Showing 18001 words to 21000 words out of 109746 words

Chapter 7 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2957

b’acin raine, ashe.

Tattaro duk wata basira da wayon da Allah ya bata tayi kana ta had’a da y’ar ragowar jarumta da kwarin jikinta, kafin tace
“Wannan kuma matsalarkace!
Tunda har ka bijirewa Mahaifinki wanda yayi ik’irarin tsine maka a kanta, to me yasa ni zan tsaya damuwa da kishi?”
Tana gama fad’in haka ta fara k’ok’arin mik’ewa, dan tabbas In taci gaba da zama to nan da nan zai b’aro jirginta.
Dukda cewa bata da tabbacin Maryam d’in ta gaya mishi sunada baby tare, amman hatta muryarta rawa take yi, sannan idanuwanta duk sun kawo ruwa! Ga shi kuma Abban ya tsare ta da ido, it’s like akwai abinda yake son fahimta…
Dan haka ta mik’e tayi hanyar k’ofar fita da sassarfa.

Abinda bata saniba shine
tun a reaction d’inta na farko Abba ya riga ya b’aro jirginta, gashi kuma yanzu rashin wayonta na son barin d’akin ya sake tabbatar mishi! Dan haka yayi hanzarin mik’ewa shima, ya rigata isa ga k’ofar ya shiga gabanta ya tsaya!.

Kasa d’agowa tayi ta kalleshi..

He can feel yadda numfashinta suke korar juna daga inda yake tsaye!.

Juyawa kawai yai ya murza key d’in ya zare shi, sannan ya cilla cikin aljihun wandon shi.

A take razana da firgicin da take ciki suka sake hauhawa!
Tun ba ma daya juyo taga yadda ya tamke fuska kamar bai tab’a dariya ba, zata iya rantsuwa tunda aka haifota duniya bata tab’a ganin Abba a irin wannan yanayin ba.

Cikin dakakkiyar muryar da bata da alamun wasa a cikinta yace
“Ummi!! A cikin biyun nan, inaso ki zab’i d’aya.”
Yayi maganar yana mata alamu da y’an yatsun hannunshi na dama daya d’aga mata su daidai setin fuskarta.

Na farko
Ko ki gaya min gaskiya tun farko abunda ya faru…yadda kuka yi kuka rufe ba tare da kowa ya ji ba, da yadda aka y munanan kalaman da ban san na rubuta suba suka isa ga Maryam,
Inason jin komai da komai karki b’oye min ko, alif.
Ko kuma (na biyu)
In yi miki dukan mutuwar da ko Mahaifiyar ki in da ace zata dawo duniya ba lalle ta shaidakiba, sannan in k’ara miki da saki, kuma in kulle ki dake da duk wanda ya taimaka miki.!

Sannan inaso ki sani sharia zan yi ta gaskiya yadda ko Granpa bai isa ya kwatoki ba wallahi, idan kuma ya tilastamin to tabbas zamu iya samun matsala da shi dan ba zan iya yi mishi biyayya wajen wofantar da hukunta waenda suka raba ni da y’ata ba!.”

Wani irin mahaukacin bugawa k’irjin Ummi ya hau yi, especially ma da taji zancenshi na k’arshe.

Amma Maryam an yi shegiyar mata!! Wato fad’a mishi tayi kenan! Yanzu Ina mafita?? K’aryatawa za tayi ko kuma ya zata yi?
Itakam yau ta shiga tara ma ba uku ba!
Ga shi ba Mom a kusa.

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ta fara maimaitawa tana neman taimakon Ubangiji, dan tabbas shi kad’ai ne zai iya cetonta a hannun Abba a yau.

Tsawar da ya daka mata ne, ya katse mata tunanin, a take ta durk’ushe a wajen ta fara kuka.

“Ba kya ji na ne!!!!”
Ya fad’a cikin hargowa
har wata kwalla tana zuba daga idonshi tsabar b’acin rai.

Shiru tayi in banda kuka ba abunda take yi.

Dukan mace kwata kwata baya cikin tsarin Abba
But Ummi left him with no other choice, bai san lokacin da ya fincikota ya mik’ar da ita tsaye ba!
Bata gama sosa, gefen wuyanta da takeji kamar ta yanke sakamokon janyotan da yayi da hannun rigarta ba, taji sauk’ar wani irin gigitaccen Marin da ya kusan d’auke mata nunfashi, bata gama dawowa dede ba ya sake d’auke ta da wani!
Cikin tsananin b’acin rai yace
“na fahimci option 1 kika d’auka!”
Sannan ya juya ya nufi wardrobe da sassarfa.

