Showing 105001 words to 108000 words out of 109746 words
cikin tashin hankali dole zan yi kuka.....”
Kasa cigaba ta yi da maganar dan haka ta yi jifa da wayar akan gadon ta durk’ushe a k’asa tana kuka.
Sakina na shirin yin magana Ummu da Mommy suka shigo.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e tanaji itama kamar ta fashe da kukan, a hankali ta d’an matso Maman sannan tace
“Wannan dalilin fa shiyasa nak’i gaya miki tun farko,
kin yi min alk’awarin ba zaki d’aga hankalinki ba yanzu menene haka?
Ki kwantar da hankalinki ni na san Mammy bata isa ta hana komai ba!
Dad ba zai barta ba.”
Cikin katseta Mama tace “Wallahi ko Dad ya barta ko bai barta ba babu maganar aure tsakanin Huda da Arshaad
Idan ita ta hak’ura to gobe ni zan hana!
Ta yaya kuke tunanin zan bar y’ata ta rayu da surukar da bata sonta?
Mommy na san mecece k’iyayyar surukai!
Kullum addua ta Allah ya had’a Huda da surukan da zasu k’aunaceta.
Taya za ki yi tunanin yanzu zan amince ta auri Arshaad??”
Cikin katseta Mommy tace
“Kar kiyi haka dan Allah,
kawai mu zuba ido amman kar kice zaki shiga tsakanin kaddara!
Idan kika yi hakan ai kun zama d’aya ke da Mammy kenan.”
Cikin katseta tace
“In zuba ido y’ata ta tafi inda ba a k’aunarta kome kike nufi?
In zuba ido rayuwar Huda ta lalace kamar yadda tawa ta lalace?”
Cikin rashin jin dad’i Mommy tace
“Haba Maryam,
rayuwarki bata lalace ba,
da ni da ke fa kusan mataki d’aya muka taka a rayuwar aure. Tabbas mun jigatu kuma mun sha wahala
amman a ko da yaushe idan na kalli Aslam wallahi ji nake gaba d’aya wahalar it’s worth it!
Dan Allah yayi mana kyauta.
Kuma dama a rayuwa dole akwai jarabta da kuma gwajin imani.
Ni dai shawarar da zan Baki itace
Dan Allah kar kiyi interfering
ki zuba ido ki barwa mazan komai, su sun san me za suyi.”
Cikin sharar kwallah Ummu tace
“hakane tabbas!
Mama dan Allah ki gwada yin hak’urin da kika saba
wata rana sai labari.”
Da sauri Baaba Talatu wadda bama su san ta biyo su ba
ta k’araso tace
“Taya zaku ce mata haka?
In dai uwar Yaro tace batayi to muma ba zamu kai jikarmu mai tsada inda ba’a k’aunarta ba wallahi!
Allah na tuba maza da yawa a gari..
Ga mai sunan kakan ta nan, d’an wajen Jamilu, idan Arshaad d’in zai kawo matsala ana iya d’aura musu aure gobe in sha Allah.
Na san ba zai tab’a cewa a’a ba, saboda daman ni na d’an so in fahimci take takenshi tun ba yau ba.”
Gyaran murya Shuwa wadda ta shigo yanzu tayi, dan haka duk suka juya suna kallonta.
A hankali ta k’araso cikin tafiyar ta wadda ke nuna tsufan da ya rufar mata.
Sai da tazo gaban Maryam
tukunna ta kama hannuwanta duka biyu ta fara magana
“Dan Allah dan annabi kar ki yi komai kar ki yi kuka kar ki d’agawa y’ar ki hankali.
Ki bar komai a hannun Ubangiji, tun kafin ki haifi Huda already an riga an gama rubuta k’addararta da komai nata.
Kar ki yi interfering wai dan kina tunanin zaki iya kub’utar da ita!
ki zuba ido ki yi mata addua
komai zai tafi bisa yanda Ubangiji ya riga ya tsara.
Bamu isa mu saka ko mu hana komai ba. Kin ji y’ar albarka?”
Ta k’arashe maganar tana mai sa hannu ta share mata hawayenta duka biyu.
Kuka Mama ta sake fashewa da shi ta fad’a jikin Shuwa suka rungume juna. Ita kanta Shuwan k’arfin hali ne kawai da dauriya suka hanata kukan
Ta rasa gane wachche iriyar k’addara ce
A rayuwar Maryam da Huda,
Astaghfirullah.....
