Showing 81001 words to 84000 words out of 109746 words
Arshaad da Aaima yadda
suka girma da shi kanshi Aslam d’in, ta shiga alhinin
‘shikenan tayi missing teen age d’insu, da yanda suka taso kenan har abada?’
Gaba d’aya tausayin kanta da Aslam d’in sai ya lullub’eta..
Da kyar ta iya cin abinci, in banda kuka ba abunda take yi,
tun ba ma da Dad ya gaya mata irin abubuwan data dinga yiwa Aslam d’inba, da irin rayuwar da yayi, gaba daya sai ta sake birkice musu, tana kuka tana cewa Aslam do yayi hak’uri ya yafe mata.
K’arshe dai barin gidan ma yayi dan ba zai iya tsayawa tana kuka haka tana neman gafarar sa ba bayan ya san ba laifinta bane ba.
Dad kanshi kasa zama yayi sai gidan su Abba yaje, ya d’an zauna yana dana sanin fad’a mata d’in da yayi.
Sai dare aka samu damar kaita wajen Granpa, dan Gramma ita tunda taji labari ta taho itama suna tare ranar har dare.
Ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwarta ya yi mata ya jiki.
Ba abunda yake b’ata mishi rai irin yanda Gramma take ta faman yayatawa
cewa
“Ai Hudan ce ta bada shawarar yi mata sauk’ar Qur’ani kullum”.
Har sai da ya kwab’eta ta hanyar cewa
“Ta daina cewa ‘Huda’!
Kawai ta dinga cewa
Allah ne ya bata lafiya ya warkar da ita.”
Gramma ta so yi mishi bayani, amman ganin kamar ranshi a d’an b’ace yake kuma ta son ba ya son jayayya yasa kawai tace
“In sha Allah, Granpa.
Zan gyara.”
Tun daga kan Gramma har Aaima ba wanda bai bada zakka da sadaka ba na ban mamaki!
Sauk’a kuwa ba su daina ba
ana kan yi dan
Dad cewa yayi “zuwa k’arshen watan nan ma in Allah ya yarda aka kammala na Mommy
to ba dainawa za ayi ba
duk sati sai an yi sauk’a a cikin eatate d’in a tsakanin su, in shaa Allah”.
Yau kusan sati d’aya da warkewar Mommy, har su Hudan sai da suka zo suka yi mata sannu da barka a b’oye da daddare.
Mommy tayi matuk’ar murnar ganin Sudais da Shuraim
ita daman tana son twins, kuma tunda taji labarin suna da twins a family d’in taketa so ta gansu da su da Huda.
Tunda Mommy taga Huda Allah ya d’aura mata k’aunarta, especially ma da taji gudummawar data bayar akan rashin lafiyarta..
Tayi mata godiya yafi a k’irga!
Ita kam Hudan wani tsoron Allah da girman zatin shine ya sake shigarta, tana tunawa ko 2 month ba ai ba ta ganta a hargitse amman kalleta yanzu garau!
Tabbas a rayuwa, in dai mutum yana neman sauk’i! Waraka!
Taimako! To kuwa ya nema a wajen Ubangijin Talikai wanda bashi da kishiya.
Da kyar ranar ta barsu suka tafi, ita Huda mamakin ma yanda matar take mata take yi, kamar ta santa tun daa chan amman da ta tuna yanda Mommyn ta bata labarin shak’uwarsu ita da Mama sai tayi tunanin ko saboda Maman ne yasa take yi mata haka....
Sannan itama a lokaci d’aya taji girma da k’aunar matar ya shige ta.
A b’angaren Mommy kuwa, kawai tsintar kanta tayi da tsananin k’aunar Huda, dan koda bata kasance y’a ga Maryam ba tabbas Ubangiji ya d’aura mata k’aunar Yarinyar a ranta.
Ba abunda yafi sosa mata rai irin da taji cewa ‘an sa ranar ta da Arshaad!’ Saboda ita har ga Allah tun da ta d’aura idonta akan Yarinyar ta fara kwad’ayin ganinta da Aslam d’inta a matsayin maaurata!
Amman kuma da ta duba taga
abunda yayi Aslam shi yayi Arshaad sai ta hak’ura ta barwa Allah komai sannan ta bisu da fatan alkhairi.........................
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
50.
Yau saura sati biyu auren su Hudan, sai shirye shirye ake yi.
