Showing 54001 words to 57000 words out of 109746 words
Arshaad Ina wuni.”
Da sauri ya d’ago, ya d’an zaro ido alamun mamaki, sai
kuma ya fara murmushi yace
“Lafiya, Alhamdulillah.
Ashe kece da kanki!
Welcome, ya gida?”
“Alhamdulillah” tace kafin ta d’an turo baki tace
“Ai gani nayi da farko ka wani had’e rai ko kallon inda muke ma bakayi ba”
Dariya yayi kafin yace
“Hankalina baya wajen ne,
sorry”
Itama murmushi tayi ta sake gaida Abba da Aslam wanda ya amsa ko kallonta bai yi ba!
Tunda suka sauk’o ma ta lura bai ko kallesu ba…
Tana ganinshi tashi d’aya ta fahimci shine Aslam.
Lokacin da Hudan take zuzuta mata kyawun Aslam d’in bata yarda ba, dan har ta fara tunanin wani abun a tare da Hudan na daban,
but yanzu kam tagani itama!
“Tubarakallah!”
Ta fad’a a k’asan ranta.
Cikin nutsuwa taji Hudan suna gaisawa da Abba wanda yake zaune a opposite d’insu shi da Aslam. Da kulawa yake tambayanta hope taji dad’in ganin Sakina? Is she happy now? Taji dad’in zuwa munjibir park d’in? Ba wata damuwa ko?……
Murmushi Hudan tayi duk tana ta binshi da “Alhamdulillah komai Alhamdulillah..”
Abun yayi matuk’ar burge Sakina a ranta tace “yau ina Baba da Umma suzo suga gatan da akewa Huda, suga yanda Abbanta yake janta a jiki yana lallab’a ta”
Wani farin ciki ne taji ya lullub’eta, tabbas tana yiwa Hudan murna da baiyyanar Mahaifinta!
Itafa sometimes ji take a ranta kamar ma tafi Hudan farin ciki.
A hankali taji sun gaisa da Aslam, taga ita Hudan ta d’an samu darajar kallo a wajenshi tukunna yace “lafiya” da d’an mitsitsin bakinshi.
Har an fara serving ta mintsili Huda da k’arfi ta k’asa k’asa inda ba za a gani ba.
“Ouch” tace, a hankali sannan ta juyo tana kallon ta, harara Sakina ta zabga mata k’asa k’asa tace “shi ba zaki gaidashi ba???”
Itama Hudan hararar ta maida mata ta cigaba da zuba abincinta!
Mintsilinta Sakina ta sake yi, kafin tace
“Wallahi ko ki gaisheshi ko kiyi ta karb’ar ruwan mintsili kala kala!”
Dai dai nan wayar Abba tayi k’ara …
Excusing kanshi yayi ya mik’e ya d’an koma gefe yana amsa wayar dan it’s a very important call ba zai yiu yayi ignoring ba.
Kamar jira Sakina take, nan ta sake sakar mata wani sabon mintsinin da sai da tayi k’ara mai sauti sosai this time around har su Aslam sai da sukaji suka juyo suna kallonsu…
Sudais kuma ya fara kyalkyala dariya dan shine a kusa da Sakina yana kallonta tun d’azu!
Ganin da Huda tayi Sakina ba zata hak’ura ba yasa ta juya, kujera biyu ne tsakaninta da Arshaad d’in dan haka ta d’an kalleshi tace “ina wuni”
Sai da ya sake tamke fuska tukun yace
“Lafiya”
Yanajin haushi a ranshi, wato gaisuwar ma sai ta ga dama zata yi, kuma shine na k’arshe! Har su Sudais sai da ta gama kulawa tukunna shine last!
Tashi Sakina tayi daga kan kujerarta ta dawo ta gefen Hudan side d’in da Arshaad yake ta zauna kafin tace
“Am i missing something here???”
Tayi musu maganar tana juyowa ta kalli wannan ta kalli wannan.
“Eat!”
Arshaad yace sannan yaci gaba da cin abincin shi.
Dawowar da Abba yayi ne ya katse mata maganganun da suka taso mata don haka tayi shiru…
Luckily aka sake kiran Abba a waya dan haka ya mik’e yace “bara ya shiga wajen Daddy”
Ba a jima ba Aslam shima ya mik’e, da sauri Hudan ta mik’e ta mik’a mishi Goron ruwan hannunta
Opposite yau ma suke dan haka ya kalle ta yace
“thankyou!” a hankali yana kallonta.
