Showing 90001 words to 93000 words out of 109746 words

Chapter 31 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2949

dake side d’in Auwal ya nufa.
Yana shiga ya ganshi yashe a k’asa da jikakkun kaya.
Da sauri ya k’arasa wajen ya durk’usa ya hau jijjigashi yana kiran sunanshi….

Dai dai nan Aaima ta shigo,
duk da fushin da take yi dashi hakan bai hanata fashewa da kuka ba da ganin halin da yayan nata ke ciki.
Da sauri Auwal ya juya gareta yace
“Yi maza Aaima d’ebo ruwa a toilet yi sauri plss..”
Ya fad’a cikin gigita da kid’ima.

Da gudu ta nufi toilet d’in ta d’ebo ruwan ta fito ta na zuwa Auwal ya amsa ya hau yayyafa mishi….

Sai da suka fidda ran ma zai farfad’o tukunna yayi wata wawiyar ajiyar zuciya wadda ta taho mishi tare da tari!
Auwal ne ya d’an d’ago shi kad’an yahau bubbuga mishi baya yana jera mishi sannu.
Da kyar ya samu tarin ya tsaya
ya shiga jejjera ajiyar zuciya....

Sai da Auwal ya kamashi ya kaishi kan gadonshi, tukun ya zaro waya ya fara k’ok’arin kiran family doctor d’insu….
Kamar Arshaad d’in ya san me yake shirin yi, yace nasa
“Kar ka kira kowa Auwal,
i’m fine.
Please.”
Kallonshi Auwal d’in yayi kafin shima yace
“Dan Allah kar ka gwada yin wannan taurin kan!
Ka bari a kirashi ya duba ka kawai.”
Cikin d’an fushi Arshaad yace
“Auwal zamewa nayi na fad’i na buga kaina!
Yanzu kuma na farfad’o…
Ka gaya min in akwai abinda Doc zai yimin idan ya zo d’in
bayan wanda kukai min.”

D’an k’uraa mishi ido Auwal d’in yayi kawai ya tsaya yana kallonshi.

A hankali Arshaad d’in ya koma ya jinjina a jikin gadon
sannan yace
“sorry”

Ajiyar zuciya Auwal ya sauk’e
kafin yace
“Are you sure that’s all?”

Jinjina kai kawai Arshaad d’in yayi.

Auwal bai wani gamsu da maganan shi ba
but yaga kamar he wants to be alone shiyasa yace
“Shikenan,
Allah ya kare gaba, ka kira su Hudan hankalinsu ya tashi sosai.
And dan Allah ka sauya kayan jikin nan naka, sai da safe.”

“Ok”
shine abunda Arshaad yace sannan ya k’ara da cewa
“Thanks a lot”

Murmushi yayi kawai yace mishi
“Good night”
Daganan ya nufi hanyar fita.

Kallonshi (Arshaad) itama Aaima tayi tace
“Ka kira wayana if you need anything”

Jinjina mata kai kawai yayi sannan ya fara k’ok’arin mik’ewa dan chanja kayan jikinshi.

Ganin haka yasa Aaiman yi mishi sai da safe itama ta juya tabi bayan Auwal wanda
har ya kusan ficewa…
Sai da ya kusan isa k’ofar fita ta main parlour tukun ta samu ta cin mishi ta wuce ta isa bakin k’ofar ta sa hannu ta bud’e.
Ba tare da ya kalletaba dan shi har ga Allah ta fara k’ular dashi
Ya sa kai zai fice.

Daurewa tayi tace
“Mun gode sai da safe”

“Allah ya kaimu” yace
daga nan ya fice.

Ta jima a parlourn bayan ya fita..
Daga k’arshe ta nufi side d’in Arshaad har bedroom ta lek’a ganin yayi bacci yasa ta fito ta nufi sama ta koma d’aki.
Da kyar ta samu bacci ya d’auketa.


Shi kuwa Arshaad yanda yaga rana haka ya ga dare!
Yana jinta lokacin da ta shigo,
baya san ganin kowa shiyasa yayi baccin k’arya, ko
Hudan text kawai ya iya tura mata cewar ‘he’s okay’.

Kafin safiya ya gama deciding yanda zai yi da abunda zai cewa Mammy amman still yana d’an d’arr! Ga fargaba
ga tunani barkatai
shiyasa zazzab’i yace salama alaikom...........




Zazzab’in da ya rufar masa ne yaasa da kyar ya iya mik’ewa yayi sallah a daddafe!
Kafin 7 kuwa zazzab’in yayi masa rufdugu….