Yayinda jikin Mama yayi sauk’i sosai abun har mamaki yake bawa jamaa kamar ba wadda ta karye ba, follow up kawai take zuwa abunta.
Abba da kanshi yaje ya siyowa y’arsa kayan d’aki na gani na fad’a, hatta cokali bai bari ba sai da ya siyo mata komai bayab ya tambayeta taste d’inta, wasu kuma yana daga chan d’in yake turo mata Sakina ta tayata zab’a.
Sannan ya had’a mata gara nan ma na gani na fad’a.
Lokacin da bikin ya rage saura sati d’aya already
kayan gara da kayan d’akin amarya suna gidanta.
Duk da ba wai zama za suyi anan d’in ba, kai ta
kawai zaayi gidan daganan su wuce karatunsu amman hakan bai sanya an k’i yi mata kayan d’aki ba saboda
time to time za su ke zuwa hutu.
Shima Arshaad a nasa b’angaren hakan bai hana sa siyan gida ba!
Daa a cikin estate d’in zai zauna amman da yake Granpa ya san Hudan zai aura haka nan k’iri k’iri sai ya hana sa gida!
Da farko Granpa d’in cewa ma yayi ya bar mishi estate d’inshi,
tun kafin auren! Da kyar Aslam ya lallab’ashi
ya hak’ura amman dukda haka sai faman neman fad’a yake yi
kuma fa sai da Dad ya tambayeshi tun farko lokacin kafin ma a saka rana amma sai ya nuna irin shi ba ruwanshi d’innan su yi abunda sukeso..
Yanzu kuma da bikin ya taho sai neman rigima yake yi yana neman abokin fad’a!
Shiyasa kowa ya sha jinin jikinshi dan duk wanda yayi rashin sa’a ya yarda ya samu matsala da Granpa a wannan yanayin da yake, tou tabbas kashin shi ya bushe!
Wannan dalili yasa Arshaad ya sayi gidanshi da kanshi daman kuma shi har ga Allah ya ma fi son ya yi komai da kanshi, dan
da kyar ma ya yarda ya bari Daddy ya bawa Mommy mak’udan kud’ad’e take had’a mishi zazzafan lefe..
Gida kuwa da Abba yace zai siya mishi yi yayi kamar zai yi kuka, shi kuma Abban ya dage!
Sai da Mommy ta saka baki tukunna Abban ya hak’ura ya bar Arshaad d’in ya sayi gidanshi mai hawa biyu d’aki bakwai da parlour hud’u har da d’an k’aramin bq a gefe a nan cikin Nasarawa sai dai da d’an tafiya tsakaninsu da gida da estate....
Su Ummu da Mommy ne suka je suka yi mata jerenta tsaf!
Wanda yanzu kawanchen Mama da Mommy ya dawo sabo fil! Dan har gida Mommy taje ta dubota, duk da Dad ba wani son yawan fitar tata yake yi ba amman indai abu ya shafi Maryam to ya kan bari saboda Mommyn tana yi musu campaign a lamarin Abba,
sai ita kuwa Mama duk maganganu da Mommy take mata akan Abban amsa
d’aya zuwa biyu take bata kullum
‘Allah ya zab’a mafi alkhairi’ ko kuma tace ‘ita fa ta riga ta hak’ura da Abba har abada! Ba akan dalili d’aya ba sai akan dalilai barkatai’.
Amman duk hakan bai sanya Mommy ta hak’ura ba, haka nan suke fama kullum.........
Yau sauran kwana uku d’aurin auren!
Su Hudam basu samu komawa wajen Mama ba sai a yau d’in.
Kafin su wuce Abba ya nemi ganinta..
Kamar ko wanne uba haka nan ya zaunar da ita yayi mata nasiha mai ratsa jiki!
Yana hawaye tana kuka
haka su Sudais suma da suka zo yi mata sallama…
A haka dai ba dan suna so ba suka yi sallama Abba ya sanya mata albarka.
Mommy da kanta ta kaita har gidan Shuwa gaban Mama
Hudan tayi mamakin ganin baki y’an Maiduguri da suka zo dan gidan a cike tap! Suka tarar anata hada hada.
A yau d’in zasu fara event!
Dan haka suna isa suka tarar har mai kwalliya ta k’araso
tana jiransu, waensu a cikin friends d’in su ma duk sun zo,
da yake mai kwalliyar da tayi mata ita ce za tayi musu saboda Arshaad Maiduguri style yayi..duk shi ya biyawa friends d’inta kud’in makeup da anko.