Da sauri Ummi wadda take ji kamar an yi mata b’arin wuta a kumatunta duka biyu ta k’arasa jikin k’ofar tana bubbugawa tana neman taimako, dan ta lura Abba baya a haiyyacinshi…

Babu wanda ya jiyota, dan k’ofofin gidan gaba d’aya sound proof ne, ko bayaga haka ma yanayin girman gidan ba lalle a iya jiyota ba!

Bata ankara ba taji ya janyota da dukkan k’arfin shi ya zuga mata belt…wani mahaukacin ihu tayi ta fad’a kan gado ta rarumo blanket da quilt d’in kai ta k’udundunu a ciki.
Cikin zafin nama ya fincike bargunan yayi cilli da su sannan ya shak’o ta, kafin yasa dukkanin k’arfin da Allah yayi mishi ya fincikota daga kan gadon ya tsayar, still yana rik’e da wuyanta da ya yiwa muguwar shak’a!
Ita ya shak’e amman yadda idonshi yayi jaaa zaka d’auka shi aka shak’e!.
Cikin d’acin zuciya yace
“na fasa sakinki da kaiki kotu Ummi kashe ki zan yi kowa ya huta!!”

Ummi kuwa ganin Abba yana shirin kaita lahira ne ya sanya ta fara dukan hannunshi, tana tarin wahala, da y’ar ragowar muryar data ragemata tayi amfani wajen cewa
“Za.z.Zan fa ff fad’a”
Tana kallon kwayar idanunsa waenda take hango tsananin tashin hankali a cikinsu.

Jifa yayi da ita sannan cikin b’acin rai ya juya mata baya kafin yace
“Ina jinki, kuma kar kiyi kuskuren b’ata mini lokaci, dan ba zan baki wani chance d’in a karo na biyu ba.”

Ajiyar zuciya kawai take ta faman sauk’ewa mai had’e da tarin wahala…
Jin shiru ya sanya shi juyowa
yana mata wani irin kallo.

Ganin haka yasata fara magana
“Ranar bayan mun ji labarin sakin da kayi mata….
Muna zaune da ni da Mom, kawai sai ga Daniel ya zo a rikice….dama duk wani abu idan ya faru ya kan fara fad’a mana kafin Granpa, in na dannewa ne mu danne ko kuma mu sakashi ya juya zancen sai mu bashi kud’i.

To kamar kullum haka ranar ma yazo mana da takardar sak’on Maryam, yake cewa ‘k’anwarta ce ta kawo kuma tace dan Allah a baka tana waje tana jira’
Ba komai ne a cikin takardar ba fa ce
‘Baka hak’uri da take yi akan duk laifin da tayi maka har ya kaika ga d’auke k’afa wanda ita bata san laifin ba! Sannan tana buk’atar ka a asibiti zata haihu.’

A lokacin kusan sumewa nayi, dan ni ko had’a shimfid’a baka yi da ni amman ita Maryam gata harda ciki zata haihu! Kuma na tabbatar muddin kaji labarin cikin nan to baza ka tab’a yarda mu koma ba, sannan definitely zaka mayar da ita tunda saki d’aya ne a tsakanin ku.

Rasa yadda za muyi mukai. Murnar mu gaba d’aya sai ta koma ciki......

Tun muna Yara Allah ya yiwa Adama baiwar kwafar duk wani zane da rubutu duk kuwa wahalarshi tsaf zata kwafe tayi irinshi exactly..

Ganin yadda duk na rikice ne yasa ta ce mini ‘inje In d’auko littafin ka’
Na fahimci me take shirin yi shiyasa da gudu, na fita naje d’akinka na kuwa ci sa’a baka nan hakan ya bani damar d’auko diary d’inka.

Da farko da muka zo, mun tsara ne akan zamu rubuta mata ‘ta jiraka nan da 2 weeks in shaa Allah in ka gama settling da Granpa, zaka je ka sameta’
Kaga kafin nan tunda haihuwa zata yi already ta fita iddarka, ni kuma sai in san yadda zan yi in ja hankalinka mu koma, kuma mun tsara zamu tura wani yaje ya aure Maryam d’in kafin mu dawo tukunna mu saka ka fahimci kana da y’a ba tare da sunan mu ko laifin mu ya fito ba!