Bata san daliliba! Dan kwata kwata sam sai ta kasa janye idanunta daga nashi. Tunda Mama ta kawota duniya ko a tv bata tab’a ganin kwayar ido mai kyan nashi ba! Shape d’in Idon kansa abun son ka kalla ne! Komai na idanun nasa masu kyau ne
Itakam wata rana zata tambayeshi ‘me yake shafawa eyelid d’insa?’ Dan wani haskene yake fitowa daga wajen .....
Dukda yadda zuciyarta ta tsananta bugu hakan bai sanyata ta d’auke idanunta daga kansa ba kuma baisanya ta sakar mishi robar ruwan da ta mik’a masa ba!
“GOOD NIGHT Sakina!!”
Suka ji Arshaad ya fad’a da d’an k’arfi!
Da sauri Aslam yayi firgigit, ya janye robar da mugun k’arfi, sannan ya juya yayi hanyar fita. Har ya fice daga parlourn bai yarda ya sake juyowa ba.
Hudan ita kam kunya ce gaba d’aya ta lullub’eta.. Ashe har Arshaad da Sakina sun mik’e
su shuraim kuma suna shirin fara hawa bene ita bata ma sani ba!.
Yana shirin barin wajen Sakina tace “pls mana”
Tana d’an karkartar da wuyanta.
Murmushi yayi yace
“she’s busy rn, let it go kawai.”
A hankali Sakina tace
“Plss”
Tana had’e hannuwanta biyu waje d’aya alamun rok’o.
Ajiyar zuciya ya sauk’e ya d’an ja ya tsaya.
Hudan na ganin wucewar su Shuraim sama ta juya itama zata bar wajen.
Hannu Sakina tasa ta rik’eta.
Ba tare data juyo ta kalleta ba tace
“Sakin mani hannu plss, bacci nake ji”
Jin abunda tace ya sake tunzurashi
don haka kawai ya fice fuuu!! Ko sauraron Sakina bai sake yi ba.
Haushi Sakina taji ta saki mata hannu suka haura sama…
Har suka shafa addua suka kwanta suka ja bargo ba wanda ya yiwa d’an uwanshi magana...........
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
44
Tun Asuba Hudan ta sauk’o ta fara kula Sakina, dan ita ta tasheta ma sallar Asuba.
Sakina kuwa har suka yi wanka suka shirya, aka je aka yi breakfast aka dawo bata kula Hudan.nKo tayi mata magana ma sai dai tayi mata banza:
Hankalin Hudan bai tashi ba, sai da taga Sakina ta saka kayanta waenda tazo dasu chap ta shirya, tace mata “sai sunyi waya”.
Da sauri ta shiga gabanta ta tsaya dan har ta kusa k’ofa,
kafin tace
“Ban gane ‘sai munyi waya’ ba!
Me hakan yake nufi?”
Ba tare data kalletaba tace
“Tafiya zan yi”
Cikin rashin jin dad’i Hudan tace “Akan Ya Arshaad kikayi fushi dani haka har kika yanke hukuncin tafiya ki bar ni??
Kin san kuwa me yayi min?”
D’ago dara daran idanuwanta Sakina tayi, kafin tace
“Nasani Hudan, sanin abunda ya had’akun ne ma har yasa kike fushi dashi hakan ne zai sanya in tafi..
Jiya baki b’ata min rai sosai ba
amman dana san dalilin fad’an naku wallahi bakiji yadda raina ya b’aci ba.”
Cikin takaici da son fahimtar da ita Huda tace
“Sakina Jalila fa yaje........”
Cikin katseta Sakinar tace
“Na fad’a miki fa, na sani.
Jiya mun yi chatting da shi sosai ya fad’amin komai!
Haba Huda, kamar baki san wacece Jalila ba?
Dan ta fad’a miki magana sai ki hau ki zauna??
Kishi ne ya rufe miki ido ko rashin wayo?
A tsakaninki keda Ya Arshaad bai kamata a samu haka ba.
Jiya cemin yayi kawai bakya sonshi, maybe akwai wanda kike so yanzu saboda he can recall yadda kikayi calling off engagement d’inku saboda Ya Junaidu kawai don bakya son ki b’ata mishi rai! Amman shi yanzu lokaci d’aya kin murzawa idonki tuka kinata zuba mishi rashin kirki!
Ba abunda yafi b’ata mishi rai irin yadda ana fad’a miki kika hau kika zauna, kamar daman tun farko kina zarginshi…
Anyways yace yana neman alfarma a wajenki, anjima zai san yadda zai yi ya kawo Jalila nan, akawo AlQurani suyi alwala shi da ita
kowa ya rantse akan gaskiya yake fad’a!
