Showing 15001 words to 18000 words out of 109746 words

Chapter 6 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2929

ya yanke shawarar cin uban Auwal dan ya lura bayan rainin hankalin da yake yi mishi, harda hauka ma ya fara damunshi kwana biyu, gara a yita ta k’are ko zai dawo hankalin shi, in hauka ya za ayi ya d’auko Yarinyar da bai tab’a ganiba a rayuwarshi ya hau yi mishi wani maganan banza da wofi??!

A fusace ya juyo yana shirin yin kan Auwal, sukaji k’arar fad’uwar abu, da sauri duk suka juya suna kallon k’ofa..

Arshaad, ya san yana da gaskiya amman kalar kallon tuhumar da Hudan take yi mishi da kuma yanayin fuskantar, ne
ya sanya gabanshi yayi mugun fad’uwa sannan wata zazzafar zufa ta hau keto mishi, tabbas ya san taji shirmen da Auwal ya gama fad’a yanzu.
Auwal kam tsayawa yayi yana kallonta yana mamakin tsananin kamanninta da Abba da Aslam!
“Who’s she!?”
Ya fad’a a hankali ba tare da kowa ya jishi ba.
Chan kuma sai ya tuno da case din y’ar gidan Abba da har ta kaiga kulle su Mom d’inshi a cell!
Antake kwakwalwarshi ta d’au chaji, don haka a zafafe ya nufeta, daman neman ta yake yi ya kora mata warning!!
Jalila kuwa tsorone ya rufeta ganin Huda, a tunanin ta Umma ce ta fad’i inda take, su kuma suka zo har da su Kaka tafiya da ita, dan haka karkarwar jikinta ya tsananta ba abunda take tunawa irin auren ta da Mati mai wanki ta san yanzu kam babu fashi!.

Cikin zafin nama Auwal yana karasawa inda Huda take tsaye yace
“Hey! Couz…
You must be Huda right?
Inaso kije ki samu uban ki kice mishi......”

Cikin katseshi Arshaad wanda shima ya k’araso inda take yanzun yace
“Huda lets go don’t mind him, he’s crazy!!
Muje kawai za mu yi magana a waje.”
Ya k’arashe maganar yana durk’usawa don k’ok’arin d’aukar wayarshi data jifar a k’asa.

Hudan ita kanta bata san tana da kishi irin haka ba, sai yau. Wato ba zai ma iya fuskantanta a gaban Jalilan ba?!
Gashi yadda duk ya rikice jikinshi yana d’an karkarwa yasa ta d’aura ayar tambaya akanshi…
Ita Arshaad zai yiwa haka? Why? Of all people kuma yayarta!!!
Bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba!.

Ai kuwa a rikice, Arshaad yace
“Oh nooo, Huda dan Allah kar muyi haka dake mana, na rantse miki da girman Allah ban san wacece waccar ba!
Ban tab’a ganinta ba a rayuwata, wallahi!
Muje waje we ‘ll talk outside.”
Yai maganan yana k’ok’arin kama hannunta..

Da sauri ta fisge cikin kuka tace
“Don’t touch me! Ai dole kace baka santa ba mana, Ya Jalilan ce baka sani ba?
Daman Mama tace min rannan kaje kana nemanta, kuma nima naji Umma ma rannan suna wani magana da Anty Zainab dana kasa fahimta a kanka kaida Ya Jalila.
And if baka santa ba mai take yi a nan ya akayi ta san gidanku da ni kaina ban saniba?
Ana tunanin tana gidan Anty d’inta a gida ashe tana wajen ka!
I trusted you,I tot.....”

Arshaad kam zuwa yanzu ranshi yayi mugun b’aci dan a tunaninshi ko Sakina ce zata fad’awa Hudan wannan maganar a kanshi bai ci ache ta yarda ba, balle a bakin mutumin da bata tab’a gani ba sai yau!
Dan haka cikin katseta yace
“Ba kiyi trusting d’ina ba Huda! Tunda gashi har kin d’auki maganan da aka fad’a miki a kaina…
Rantsuwa ta k’arshe da zan yi miki shine ‘wallahi ban san Yarinyar nan ba!’ Mutum d’aya na sani a gidanku age mate d’inki itace Sakina. Kuma ban san wanne Arshaad d’inne yaje nemanta gida ba rannan d’in da kikace, amman bani bane ba!. Maganar su Umman shima i don’t know anything about it, wallahi!.
Anyways
Na gode da irin shaidar da kika yi mini..
Hudan aure za muyi ya kamata ace kinyi trusting d’ina tunda as far as i know inda ace ni d’an iskane da tuni ke zaki fara fad’a ba wai ita ko shi ba.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita dan in ya ci gaba da tsayawa a wajen zai iya yin abunda zai yi ending up yana regretting…