Shigowar ta tare da matan da suka ruk’o ta ne ya sanya d’akin yin shiru. Har yanzu
fuskarta a rufe take amman kana gani ka san kuka take yi.
Sakina na ganinta taji kuka na shirin kufce mata dan haka da sauri ta fita a d’akin.
Suna zaunar da ita a bakin gado Mama ma ta
saki Shuwa ta fice.
Shuwan ce tayi k’arfin halin cewa
“Mommy da Ummu da kuma mata biyun da suka shigo da ita “Su je akwai motoci
a fara kwasar kayan Amarya ana kaiwa gidanta, dan ba zata yarda da ajjiye wannan dukiyar a gidanta ba, tunda kowa ya gani kawai su kai mata abunta gidanta.”
Murmushi Mommy tayi kafin tace
“Ni kam gida zan wuce..
Ina a matsayin uwar Ango ina ni ina ziryar gidansu
Ai nayi jere sai kuma in ta haihu nan da wata tara in sha Allah ni da in koma.”
Da sauri cikin raha ragowar matan suka ce
“In shaa Allah”
Ba a wani dad’e ba suka fito dukkansu a tare
Mommy ta d’anso ta sake ganin Mama amman kuma kawai sai ta rabu da ita, a cewarta ‘in ta d’an sauk’o zuwa anjima zata kira ta a waya’…..
A tare suka fito da Ummu,
su suka fara yin gaba da akwatuna ita kuma ta shiga mota ta nufi MT estate dan already drivern ya zo tun d’azu.
NASARAWA g r a.
Daddy da Dad na zaune sai zazzagawa Abba fad’a suke yi akan ‘ya mayar da Ummi tun kafin zance ya isa kunnen Granpa’ shi kuma ya tubure ya k’i!.
Suna a haka wayar Mama ta shigo…
Tsaf! Duk sun ji abubuwan da ta fad’a, dan wayar a high volume take kuma suna kurkusa da juna.
Yana gama wayar Dad yace
“Abba ka mayar da Ummi yanzunnan in dai na isa da kai.”
Haka shima Daddy
same thing ya fad’a mishi.
Ba yadda ya iya haka ya maida ita yana ji kamar yayi ta kurma uban ihu!.
Daganan Dad ya mik’e!
Kamar Daddy ya san meye a ranshi yayi saurin mik’ewa shima ya tsaya a gabanshi sannan yace
“Dan Allah kar ka yi haka.
Ka tsaya zan yiwa Adama magana, na san kafin zuwa gobe in sha Allah zata nutsu.”
Cikin fad’a fad’a Dad yace
“Ba zata nutsu ba!
Sam ba zata nutsu ba.
Da ace zata nutsu da tun tuni ta nutsu, ku bar ni kawai!!”
Ya fad’i haka yana k’ok’arin zagaye Daddy ya wuce.
Da sauri Daddy ya kuma tareshi sannan yace
“Ya abunda muka gama gyarawa yanzu! Da girman ka kake k’ok’arin aikatawa?”
Cikin tsananin b’acin rai Dad yace
“This is a different case..”
Cikin katseshi Daddy yace
“Ba wani different case anan duk abu d’aya ne!
Idan kayi mata haka ma ai ka ji haushi kenan, wato ta ci
riba ma kenan tunda har kaji haushi ka hukuntata, ai idan mata suna haukarsu ba a biye musu.
Tabbas na san dole ana buk’atar albarkar ta
amman ka b’ullo mata ta bayan fage.
Wani abun fa dole sai ka sauk’o, ka san yadda za ayi a d’aura auren shine ka ci riba!
Amman yanzu idan ka biyeta
ka saketa aka zo ta sake birkicewa
Wa gari ya waya?
Abunda ya kamata kayi shine
ka san ta inda zaka b’ullo mata
ka bawa iska ajiyar ta
ka nuna kamar bama ka san me take yi ba! Ka d’aure ta da jijiyoyin jikinta
Tana ji tana gani a d’aura auren gobe kamar bata existing a duniyar!
This is the best punishment da tayi deserving, amma
yanzu idan kayi haka( ka saketa) ai jagula komai za kayi,
kuma itace zata yi nasara at the end of the day tunda
Uwa ce.
Ka ga dai
ga Granpa a gefe wanda a yanzu haka jira kawai yake yi a tab’a shi!
Kai da kanka kace yayi mana warning a kansu duk mu ukun
I assure you wallahi idan kayi wani abun ba zai duba laifintaba zai bi takanka......”
