Showing 3001 words to 6000 words out of 109746 words

Chapter 2 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2959

bayan ta gama karantawa sannan ta cillawa Aslam a dede setin fuskar shi.

Da sauri jin takardar tana shirin sauk’a k’asa yasa hannu ya cafe ta sannan ya d’ago ta ya fara karantawa…

Mama bata jira ya k’arasa karantawan ba ta fara magana
“Aslam za ka iya kaini kotu! amman ka sani ni ba zan biyeka inyi shariah da kai ba, nasan kun fi k’arfi na ta ko wacce siga, sai dai kuma ni kotun Allah zan kaiku! Nan ce k’arshe kuma shine zai bi mini hakkina!
Dan ba zan yarda ku dake ni kuma ku hanani kuka ba!”
Tana gama fad’in haka kuka ya kufce mata ba tare da ta shirya ba.

Da mamaki Abba wanda ya k’araso ya karb’i takardar ya hau karantawa yake sake maimaitawa….
Shiruuuu, ya d’an yi sai kuma kawai ya ninke takardar ya sa a aljihun gaban rigarshi!
Dan tabbas yau za a yita ta k’are a estate d’insu!! Ba zai yiu ace yana rubuta takardun da bai san lokacin da ya rubuta su ba!
A daa yana kokwanto yanzu kam ya samu clue.

Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya k’araso gaban Mama yace
“Maryam! na rantse da girman Allah ba nine na rubuta wannan takardar ba! Ban san da zamanta ba kuma ban san dalilinta da ranar data iso gareki ba!”

Cikin kuka Mama tace “naji Abba baka san da takardar nan ba ita kuma Hudan laifin me tayi maka!? Ko sau d’aya fa baka tab’a lek’ota ba!
Cinta shanta suturarta duk baka sansu ba!
Idan ni nayi maka laifi ka datse igiyoyin aurenka a kaina ita kuma laifin me tayi maka daka kasa koda
lek’o ta ne????”

Kamar Abba zai yi kuka da ihu yace
“Maryam, zabi aka bani ko in fita harkar ki for ever ko kuma ku k’are rayuwanku a jail ke da family d’inki har abada!!!Daman kuma an riga anyi agreement dani ke kin sani an yi agreement akan ‘duk ranar da wani naki ko ke kukaje inda yake dole akwai consequences !’
Duk da haka ban hak’ura ba
Inata k’ok’ari da
adduar in samu a gyara abun
sai kawai naji d’aurin aurenki bagatatan!! Ya kikeso in yi??”

“Nifa duk ba wannan nake son ji ba, tsakani na da kai it’s over! Ko ma menene ya faru ya riga ya wuce!
Laifi yanzu da nake magana a kai ba ni ka yiwa ba! Y’ar ka ka yiwa, kuma ko ita ta yafe maka ni ba zan yafe in yarda ba!! Dan haka kawai ka juya ka tafi dan ban san me ka zo yi anan ba!.”

Aslam wanda yake ji kamar zuciyarshi zata tarwatse ne yace
“Wai sau nawa zai yi miki bayanin ‘bai san kin haihu ba’
Hatta shi kanshi Granpa d’in bai san kin haihu ba!!
Kuma da kike ta cewa bai zo inda kike ba, was ita not you da kika yi ta aika mishi da threats kala kala ba?”

Shigowar Doc ce ta katsewa Arshaad maganar da yake shirin yiwa Aslam akan attitude d’inshi towards Mama!! He’s is not like this kwata kwata, he wonders why yake yiwa Maman haka.

Ba tare da Likitan yace “k’ala ba ya juya ya fita, ko minti d’aya bai yi ba ya dawo da takardar sallama ya bawa Aslam sannan yace
“Kuje gida kuyi solving issue d’inku, dan har ga Allah kun hana marasa lafiya sukuni!! Ba sai kun rufe file ba, zaku iya tafiya kawai…”
Yana gama fad’an haka ya kama hannun Mama ya cire mata cannular yana cewa “kuna gama cases d’inku ki tafi asibiti, dan ina jin tsoron jikin nan naki a haka!.”

Yana fita Mama wadda daman abunda takeso kenan, ta yafa mayafinta, sannan ta cewa Huda “wuce mu tafi!”
……….
Kasa sauk’e kafarta data d’aga da niyyar tafiya tayi jin Abba yana cewa “Babu inda Huda zata bii ki!!”