A hankali Hudan ta k’arasa ciki wajen Jalila ta kama hannun ta kafin tace
“Ya Jalila”
Cikin kukan makirci Jalila ta fashe da kuka ta rungune Hudan kafin tace “Hudan Allah da gaske ne abunda Auwal ya fad’a yanzu, gashi na kasa fad’awa kowa, ban san ya zanyi ba! Arshaad ya cuceni.”
Ta k’arashe maganar da wani mugun kuka, don ta lura Hudan ta yarda da ita,,dukda kuwa
har yanzu tana cikin rud’u akan ‘’me Hudan take yi a gidan’ Dan kalaman Auwal da yadda yace mata cousin ya sake dilmiyar da tunanin ta…
Amman yanzu ba wannan ne a gabantaba, raba Hudan da Arshaad shine first! Ga kuma zancen miliyan biyar! Don haka dole ta ajjiye komai a gefe ta duk’ufa ta cimma burinta.

Da kyar Hudan ta lallasheta, ta samu tayi shiru..
Rasa abunyi yasa Huda tace mata “bara taje ta dawo”
da taso ta tafi da ita, amman tak’i, dan haka ta mik’e tace “tana zuwa, tukunna sai su san me za suyi”

Cikin share ragowan hawayenta ta d’agawa Hudan kai, Hudan kuma ta fita a zuciyarta tana rayawa yanzu zata kira su Ummu dan ba zata iya wannan abun ita kad’ai ba! dole a kwatarma Jalila hakk’inta, tana tafe zuciyarta na tafarfasa, ita kawai idonta ya rufe da kishi har ya kaita ga kasa yin lisaafi mai kyau a kwakwalwarta.

Jalila na ganin fitar Huda ta share hawayenta ranta fess!
Sannan ta mik’e ta k’arasa inda Auwal ya daskare yake k’ok’arin hada 1+1 akan alamarin da ya gudana yanzun nan dan in dai shi ba dak’ik’i bane ba tou abu na farko daya fara fahimta shine ‘Arshaad Huda yake dating!’ And tabbas bai san Jalila ba, to who…..
Muryar Jalila wadda ta k’araso yanzu ne ta katseshi jin tana cewa
“Nayi duk abunda kace, yanzu abunda nakeso da kai shine ka kawo miliyan d’aya, ragowar kuma in aiki ya kusan kammaluwa, dan..”
Shak’ar!! Da yayi mata ce ta katse mata maganar tata, cikin d’acin zuciya da k’arfi yace
“Who are you?”.

BULAMA ✍️

Cikin fushi tace “kafi kowa sanin me kayi!
Kuma ina so ka sani Allah sai ya bi ma Hudan hakkinta dan wallahi kaji na rantse ita d’in son gaskiya da tsakani da Allah take yi maka!
Amman duk da hakan zan yi k’ok’ari inga na cire mata kai a ranta!.
Sannan ga sak’o ka gayawa Abba!
‘ in duk duniya ce zata taru a kaina to ba zan yarda ba!!
Nima ina nan zuwa karb’arta, daganan in Mahaifinsa yaga dama ya kulle kaf jinsina ba wai iya danginaba!!”.
Tana gama fad’in haka ta wuce ta barshi nan, a daskare!!


Da kyar ya iya tattaro ragowar kuzarinsa ya fice shima a d’akin, saboda iya yadda yaga ta fita tana layi ya tabbatar mishi ba zata iya kai kanta ko da nan da gate ba!
Sai dai kuma, ko da ya fita d’in sai bai ganta ba bai ga alamartaba kamar wadda tayi layar zana ta b’ace!

Duddubawa ya hau yi har buildings d’in gefen emergency amman babu ita babu alamar ta!
Abun ba k’aramin sake d’aga mishi hankali yayi ba dan babu inda bai duba Mama ba amman bai ganta ba har unguwar su yaje a tunanin shi ko ta koma amma tun kafin ya k’arasa gidan ya hango ana (Baba) datsa datsa kwad’o a gidan, ya fitar da machine da alamun fita zai yi.

