Showing 27001 words to 30000 words out of 109746 words
Arshaad ya katseshi ta hanyar cewa
“It wasn’t your fault, tayi laifi, so ko baka yi abunda kayi ba dole na san wata rana gaskiya zata fito, kuma za ayi punishing nata. Kawai dai i was disappointed in you ne that’s all”
Sai da ya d’anyi shiru yaji hucin da yake yi ya d’an ragu
tukunna ya ci gaba da magana
“Ko sabon mai aiki aka chanja a gidan nan baka nan Aslam kana Uk but sai na kiraka na fad’a maka!
Ya kamata ace lissafinka ya baka ‘if Abba yana da y’a and bai san da ita ba, to dole akwai wani abu a k’asa’!.
Da kayi finding out about Huda you should have talk to me first mu samu mu fara bincike first!
Because that is wat i’ll definitely have done if i were in your shoes.
But you just went ahead and ruin everything.
Yanzu because of you Mahaifiyata is there a cell da anty Adama su da basu da laifin komai, they just help a friend.”
A hankali yace
“i tot we were brothers, best friends.”
Cikin katseshi Aslam yace “and yes we still are, yana matsowa kusa dashi da rik’eshi”.
Murmushi kawai Arshaad yayi ya zare hannunshi
sannan ya zagayeshi ya fara k’ok’arin shiga d’akin mai gadi.
Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Ok, I’m sorry”
yana mai sake ruk’o hannunshi.
Sai da Aslam d’in ya maimaita sannan Arshaad ya juyo ya kalleshi na y’an seconds kafin yace
“Apology accepted.”
“Thankyou “
shine abinda Aslam d’in yace kafin ya d’aura da
“And about what you just saw, i’m..”
Cikin katseshi Arshaad yace
“Aslam we’re good fa, komai ya wuce, let me check on her, ta shiga toilet d’in mutumin nan barefoot kuma i don’t even know ko yana ciki dan ban ganshi a d’akin ba.”
Yana gama fad’in haka ya zare hannunshi sannan yayi cikin d’akin ya isa bak’in k’ofar toilet d’in yana cewa
“Hudan open the door, it’s me, su Abba sun tafi.”
A hankali take bud’e k’ofar tana d’an lek’owa..
Sai da ta tabbatar da shi d’inne tukunna ta k’arasa bud’ewa.
Murmushi ya d’anyi mata..
Gaba d’aya ta had’a gumi tayi zuru zuru!
A hankali yace “matsoraciya kawai”
A hankali tayi k’asa da kanta sannan ta fito, Allah ya taimaketa ba kowa a toilet d’in kuma mutumin yanada tsafta dan band’akin tass yake gashi tiles ko ina kuma a bushe. Amman dukda haka sai da Arshaad yayi amfani da ruwan butan da ya gani bayan sun fito ya zuba mata akan k’afafunta.
Suna fitowa ya cire takalminshi ya bata ta saka sannan yace “ta zo ta rakashi ya saka takalmi.”
A hankali ta fara kuka kafin tace masa “Ita wajen Mama zata je”
Gaba d’aya sai yaji wani matsanancin tausayinta ya kama shi. Shiruuu, yai yana tunanin ta yadda zai fita da ita bayan shi aka d’orawa alhakin curfew.
Dole ya lallab’ata ta d’an hak’ura ko zuwa gobe ne sai su je.
Matsowa yayi yana shirin lallashinta wayarshi ta hau k’ara, ganin sunan Sakina ya sanaya shi ce mata su k’arasa ciki akwai maganar da yake ai suyi da ita, dama. Tukunna sai ya kaita gurin Maman.
Ba tare da musu ba ta bishi suka yi hanyar shiga parlourn gidan, Aslam har zai bisu dan still ya lura Arshaad d’in is still mad, saboda da suka fito ko inda yake bai yarda ya kalla ba..
Sai kuma kawai ya chanja shawara ya juya kawai, duba da yayi ba shi kad’ai bane kuma ya lura soyayyar Mahaifiya ta rufe mishi ido, if not tayaya zai ce “ita da Mom basu da laifil!” ko kuma may be bai san story d’in gaba d’aya ba, dai.