Ganin yana shirin mutuwa ya sanya shi kiran family Doctor d’in da baya so, dole! Ya kira fad’amshi yana zazzab’i mai k’arfi.

Ba a rufe 30 minutes ba Doctor d’in ya iso..

Allurai yayi mishi bayan ya duddubashi dan ya san Arshaad ya tsani magani,
daga nan ya jona mishi drip yayi mishi sallama…

Sai wajajen 11 drip d’in ya k’are
da kansa ya zare ya danne,
bayan some minutes ya mik’e ya fad’a wanka.
Yaji dad’in jikinshi ba kad’an ba kuwa.
Yana fitowa ya d’an shafa mai da turaruka ya zura wata cream jallabiya mai gajeran hannu…
A hankali ya k’arasa bakin gadon ya d’au wayarshi ya fara kiran Hudan dan tun da safe yaga message d’inta.

Bata wani dad’e tana ringin ba ta d’auka!
Bayan sun gaisa ya tabbatar mata da ‘he’s okay daman kawai dan zazzab’i ne’.
Tace mishi
“Anjima around 1 ana buk’atar shi za suyi traditional event d’insu na yaren Shuwa kuma
dole sai yana wajen!
Inda hali ya turo driver kafin nan, yazo ya karb’a mishi kayan tradition d’in da aka tanada domin shi (wanda zai saka a event d’in)
Kayan ba su iso ba sai d’azu shiyasa bata bashi da wuri ba.”

Da “to” ya amsa ta
daga nan suka hau hirarsu
dan yaga kamar hankalinta still a d’an tashe yake.

Sun jima suna hira dan sun fi 30 minutes kafin suyi sallama.

A hankali yayi shiruuu, yana y’an tunane tunane..
Chaaan! Ya turawa driver d’in da zai karb’o mishi kayan nashi message daga nan
ya mik’e yayi kalmar shahada ya fita ya nufi sama wajen Mammy.


A stairs suka had’u da ita tana k’ok’arin sauk’owa!
Kamar bata ganshiba haka tazo ta wuceshi.

Hannunta yayi saurin rik’ewa ya juyo a hankali yace “Haba Mammy..
Ki saurareni please mana.”
Ya fad’i hakan kamar mai shirim fashewa da kuka.
Ba tare da ta kalle shi ba tace
“Ka bari idan Allah ya kaimu gobe naga kayi abunda nace sai in saurareka”

“Meye abunda kike so yayi miki goben??”
Suka ji muryar Dad a bayan su!.

Da sauri Arshaad ya juya yana kallonshi gabanshi na tsananta fad’uwa!

Ba tare data juyo ko ta damu da Dad d’inba
tace
“Ai gaka ga shi nan!
Kana iya tambayarshi.”
Tana gama fad’in haka ta nufi k’asa wajen bakinsa da take expecting dan sune ma suka ce mata sun kusan shigowa
ba daban su ba da babu abinda zai sauk’o da ita k’asan!
Tana buk’atar time ita kad’ai,
dan ita kanta bata san daliliba amman komai ya kunce mata..


Kame kame Arshaad ya fara bayan ta sauk’a…
Babu yadda Dad bai yi da shi ba amman yace mishi “ba komai! Kawai sun d’an samu issue ne shi da ita lokacin tana cell shine yake so suyi settling”.

Sam Dad bai yarda da shi ba
dan kwata kwata babu kamanceceniya a cikin maganar shi da tata!.
Fahimtar da Dad yayi Arshaad d’in ba zai gaya mishi komai ba ne yasa kawai yace “to, shikenan ka samu ku shirya d’in kafin ka bar gidan nan.”
Yana gama fad’in haka ya wuce shi shima yayi k’asan.


Sai a sannan Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya
He needs to talk to Mammy!
Idan tak’i ta lallashi tabbas zai b’ullo mata ta hanyar da bata zata ba! Akwai abubuwa da dama waenda ya sani amma yayi shiru kuma ta san ya sani but it’s like kamar ta manta, so he has to remind her!.

Sannan ya san ta inda zai b’ullo mata ta yarda
dan yaga alamun ba lalle ta yarda cikin sauk’i ba gashi babu enough time!….

Ya jima a wajen
kafin ya juya ya wuce sama da niyyar d’an bata time Kafin ya sake ganinta!
Yana da full hope d’in zai yi nasara bi izinillahi.