Sannu a hankali Daddy ya samu ya shawo kan Dad da kyar! Ya hak’ura.
Shi dai Abba yana nan zaune bai ce musu uffan ba!
Dan ba fahimtarsu yake yi ba
har yanzu ba abunda yake yi mishi yawo a kunne sai kukan Maryam da tashin hankalin da ya jita a ciki.
Tabbbas sai ya gasawa Ummi aya a hannunta!
Hakan ba halinshi bane ba kuma bai kamata yayi mata hakaba a matsayin ta na mahaifiyar su Sudais
amman ba yanda ya iya…Dole ta san waye Abba! Ba ita kad’ai ba har su Mammmy, kasancewar su yayu a gareshi ba zai hanashi ya ja musu fasali ba.
A hankali ya mik’e ya yiwa su yaya rakiya, daga nan shima ya fita ya bar gidan.
Dad da Daddy direct asibitin da aka kwantar da Ummi suka je, an samu ta farfad’o sai dai har yanzu jikin nata ba kwari.
Likitan ne ya ke gaya musu “jininta ne ya hau sannan tana da buk’atar rest mai kyau.
Za su iya tafiya da ita gida idan suna ganin gidan will be more comfortable for her dan
ba abunda za suyi mata anan (asibitin) sai y’an drip da y’an allurai da maganin bp d’inta.
Hutun ta da kwanciyar hankalinta shine abun buk’ata a yanzu.”
Dad ne yayi signing discharge papers d’in daga nan suka nufi gida da ita.
Tunda aka kamo hanya
Ummi take ji inama mutum zai iya kashe kanshi babu zunubi, wallahi da ba abunda zai hanata commiting suicide a yau d’innan!
Atime d’in da ta farfad’o taso a ce mutuwa tayi..
Tun da ta taso tayi wayo ta san kanta
Soyayyar mutane biyu zxuwa uku ta sani
Abba Gramma sai Granpa!
Yanzu kuwa da ta kawo yanzu
ta san menene so
ta san tabbas muddin babu Abba a rayuwarta to mutuwa ce tayi saura! Shiyasa kawai ta koma kamar mutun mutumi
Ba abunda ya cika zuciyarta sai d’umbin dana sani
Ita inda Abba zai yarda wallahi ya auro Maryam uku!
Ya kawo ya had’a da ita su zama su hud’u, ta san za tayi kishi tabbas amma kuma zata hak’ura ta daure ta danne zuciyarta su zauna lafiya……
Tana cikin wannan tunanin taji su Dad suna danna horn!
D’ago kanta tayi ga mamakinta sai ta gansu a mansion d’in su Abba instead of estate,
addua ta fara yi a k’asan ranta ‘Allah yasa su Dad su saka Abba ya mayar da ita’.
Ba wanda yace mata komai.
Sai da suka shiga cikin parlourn suka zauna tukunna Dad yace mata
“Ummi sai kin yi hak’uri da Abba a yanzu.
Kar ki damu
In sha Allah zai sauk’o.
Kin ji.
Ki tashi kije d’akinki ki huta.
Ya gyara abunda ya b’ata d’azu.
Ki kwantar da hankalinki
Naki biyayyane, kin ji?”
A hankali take jan numfashi tana share hawayenta
tana jin wani farin ciki yana ratsa ta.
“Tam Dad mun gode”
Tace.
Sannan ta fara k’ok’arin mik’ewa dai dai nan
su Sudais da Shuraim da Aslam suka shigo!
Suna ganinta suka yi kanta da gudu suna Ihun murna
Shuraim harda y’ar kwallar shi
Itama sai da tayi kwallar murnar ganin gudan jininta.
Daga nan suka gaisa da Aslam ta wuce tayi sama ita da su Sudais.
Tun a hanya Sudais ya fara zuba surutu yana bata labarin event d’in, da kalar hotunan da suka yi da kuma yanda Ya Aslam ya zauna a kusa da Huda….
Gaisawa kawai Aslam yayi da su Dad daga nan suka fice gaba d’ayansu..
Basu yi mishi zancen event ba
shima daman hakan yake so..
Iya kar abunda suka sani shine Arshaad bai yi attending ba!.
Shi da Dad suka yi gida Daddy kuma yayi side d’inshi.
Sai dare Jalila ta farfad’o!
Ba kowa a d’akin sai ita kad’ai.
Jiri da ciwo a mararta
take ji ba na wasa ba!
