Showing 57001 words to 60000 words out of 109746 words
k’arasawa, in ta kwab’e!!
Ke kuma!”
Ta juyo kan Jalila,
sannan tace “ki karb’a ki rantse a gaban kowa, sannan ki yi Allah ya isa a duk wanda ya cutar dake haka, a tsakanin Ya Arshaad da wannan Auwal d’in.
Hudan Dan Allah ki bawa ya Arshaad, yau zan ga k’aryar iskanci.”
Tunda Sakina ta fara magana Auwal yake kallonta ya kasa d’auke ido, k’arshe ma murmushi ya fara yana jin inama kar ta daina.
Muryar Jalila ce ta katseshi jin tana cewa “Tou uwata! Ke har kin isa ki gaya min abunda zan yi?”
Da sauri Arshaad ya juyo yace “in baki da alwala kije kiyi kizo yanzu” Yayi maganar babu
alamun wasa a tattare da shi.
Gaba d’aya jikin Jalila ya jik’e da gumi, tun lokacin da aka fara maganar, tsabar tsoro!
“Ko bakya ji ne?”
Arshaad ya fad’a cikin b’acin rai dan takaicin Yarinyar yake ji ba kad’an ba, ji yake yi kamar yaje yayi ball da ita.
Auwal ta d’ago ta kalla, taga yayi mata wani kallon data fassarashi da warning!! Ganin kowa ita yake kallo yasa ta cire mayafinta ta ajjiye ta wuce tana cewa
“ina ne toilet?”
Wata k’ofa kurkusa Arshaad ya nuna mata yace “ta shiga”.
Tana shiga ta turo k’ofar ta jingina tana haki, kamar wadda tayi y’ar tsere!
Tunda take bata tab’a shiga tashin hankali irin na yau ba…ko hauka take yi ba zata tab’a dafa Qur’ani akan k’arya ba, akan gaskiyar ka ma ba a cika son kana dafawa ba, balle k’arya!
Da albarkar ka ma ya ka k’are
ballantana babu!
Kuma ita a halin yanzu
tana buk’atar albarkarta fiye da ko yaushe, da kusanci da Ubangijin ta! Tana so ta rok’esa arzik’i da soyayyar Arshaad
dan muddin taci gaba da ganin Huda a cikin wannan daular alhalin ita bata da shi, to wallahi ta san zuciyarta sai tayi ajalinta….
Ta dad’e a cikin band’akin sosai, har sai da Sakina taje tayi mata knocking tukunna ta bud’e, tana bud’ewa ta zabga mata harara kafin tace
“Banza y’ar karere kawai, sarkin zak’ewa!”
Dariya Sakina tayi kafin tace
“Ai gara ni y’ar karere ce
Kuma kirana aka yi takanas! Nazo ba abun kunya ne ya zaunar dani a gidan ba.”
Jalila bata ita take ba, dan haka tayi shiru kawai ta fito suka k’arasa parlourn
tana tunanin next stage!
Gabanta in banda fad’uwa ba abunda yake yi..
Ana tsayawa Sakina ta amshi Al Qur’ani n ta ajjiye akan centre inda yake tun farko, kafin ta kamo hannun Jalila ta kaita wajen tace “Bismillah!”
Fusge hannunta Jalila tayi
tana hararar ta
Kallonta Sakina take sosai da mamaki akan fuskarta kafin tace
“Da alama dai taimama kika yi ko?
Dan banji alamun danshin ruwa a hannunki ba, ga d’aurin vail d’inki shima rad’au!! Powder ki kuwa kamar ma k’arawa kikayi.”
….Gaskiya In Sakina bata daina shiga huruminta ba wallahi zata illatata a wajen nan!! Wanne irin iskancine wannan??…
Jalilan ta aiyyana hakan a ranta.
Muryar Hudan taji tana cewa
“Ya Jalila idan kin san baki yi alwala ba karki tab’a Qur’anin nan fa, Dan Allah.”