M T
Tunda Mommy ta warke
kullum itake ce take yiwa Aslam girki…
Wani special kulawa take bashi amman ta rasa dalilin damuwarshi dan ko jiya ma sai da Doc ya zo ya dubashi kuma ya tabbatar musu jininshi ya k’i sauk’a instead ma k’ara hawa yayi!
Sannan ga zazzab’insa shima ya dawo.
Gaba d’aya hankalinsu duk a tashe yake, dan sun rasa gane kan Aslam kwata kwata.
Arshaad tun yana kulashi, yana tambayarshi meke damunshi yana lallab’ashi,
har ya zo ya hak’ura kawai ya watsa shi a kwandon shara
Dan Arshaad d’in gani yayi kamar ma Aslam d’in haushinshi yake ji!
Idan ma yana waje Arshaad d’in ya shigo kawai sai dai ya tashi ya fice ya bar mishi wajen, ko magana baya so ta had’asa da shi!
Kamar ma wanda yake k’ok’arin yin gaba da shi ta k’arfi da yaji! Shiyasa Arshaad d’in kawai ya rabu da shi
amman a chan k’asan zuciyarshi mamakin abubuwan da Aslam d’in yake mishi a wannan lokacin da ya kamata yafi kowa tayashi murna, yake yi.
Hatta Dad Abba da Daddy sun lura da hakan, basa son shiga tsakaninsu tunda sun fi kusa shiyasa kawai suka zuba musu ido a ransu suna mamakin mai ya had’a best friends haka??…….
Da yamma, Mommy na d’aki tana jera kaya a wardrobe
Dad ya shigo..
A bayanta ya tsaya yayi hugging d’inta.
A hankali tayi murmushi kafin ta juyo still yana rik’e da ita tace
“ina wuni Dad”
Murmushi shima yayi mata yana jin tsananin k’aunarta tana nunkuwa a cikin zuciyarshi, a hankali yace
“Bayan waennan akwai wasu kuma da kike buk’ata??”
A hankali ta girgiza mishi kai alamun ‘a’a’.
Ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya jawo hannunta suka nufi gadon dake d’akin.
Sai da ya zaunar da ita shima ya zauna a daff da ita tukunna yace
“Aisha, magana nake so muyi dake ta gaskiya da gaskiya”
Da sauri ta mik’e tana k’ok’arin kawar da kanta daga gareshi kafin tace
“Not again Dad, na gaya maka ban tuna komai ba, please Dad ka bar maganar nan.”
Mik’ewa shima yayi ya sake rik’o hannunta kafin yace
“Look at me kice mini ‘wallahi Dad ban tuna komai ba‘.”
Hannunta ta fara k’ok’arin kwacewa a cikin nashi ta had rai sosai cikin fushi tace
“Tunda baka yarda da ni ba, shikenan!”
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace
“Jiya da yamma kin manta wayarki a d’akina kin tafi kitchen, naje kai miki wayar saboda a nata kira..
I didn’t mean to eavesdrop but i have no choice!
Naji komai maganan ku da kuka yi ke da Asabe!..
Mai yasa kika b’oye min?”.
Gabanta ne ya yanke ya fad’i!
A hankali ta tsaya tayi tsit ta nutsu ba tare da tace komai ba, sannan ta kasa d’agowa ta kalleshi…
Hannu yasa ya kamo hab’arta ya juyo da fuskarta ya d’ago fuskar, da sauri ta runtse idanuwanta.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin a hankali yace
“Maimaita min abinda ya faru that very day da kika fad’o, waye ya turoki?! Ina so inji daga bakinki, don’t lie, kin san naji komai..
Kawai i want you to tell me.”
A hankali tace zan fad’a maka amman sai ka yi min rantsuwar ba zaka fad’awa kowa ba sannan ba zaka nuna ko da a fuskarka ne ba.”
Cika fuskarta yayi cikin fad’a yace “Ba zan iya ba Aisha!
Ya zama dole in fad’a sanann in nuna fushi kuma in d’auki mataki! Dole ne in hukunta mai laifi!
Kin san irin ciwon da kika yi kuwa?
Kin san irin wahalar..”
Cikin katseshi tace
“To kaga dalilin da ya sanya na b’oye maka ko?”
