroke ba.

Mommy kuwa da kyar aka tsaida jinin aka kuma samu ta farfad’o bayan kwana biyu sai dai kuma scan d’in da aka yi mata na kwakwalwa ya tabbatar da cewa jini ya shiga kwakwalwarta, wanda sai anyi aiki an kwashe an kuma d’inke inda ya samu rauni.
Dad bai yadda anyi aikin anan ba, waje ya fita da ita aka yi komai, sai dai kuma tun kafin ayi aikin dama sun tabbatar da cewa ba lalle inta farfad’o ta dawo kamar daa ba sai dai a hankali, wasu kan iya d’aukar 1 year wasu 10 wasu 20 wasu kuma 4eva ma basu dawo normal d’in ba!
But ita case d’inta minor ne so ana saka ran ma ba lalle ta d’auki 1 year d’inba in shaa Allah komai zai dawo normal.

Granpa yayi mugun sauk’owa, ko dan ganin yadda hankalin Aslam ya tashi yasa shima nashi hankalin tashi, Allah kad’ai ya sani, dan tare ma suka tafi har shi
da Mammy wadda itama ta d’aga hankalinta da ganin halinda Abokiyar zaman nata take ciki, dan da Dad yak’i biya mata kud’in jirgi ma da kanta ta biya ta bisu daga baya.
Tunda aka yi aikin kuwa ita take kula da Mammy sai Dad yayi da gaske take yarda taje hotel ta d’an huta, tayi bacci.

Aslam, tunda aka yi wa Mommy aiki, yake azumi kulli yaumin, har ranar data farfad’o. Da farko b’oyewa yayi dan ya san za a hanashi, dan har yi yakeyi kamar yaci abincin sai daga baya aka fahimta, ba yadda ba ai ba amman yak’i ajjiyewa, ganin haka yasa Granpa yace a barshi,
sanadiyyar azumin da yayi tayi a jejjere gashi da k’arancin shekaru ya sanyashi kamuwa da cutar ulcer.

Kamar yadda Likitocin suka fad’a, haka Mommy ta farfad’o amman a iya rayuwarta Aslam kawai ta iya ganewa, bata magana sannan komai sai an nuna mata sai an koya mata!
Abu d’aya ta sani ta gane take iya fad’i, shine ‘ASLAM’.

Anji ciwon hakan sosai, amman kwarin guiwar da ake ta samu a wajen manyan Likitoci ne yad’an kwantar da hankalin Jama’a,
dan suna ta bada assurance d’in ‘zata dawo normal!’

Sai dai kuma ana yin wata d’aya komai ya burkice!!! Dan Aslam d’in da ta fara fahimta sai ya dawo ya zame mata dodo!!! Da farko yana shigowa zata fara kuka!! Sai kuma ta dawo ihu!!! Daga k’arshe dai ko asibitin in Aslam ya shigo tun kafin ya k’araso inda take zata hau kururuwa tana kuka
kowa ta nan ne yake gane Aslam ya iso!
Wani abun mamaki shine ta warke garau ta fara magana ta gane kowa amman fa ko a labari idan aka sako Aslam tou yanzu hankalin kowa zai tashi!!

Ba k’aramin kid’ima Likitocin suka yi ba dan su kansu sun zama confuse..A iyaka sanin su masu irin wannan matsalar basa haka amman duba da suka yi da shi ta fara ganewa a lokacin data farfad’o ya sanya suka yi y’an bincikensu, iya abunda tunanin su ya basu ne ya sanya su dangantata da psychiatric.

Allah sarki Aslam, a lokacin
sai da ta kai ga shima aka bashi gado a asibitin tsabar tashin hankalin daya shiga.
Yaro ne shi a lokacin amman kasancewarshi mai kaifin basira yasa ya fahimci komai.
Dan zan iya ce miki har yau ban tab’a ganin Yaro mai wayo tarin ilimi da kaifin basira irin Aslam ba, har gobe in da wani d’an ajinsu da suka yi makaranta zai zo gidannan to ba zaki tab’a ji ya kirashi da aslam ba , sai dai suce mishi ‘gifted’
Dan wani abun time d’in a makaranta ba sai an koya mishi bama yake iyawa, in kuma ya iya to ya zauna kenan!
Ga wayo kamar wani d’an shekaru dayawa.”

Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan ta ci gaba
“A lokacin hankalin kowa a tashe yake, ni kaina da nake nan da ban ganta ido da ido tana haukan ba sai da naji a jikina, abu yak’i ci yak’i cinyewa har aka shafe wata biyu a haka, ga Aslam a kwance…
Tausayin shi da ya lullub’e Granpa gashi yana ganin yana neman mutuwa
ne
yasashi fara nemawa Aisha magani gadan gadan ba kama hannun Yaro, duk inda yaji labarin Likitan kwakwalwa nan zai tarkata su su nufi k’asar! Cikin shekara biyu zan iya ce miki sun kusa zagaye duniya dan ba k’asar da ba a je ba, in dai kinajin ta kuma sananniyace.
Amman dukda haka Allah bai kawo sauk’in ba, saboda lokacin samun sauk’in bai yi ba.
Daga karshe dai hak’ura suka yi suka dawo gida Nigeria.

Ai ana dawowa abun yafi na daa, ba k’aramin tsorata muka yi ba dan nima nazo a lokacin…Idan Aslam baya gidan nan to k’alau amman ko bakin MT yazo yanzu zata birkice, abun tausayi In kana nan dole kayi kuka, don Aisha mahaukaciya tuburan ta koma.