Takaici kamar ta shak’eta haka Jalila taji, a ranta tace
“Y’ar ‘Yaa Jalilan’ uwa!”.
Muryar Arshaad taji yace “Ba kiyi alwalar ba?”
Cikin rawar murya tace
“Eeh bbb ban dd’akin babu ruwa”
Da sauri Hudan tace
“Zo muje d’akina, kiyi a chan”
Sakina ta yunk’uro za tayi magana taji Arshaad yace
“Muje in kunna miki famfon, yana da wuyar sha’ani dama.”
Ya fad’i haka yana wucewa gaba.
Jikinta har karkarwa yake yi haka ta wuce, ta bishi….
Suna shiga ya kunna mata shower ya kunna famfon sink, da wani famfo a gefe ya nuna mata yanda zata matsa abun tsarkin jikin toilet sannan ya fito ya bata waje ya bar ruwan yanata zuba bai kashe ko d’aya ba.
Alwalar tayi ba yadda ta iya, ta kashe famfunan, ta tsaya tana kallon fuskarta a mudubi.
Jin yayi knocking yasa gabanta mugun fad’uwa!
Ita kam yau ta ga talatar kanta, gashi ba daman tace tana fashin sallah!
Da kyar ta iya daurewa ta fice, k’irjinta na dukan uku uku.
Suna k’arasowa, Sakina ta mik’a mata vail d’in da ta cire a jikinta d’azu ta ajjiye
tace “Bismillah”
Fisgewa tayi tana hararar ta.
Murmushi Sakina tayi kafin tace
“Yarinya yau ko idanunki zasu fad’o k’asa sai kin rantse!”….
……A nan fa ake yinta, ga Jalila ga Al Qur’ani a gabanta ga jama’a kowa ya zuba mata ido…
Parlourn yayi shiruuuu.
Ba abunda yafi bawa Arshaad mamaki irin yanda Auwal ya d’auke wuta diff!!! Don gaba d’aya kamar babu shi a wajen..
Shi kam Auwal yana chaan ya sha’afa da kallon Sakina kamar ya samu tv, sam! Bai damu da kalar harar da take zabga masa a duk sanda suka hada ido ba! Babu abunda yafi tafiya da imaninshi kamar idanuwanta waenda idan ta kalleshi dasu yake ji gaba d’aya kamar an zare mishi lakka bayan fad’uwar gaban da yake tsintar kanshi a ciki..duk wata hayaniyar shi yau ya ji babu ita, yanaso yasa baki a lamarin su Jalilan amman ya kasa, don bashi da wani sauran energy, gaba d’aya jikin shi yayi lakwass!!!.
Sakina kuwa so take ta gama da Jalila ta koma kanshi idan bai daina yi mata wannan kallon k’urillar ba!.
Hudan tana lura dasu, dan haka ta gama aiyyanawa a ranta suna komawa d’aki zata zaiyyanewa Sakinan waye shi!!
Kar ma ta soma bashi fuska dan ita tun zuwan su Munjibir park ta gama aminta da Auwal ba mutumin kirki bane ba!.
...duk sunyi shiruuu, kowa da abunda yake tunani a ranshi.
Nishi suka fara ji sama sama,
da sauri duk suka juya kanta..
Wani lumlumshe ido take yi tana layi, kafin ta tafi luuuu ta fad’i akan kafet d’in!
Da mugun sauri Sakina ta d’auki robar ruwan dake gefenta ta nufeta, ta na zxuwa ta bud’e murfin ta kelaya mata
ruwan mai mugun sanyi dan har da k’ank’ara k’ank’ara ma a ciki!!
Ai kuwa a firgice Jalila ta bud’e idonta tana wani mugun tari dan ruwan har cikin hancinta ya shige sosai….
Da kyar ta samu ta seseta kanta ta fara k’ok’arin mik’ewa,
tana mikewa kuwa ta d’aga hannunta zata zabgawa Sakina mari shi kuma Arshaad a take ya rik’e hannun da sauri.
Wani kalan shock taji a jikinta da wani sanyi a zuciyarta wanda ya sanyata kasa yin motsi!