Mammy na sauk’a k’asan ta fara shan mamaki..
Kulolin abinci kala kala da su drinks ake ta shigowa da su!
Bata ida fita daga wannan mamakin ba taga friends d’inta da sisters d’inta har da Mahaifiyarta suna ta shigowa
har da ankon super d’in su da suka yi a jikinsu….
Da sauri ta k’arasa kusa da yayarta ta kamota tace
“Me kenan? Wats the big idea?”

Murmushi Haj Binta tayi kafin tace “Wunin d’an mu za muyi mana!
Anjima kad’an kuma muje muga Amarya naji Dad yace za suyi traditional day d’insu suma daga nan mu bata kyaututtuka
Naga ke baki son zancen shiyasa ma na zagayeki na kira Dad.
Anko kuwa ni na fitar kuma gashi kowa yayi, ni da su Hajiya ( Mahaifiyar su) tun lokacin da aka sa rana dama muke ta shirye shiryen mu.

Matsowa Mahaifiyar tasu tayi kusa da su ( ita da sister d’in tata ) kafin itama ta fara magana
“Ki nutsu ki bari ayi komai a gama daga nan sai a san abun yi!
Ni na hanasu su fad’a miki komai akan lamarin auren, gudun samun matsala dan na san halinki.
In dai ni na haifeki to inaso ki kwantar da hankalinki kiyi hak’uri, ni kaina ba wai son had’in nake yi ba!
Amman ki bar ni da su kawai
ai in sun san wata basu san wata ba!
Kuma kar ki bari kowa ya fahimci halin da ake ciki, ki nuna kina so inda hali ma ki shirya muje ki bawa ita Yarinyar kyauta da hannunki a gaban kowa…”
Ganin friends d’in Mammyn sun tunkarosu ne yasa Mahaifiyar tata yin shiru ta fara yak’e..
Suna zuwa kuwa suka hau tayata murna kowa na farin ciki tare da yi mata ya jiki (dan ce musu aka yi ita da su Mom duk sun yi inhealing dangerous abu shine aka fitar da su k’asar waje suka yi jinya sai jiya suka dawo).

Haka nan suka k’arasa tsakar falon aka zazzauna…

Masu decoration suka shigo suka hau d’an gyaggyara parlourn
Yayar tata ce tace “bara taje ta ajjiye abu daga nan ta cewa Arshaad ya shirya, su d’anyi hotuna a nan kafin a tafi event d’in su Hudan..”
Sama ta nufa da niyyar ajjiye abu tukun ta je ta kira Arshaad d’in
Tana shirin hawa suka had’u da Dad yana sauk’owa…
Cikin mutunta juna da barkwanci suka gaisa
daga nan yace mata
“Ta kirawo masa Mammy, su sameshi su biyu a side d’in Arshaad.”


Mammy na zaune a cikin friends da y’an uwanta
amman kwata kwata hankalinta baya a garesu!
K’ok’ari take taga ta tirsasa zuciyarta ta aminta da abinda Mamanta tace mata yanzun, amman furr ta kasa...
A wannan yanayin sister d’in nata tazo ta rad’a mata sak’on Dad a kunne daga nan ta wuce ta nufi parlourn Arshaad.
Da kyar Mammy ta iya mik’ewa tabi bayan ta..
Sauk’owar Arshaad kenan yaga sun nufi side d’inshi,
A ranshi yace “perfect”
Duk fa bai san me za suyi anan d’in ba.

K’arasawa yayi ya gaggaisa da bak’in, kakarshi tana ta tsokanarshi, daga nan ya wuce shima.
A parlourn suka tarar da Dad yanata faman kai kawo..
Suna shigowa ba tare da b’ata lokaci ba yace
“Binta, ga y’ar uwarki nan, ki tayani tambayarta..
Akwai abunda suke b’oye min ita da Arshaad wanda ban sani ba!
Na san halinta da sanabe kala kala dan haka idan akwai wani abun gara tun farko ta fito ta fad’a kar taje ta yiwa mutane shirme!..”