But yace b4 then dan Allah ki d’au waya ki kira Aaima ki tambayeta waye Auwal ya halinshi yake!”
Tunda Sakina ta fara magana jikinta yayi sanyi
Sai yanzu take ganin rashin kyautawarta….
Ganin Sakina, tana shirin zagayeta ta fita ne yasa ta kuma tararta ta tare hanyar kafin tace “To kiyi hak’uri ki fasa tafiya, haba Sakina, ko kece kikaji haka fa dole kiji haushi”
Da sauri Sakina tace
“Hudan zan tafi! Dan ba zan iya tsayawa inga wai Ya Arshaad yana dafa Qur’ani yana rantse miki akan ba shi ne ya yiwa Jalila ciki ba!
So that ki yarda kuyi getting back together..
Haba Huda! Ya Arshaad ne fa, wallahi sam bai chanchanci haka daga gareki ba!.
But ba zan hanaki ba,
ki barshi yayi dan na san tunda kin riga kin saka haka a ranki to in ba rantsuwar yayi miki ba ba zaki tab’a yarda ba!.
Amman wallahi kinji dai na rantse miki ba ruwan Ya Arshaad a lamarin nan!
Shi wannan Auwal d’in shine yayi aika aikar shi kuma zaki ce na gaya miki, Ya Arshaad ya fad’a min baki tab’a ganinshi ba sai ranar amma yana fad’a miki magana kika hau kika zauna shi kuma da kika sanshi for almost 4 years kika k’i yarda dashi.
Hudan Ya Junaidu, kwatar ki yake yi a hannun su Jalila idan suna kimar ki amman kince ba zaki tab’a manta alkairinshi gareka ba
Ya arshaad fa?
Zaki iya gaya min irin tarin alkairan da yayi miki?
Ba ke ba har ni kaina da nake kusa dake sai da alkairinshi ya shafeni.”
Ahankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“Sakina ranar nan fa a gaban ki Mama tace min taji Yaro yazo yace wai Jalila taje inji Arshaad..”
Murmushin takaici Sakina tayi kafin tace “kuma a same day da time ne ke da Ya Arshaad d’in kuka yi dogon video call ba! Ba ma voice call ba video call and a d’aki muka ganshi throughout bai fita ba har kuka gama, ba a mota ba!.
Kinsan wani abu Huda?
Bata jira jin amsarta ba tace “wallahi duk makirci ne, so sukeyi kawai su shiga tsakaninku!
That Auwal shi yayi planning komai, ban san mecece agenda d’inshi ba, but na san shine master mind!
Ban ganshi ba amman na tsaneshi!.
Ni dai shawarata a gareki itace ki bud’e idonki da kyau, ki fahimci gaskiya tun kafin dare yayi miki!
Arshaad ya sanki ya soki tun kina Hudan ki! Idan kikace
zaki juya mishi baya yanzu gaskiya baki kyauta ba!.
Ban hanya in wuce, dan ba zan iya ganin wannan abun takaicin ba.”
Rugumeta Huda tayi kafin tace
“Shikenan ya wuce
Na hak’ura!
Dan Allah karki tafi.”
“No, Hudan seriously ki bari yayi miki clearing confusion d’inki, saboda kar ki dinga ganinshi da abun dan na sanki da taurin kai! Kar kije an kashe case but still kina zarginshi
so just ki barshi su zo d’in.”
A hankali tace “komai ya wuce, ki cire hijabin please haba mana”!Ta k’arashe maganar kamar zatayi kuka.
Sai yanzu Sakina tayi murmushi kafin tace
“Shikenan na faasa tafiya
amman ki barsu kawai suzo d’in ayi a gama”
D’aga mata kai Hudan tayi.
A hankali Sakina ta koma ta zauna akan gado, bayan ta cire hijabin.
Da kad’an kad’an Hudan ta dinga janta da hira har ta samu ta sake ta daina fushin..
Nan take bata labarin Ya Junaidu, amman the good news is that
DNA d’in su Baba bai yi matching da gawarwakin ba
Both wanda akayi a Lagos
da wanda suka taho da sample d’in nan Kano aka yi.
Hawaye Hudan ta share kafin tace Yanzu Ya Junaidu ya b’ata kenan?”
A hankali Sakina tace
“Mu yita addua kawai
Allah ya baiyyana shi”
“Ameen” tace.
Ba abunyi dan haka daga kallo sai chatting da hira..
Yau su biyu tol suka yi lunch, su Shuraim suna school Abba kuma ya d’an fita wasu ayyuka, Arshaad bai lek’o ba Aslam ma haka.