Da wannan tunanin ya fita a gidan bayan ya yanke shawarar sai nan da 4 to 5 days haka zai nemeshi ya sake bashi hak’uri, by then ya san ya sak’k’o.....
Suna shiga parlour ya umarceta da “ta zauna akan kujera”
Bayan ta zauna shi kuma ya nufi fridge ya d’auko mata ruwa da glass cup a kan dining ya kawo.
Dama kuwa tana buk’ata hakan yasa yana zuba mata ta k’arb’a ta hau sha. Sai da ta shanye tass sannan ta ajjiye tana sauk’e ajjiyar zuciya a jejjere.
Kallonta yayi da idanuwanshi da har yanzun basu gama dawowa dede ba sannan a hankali yace
“In kara?”
Girgiza mishi kai tayi tana y’ar mitsitsiyar gyatsa kafin tace “Alhamdulillah”
Sai kuma anhankali ta mik’e tace “Bara inje wajen Aaima”
Mik’ewa shima yayi yace
“bata nan, bata dawo daga school ba tukun!
Mammy kuma tana cell!
It’s just me.”
Ya fad’i hakan yana tsareta da ido.
Saurin yin k’asa tayi da kanta, kafin a hankali tace
“Kayi hak’uri dan Allah.”
Murmushi ya d’an yi yana kallonta kawai ba tare da yace komai ba.
A hankali tace “bara in tafi, nayi tunanin Aaima tana nan ma.”
Bata jira jin me zai ce ba ta fara k’ok’arin fita tana cewa “ka d’auko takalmin naka muje mu duba Mama da wuri, ko?”.
Dede nan wayarshi ta sake ringing, ganin me kiran ne yasa shi kai mata wayar har bakin k’ofa sannan yace
“Na so muyi magana but it’s like kamar tsorona ma kikeji!
Gashi ungo, Sakina ta gaya miki, bara in d’auko takalmin nawa”
Yana gama fad’an haka ya kara mata a kunne bayan ya amsa kiran daga nan yayi hanyar part d’in nashi.
Da sallama ta amsa wayar..
Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e jin muryar Huda sannan tace
“Alhamdulillah”
Jin yanayin muryar Sakina yasa ta fahimci akwai matsala.
Cikin sanyin muryar da bata santa da shi ba taji tace
“Huda kuna Ina? bakya hawa watsapp, ba kwa amsa waya tun jiya, gamu kuma mun dawo gida bakwa nan. Ina kukaje gaba d’aya hankalin mu ya sake tashi.”
Da sauri Huda tace “Sakina Mama bata gida?
Ya naji muryar ki wani iri duk ya dishe?”
Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e, har zata fad’a mata kuma sai tayi shiru (saboda su Madu sun ce a bari a fara yin test na gawarwakin da ake expecting akwai Junaidun a ciki da jinin Baba, before ayi confirming nashi as dead )
Hakan yasa tace mata
“Ban gane ‘Mama bata gida ba’ bakwa tare? Ke kina ina?”.
Gefe guda Hudan ta koma kan kujerar dining ta zauna sannan
ta fara bawa Sakina labarin tun daga sumewar da Mama tayi jiya da safe, har kawo yanzu da take son gudowa….
To fa!! Ana wata ga wata.
Numfashi Sakina ta fesar kafin tace “With all that is goin on Hudan, congratulations!
Kin had’u da Mahaifinki finally, and baya gudunki, kamar yadda mutane suke fad’a.
But first
Maama,
so yanzu ki bani kamar 20 minutes haka za sake kira in shaa Allah.”
......Su Abba kafin su koma ciki suka tsaya shi da Daddy suka yanke shawara…suna zuwa suka sanar musu cewa
“Shi da Daddy za su bar gidan, Dad da Gramma kuma za su zauna.
Addua suka dinga yi akan Allah yasa kowa ya yarda.
Ba dan su Gramma sun so ba haka nan suna ji suna gani suka amince da tafiyar su su kad’ai, Dad yaso ace shi ne yabi Abba tunda shine Babba Amman bayan sun keb’e sai suka yi mishi bayani akan kasancewar shi babban ne yasa suka ce ya zauna a estate d’in, sannan ya taimaka ya dedeta Gramma da Granpa, kafin ya koma Abuja, dan tun a wajen meeting d’in suka fahimci iyayen nasu suna fushi da juna wanda hakan it’s not usual.