Hajiya Binta tana shirin yin magana Mammy tayi caraf ta amshe ta fara magana
“Ai kai da kanka yanzu me kace?
Muna b’oye maka, ko?
To kuwa ai kaga tunda muka b’oye maka d’in to bai shafeka ba kenan!
Infact babu abunda ma ya shafeka na daga rayuwar ni da y’ay’ana.
Da kace kana kirana i thought welcoming d’ina zaka yi”
Murmushin takaici tayi kafin ta juya ga Hajiya Binta tace mata
“Ko kin san tun jiya dana dawo ban ga k’eyar bawan Allah n nan a kusa da ni ba balle ya tambayeni lafiyata ko ya nake?
Ai ko ni kad’ai na aikata laifin b’oye y’ar gold d’inku wallahi ban chanchanci haka daga gareka ba ko dan darajar Arshaad da Aaima!”
Ta fad’i haka tana takawa inda yake, daga nan taci gaba
“Sannan yanzu ka wani kwaso k’afa kazo kana wani waye waye…
Kai har kana da kunyar yi min wannan maganar?
Bayan abunda ka yi?
To bari kaji bai shafe ka ba!
Ka zuba ido zaka gani tare da kowa idan Allah ya kaimu gobe.”
Tana gama fad’in haka ta juya ta nufi hanyar fita.


“Idan kika taka k’afarki kika bar min parlourn nan ba tare da kin fad’a min abunda nake son ji ba to
a bakin auran ki.”

Ba mammy ba hatta Hajiya Binta sai da gabanta ya yanke ya fad’i.

Juyowa tayi tana kallonshi da idanuwanta da suka fara chanja launi, cikin tsananin takaici tace
“Namiji k’anin ajali!
Ai Aisha ta dawo
dole ka yi min haka.
To bari kaji in gaya maka wallah ko ka sakeni babu
inda zanje sai dai in kai ka fita ka bar mana gidan nan ni da y’ay’ana!”

Cikin katseta yace
“Rukayya kar ki yi underestimating d’ina!
Dan wallahi zan yi miki abunda ko me sunana aka kira sai kin ji kin tsani wanda ya kira sunan!
Baki san a ya’ya nake ganin ki ba a halin yanzu, kar ki kaini bango!
Wallahi ba dan darajar Aaiima da Arshaad ba da tuni na dad’e da sauya miki rayuwa..
Bana son dogon magana dan bana jin iya zama mai tsawo a inuwa d’aya da ke!
Ki fad’amin abunda nake son ji in fita.”
Ya fad’i haka cikin kakkausar muryar da take baiyyana tsanannin b’acin ran da yake ciki.

Haj Binta ce tace
“Kayi hak’uri dan Allah,
Mammy ke kuma ba a haka!
Ki bari wannan matsalarku ce daga baya za ku yi settling ke da shi
Yanzu ki fad’i abunda yake son ji tunda ya nuna yana da buk’atar hakan”

Cikin tsananin b’acin rai Mammy tace
“Ba zan fad’a ba!
Wallahi ba zan fad’a ba”
Sannan ta juya gareshi tace
“In kana buk’atar ji Yahaya ka zo ka shak’eni sai in fad’i maka ta k’arfin tsiya!!
Da kake wani maganar sauya mini rayuwa, na nawa kuma?
Bayan azabtar da mu d’in da ku kayi me ye kuma kuke tunanin za ku yi kuma wanda yafi wannan??.
Ba dai rashin sanin ya kamata ka d’aurawa kanka ba, rana d’aya? To wallahi dede nake da k’ugunka!
Maganace nace ba zan fad’a ba
In kuma ka matsu to kazo ka shak’eni In fad’eta.”

Cikin tsannnin fushi ya tunkarota kamar wanda zai rufe ta da duka!
Dasauri Arshaad wanda shigowar shi kenan yanzun ya shiga gaban Mammy ya tsaya Hajiya Binta kuma taci gaba ta k’ok’arin hana Dad d’in k’arasawa inda Mammyn take!

Dukkannin k’arfin da Allah yayi mata tayi amfani dashi wajen ingije Arshaad d’in sannan kafin yayi nasarar tsaidata ta tafi gaban Dad ta tsaya! Tana mai jin wani tuk’uk’in bak’in ciki yana taso mata,
babu abunda idan ta tuna yake k’ona mata rai irin yanda taga Daddy yana ziryar zuwa wajen Adama last zuwanshi da yayi har kusan kuka taga yayi daga nan ma yace ‘ba zai iya sake ganinta a haka ba’
Tun daga ranar kuwa idan bai kirata sau d’aya ba tou zai kira sau biyu!
Amman ita ko lek’enta ko waya Dad bai tab’a yi yace a bata ba, ita tana chan tana tunanin sa ashe shi yana nan Aisha ta d’auke masa hankali!
Kalli fa sarai ya san ta dawo amman ko lek’enta bai yi ba kuma suna cikin gida d’aya, sai yanzu dan rashin kunya da tsaurin ido ya buk’aci ganinta
kuma ko alamar tambayarta ya take bai yi ba instead
ya hau wani tsattsare ido yana hucin banza..
Waennan takaicin ne suka sanya ta kasa cewa komai kawai ta zube a wajen ta fashe da wani mugun kukan bak’in ciki.