Cikin karyewar zuciya taci gaba da cewa
“I have lost a lot, shekaru sun jaa..
Na ci burin yiwa y’ay’ana tarbiyya especially ma Aaima da ta kasance mace amma kalli fa duk nayi missing
Mai ya rage yanzu?.
Ni za kayi wa abun nan ko?
A kaina kake so ka hukunta me laifin ina?
To ni d’in nace ‘na yafe
har abada har gaban abada!’
Meye kuma na dawo da abunda ya riga ya wuce??.
All i need to do now shine ibada dan kwata kwata ban gamsu da sallolina da kuka ce inayi ba, Nafilfili da ibada su kawai nake buk’atar inyi a halin yanzu, ba wai case da holding grudges ba!
I want peace.”
A hankali ganin ya d’an nutsu yana kallonta kawai, ta kamo dukkannin hannuwanshi biyu ta rik’e tace
“Dad, duniyar ma duk nawa take?
Idan fa mukayi hak’uri ma duk mutuwa za muyi!
Yanzu idan kace zaka d’auki mataki wallahi square one zamu koma, mutane ba za su tab’a duba laifin da aka yi mini ba instead gani za suyi kamar ka fifita ni ne wanda fifita Aslam da Granpa yayi tun farko ni na tabbatar shiyasa aka zamo silar zabgemin kusan rabin rayuwata haka nan na yi ta a wahala!
Please dan Allah let it go, for me..”
Mommy ta dad’e tana kwantar mishi da hankali, da nuna mishi ita kwanciyar hankali kawai take buk’ata yanzu, tukunna da kyar da mugun kyar ya yarda da buk’atarta akan ba zai yi komai ba, kuma ba zai nuna ba ko a fuska!
Tukunna a hankali ta hau fad’a mishi abunda yaji tana fad’awa Gwaggwo Asaben.....
In banda ajiyar zuciya ba abunda Dad yake sauk’ewa a jejjere…
Ji yake kamar ya mutu dan tashin hankali da takaici
gashi ta saka shi yayi mata alk’awari.
A haka Aslam ya shigo ya samesu..
Tabbas ya lura akwai abunda suke tattaunawa but yadda Dad yayi ta k’ok’arin ganin ya danne ne
yasa kawai ya basar dan ya fahimci koma menene to bai shafesa ba.
Gaidasu yayi ya nemi waje ya zauna a k’asa kan kafet yana kallonsu k’aunar iyayen nashi tana sake shigar mishi zuciya
yana jin wani farin ciki yana taso masa ta k’asan zuciyarshi just by looking at them.
Suma d’in shi suke kallo
wanda tashi d’aya
In ka kalleshi zaka hango tsananin damuwa da k’uncin da yake a ciki...
“Ya baka shirya ba?
Yanzu muka gama waya da Arshaad, yace yanzun za a tafi gudun kar ayi dare, kai da Aaima kawai ake jira.
Na kira Aaiima tace min ta shirya tun d’azu, a
tunanina kun wuce ma.”
Ajiyar zuciya Aslam d’in ya sauk’e kafin a hankali yace
“Am, daman sallama nazo in yi muku.”
Da mamaki suke kallonshi.
Bai jira jin me za su ce ba yace
“Inaso zan wuce Uk!
Akwai ayyukan da nake so In k’arasa a chan.
K’uraaa mishi ido kawai yaga sun yi, har ya fidda ran za suyi magana yaji Mommy tace
“Mai yasa?
Ka fad’i mini gaskiya dan na san akawai dalili Aslam”
Murmushi kawai yayi kafin yace
“Please ku barni in tafi, dan Allah”
Mik’ewa Dad yayi ya nufi hanyar fita kawai ba tare da yace mishi komai ba, ya fice.
Hannu Mommy ta mik’a mishi,
a hankali ya sa hannun nashi cikin nata ya mik’e ta dawo dashi kan gadon inda Dad ya tashi.
Cikin kulawa ta kallesa tace
“Aslam meye damuwar ka?
Ko har yanzu kana jin zafin abubuwan da nayi maka ne?”
Ta fad’i hakan muryanta na d’an rawa kamar wadda zata fashe da kuka.
Da sauri yace
“Mommy please mana, ki daina tunanin hakan
sam a haka bane, ai ba laifinki bane ba.”
Cikin katseshi tace
“To yaya ne?
Menene?
Talk to me dan Allah!