Amman karanta diary d’inka da muka yi ne ya sake hautsina komai!
Domin kuwa Abba kwata kwata baka da plan d’in yin rayuwa da ni, you promised maryam (a diary d’in) cewa nan da 1week zaka je ka maida ita, kuma ko parents d’inta sun yarda ko basu yarda ba zaka d’auketa ku sake barin k’asar!
Har sai lokacin da Allah yayi
Tou were willing to leave and risk everything for her, a plan na future Dinka kwata kwata babu ni a ciki!!
And you wrote it ‘a dalilina ne yasa ka tafi ka bar Nigeria, har iyayenta suka kasa hak’ura, suka biyoka, shi kuma Granpa ya yanke wannan hukunci, so I have to pay the price!’
Although ban san menene price d’inba tunda baka rubutaba, but na fahimci saki ne, tunda yadda kake tsarawa..y’ay’an da zaku haifa da sunayen da zaku saka musu, da irin tarin addu’o’in ka na burin samun babys daga gareta, na fahimci baka da tsarin zama da ni!
Kuma hankalina yayi matuk’ar tashi da naga kwad’ayi tare da kalar son da kake yiwa y’ay’an da zaku haifa( kai da ita), shiyasa kawai muka yanke hukuncin rubuta mata takardar da muka aika Daniel ya kaiwa k’anwarta!.
A baya tunani na son Maryam kakeyi, amman karanta diary Dinka da nayi tun daga farkon had’uwar ku har k’arshe bayan tafiyar Daniel, shi ya tabbatar min da cewa haukan somta kake yi
Dan haka with her in your life, Abba banida chance kwata kwata.”

Matsowa tayi kusa dashi ta kama hannunshi kafin tace
“Abba put yourself in my shoes, yadda kakeji akan Maryam wallahi nima haka nake ji a kanka!
Shiyasa da naji plans d’inka hankalina bai ida kwanciya ba har sai da muka had’u da mammy ta rakamu aka rufe maka baki akan batun mayar da ita d’in da kace zaka yi sannan aka cire ta a ranka gaba d’aya!

Sai dai kuma shekara d’aya kawai Allah ya bawa addu’o’i n namu ikon yin tasiri a kanka domin har yau zancenta kakeyi ba dare ba rana kuma na tabbatar ba dan ta yi aureba da tuni tana a gidan nan ni kuma na san karshenta zuciyata bugawa zata yi!”.

Cikin kuka tayi k’asa ta durk’usa a gaban shi still tana rik’e da hannuwanshi kafin tace
“Duk wani abunda kake buk’atar ji, gashi na fad’a maka, har wanda bai kamata kaji ba duk na fad’a maka Abba
Amman inaso ka cire son rai ka duba lamari na, wallahi duk kai ka janyo komai!
Komai kuma da nayi, na yishi ne saboda kai, saboda son da nake yi maka da kuma burin inga mun kasance tare har abada!.
Dan haka, dan Allah ka dube ni da idon rahama ka yafe min, ni kuma na yi maka alk’awarin ba zan sake wani attempt d’in tab’a rayuwar Maryam ko y’ar ta ba!
Tun farko ma da ace baka yi abinda kayi ba, da ba azo nan ba..
Inda ace ka bani time d’inka tun lokacin farkon aurenmu da ba zan yi attempting aika mata da sak’o ba wanda har yayi sanadiyyar da ya sanya ni karanta diary d’inka.

A yadda nake sonka inda zaka dinga kula da ni, sannan ka min alk’awarin adalci da zama dani har abada, wallahi Abba da zan rufe idona In danne duk wani kishi, in barka da Maryam
Amman yadda ka nuna gaba d’aya baka da plan na rayuwa dani shi......”

Hannun shi da ya warce a cikin nata ne ya sa ta had’iye ragowar maganganun data d’ebo!

Cikin b’acin rai yace
“Ummi! ban tab’a ganin selfish being irin ki ba!.
And FYI ba saboda son da kike yi mini bane ya sa kika aikata waennan abubuwan wake up!! Saboda tsananin son da kike yiwa kanki ne ya saki aikata hakan!

Kinga dai Ina son Maryam fiye da raina ko??
Amman wallahi inda ace tun farko ta nunamin bata sona kuma akwai wanda take tsananin so, kamar yadda na nuna miki, tou da tabbas zan iya hak’ura da ita, saboda farincikin ta!!