Da mamaki ta juyo tana kallon Abba kafin tace
“Ban gane ba!”

“Babu inda zata je, tare da ke!!”
Abban ya fad’a yana mai k’arasowa inda take sannan ya zuba mata idanuwanshi da ta kasa jurewa kalla tayi saurin yin k’asa da kanta.

Cikin tattaro dukkan ragowar k’arfin jiki kuzari da jarumtar ta, ta zagayeshi taje inda Hudan take ta fara k’ok’arin kama hannunta amman kafin tayi hakan tuni Aslam ya juyo da sauri ya rigata, sannan ya tura Hudan bayansa, shi ya zamana yana a gaban Maman!!
Da kyar ya iya bud’e idanuwanshi da ya runtse!! Tun lokacin da ya rik’e hannun Hudan ya zubasu a kan Mama!
Cikin wata iriyar kasala data dirar masa lokaci guda yace
“You have to pass through me first!”

Arshaad kam zuwa yanzu ya zo wuya!!! Dan haka cikin fushi ya kalli Aslam d’in yace mishi
“Let her go!!”

“No”
Yace ba tare da ya kalleshi ba!
Sannan ya dakawa Hudan wadda take ta k’ok’arin kwace hannunta tana kuka tsawa
“Ki nutsu!!”.

Wani irin irin kuka Mama ta fashe da shi a take ta durk’ushe a wajen abin tausayi.

Abba ne ya umarci Aslam da
“Ya kai Hudan mota dan in dai yaci gaba da ganin Maryam a haka tou za a samu matsala!”

Da sauri Arshaad yace “babu fa inda zata je ba tare da Mahaifiyarta ba!!! Haba Abba! Ka san kuwa shak’uwar dake a tsakanin y’a da uwa?? Ka san abubuwan da suka yi going through tare, lokaci d’aya kawai kazo kace zaka d’auketa haka nan?
Why are you trying to be selfish???”

Kallonshi Abban yayi da idanunsa da suka fara rinewa….
He‘s tired so tired of everything!! A yanzu yadda yake jin zuciyar shi tabbas idan ya tsaya kula Arshaad to zai iya yi mishi illa!!
So yake yi kawai ya isa gida tare da Huda ya fuskanci kowa da komai!
Masu laifi kuma ya hukuntasu dan bashi da tantamar cewa akwai waenda suka san da zaman Huda a dunyia a cikin estate d’in su…
Apart from that ma inda ace ya san yanada y’a tun farko to da ko kwana d’aya ba zai barta tayi a gidan Usman ba which definitely ya san anan take da zama…
Tabbas ya san bai kyautawa Maryam ba, but she’s not ready to listen!! Baya jin kuma zata yarda ta bashi Huda a cikin sauk’i! Shi kuma a halin yanzu ya kai peak!! Edge!!Limit!! Na tolerance…

So yake kawai ya isa gida.

Shiyasa cikin k’ok’arin danne zuciyar shi da yake ji tazo masa iya wuya!!! Ya cewa Aslam
“Kai ta mota!! Idan tayi tirjiya ka d’auketa!”
Yayi maganar ba tare da ya d’auke idanunsa da suka koma tamkar garwashin wuta daga kan Arshaad ba! Yace masa
“Do your best ka lallashi Maryam sannan ka maidata gida.”
Yana gama fad’an haka ya juya ya bi bayan su Aslam da Huda wadda ta bisa salin alin dan ,
gani tayi ana cewa ‘ya d’auketa’ ya durk’usa ya fara k’ok’arin ciccib’arta….
Amman fa kukan da take yi still tana k’ok’arin zame hannunta ana Aslam ya sanya gaba d’aya hankalin duk mutanen da suka wuce ta gabansu ya dawo kansu, da yawa tunanin su rasuwa aka yi mata, shiyasa ba wanda yayi k’ok’arin tsaidasu! Sai dai ‘Allah ya ji k’an rai’ kawai da wasu mutanen suka dinga cewa
Wasu kuma kallon tausayi suka bisu dashi.

Aslam yana isa bakin motar yaiyi mata key ya bud’e ya dannata a ciki ya rufe sannan ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya bata wuta, ba tare da ya jira Abba ko Arshaad ba ya d’auki hanyar MT estate da ita........