Ko kanada wadda ta fini?
Talk, kai kanka za kaji nauyin zuciyarka ya ragu.
Waye ya b’ata maka rai?
Ko kana da masaniya akan abunda ya faru ranar dana fad’o?
Fad’a kukayi da Granpa?
Ko Daddy ko wani?
Ko Arshaad ne?
Ko company d’in ne?
Naji Dad yace it was successful kun bud’e kai da Abba, akwai wani abun ne?”
Duk ta rikice tambayoyi kawai take jero mishi barkatai.
A hankali ya lumshe idanunsa, sannan ya d’auko Dayan hannun shi ya d’aura akan hannayen nasu!
Ganin haka yasa itama ta d’auko Dayan free hand d’inta ta d’aura akai ta bashi dukkannin attention d’inta a hankali tace
“Talk, I’m your mother, I can help you.”
Bud’e idanuwanshi da suka yi jaa yayi, a hankali ya fara magana
“I know I’m trying to be selfish here, but.......................... .”
Wata k’akk’arfar ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e bayan ta gama sauraran tilon d’an nata, a hankali ta janyo shi jikinta ta rungume, ta fara hawaye, cikin karyewar zuciya tace
“I’m soo sorry son, ba zan iya taimakonka akan wannan al’amarin ba!.”
Murmushi yayi wanda yafi kuka da ihu ciwo
a hankali ya zaro ta ajikinshi kafin yace
“I know, kawai ki tayani addua, thats all I need maybe zan samu sauk’in rad’ad’in da nake ji, please Mommy.”
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e
kafin yace
“Maybe i’m not destined to be happy, a duniyar nan!! Haka Allah yake son ganina, if not
why?
Tayaya zan kasa cire......”
Da sauri ta sa hannu ta toshe mishi baki, tausayinshi yana sake shigar mata zuciya…
Ahankali yasa hannu ya zare hannun nata sannan yace
“Pls Mommy ku barni In tafi, dan Allah.”
Tana shirin bashi amsa, Dad ya shigo..
Kallonsu yayi kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru ya juya kawai, yace
“Ku zo duk ku biyun gidan Granpa, yana son ganinmu, an dawo da su Adama!”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fice........
Sanye take cikin bridal gown, peach colour anyi kwalliya da white stones masu shek’i da d’aukar ido a gabad’aya k’irjin
da kuma half d’in k’asan rigar ta tsaye har ta bayan side d’in inda yake flowing….
Ta d’aura jewelry’s white,
yayinda takalmi, tauban, mayafi da head d’inta suka kasance peach….
Fuskarta ta sha casual makeup simple!
Dan cewa tayi itama ayi mata casual d’in inyaso ranar wuni, traditional day d’in da Shuwa
da su Mama za suyi
sai ayi mata bridal d’in.
Tayi masifar yin kyau kuwa
gashi kwalliyarta ta tafi da shigarta matuk’a.
Bridesmaid d’inta su 10 har da Sakina 11, Khadijah bata zo yau ba tace sai gobe zata fara zuwa saboda tana laulayi kuma jikin ya d’an motsa.
Kusan duk Sakina ce ta gayyatosu (bridesmaids d’in)
Y’an makarantar su ntic
kuma aka ci sa’a suka karb’i gayyatar aka shirya anko da su kasancewar ta fad’a musu da wuri…
White gown ne a jikinsu,
sai peach head, takalmi da jewelry’s sai vails d’insu white..
D’inkin su iri d’aya sak dan
saboda ma gudun samun mishkila dama tailor d’aya ne yayi d’inkunan ( bama anan ba )
Makeup d’insu komai iri d’aya.
Tana tsaye Sakina tana yafa mata mayafi Mama ta shigo,
suna had’a ido kawai suka fara hawaye a tare!
Sakina wadda itama taji idonta ya cicciko ne tace “Mama dan Allah ku daina” sai kuma ta fara kuka itama, ahaka Ummu ta shigo ta samesu, itama tana ganinsu ta hau kuka.
Da kyar friends d’insu suka lalllashesu aka d’an yi musu hotuna suka yi abunda ya kawosu, suka juya suka fita.
Sai da aka sake gyarawa Hudan da Sakina makeup d’in su
Allah yaso mai makeup d’in bata riga ta tafi ba.
Ana gamawa, mai makeup d’in ta fara had’a kayanta, tana shirin tafiya kiran