Cikin son kawar da lamarin Arshaad yace “Dad, dan Allah ka bar maganar nan, na fad’a maka ba komai fa”.

Banza Dad yayi da shi kawai ya juya ya fice! Yaso ace Mammy tayi mishi wani shirmen yau wallahi da sai ya yi mata abunda bata tab’a tsammani ba! Ya san at least zai samu peace of mind at last.

Yana fita Mammy ta mik’e!
Tunda take a rayuwar ta bata tab’a jin kishi da takaici da tashin hankali da bak’in ciki irin na yau ba!
Ta rasa dalili amma ko y’ar kissar da ta saba yiwa y’ay’an nata da Dad d’in ta kasa kuma bata jin zata iya, babu abunda take so kuma take buri irin taga ta b’atawa Dad rai ko ta samu zuciyarta ta d’anyi sanyi.
Tayi imani yanzu haka wajen Aisha zai tafi yaje ya ganta yad’an samu nutsuwa hankalinshi ya d’an kwanta alhalin ita kuma gashi ya k’unsa mata bak’in cikin da bata jin zata iya mantawa da shi har abada!
Taya zai yi mata haka?
Taya zai banzantar da ita har haka saboda Allah kamar
wata dabba?
‘Inaaa!! Ba zai yiu ba Wallahi’
Shine abunda ta fad’a ta gyara tsayuwarta tana k’ok’arin yin hanyar waje…..

Da sauri Hajiya Binta ta tareta tace
“Meye haka ne wai Mammy?
Ba a isa a fad’a miki kiji bane?
Ina za ki ji yanzun?”

Cikin kukan Mammy tace
“Kina ganin fa abubuwan da Yahaya yake yi mini
Ya gama b’ata min rai ya fice ya tafi wajen uwar gidan shi ya bar ni ni anan zuciyata ta kama da wuta kenan ko me?
Ki cikani kawai, wallahi bai isa yayi farin ciki ba, ba inda zai je yau, kullle k’ofar gidan nan zan yi sai dai mu kashe juna ni da shi a cikin gidan nan!”

Da sauri Arshaad ya matso kusa da su ya rik’eta, wani
tsananin takaicin sa take ji hakan yasa ta juyo da sauri ta kifa masa Mari! Sai kuma ta fashe da kuka, cikin kukan
tace
“Ai kaima baka kishina
Arshaad, a tunanina ko Hudan y’ar gwal ce wallahi ba za ka so auren ta b.
Taya za ka had’ani da ita mu zama surukai!?
Ko kasan cin mutuncin nan da aka yi min shine abu mafi muni a rayuwata?.
Na fad’a na k’ara fad’a yanzu ma zan maimaita maka
‘Wallahi idan ka aureta sai na tsine maka!’.”

Arshaad bai san lokacin da ya tsugunna a wajen ba ya fashe da wani mugun kuka.

Cikin b’acin rai da kafiya Mammy tace
“Kuma ko event d’in yau da suka gaiyyaceka ban yarda ka je ba!
In kaje kuma wallahi Allah ya isa ban yafe ba!
Zan ga wa zaka zab’a tsakanin ni da ita.”

Da sauri ya mik’e yace
“Haba Mammy ya kike so inyi ne?
Ki tsaya ki saurareni kuma kin k’i..
Dad ne ya nema min aurenta Abba kuma ya bani,
idan nayi miki biyayya
su kuma bijire musu kike so in yi?”

Da sauri cikin katsesu Hajiya Binta tace
“Rukayya ban tab’a tunanin baki da hankali ba sai yau wallahi!
Ni, na fad’a miki!
Mahaifiyarmu, itama ta fad’a miki! Amma ba za ki ji ba?
Waye a cikinmu zai fad’a miki abunda zai cutar da ke?
Munce kiyi hak’uri ko?
Waennan irin y’an iskan aljanu masu shegan taurin kai kika kwaso a cell d’in ne wai?”

In banda gunjin kuka babu abunda Mammy take yi.

Cikin son su kad’aita iyaka su biyu dan ta samu damar lallashinta da fahimtar da ita Hajiya Binta ta cewa Arshaad “wuce ka tafi ka shirya ku je ku yi event d’in, idan ka dawo sai mu k’arasa”

Ai kuwa Mammy na jin haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login