Shawara d’aya Granpa ya yanke shine na ‘kai Aslam boarding school’
don samun sauk’in kowa and ya kamata yaci gaba da karatu kuma ya maida hankali saboda an barshi a baya sosai…
A lokacin shekarunshi sun haura 14.

Da kyar Aslam d’in ya yarda, ya tafi bayan Granpa yayi mishi alkawarin ‘duk inda magani yake a duniyar nan in dai akwaishi to zai nemawa Mommy d’insa, ko nawa ne kud’in ba zai gaji da biya ba, koda kuwa zai k’arar da duk abunda ya tara ne!!!’.

Haka nan aka tarkata Aslam aka kaishi boarding cikin tsananin k’unci, yana kuka
muna kuka ba dan munso ba.

Wani abun takaicin ko hutu Aslam bai isa ya zo ba, sai dai In kana buk’atar ganinshi kai kaje ka ganshi a inda yake, k’iri k’iri zaman estate d’innan ya gagareshi…
Ganin abun na Aisha bana k’are bane yasa suka kira wani babban Likita daga k’asar waje har gida Nigeria ya dinga kula da ita, shi ne ya bada shawarar a kulle su ita da Aslam a d’aki d’aya su kad’ai, for 24 hours, to kuma abun bai yi dad’iba don shi yayi sanadiyyar da Aslam ya bar k’asar nan wanda sai yanzu ne Allah ya dawo mana da shi!

Da farko an tsara akan zai d’an dinga lek’owa Hutu sai yake sauk’a gidan Abba, yadda ba zasu had’u da ita ba, har zuwa lokacin da Allah zai kawo sauk’i
Amman abunda ya faru a wannan rana ya sanya Aslam yin yaji mai mugun tsayi ya tarkata komai nashi ya tafi
sai dai waya, shima wani lokacin sai yake gudun d’auka!.

Arshaad da su Abba suna yawan zuwa duboshi, Auwal ne ma yaje sau d’aya, amman Arshaad a shekara ma yakan je sau biyu shi da Abba..saboda shi Aslam
ko hutu idan anyi na makaranta baya iya dawowa sai dai yayi achan Oxford Uni inda yayi karatunshi.

Aslam a Oxford yayi karatu,
Arshaad kuma Dubai aka kaishi Auwal kuma Cairo.
Da yake Granpa ne duk ya kaisu..duk da halin da Aslam yake ciki sai da aka fara k’ananan maganganu, Adama da Ummi, wai ‘har yanzu Granpa bai daina nuna bambanci ba’
Sosai Granpa da maganar ta koma mishi yayi musu tataas!!!Kuma ya taso da maganar mallakawa Aslam MT gaba d’aya inyaso sai yaga me za suyi!.

Da kyar da sid’in goshi Gramma ta tausheshi, sannan ta lallabashi, sannan tai k’ok’arin fahimtar dashi abubuwan da hakan ka iya janyowa….
Awannan lokacin kuwa anci sa’a ya fahimceta sosai, don da kanshi kuma ya dawo yace ‘a tsakanin Auwal Arshaad da Aslam, duk wanda yaga he’s capable to shi zai mallakawa MT’.
Dad yayi mugun mugun yin farin ciki daga jin wannan decision na Granpa, bawai yana zargin wani ba, kawai dai yaji releaf, kuma shima baya son bambancin da Granpa d’in ya dad’e yana nunawa especially tsakanin Arshaad da Aslam, don duk abun nan da ake yi ko sau d’aya Arshaad bai tab’a nuna b’acin ranshi ba, dukda kuwa uba d’aya ne ya haifesu shi da Aslam d’in,
Idan akwai fitinanne tou Auwal ne!
Amman Arshaad shi ba ruwanshi yana da kauda kai
kunyarshi ce ma ta sanya Dad yake yiwa Mahaifiyarshi wani abun dan kar yaga ga kamar bai damu da ita sosai ba.
Kowa idan zaki tambaya a estate d’innan ya baki sheda akan Arshaad to zai ce miki ‘yanada hak’uri da kauda kai da kuma saurin yafiya’.


Aslam yana kammala degree na farko aka d’aura shi a matsayin MD na MT branch d’in dake achan k’asar da yake, wanda ada Abba ne a wajen.

Ayyuka Aslam yake yi bashi da lokacin kanshima,
kuma daman hakan yake so dan hakan ya tsarawa kanshi tun farkon komawarshi UK d’in,
yana k’ok’arin kullum yaga ya zama busy dan kar ma ya bawa kanshi daman yin tunani..
Aikin kuwa ya taimakeshi ta b’angarori da dama
dan
Yana da nashi campny d’in a chan, na sarrafa takalma wanda k’wazonshi guminshi da kuma taimakon Granpa wanda yake aika mishi kud’i kamar hauka suka taimaka
masa ya had’a ya bud’e
wanda yanzu naji suna cewa yanaso ya bud’e wani branch d’in anan ko kuma ya dawo nan ma, gaba d’aya. Kuma akwai wani daban da zasu bud’e na zanen gidaje shi da Abba!
Ga mt ga kuma karatu wanda a yanzu ya kammala PHD d’inshi…
A b’angaren nasarori Aslam ya samu kam ba a magana sai dai kuma shi duk basa gabanshi, inda za ace ya tatttara ya bada abashi lafiyan Mahaifiyarshi na tabbatar kafin k’iftawar ido zai iya sallama komai!
Ba shi kad’ai ba hatta mu duk tsawon wannan lokacin buri daya muke da shi shine ‘Aisha ta warke hankalin kowa ya kwanta’
Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login