Tana so ma ta mik’e ta d’an zauna amman ta kasa…
A hankali kwakwalwarta ta shiga tariyo mata abunda ya faru da ita d’azu.
Da sauri ta zabura ta dafa cikinta, dai dai nan nurse ta shigo.
Cikin kulawa ta hau gwada ta tana mai tambayarta “ina da Ina ne suke yi mata ciwo?”
A hankali Jalilan tace mata
“Mai ya sameni?
Marata tana yi min ciwo.”
Cikin kulawa nurse d’in tace
“I’m sorry ma’am, kin yi loosing baby d’inki ne”
“L lo Loosing, me?”
Cewar Jalila.
Ganin kamar bata fahimceta ba ya sanya tace
mata
“Kin yi miscarriage!
Cikin jikinki ya fita.”
Da mugun k’arfi ta mik’e ta zauna sai kuma ta fashe da kuka!
Dai dai nan Mom ta shigo.
Tana ganin tana kuka tayi sauri ta k’arasa ta fara bata hak’uri
sai kuma ta juya ta rufe nurse d’in da fad’a, tana cewa
“Ba ance jinin ta ya hau sosai kar a d’aga mata hankali ba?
Shine amma lokaci guda zaki zo ki fara zuba mata wannan mugun labarin?
Asibitin gwamnati ya kamata ki koma ba private ba!
Tunda baki iya tausar patient ba.
Ai inda kin bari da mu da kan mu za mu gaya mata idan mun koma gida....”
Hakanan dai Mom ta wanke nurse d’in tass!! Ta inda take shiga bata nan take fita ba
dag nan tayi signing discharge papers taja Jalila suka nufi mota driver ya jasu…..
Ita dai Jalila in banda kuka ba abunda take yi…
har ga Allah bata son cikin nan ba taso ta haihu amma
kuma yanzu da cikin ya fita ta san tabbas ba abunda zai shiga tsakaninta da komawa gandun albasa!!
Sannan ta daina samun kud’i daga Mom da Auwal kenan har abada!
Amman kuma yadda Mom take lallab’ata sai ta d’an ji zuciyarta ta d’an yi sauk’i!
Maybe tausayinta take ji amma duk da haka ta san ba zai wuce na sati ba zata tarkatata!
Dan haka a take ta yanke shawarar nemawa kanta mafita..
Zata lallab’a Mom ta bata hak’urin abubuwan da ta dinga yi mata
Idan ta kama ma sai tayi k’aryar aljanune da ita tace mata su ne suke sakata yiwa mutane rashin kunya.
Ta samu dai Mom d’in ta ara mata ko da sati uku ne
daga nan ita kuma da ita had’a y’an kud’ad’en hannunta ta sake turawa Umma
a san abunyi ta auri Arshaad ko ta halin yaya ne da wurwuri cikin gaggawa!
Itafa wallahi yadda ta d’and’ana daular nan
to kuwa batajin zata iya minti uku a cikin gidan Baba!….
Tanata sak’e sak’e a ranta a haka suka iso gida!
Sai wani nonnok’ewa take yi gudun abunda Mom zata yi mata, amman suna shiga sai taji Mom d’in tace mata “ta tafi d’akinta ta huta
Coook zata kawo mata abinci yanzu.”
A hankali tace
“Na gode Mom”
Wani kalan murmushi Mom d’in tayi wanda Jalilan ta kasa ganewa.’Daganan Mom d’in ta juya ta nufi hanyar kitchen a ranta tace
“Yarinya kenan!
Sarai na san zaki iya yi mana bori, kice ba zaki tafi ba ki tada mana hankali
Kuma ko yanzu na san idan akai test a jikinki positive za a gani..
Ki jira nan da kwana uku
In sha Allah za ki san wacece Adama.”
GANDUN ALBASA
Tun da garin Allah ya waye Huda take kuka
Idan zaka titsiyeta ka tambayeta ba zata tab’a iya gaya maka menene tak’amemen abinda ya sanya ta kukan ba!
Ita dai ta san bata da nutsuwa
sannan a mugun tsorace take
amman tabbas ba wai shariyar Arshaad kad’ai ne dalilin tashin hankalinta ba.
Sakina da Khadija sun yi lallashin sun yi har sun gaji sun rabu da ita.
Hankalinta bai sake tashi ba
sai da k’awayenta suka zo
sannan mai makeup itama ta zo ta fara shiryata!