Arshaad gaba d’aya ya tsorata da ganin yanayin Abba
Dan tabbas bai tab’a ganinshi a irin wannan yanayin ba!
Duk inda bacin rai ya kai b’acin rai to yau ya hango shi a kwayar idanun Abba!
Shiyasa ya kasa tsaidashi.


A hankali bayan fitar shi yaje inda Mama ke durk’ushe tanata faman kuka shima ya durk’usa gaba d’aya ranshi ba dad’i!
A hankali yace “Mama dan Allah k.....”
Kallon da ta d’ago tana yi mishi ne ya sa ya had’iye ragowar maganar sa!
A hankali ta mik’e ta gyara mayafin jikinta sannan tace
“Arshaad mai yasa kayi mana haka?”

Da mamaki yake kallon ta kafin yace
“Mama ni kuma mai nayi?”

So da Buri
Free Book
39

Da sauri Sakina tace “Mamaa” sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tattab’a ta,
ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita!
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare, dan a yadda Sakina ta juyo da ita haka ta biyo hannun Sakinan ta taho yuuu ta zube wanwar kwanciyar rigingine.

Ummu mutuwar tsaye tayi a wajen, so take ta k’arasa inda suke amman ta gagara sakamokon ganin y’ar uwartata da tayi kwance tamkar gawa!
Ta kasa tab’uka komai banda hawaye ba abunda take yi.

Sakina wadda ta rikice tanata tattab’a Maman ne ta juyo tace
“Ummu ki zo ki kamata mu mik’ata emergency..
Mama ce amman bata numfashi.”

Jin hakan ba k’aramin sake rikita Ummu yayi ba, ita dai kawai ta ganta a gabansu a tsaye amman bata san ya aka yi ta isa wajen ba.

Matar nan ce ta matso itama ta hau jijjiga
Mama tana cewa “kumafa yanzun nan muka gama magana da ita, tun jiya muke nan tare da ita. In banda kuka ba abunda take yi, nayi tambayar duniyar nan tak’i kulani…
Sai dai kawai taje tayo alwala tazo tayi ta sallah.
Sai d’azu ne da naga kamar batta lafiya nace ‘tazo muje in rakata taga Likita’, shine na samu ta d’an kulani ta inda take ce min ‘bara ta d’an yi bacci, idan ta farka sai muje’.”

Ita dai Sakina cicib’arta ta fara k’ok’arin yi hakan yasa suma suka sa hannu suka taimaka mata suka yi waje da ita.....


Su Madu suna tsaye a k’ofar shiga emergency..
Kana ganinsu ka san hankalinsu ba a jikinshi yake ba!
Ga tsananin gajiyar da suke tare da ita
Dan ma Allah ya taimaka Abokin Junaidu ne ya biya musu kud’in jirgi su kuma suka biyawa Baba
Saboda yaga yanayin tsufansu gashi da ya kira Baban ma a hanya ya jisu suna dawowa daga wata tafiyar….
Ba dan haka ba
da gajiyar ba zata yi musu da sauk’i ba.

Suna tsaye suna tunanin abunyi next suka hango su Ummu d’auke da mata suna nufusu, sai da suka matso su sosai sannan suka gane Mama ce.
Basu samu damar tambayar su ba dan da sauri mai gadin k’ofar ya wangale suka shige kawai dukkansu…

Ana ganin su aka karb’esu bayan an kawo gado an d’aurata, aka tura ta ciki don yin bincike..
Ba a jima ba sosai, Dr ya fito! Likitan dai da ya karb’eta jiya shine, magana d’aya ce ya maimaita musu “hawa da jininta yayi over ne ya janyo komai..amman this time around har eco za suyi”
Nan yake ce musu “ba yadda bai yi da ita jiya akan ta zauna ta shanye drip d’inta ba amma tak’i, ta biyewa wasu suka dinga hayaniya suna fad’a! Yayi yayi akan suyi shiru suka k’i, shiyasa shi kuma ya sallameta, so suma in sun san hayaniyar za suyi gara karma su shiga inda take, dan zai sake korar su ne!”.
Yana gama fad’in haka ya nuna musu inda take sannan ya wuce........