Sanin da yayi in dai napep ta hau to ba lalle ta rigashi isowa gidan ba ne, ya sanyashi zaman jiranta, anan cikin mota!
Sai dai almost 2 hours amman bata dawoba.

Zuwa yanzu kam hankalinshi ya kai k’ololuwar tashi!…..
…….Tun farkon had’uwar shi da Hudan yake k’ok’arin toshe duk wata hanyar da zata kawo musu matsala, yanzu haka ya ware millions zai siya musu gida, ta yadda In su Mammy sun zo ba zasu samu abun kushewa ba balle har Granpa yaji ya hana, su Abba kuwa ya san su zasu zo nema mishi aure, so gidan uncle Muhammad ba zai zama matsala ba!
Dan anan aka shirya za a had’u dan ba daban jiran
Dad d’in da suka tsaya yi ba ma to da tuni sun zo an gama magana.

Har ga Allah ba zai tab’a iya rayuwa babu Hudan ba, kwata kwata, shi baya jin ma a tarihi akwai wani mahaluk’in da ya tab’a yiwa wata kalar son da yake yiwa Huda since day 1,
gashi kuma yau Mahaifiyarta da kanta ta kalle shi tace ‘zata rabashi da ita!’

Bai ankaraba kawai yaji hawaye yana wanke mishi fuska!
Sunayen Allah ya fara ambata yanayi yana kuka, kamar k’aramin Yaro.
Da kyar ya samu zuciyar data yunk’ura mishi ta d’an lafa.

Ganin babu Mama ba labarin ta, ya sanya kawai ya yanke shawarar komawa gida yayi wanka daga nan ya kira Ummu a san abunyi!
Dan in ba ruwa ya samu ya sakarwa kanshi ba baya jin kalmar ‘A’ zata iya futowa daga bakinshi a halin da yake ciki...........


BULAMA ✍️


So da Buri
Free Book
37


Kamar yadda Arshaad ya tsara, sai da ya lallab’a yayi wanka da kyar tare da hutun awa d’aya! Tukunna yaji d’an dama dama, cikin tsantsar mutuwar jiki ya lalubo wayarshi ya danna kiran Ummu.
Sai da ta kusan katsewa tukunna aka d’auka, a tunanin shi ko hayaniyar biki ne yasa ta jinkirin amsawa sai dai kuma tana d’auka yaji hayaniya da koke koke!
Cike da fargaba ya hau tambayarta, nan take gayamishi.....
....”Suna shirin shigowa Kano, wani Abokin Junaidu ya kira Baba! Bayan sun gaisa ne
yake ce mishi ‘dama ya kira ne a kan maganar Junaidu!
Wai an sake shi tun satin baya da ya wuce sai dai kuma
babu irin kalar binciken da basu yi ba amman an rasa shi!
Wajen kwana uku kenan yau.
Lokacin da aka sallameshi yayi mishi waya yace ‘zai zo gidanshi, ya d’an kimtsa tukunna ya wuce Kano, bayaso ya sanar da kowa dan surprise zai yi musu’.
Yayi ta zaman jiran nashi amma shiru! Sau daga baya yaji labarin accident da aka samu a garin guda uku ata wajajen k’iri k’iri d’in! mota biyu ta y’an kasuwa ce, d’ayar kuwa ta prisoners d’in ne
waenda aka saki sai dai kuma duk sun k’one k’urmus! Dan ko iya tantancesu ba a yi!

Yayi shiru ya tsaya bai fad’a musu ba domin yanaso yayi bincike sosai tukunna
dan shi tunanin shi yana bashi
ba lalle har da Junaidun ba
amman duk wani investigation yana tabbatar da akwai gawar Junaidun a ciki!
Shiyasa kawai ya yanke shawarar kira ya fad’a musu..’

Gashinan yanzu haka a mutuary in babu damuwa wasu a cikinsu suzo
dan ana da buk’atar su
wajen tantance gawar da kuma ragowar abubuwan da ya kamata!!’.”
(Da kyar Baba ya iya k’arasawa gida ya d’auki kud’ad’e
da atms da abun buk’ata ya mik’a Ja’afar wajen K’asimu
suka kama hanyar Lagos!
Suma su Abba Madu suna ajjiyesu a gidan Baaba Talatu ya juya shi da su Ya Jamilu.
Yanzu haka sun kama hanyar Lagos d’in.)