Tayi alk’awarin ba zata sake kiran Arshaad ba amman haka ta daure ta kirashi
wannan karan kam a kashe ma taji wayar tashi gaba d’aya
dan haka hankalinta ya sake tashi!
Ba abunda yafi d’aga mata hankali irin kar azo d’aurin aure yace ya fasa!
Ita gara ya fito ya fad’a mata gaskiya
akan yayi mata hakan...
Nasarawa gra.
A b’angaren Arshaad kuwa jiya ya gama shirya plan d’inshi
amman ga mamakinshi kamar wani ya gayawa Mammy bayan Magrib nayi ta shigo d’akin nashi ta kafa ta tsare!
K’arshema a d’akin a kan couch ta kwana tsabar bala’i.
Tun jiyan da ta shigo har yanzu k’arfe 10 bata fita ba!
Ko wanka ko brush bata yi ba, har gara ma shi yanata watsa ruwa saboda zazzab’in da yake jikinshi..
Yana lura da ita ko mik’ewa yayi ya shiga shiga toilet zai yi wanka ko alwalla sai taje bakin k’ofar ta lab’e mishi har sai ya fito sai kace wani wanda akace mata zai b’ace!
Dagashi har ita ba wanda ya samu bacci jiya
Idan ka gansu duk a gigice.
Ko da Aaima ta kawo musu breakfast ma ba wanda ya tab’a har yanzunnan
Tun jiyan da ta shigo har yanzu ba wanda ya cewa wani uffan a tsakaninsu.
Amman duk wani motsinshi idanunta na akanshi.
Ba abunda yafi d’aga mishi hankali kuma ya bashi mamaki irin yanda ta kasa tashi ko sallah tayi
Yanzu haka yana lura da yadda ta kasa zama mai kyau sai faman mutsu mutsu take yi
wanda ya tabbatar fitsari take ji amman gudun kar ta shiga ya gudu ta gwammace ta zauna a haka!.
Suna a haka Dad ya shigo cikin d’akin.
Yayi mamamkin ganinta a zaune amman sai ya d’auke kai kawai ya maida hankalinshi ga Arshaad, ransa a d’an b’ace yace
“Ka san fa k’arfe 11:30pm ne d’aurin auren, uban me kake yi a zaune a haka?”
A hankali yace
“Ina kwana Dad”
“Lafiya” kawai yace masa, daga nan ya nemi waje ya zauna kafin yace
“Mik’e maza, yanzun nan Aslam zai kawo maka kayanka”
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yanayin k’asa k’asa yana kallon Mammy wadda ta d’auke kai tana kallon gefe.
Mik’ewa yayi jikinshi ba kwari ya fad’a band’aki!
Ya kai kusan 20 minutes tukunna ya fito sanye da bathrobe a d’akin ya tarar da Aslam sanye cikin sky blue d’in rantsattsiyar shadda aikin gaban rigar white da d’an ratsin blue ya murza farar hula mai asalin kyau da tsada sai kyalli take yi da farin takalmi
hatta agogon hannunshi white ne. Yana rik’e da babbar rigarshi a hannu wadda take a ninke, k’amshinsa gaba d’aya ya cika ilahirin d’akin….
Suna had’a ido
ya sakar mishi murmushi
a hankali yace
“Ango”
Murmushi shima Arshaad d’in yayi sannan ya wuce jikin wardrobe d’inshi ya na mamakin ta yanda zai shirya a gaban waennnan body guards d’in!
Inner wears d’inshi ya kwasa
ya d’auki jakar kayan da yaga an ajjiye akan gadon ya juya ya wuce toilet.
Bai yi minti biyar cikakku ba ya fito!
Murmushi Dad yayi yana kallon shi yana mai jin wani sanyi a ranshi!
Kana ganinshi kaga Ango..
A hankali jikinshi a mugun sanyaye ya k’arasa gaban mirror ya d’an shafa mai sama sama a hannu da fuskar shi sannan da k’afa, ya fesa perfumes ya d’auko takalmin da ya fito da shi a jakar kayan nashi ya sanya…
Farar shadda ce k’all! Mai babbar riga sai bak’in takalmi hula da agogo..
Yana gyara d’aurin agogon suka ji knocking
Aslam ne ya juya ya d’an bud’e k’ofar dake a kusanta yake.
Da mamaki yake kallon Abba da Daddy
da Auwal a bayansu.
Dad Abba da Daddy duk ankon shadda ruwan goro light suka