Ahaka ba dan rai yaso ba aka tsara akan gobe zasu bar estate d’in kafin a samu komai ya dedeta In Granpa ya sauk’o su dawo, Dad ne ya basu mukullin makeken mansion d’inshi wanda ke anan bayan su kad’an yace “su zauna su biyu a tare ba sai sun raba gidaje ba.” Dan ana hoping d’in daidaituwar komai soon in shaa Allah.
Daddy yayita jiran Granpa ya kirashi yace “yayi resigning, ya kawo takardun companies d’in da yake rik’e dasu sannan ya sauk’a a md d’in MT UK branch Amman ga mamakin shi sai yaji shiru, bai ce masa komai ba.........
Sakina tana katse kiran ta mik’e ta isa inda Ummu take ta jaa hannunta suka koma gefe, ganin haka yasa Shuwa itama ta iso inda suke, nan Sakina ta zayyane musu komai.
Kafin awa d’aya gaba d’aya su Kaka kowa ya hargitse a neman Mama har da Madu wanda ba kad’an ba kowa yaji dad’in yadda ya shiga cikin lamarin.
Babu inda ba a duba ba har wajen 10 amman shiru.
Ummu ce ta bada shawarar “aje asibitin malan d’in a sake bincika ta!.”
Nan d’inma ba Inda basu duba ba dan rarrabuwa ma suka yi amman shiru…
Tunda suka fito Baba yake ta maimaita magana d’aya
“Aje gidansu Abba! Shi ya tabbatar idan aka yi kwakkwaran bincike a gidan za a ganta. Ya san tabbas
Abba ne ya d’auke Maryam ya b’oyeta bashi da tantama!
A kira y’an sanda a kama Abba…waye waye.”
Su Ummu tun suna k’ok’arin fahimtar da shi har suka hak’ura suka kyaleshi kawai dan sun lura abun nashi ba na k’are bane.
Ganin dare ya lula yasa Ummu tace bara kafin su koma gida ta shiga masallacin can tayi sallar isha dan gaba d’aya ta sha’afa bata yi ba gashi lokaci ya tafi sosai, sai a lokacin Sakina itama ta tuna bata yi ba hakan yasa suka nufi famfo suka yi alwalla tare daga nan suka shiga masallacin domin gabatar da sallah…
Babu kowa a ciki sai wasu mata guda biyu a chaan k’uryar masallacin, d’ayar a zaune da Yaro a hannunta d’ayar kuma ta juya baya tana kallon bango alamun bacci ma take yi.
Cikin nutsuwa suka gabataar da sallar su suka d’ora da doguwar Adduar Allah ya baiyyana musu Mama.
Daga nan suka mik’e suka fara k’ok’arin fita.
Ummi ji tayi kawai gabanta ya yanke ya fad’i, kamar kuma ance ta juya…bata san daliliba amman taji tana buk’atar juyawan…
Matan nan na d’azu ta sake kallo still suna a yadda suke, har tana shirin juyawa idanunta suka kai kan atamfar jikin matar kwance da mayafinta, sai a yanzu ma ta lura da kayan dan sanda suka shigo kwata kwata hankalinsu baya tare dasu, gasu a gajiye.
Kusan a tare zuciyoyinsu suka buga ita da Sakina wadda itama taga atamfa da mayafin jikin Mama
Tabbas mayafin Mama ne wannan
Atamfar kuma ankon wunin kai amarya Khadijah ne.
Da sauri Sakina tace “Maamaa!” Sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tab’ata ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita.
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare.
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
39
Da sauri Sakina tace “Mamaa” sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tattab’a ta,
ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita!
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare, dan a yadda Sakina ta juyo da ita haka ta biyo hannun Sakinan ta taho yuuu ta zube wanwar kwanciyar rigingine.
Ummu mutuwar tsaye tayi a wajen, so take ta k’arasa inda suke amman ta gagara sakamokon ganin y’ar uwartata da tayi kwance tamkar gawa!
Ta kasa tab’uka komai banda hawaye ba abunda take yi.
Sakina wadda ta rikice tanata tattab’a Maman ne ta juyo tace
“Ummu ki zo ki kamata mu mik’ata emergency..
Mama ce amman bata numfashi.”