Bayan kamar awa d’aya, Kaka da su Baba suka wuce aka bar Sakina da Ummu.
Su Kaka na fita Hudan wadda take kiran Sakina a kai a kai ta kira, nan Sakina ta gaya mata “sun ganta suna tare ma yanzu haka”
Sai a lokacin hankalinta yad’an kwanta.
Nan itama Sakinan take tambayarta “tana Ina?” Hudan tace mata “tana wajen Gwaggon su Aslam, amman still Abba bai san tana gidan ba, dan a b’oye ma Arshaad ya kawo mata wayarta data bari a gidan Gramma, so in shaa Allah gobe da sassafe za ta san dabarar da zata yi ta gudo.”
shiruu, Sakina tayi chan tace “ki bari mu yi magana da Ummu tukunna, kar ki yi komai, kinji?”
Ummun ce tasa hannu ta karb’i wayar suka yi magana da Hudan ta d’an kwantar mata da hankali, kafin suka yi sallama.

Da kyar suka samu bacci ya kwashesu wajen k’arfe 3 na dare.

Da sassafe su Madu da Baaba Talatu suka zo kawo musu breakfast, har lokacin Mama bata farfad’o ba.
Sama sama take jin hayaniyar su dan haka ta fara k’ok’arin bud’e idanunta.
Sakina wadda take a kusa da ita ce ta lura dan haka ta maida gaba d’ayan hankalinta gareta, ganin Sakina ta k’ura mata ido ne ya sanya suma duk suka taso suka zagaye gadon suna tambayar “mai ya faru?”
Basu ida tambaya ba Mama ta k’arasa bud’e idanunta…
Tsantsar farin ciki ne ya baiyyana a fuskokinsu gaba d’ayansu, cikin murna suka hau furta “Alhamdulillah” suna tambayarta “ya jiki?”.
Da kyar Baaba Talatu ta taimaka mata ta mik’e ta zauna..

Tana zama suka had’a ido da Ummu!
Kawai sai ta fashe da kuka abun tausayi……

Duk shiru suka yi.

Da kyar Madu ya samu ya k’araso inda take ya dafa ta sannan ya d’an fara bubbuga bayanta alamun lallashi.

Farin ciki ne ya mamaye zuciyoyinsu gaba d’aya, duk sai suka hau murmushi
Kaka har da y’a kwallarshi, ya sa hannu share ba tare daya bari kowa ya lura ba.
Ita kanta Mama duk da yanayin da take ciki hakan sai da ya sanyata zubar da kwallar farin ciki, dan rabonta da Madu ya nuna kulawarshi a kanta kaman haka, yau
yau shekaru ashirin da bakwai kenan!.

Share hawayenta tayi sannan ta d’ago ta kalleshi, shima itan yake kallo, ba abinda ta hango a idanuwanshi sai tsantsar tausayinta, bakinta na rawa cikin kuka tace
“Abba, ya raba ni da Huda! Dan Allah ku karb’o min ita, wallahi mutuwa zan yi in ba y’ata, na shak’u da ita sosai,
ba zan iya yarda in bar mishi ita ba.”

Da sauri Ummu ta k’araso ta rungumeta, sannan cikin tsananin tausayinta
tace
“Ki yi hak’uri ki huta, munji komai, in kika warke sai a san abun yi, ki kwantar da hankalin ki dan Allah.”

Cikin jujjuya kai Mama ta zare Ummu a jikinta kafin tace
“Bilkisu ba zan iya yin hak’urin nan ba!! Abba ya zama wani irin mutum! Mugun mutun..
Shi ne fa ya turo Arshaad wajen Huda, Arshaad cousin d’inta ne!
Suka dinga yaudarar mu, idanunsa akan mu yake all this time amman bai baiyyana kanshi ba sai yanzu?
Saboda ko nace ba zata koma wajenshi ba ya san ai Arshaad zata aura, kenan ko?
Wanne irin ubane zai yiwa y’arsa haka?
Bilkisu gaba d’aya kaina ya kulle, a baya yace ‘baya buk’atar ta’, yanzu kuma yazo ya raba ni da ita a lokacin da nafi buk’atar ta, mai yasa zai yi haka? Laifin me na yiwa Abba da zafi haka??”.
Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka.