Sai bayan Magrib Arshaad ya kira Sakina yace mata “suna k’asa shi da Jalila, su sauk’o!”.
Jalila tunda take bata tab’a jin farin ciki irin wannan ba!…….
D’azun tana d’aki Gwaggo Asabe tazo tace mata “taje, inji Arshaad, yana kiran ta.”
Kasa b’oye farin cikin ta tayi a gaban Gwaggwo Asaben har
da su fesa turare da shafa jambaki, daman already idanunta da kwalli fuskarta kuma da powder!
Ita dai Gwaggo Asabe tsayawa tayi tana kallon ikon Allah,
Allah yasa dai ba wannan Yarinyar Arshaad zai kwaso musu ba, ita tunda tazo gidan gaisuwa bata tab’a had’asu ba, gashi bata son aiki, hatta d’akin da take ciki sai dai tazo ta kira aje a gyara mata.
Doguwar riga y’ar kanti mai kyau ce a jikinta, dan haka ta d’auko d’an k’aramin mayafi tayi d’auri sannan ta d’auko wani ta yafa shima d’an mitsitsi daga nan ta d’au wayarta tazo ta wuce ta fita ta bar Gwaggo Asabe da baki a sake.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e, kafin ta lek’a da d’an k’arfi tace mata
“yana chaan waje a bakin mota”
Don har tayi nisa.
“Ok”
Kawai Jalila tace
tayi gaba abunta.
A bakin motarshi ta ganshi a tsaye. Bai yi wani kwalliya ba
hasalima Jallabiya ce a jikinshi bak’a amman sai da numfashin Jalila ya kusan d’aukewa dan yayi mugun tafiya da imaninta!
A k’asan ranta tace
“Ma shaa Allah”
Tanajin tsananin tsantsar k’aunarsa tana sake ratsa dukkannin ilahirin jikinta,
itafa ko da ace Arshaad zai dinga yi mata dukan tsiya kullum! Muddin zai yarda ya aure ta su zama k’ark’ashin inuwa d’aya, ta na amsa sunan matarshi to
wallahi zata iya zama da shi!.
Tsabar kallon da take yi mishi har tuntub’e tayi ta kusan fad’uwa wanda hakan ne ya janyo hankalinshi gareta dan shi bai ma san ta fito ba!.
Suna had’a ido ya tamke fuskar shi kamar bai tab’a dariya ba.
A take taji gabanta ya fad’i amma sai ta dake ta k’arasa inda yake
still tanata satan kallonshi….
Sai da ta d’an risssina tukunna tace mishi “Ina wuni” cikin wani kalan yauk’i da kissa.
Sake had’e rai yayi, ya bud’e mata murfin motar tukun yace “lafiya, shiga mu je!”
A take tsoro ya rufeta, D’an bata san mai ya shirya mata ba
Tana shiga, ya rufe ya zagayo ya zauna mazaunin drivern.
Sai da taji tashin motar tukun ta bud’e idanunta dan tun lokacin da ya rufe mata motar ta wani lumshe ido tana murmushi saboda ba k’aramin dad’i taji ba.
D’an juyowa tayi ta kalleshi
fuskar shi yanda kasan wanda bai tab’a dariya ba!
A hankali ta zaro wayarta ta turawa Auwal message
saboda
gaskiya in dai daga ita sai Arshaad ne a waje tou za a iya samun matsala dan tabbas tsaf! Zata Fallasa komai kuma ta san Auwal uban ta zai ci idan tayi hakan.
Suna parking a cikin gidan dai dai message d’in Auwal ya shigo wayarta…
Sai da su Hudan suka sauk’o tukun ta fahimci inda suka zo dan haka tayi mishi reply ta ajjiye wayar.
Tunda ta sauk’o take maka mata harara!!
A kujerun tsakiyar parlourn suke dan haka suma suka nufi wajen suka zauna.
A hankali suka gaidashi ya amsa
Sannan Huda ta kalli Jalilan tace “Ya Jalila ina wuni”
Wani uban tsaki Sakina taja ta d’auke kai.
“Hmm”
Kawai Jalilan tace, wallahi ba don Arshaad yana wajen ba da sai ta tashi ta bugewa Sakina baki, dama a k’ule take dan ita kad’ai ta san tashin hankalin data shiga tun saukowarsu…..
Ajiyar zuciya ta sauk’e
kafin ta kalli Hudan tace “lafiya”
Kawai! Amman a k’asan zuciyarta ji take yi kamar ta mutu dan tsananin bak’in ciki! Wani irin tuk’uk’i ne yake taso mata saboda abunda idanunta suka yanzu nan ne gidan Mahaifin Huda??