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Shine abunda Arshaad yayi ta maimaitawa, yana jiwo Sadiya tana ihu tana wallahi “sai tayi sharia da y’an sanda da sojojin da suka rik’e mata Yaro bayan sun gano bashi da laifin komai! Inda ace sun bari ranar su Madu sun dawo da shi ai da duk haka ba ta faru ba!
Allah ya isanta”

Baba Talatu ce ta hau yi mata fad’a, tana cewa
“Bata da tawakkali ne?
In Allah ya riga ya tsara abu dole sai ya faru! Ta daina yi mishi kururuwa da ihu…”
Amman inaaa, bata ji bata gani sai rafka kuka da kururuwar kawai take yi.

Jin yadda gidan ya hautsine ne ya sanya kawai yanke shawarar zai nemo Mama da kanshi in shaa Allah, dan haka yayiwa Ummu gaisuwa, kafin ya kashe wayar.

..............
Kusan a tare motar Abba da ta Aslam suka k’araso cikin estate d’in! Basu shiga ko wanne gida ba suka yi parking a babban parking lot d’in estate d’in kamar had’in baki.
Abba ne ya fara fitowa kafin Aslam, yana k’arasowa inda yake yace “Ka kaita wajen Gwaggo Asabe.
Zan nemaku zuwa anjima.”

“Ok”
Shine abinda Aslam d’in yace
sannan ya juya ya fara k’ok’arin bud’e inda Huda take zaune tana kuka har yanzun, shi kuma Abba ya juya ya nufi gidan Ummi.

Hannunta ya sake fincika bayan ya bud’e motar
ya fito da ita!!
Sannan ya zaro wayarshi ya danna kiran Gwaggo Asabe ya kara wayar a kunnenshi…

Fisge hannunta tayi da duk k’arfin ta! Sannan ta juya ta bud’e motar ta d’au wayarta tana dubawa dan ita a nata tunanin ma ta fashe ne
saboda yadda Aslam d’in ya had’a wayar da hannunta ya runtse a nasa hannunt tun lokacin da yace ‘Mama ba zata tafi da ita ba’ har sanda ya kaita mota….
Rad’ad’i da zugin da hannunta yake mata da kuma tsananin tashin hankalin da take a ciki ne suka hanata d’aukar wayar data fad’i daga hannunta tun shigar ta motar, sai yanzu Ajiyar zuciya ta sauk’e ganin bata yi komai ba hakan yasa ta
rufe motar ta d’an juyo da niyyar kiran Mama.
D’an satar kallonshi tayi, ganin ya tsareta da dara daran idanuwanshi ne ya sanya ta yin k’asa da kanta sannan tace
“Ko baka ja ni ba zan bika!
Wayata kawai na d’auka”
Tayi maganar cikin muryar kuka.

Murmushin rainin wayo yayi mata, kafin yace
“Better!”
Sannan ya juya ya fara tafiya yana cewa “Gwaggon ta fito, yanada bak’uwar da zai bata, ta same shi a gate!”

Hudan kuwa wata zuciyar ce take ce mata ‘ta d’iba a guje ta fice a estate din!’ Amman kuma ta na juyawa tayi ido hud’u da sojoji har hud’u a wajen gate d’in suna zazzaune.
Wani sabon kuka ta fashe da shi kafin ta durk’ushe a wajen abun tausayi…
A hankali kuma sai ta d’ago wayar tata ta fara k’ok’arin kiran Mama tana adduar Allah yasa taga purse d’inta ta d’auka a cikin d’akin, dan
lokacin da Aslam ya jawota
purse d’in ta fad’i a k’asa.

Aslam kuwa jin da yayi kamar ba mutun a bayan shi ne ya sanya ya juyo dai dai ita kuma da d’ago kanta sukai ido biyu!
A zuciye ya taho gadan gadan yana nad’e hannun rigar shi,
Ta san me yake shirin yi hakan yasa ta mik’e da sauri, kafin ya k’araso ita tayi hanyar da taga yayi…..
Rashin kwarin jiki da kukan da taci ne yasa har yazo ya gota ta ya zamana ita take binshi a baya.

Kamar yadda suka yi a bakin Gate d’in ya tarar da Gwaggo Asabe tana jira, nuna mata Hudan kawai yayi sannan yace
“Zuwa anjima zan kiraki!”
Da mamaki tab fuskarta take kallon Hudan ganin yadda yake kallonta ne ya sata kawai jan hannunta suka shige ciki
shi kuma ya nufi gidan Mammy
a falon ta na sama ya samu doguwar kujera ya kwanta, zuciyarshi fal da tunani barkatai.
.......