Jin hakan ba k’aramin sake rikita Ummu yayi ba, ita dai kawai ta ganta a gabansu a tsaye amman bata san ya aka yi ta isa wajen ba.
Matar nan ce ta matso itama ta hau jijjiga
Mama tana cewa “kumafa yanzun nan muka gama magana da ita, tun jiya muke nan tare da ita. In banda kuka ba abunda take yi, nayi tambayar duniyar nan tak’i kulani…
Sai dai kawai taje tayo alwala tazo tayi ta sallah.
Sai d’azu ne da naga kamar batta lafiya nace ‘tazo muje in rakata taga Likita’, shine na samu ta d’an kulani ta inda take ce min ‘bara ta d’an yi bacci, idan ta farka sai muje’.”
Ita dai Sakina cicib’arta ta fara k’ok’arin yi hakan yasa suma suka sa hannu suka taimaka mata suka yi waje da ita.....
Su Madu suna tsaye a k’ofar shiga emergency..
Kana ganinsu ka san hankalinsu ba a jikinshi yake ba!
Ga tsananin gajiyar da suke tare da ita
Dan ma Allah ya taimaka Abokin Junaidu ne ya biya musu kud’in jirgi su kuma suka biyawa Baba
Saboda yaga yanayin tsufansu gashi da ya kira Baban ma a hanya ya jisu suna dawowa daga wata tafiyar….
Ba dan haka ba
da gajiyar ba zata yi musu da sauk’i ba.
Suna tsaye suna tunanin abunyi next suka hango su Ummu d’auke da mata suna nufusu, sai da suka matso su sosai sannan suka gane Mama ce.
Basu samu damar tambayar su ba dan da sauri mai gadin k’ofar ya wangale suka shige kawai dukkansu…
Ana ganin su aka karb’esu bayan an kawo gado an d’aurata, aka tura ta ciki don yin bincike..
Ba a jima ba sosai, Dr ya fito! Likitan dai da ya karb’eta jiya shine, magana d’aya ce ya maimaita musu “hawa da jininta yayi over ne ya janyo komai..amman this time around har eco za suyi”
Nan yake ce musu “ba yadda bai yi da ita jiya akan ta zauna ta shanye drip d’inta ba amma tak’i, ta biyewa wasu suka dinga hayaniya suna fad’a! Yayi yayi akan suyi shiru suka k’i, shiyasa shi kuma ya sallameta, so suma in sun san hayaniyar za suyi gara karma su shiga inda take, dan zai sake korar su ne!”.
Yana gama fad’in haka ya nuna musu inda take sannan ya wuce........
Bayan kamar awa d’aya, Kaka da su Baba suka wuce aka bar Sakina da Ummu.
Su Kaka na fita Hudan wadda take kiran Sakina a kai a kai ta kira, nan Sakina ta gaya mata “sun ganta suna tare ma yanzu haka”
Sai a lokacin hankalinta yad’an kwanta.
Nan itama Sakinan take tambayarta “tana Ina?” Hudan tace mata “tana wajen Gwaggon su Aslam, amman still Abba bai san tana gidan ba, dan a b’oye ma Arshaad ya kawo mata wayarta data bari a gidan Gramma, so in shaa Allah gobe da sassafe za ta san dabarar da zata yi ta gudo.”
shiruu, Sakina tayi chan tace “ki bari mu yi magana da Ummu tukunna, kar ki yi komai, kinji?”
Ummun ce tasa hannu ta karb’i wayar suka yi magana da Hudan ta d’an kwantar mata da hankali, kafin suka yi sallama.
Da kyar suka samu bacci ya kwashesu wajen k’arfe 3 na dare.
Da sassafe su Madu da Baaba Talatu suka zo kawo musu breakfast, har lokacin Mama bata farfad’o ba.
Sama sama take jin hayaniyar su dan haka ta fara k’ok’arin bud’e idanunta.
Sakina wadda take a kusa da ita ce ta lura dan haka ta maida gaba d’ayan hankalinta gareta, ganin Sakina ta k’ura mata ido ne ya sanya suma duk suka taso suka zagaye gadon suna tambayar “mai ya faru?”
Basu ida tambaya ba Mama ta k’arasa bud’e idanunta…
Tsantsar farin ciki ne ya baiyyana a fuskokinsu gaba d’ayansu, cikin murna suka hau furta “Alhamdulillah” suna tambayarta “ya jiki?”.