Ba abunda yafi d’aga mata hankali daman tuntuni irin labarin da taji Gwaggo Asabe tanayi da wata mai aiki dattijuwa akan ‘Mahaifin nata ya bar gidan saboda Babansa yace ya zab’a ko shi ko ita!!’
Ita a tunaninta bashi da wani kud’i sosai dan tama d’auka gidan haya suka je suka kama suna zaune
Ashe shima mugun mai kud’i ne.
Ta tabbata Hudan y’ar masu kud’i ce kenan yanzu? Kuma Babanta yana matuk’ar sonta!
Muryan Arshaad ce ta katse mata tunani jin yana cewa
“Jalila ga Al Qurani, izu sittin.” yayi maganar yana nuna mata kan center table kafin yaci gaba
“Idan baki da alwalla kije kiyi kizo yanzu!
Zan rantse akan ‘cikin jikinki ba nawa bane ba! Sharri kika yi mini’ kema kuma zaki rantse akan ‘gaskiya kike fad’a (cikin nawa ne).
Tsakanin ni da ke duk wanda yayi karya Al Qur’ani ya ci shi!.”
Wata zazzafar zufa ce ta keto mata, tana shirin yin magana taji ance
“Sannu Ya Sheik! Akaramakallahu.”
Suka ji muryarshi yana takowa cikin parlour…
Cikin gadara Auwal ya k’araso wajen, kafin one by one ya kalle su! Da kyar ya iya janye idanuwanshi daga kan Sakina! Sannan ya d’anyi murmushi yace “Ai ya kamata ni ma a gaiyyaceni meeting d’in ko?”
Ya fad’i hakan yana mai neman kujera ya zauna kafin yace
“Ya sheikh!! You were saying??”
Banza Arshaad yayi da shi ya tashi ya matsa yana k’ok’arin d’aukar Qur’ani n Hudan tasa hannu ta d’auka
a hankali tayi k’asa da kanta ta fara magana
“Ya Arshaad dan Allah kayi hak’uri akan abunda nayi maka, na yarda da kai please ba sai ka rantse ba!”
Wani farin ciki ne ya lullub’e Arshaad da Sakina a take.
A hankali shima, yace
“Thanks for trusting me Hudan, but i’ve to do this, please don’t stop me, okay?”
Cikin katseshi tace
“Nima please kar kayi haka, wallahi i trust you, in kuma kak’i yarda har kayi, to
it means stilll baka hak’ura ba kenan da abunda nayi maka.”
This time around murmushi yayi, kafin yace
“Tou kawo, bani”
Yayi maganan yana mik’a mata hannunshi
Tana shirin yin magana, suka ji Auwal ya kwashe da dariya, cikin dariyar yace ,
“Yayi Romeo and Juliet!!
Hey, look here”
Yayi maganan referring to Hudan, kafin yace
“Ki yarda da shi ko kar ki yarda da shi wannan matsalarku ce!!
Ba wai dama na fad’a miki dan wani abun bane, that very day
kin shigone a time d’in da case d’in yake goin that’s why har kika san maganar!
Anyways
Jalila it’s up to you, sai ki san abun yi…
Tunda gashi yanzu ya nace akan ba nashi bane!
I think su Granpa ne kawai zasu iya kwatar miki hakkinki dan ni kam daga yau na cire hannuna a case d’innan naku, in shaa Allah.”
Ya k’arashe maganar yana mai bud’e hannayenshi biyu ya kai bayan k’eyarsa ya sak’ale sannan yayi resting gaba d’ayansa akan kujerar ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya.
Wani tuk’uk’i ne ya turnuk’e Sakina, bata san lokacin da ta fara magana ba!
Kamar yadda ya yiwa Huda itama hakan tayi mishi
Hey! You look here, Auwal kake ko wa?
Waye ne ya gayyatoka nan?
Wa ya kira ka?
Waye ya kasa da kai?
Wa yace maka ana son jin opinion d’in ka a cikin maganar nan?
Hakanan kawai ka kama ka shigo tsulum! Ka tarar da mutane ko sallama baka yi ba
ka hau magana kamar wani kwarkwar!.
And let me tell you something abunda kayi yanzun, ya tabbatar da you got something to do with her and the baby!
Kuma da kake wani cewa ‘zaka kai magana sama’ Ai da kai! Da mu! Da ita munafukar taka duk munsan gaskiya dan
haka ina mai shawartarka da ka tabbatar ka d’auko fad’an da ka san zaka iya