That is love, ba wannan shirmen naki ba.”
Yana gama fad’in haka ya warce k’asan rigarshi da ta kamo ya wuce ya bud’e k’ofar ya fice a d’akin ya barta nan durk’ushe tana kuka tana kiran sunanshi…..

Mom tana zaune a falon da k’unshinta, taga sauk’k’owar Abba…
Da k’arfi k’irjinta ya buga!
Yadda taga ya sauk’o ya wuce fuuu ranshi a mugun b’ace ko adawo lafiyanta bai amsa ba.

Gaba d’aya sai ta kasa nutsuwa…
kusan minti biyar ta bayar amman shiru ba Ummi ba labarin ta, dan haka ta yanke shawarar cire lallen!
Ko bi takan mai k’unshi da take ta ce mata “bai kamaba” Bata yi ba ta bata kud’inta ta kira mai aiki tace “ta tattare wajen”dan gaba d’aya k’irjinta bugawa yake yi ta rasa dalili.

Kaf falon sama da d’akunan ta duba bata nan, har d’ayan side d’in ta sauko ta hau ta sake dubawa nan ma bata nan.
Tunawa da tayi Abba yace ta kai mishi abinci bedroom d’inshi ne, yasa da sauri ta nufi stairs d’in da zai kaita side d’in nasa.

Tun kafin ta k’arasa d’akin ta fara jiyo sheshshek’ar kuka..dan haka ko sallama bata yi ba ta k’arasa ciki da mugun sauri.

A yadda Abba ya fita ya barta a haka ta tarar da ita, da sauri ta k’arasa ta d’ago ta kafin a rikice ta hau tambayarta “mai ya faru?”

Kukanta ne ya k’aru, wanda hakan ya sake rikita Mom! Ta d’ago hannu kenan zata tab’ata taga shatin yatsu kwance akan farar fuskarta..
Cikin gigita ta cigaba ta tambayarta tana faman jijjigata
Da kyar Ummi wada tun shigowar Mom kukanta ya tsananta ta iya sassauta kukan nata da kyar
ta hau gayawa Mom dukkanin abunda ya faru, tana sheshshek’a….


Tunda ta fara magana Mom tayi mutuwar tsaye! Har ta kai aya ta d’ago tana kallonta amma ko gezau bata yi ba.
Sai da Ummin ta d’an tab’ata tukunna ta juyo da hankalinta gareta kafin cikin b’acin rai ta fara magana
“Ban tab’a ganin dak’ik’iya Irin ki ba! A tunanina rashin wayon ki bai kai haka ba!
Amman yau kam na gasgata ya kai har ma ya wuce zatona.
In banda rashin hankali, ba duka ba ko kanki Abba zai saka a gabas da wak’a a hannunshi, ya kamata ki fad’a mishi wannan maganganun da muka yi alk’awarin rufawa juna asiri akai har abada???
Barazana ce fa yayi miki!! Tayay ma za kiyi tunanin Abba zai iya yi miki illa?? Na tabbatar ko suman k’arya kika yi tuni zai dawo dai dai hankalinshi kuma ya tashi!!

Amman da yake ke d’in dabba ce!! Shine kika tonawa kanki asiri da mu da muka taimakeki, gaba d’aya!! Yanzu ya kike so muy.....”.