Da kyar Baaba Talatu ta taimaka mata ta mik’e ta zauna..
Tana zama suka had’a ido da Ummu!
Kawai sai ta fashe da kuka abun tausayi……
Duk shiru suka yi.
Da kyar Madu ya samu ya k’araso inda take ya dafa ta sannan ya d’an fara bubbuga bayanta alamun lallashi.
Farin ciki ne ya mamaye zuciyoyinsu gaba d’aya, duk sai suka hau murmushi
Kaka har da y’a kwallarshi, ya sa hannu share ba tare daya bari kowa ya lura ba.
Ita kanta Mama duk da yanayin da take ciki hakan sai da ya sanyata zubar da kwallar farin ciki, dan rabonta da Madu ya nuna kulawarshi a kanta kaman haka, yau
yau shekaru ashirin da bakwai kenan!.
Share hawayenta tayi sannan ta d’ago ta kalleshi, shima itan yake kallo, ba abinda ta hango a idanuwanshi sai tsantsar tausayinta, bakinta na rawa cikin kuka tace
“Abba, ya raba ni da Huda! Dan Allah ku karb’o min ita, wallahi mutuwa zan yi in ba y’ata, na shak’u da ita sosai,
ba zan iya yarda in bar mishi ita ba.”
Da sauri Ummu ta k’araso ta rungumeta, sannan cikin tsananin tausayinta
tace
“Ki yi hak’uri ki huta, munji komai, in kika warke sai a san abun yi, ki kwantar da hankalin ki dan Allah.”
Cikin jujjuya kai Mama ta zare Ummu a jikinta kafin tace
“Bilkisu ba zan iya yin hak’urin nan ba!! Abba ya zama wani irin mutum! Mugun mutun..
Shi ne fa ya turo Arshaad wajen Huda, Arshaad cousin d’inta ne!
Suka dinga yaudarar mu, idanunsa akan mu yake all this time amman bai baiyyana kanshi ba sai yanzu?
Saboda ko nace ba zata koma wajenshi ba ya san ai Arshaad zata aura, kenan ko?
Wanne irin ubane zai yiwa y’arsa haka?
Bilkisu gaba d’aya kaina ya kulle, a baya yace ‘baya buk’atar ta’, yanzu kuma yazo ya raba ni da ita a lokacin da nafi buk’atar ta, mai yasa zai yi haka? Laifin me na yiwa Abba da zafi haka??”.
Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka.
Lallashinta Kaka Baaba Talatu da Ummu suka hau yi, amman furr!! Tace “ba zata hak’ura ba! Ba zata iya yin hak’urin da suke so tayi ba, yanzu zata je ta taho da y’arta, barinta a hannun Abba danger ne! Tunda har ya iya turo wani wajenta saboda son zuciyarshi bai damu da yana sonta tsakani da Allah ba ko akasin hakan ba
Tou tabbas zai iya yin komai.
Ko bayaga haka ma
idan duk duniya zata taru a kanta tofa ba zata d’auki y’arta wadda Abban yace ‘bayaso ta fad’a mata ko da sunan shi ne’ ba, ta bayar a shi yanzu! Sai dai duk abinda zai faru ya faru.
Suyi mata kwatancen gidan ko kar suyi mata zata tafi ta nema, tunda Allah yasa taji kwarin jikinta yanzu, daman jiya ma jiri ne ya hanata motsawa daga inda take.”
Gaba d’aya Mama ta hargitse musu, data ga ma ba zasu bata goyon baya ba,
Sai ta fara k’ok’arin sauk’a daga kan gadon sannan tasa hannu zata cisge cannular hannunta.
Madu ne ya rik’e hannun nata, kafin cikin lallashi yace
“Maryam koma ki zauna muyi magana.”
Cikin sheshshek’ar kuka ta koma ta zauna tana share hawayenta.
Sai da yaga ta d’an sassauta kukan nata, sannan ya fara magana
“Ki kwanta ki huta,
baki da lafiya.
Koda kin fita za ki sake fad’uwa ne, saboda baki gama dawowa normal ba!
Ki zauna ki shanye allurai da magungunan ki, da ni da Babanku