A parlourn k’asa Abba ya samu Ummi tana shafa wa jan lallen da aka gama cire mata yanzu mahallabiya.
Sallamarshi ce ta katse musu k’us k’us d’in da suke yi ita da Mom wadda ake k’arasa saka mata nata lallen yanzu.
Da sauri ta d’ago jin muryar shi, su na had’a ido ta sakar mishi murmushi sannan ta mik’e ta nufe shi….
Bata damu da Mom da mai lallen da suke parlourn ba! Tana isa gareshi tayi hugging d’inshi tana mai yi masa sannu da zuwa……

Binta kawai yake yi da ido, tanata karairaya…
A hankali yasa hannu ya zarota daga jikinshi kafin yace
“Ki kawo mini abincina sama, kaina yana d’an yi min ciwo.”
Murmushi ta kuma saki kafin tace “ok dear”
Ta juya, shi kuma ya kama hanyar b’angaren shi.

Sai da taga hayewarshi
sannan taje wajen Mom ta rad’a mata wata magana, a take suka kwashe da dariya
kafin Mom d’in tace “ki tabbatar kin yi amfani da abunda na baki.”
Dariya tayi sannan tace “da gudu ma kuwa” kafin ta nufi hanyar kitchen tanata rawar kai!

A nutse ta sake gyara kulolin har da ruwan tea tayi mishi warming da duk wani abunda ta san zai buk’ata.
Haka nan ta had’o abincin a k’aton baske tayi saman itama.



Abba yana shiga d’aki ya kira Dad…bayan sun gaisa ya zayyanewa Dad d’in komai bai b’oye mishi ba!
Dad was very shocked daga jin Abba yana da y’a da Maryam!!
Tabbas shima ya na zargin waenda Abban yake zargi…

Maganar Abban ce ta katse mishi tunani jin yana cewa “Yaya kayi hak’uri da abunda zan aikata, dan Wallahi ko waye yake da hannu, a cikin lamarin nan zan hukuntashi!!Ba zan duba relationship d’in ka da shi ba, gaskiya.”

Ajiyar zuciya Dad ya sauk’e sannan yace “Kayi kwakkwaran bincike, kafin In k’araso, in shaa Allah ni da kaina zan tayaka hukunta masu laifi…..
Daman jikin Mommy ne ya d’an tsaidamu amma da tuni mun iso ma.”

A haka Ummi ta shigo ta sameshi, yana ganinta ya yiwa Yaya sallama ya katse wayar.

A hankali ta k’araso ta ajjiye kafin cikin nutsuwa da karairaya ta hau serving nashi. Sai da ta gama ta ajjiye mishi a kan kafet sannan ta d’ago hannuwanta tace
“Kaga k’unshi da nayi saboda na san kanaso, in je a zana min bak’in flower ko ka fi son shi ahaka??”
Fararaen hannun nata ya kalla da jan lallen ya yiwa matuk’ar kyau amma sai dai shi memokon yaga kyan shi ma, gaba d’aya sai yaji ya tsani jan lalle a take a lokacin!.

“Ki barshi haka.”
Shine kawai abinda ya iya fitowa daga bakinshi.

Mamakin yadda idanunsa suka kad’a suka jazirr!! take
Chan kuma sai tayi murmushi..yanayin yadda ya shigo jikinshi a sanyaye, da kuma yadda yanzu taga yanayinshi tabbas ta gane mai yake buk’ata!
Hakan yasa ta fara k’ok’arin mik’ewa dan ta samu taje ta yi amfani da abunda Mom ta bata.

“Na had’u da Maryam yau...”

Wata mahaukaciyar razana tayi kafin ta koma ta zauna kamar wadda aka jawo da k’arfi!!!.

Kafeta yayi da idanuwanshi…
Yana ganin yadda gaba d’aya ilahirin jikinta yake karkarwa ga wata uwar zufa da take keto mata dukda kuwa sanyin ACn da ya ratsa ko wacece kusurwa ta d’akin.

Ya akai suka had’u?
A ina suka had’u?
Sun yu magana kenan?
Ta fad’a mishi komai?…
Sune tambayoyin da suka taru suka sake gigitata!
D’agowa tayi za tayi magana, sai kuma taga yadda ya zuba mata lulu eyes d’inshi da sukai jaa, wanda sai yanzu ne ta gane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login