Lallashinta Kaka Baaba Talatu da Ummu suka hau yi, amman furr!! Tace “ba zata hak’ura ba! Ba zata iya yin hak’urin da suke so tayi ba, yanzu zata je ta taho da y’arta, barinta a hannun Abba danger ne! Tunda har ya iya turo wani wajenta saboda son zuciyarshi bai damu da yana sonta tsakani da Allah ba ko akasin hakan ba
Tou tabbas zai iya yin komai.
Ko bayaga haka ma
idan duk duniya zata taru a kanta tofa ba zata d’auki y’arta wadda Abban yace ‘bayaso ta fad’a mata ko da sunan shi ne’ ba, ta bayar a shi yanzu! Sai dai duk abinda zai faru ya faru.
Suyi mata kwatancen gidan ko kar suyi mata zata tafi ta nema, tunda Allah yasa taji kwarin jikinta yanzu, daman jiya ma jiri ne ya hanata motsawa daga inda take.”


Gaba d’aya Mama ta hargitse musu, data ga ma ba zasu bata goyon baya ba,
Sai ta fara k’ok’arin sauk’a daga kan gadon sannan tasa hannu zata cisge cannular hannunta.

Madu ne ya rik’e hannun nata, kafin cikin lallashi yace
“Maryam koma ki zauna muyi magana.”
Cikin sheshshek’ar kuka ta koma ta zauna tana share hawayenta.

Sai da yaga ta d’an sassauta kukan nata, sannan ya fara magana
“Ki kwanta ki huta,
baki da lafiya.
Koda kin fita za ki sake fad’uwa ne, saboda baki gama dawowa normal ba!
Ki zauna ki shanye allurai da magungunan ki, da ni da Babanku Bashir za muje mu samu Abba, in shaa Allah, kinji ko??”
Da sauri Kaka yace
“Za muje a yau! Ki kwantar da hankalin ki kinji?”

A hankali taji kad’an daga cikin nauyin da zuciyarta tayi ya d’an sauk’a, dan haka ta d’aga musu kai alamar ‘to’ kawai,
tana sharar hawaye.


Ajiyar zuciya Baaba Talatu ta sauk’e, sannan ta nufi wajen kulolin da suka kawo ta zubowa Mama abinci ta kawo mata.
Sakina ce ta karb’a ta fara k’ok’arin bata, amma sai ta kauda kai gefe tace “ta k’oshi”
Cikin turo baki Sakina tace “haba Mama ki ce mana, kin ganki kuwa yadda kika koma? Gashi duk kin yi wata zuru zuru kamar…”
Dukan da Maman ta kawo mata tayi saurin kaucewa, duk kuwa sai suka hau murmushi….

Da naci da komai hakanan sai da Sakina ta d’urawa Mama abincin nan, ta kuwa ci sosai, dan sai da su Madu suka sa baki tukun Sakina ta hak’ura.

Sai wajen 11 na safe su Sakina suka fara shirin tafiya don suke suyi wanka suyi girki, ita da Ummu.

Baban su Sakina ne yazo d’aukar su!
Ya d’auka Mama ko wani zai yi mishi maganan Arshaad amman yaji shiru shiyasa shima yana yiwa Maman ‘ya jiki’ ya fita, dan baya so suyi mishi d’in, but ya tsara a ranshi zai gayawa matarshi, duk abinda ya sani, da kuma dalilin yin shirun da yai, saboda kar ayi mishi kallon munafuki.

Sai da suka biya duk wani bill sannan suka tafi
a lokacin an tafi da mama yi mata eco.
Su Kaka ma shirin tafiya gidan su Abba suka yi, aka bar Baaba Talatu. Sai a sannan ne Baba yazo, ganin Maman bata nan yasa suka gaisa da Baaba Talatu ya wuce kasuwa akan zai dawo da azahar in shaa Allah.

Su Kaka basu samu damar zuwa gidan su Abba ba, sai la’asar, a sakamokon kiran da aka yi musu akan results d’in da ya fito, dangane da case d’in Junaidu.........



Yadda Hudan taga rana haka taga dare, Gwaggo Asabe har mamakinta take yi dan duk juyi in tayi sai taga idonta biyu!
Gaba d’aya ta kasa bacci ta k’agu Safiya tayi taje taga jikin Maama, da taga safiya ta k’i yi k’arshe kawai mik’ewa tayi taje ta d’auro alwalla, tazo ta fara jero nafilfili.

Tana idar da sallar asuba kuwa bayan ta gama Azkar ta d’anyi karatu, ta shiga tayi wanka.
Tana fitowa ta tarar Gwaggo Asabe bata d’akin, hatta sallayar data barta akai ta nad’e.
Doguwar rigar da Gwaggo Asaben ta bata jiya had’e da Maclean da brush sabbi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login