Cikin katseta Ummi, tace
“Adama wallahi ke kike ganin kamar barazana ce amman ba haka baneba, da gaske na hango tashin hankalin da ban tab’a gani ba a cikin kwayar idanunsa, kuma na tabbatar zai iya aikata dukkanin abunda ya fad’a din.
Ba abinda yafi d’aga mini hankali irin kalmar ‘saki’ da ya ambata!
Shiyasa kika ga nayi haka, kin sanni zan iya yin komai domin inga na kare aurena!
Kuma baya ga haka a tunanina idan na fad’a mishi gaskiya to zai yarda da ni kuma ya fara trusting d’ina daganan ya so ni!
Shi da bakinshi yace ‘In na fad’a mishi gaskiya komai zai wuce, in kuma ban fad’a ba har saki sai ya had’a mini dashi km....”
Marin da Mom ta d’auketa da shi ne ya katse mata ragowan maganartata…
Cike da mamaki ta d’ago tana kallon Mom….za ta yi magana Mom d’in tayi saurin d’aga mata hannu sannan tace
“Lalle Ummi, wato kin yi komai saboda kare aurenki da jawo hankalin mijinki gareki ko?
Mu kuma fa? Da kika zubar mana da k’ima, kika sakamu a matsala? Ke a ganinki kin yi mana adalci kenan?.
Ko dan kinga ke baki da wani ishashshen laifi a cikin lamarin shiyasa?
To bari kiji in gaya miki
kinga wannan abunda kika yi?”
Bata jira jin amsartaba tace “ba zai jawo yarda tsakaninki ke da Abba ba ballantana a tafi kan maganar so, in banda bak’in jini da tsana ba abunda rashin tunaninki ya jawo miki!!!.
Kuma inaso ki sani, ni da sake shiga harkarki har gaban abada!! Saboda na lura kowa kanshi ya sani dan haka kowa yayi ta kansa.”
Tana gama fad’an haka ta juya tayi hanyar fita, sai kuma ta sake juyowa kana tace mata
“In zan baki shawara ki d’auka, gara ki hak’ura, saboda inda ace Abba zai so ki to da tuni an wuce wajen!! Amman har yanzu shiru..
Ga kuma sababbin obstacles a gabanki
Kin tonawa kanki asiri
kuma ga Maryam ta dawo rayuwar shi
sannan ga y’arsa da mukeda tabbacin ita zata had’a su!!
So kawai gara….”
K’arar jiniyar y’an sandan da ta jiyo ne ya sakata yin shiru!!
Take gabanta ya yanke ya fad’i, kallon Ummi take yi wadda itama jin jiniyar y’an sanda ya sakata sake rud’ewa!
Cikin karkarwar jiki tace
“Kamar jiniyar y’an sanda nake ji.”
Tun kafin ta rufe bakinta, Mom tace “Ba ‘kamar’ baneba tabbas jini y’ar y’an sanda ne.

Tuni ilahirin jikin Ummi ya sake rikicewa da karkarwa, ga uban gumi sai sake keto mata yake yi ta ko wacce k’ofar gashin jikinta, kana ganin ta ka san bata da gaskiya, fuskarta tayi jajir.

Da sauri ta k’araso kusa da Mom kafin tace
“Adama me kenan hakan yake nufi?
Kina tunanin Abb....”

“Tabbas Zainab mijinki ya cika tantirin d’an iska kuma mara mutunci!
Da y’an sanda zai had’a mu kenan ko me??”
Cewar Mom.

Ummi bata san lokacin da ta fashe da wani irin mahaukacin kuka ba!
Tsoronta d’aya a yanzu
kar Granpa yaji zancen nan.
“Innalillahi wa innailaihirraji un”
Ta shiga maimaitawa, sannan ta fara kallon d’akin tana neman hanyar guduwa, da sauri ta juya ta nufi k’ofar closet, da mugun gudu.

Daidai nan Abba ya shigo da y’an sanda mata guda biyu!
Mom ya nuna musu yace “suyi arresting d’inta”
A take kuwa suka yo kanta..
Babu abinda yafi d’agawa Mom hankali kamar ankwar da suka saka mata, bata san lokacin da idanunta suka kawo ruwa ba.

Waige waige Abba ya hau yi…Chan ya hango k’ofar closet a d’an bud’e kad’an hakan yasa ya isa wajen gadan gadan ya bud’e k’ofar ya shiga, ya fara dube dube!
Idanuwanshine suka sauk’a a
,wajen jallabiyoyin da aka rar rataye…gani yai wajen yana d’an motsi, hakan yasa ya k’urawa wajen ido, cikin sa’a kuwa ya hango k’afafun Ummi da suka sha jan lalle ta chan k’asa
Ai kuwa ya janyo gaba d’aya kayan wajen da sun kusan 30 ya zubar dasu a k’asa!
Tarr!! Ummi ta baiyyana a gabanshi sai uban gumi take yi, ga fuskar nan tayi jazir.

Dukkan k’arfin shi yasa ya fincikota ya fara janta, sai da ya kaita gaban y’an sandan tukunna ya dank’a musu ita, itama aka sa mata tata ankwar.
Bai bi takan magiya da ban hak’urin da take yi masa ba, haka nan ya basu umarnin tafiya da su.

Mom kwata kwata bata yi gardama ba, amman Ummi sai da aka nuna mata bindiga tukunna ta nutsu.
Suna fita shima ya mara musu baya.

A k’asa cikin motar suka samu Mammy itama da ankwar ta .

Gidan gaba d’aya ya cika da jiniyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login