A hankali ta lumshe idanunta tanajin yanda laushin hannun nashi yake ratsa jini tsoka da b’argonta.
Muryarsa ce ta dawo da ita duniyar su, jin cikin fad’a fad’a yana cewa
“Jalila kin fara isata wallahi ranki zai yi mugun b’aci!
Inada abun yi amman kin tsaya sai b’ata mana lokaci kike yi!!
Sannan meye na yunk’urin marin nata da kika yi?
Ina taimakarki tayi?
Kar ki kaini bango, ranki zai b’aci wallahi kinji dai na rantse!!.”
Ya fad’i hakan cikin tsananin b’acin rai sannan yayi wurgi da hannun nata, ya wuce ya k’arasa ya durk’usa a wajen, ya fara kokarin dafawa….
Kuka kawai yaji Huda ta saka dan haka da sauri ya sago ya kalle ta.
Cikin kukan tace
“Ya Arshaad da Allah fa na had’a ka, nace maka komai ya wuce amman still kak’i ka yarda ka hak’ura, itama Ya Jalilan ku barta kawai, ni na fahimci gaskiya, dan Allah ku daina , Al Qur’ani fa ba abun wasa bane ba..”
Tana gama fad’an haka ta juya ta haye sama da gudu,,tana kuka.
Mik’ewa Arshaad yayi ya dafa kanshi, ya kusan one minute a haka kafin ya juya yana kallon Sakina yace
“Kice mata nace idan cikin ya kai 5 ko 7 months in shaa Allah za aje ayi dna test, plss kar tace a’a,,for me.”
Yana gama fad’in haka bai jira amsar Sakina ba ya juya ya fice.
Haushin su ne ya hana Sakina ci gaba da zama a inuwa d’aya dasu, dan haka ta juya ta haye sama itama.
Da k’arfi Jalila ta sauk’e ajjiyar zuciya, bata gama dawowa dede ba taji Auwal ya fincikota da mugun k’arfi, cikin b’acin rai yace
“Wanne shirme da iskancine ya sa kika biyo shi in the first place??? Mahaukaciya mara kamun kai kawai!! Daga ji ance tazo a tafi ta shige mota ta biyo mutum zungui zungui. Wallahi yau da wani abun ya fito, toda da hannun nan nawa zan illataki, mahaukaciya kawai.”
Ya k’arashe maganar yana sakin ta sannan ya juya yayi hanyar waje.
Da sauri ta mik’e ta bishi…..
Ba k’aramin artabu suka sha ba a wajen ma, daga k’arshe dai ya hak’ura ya mik’ata gida, yanata faman zazzaga mata ruwan bala’i!
Daga nan yace “yayi grounding d’inta! Ko wajen umma kar ta yi gangancin tambayarshi
Daga yau babu inda zata sake fita har sai yayi sorting out ma kanshi solution!”
sannan yace “ko hanya tabi in dai ta hango Arshaad to ta chanja!
Don ya lura sam Arshaad d’in bai hak’ura ba, ita kuma wawuya ce, so kasancewar su tare is very dangerous for him.”
Ita dai Jalila da “to” kawai ta bishi amman a yanda take jin Arshaad a ranta ai ko labari taji ance zai bi ta waje to fa ita mai iya zuwa ta tsayane ta jira wucewarshi.
A gate d’in estate d’in ya tsaya yace “ta fita!”
Allah ya so ta mai gadin yaga motarshi kuma ya ganeta dan haka aka barta ta shige.
Ko da Aslam yazo, Hudan Sakina ta bawa ta kai masa ruwan karatun…
Dinner kam dama a k’oshe suke, gaba d’aya kunyar Arshaad take ji bataso su had’u, iyakar yadda Ya Jalila tayi ta acting ya ishi yasa ta gane gaskiya….ita sai yanzu ma take ganin shiriritarta da ta yarda da su!
A gefe guda kuma na zuciyar ta tausayin Jalilan take ji.
Yayinda gaba d’aya hankalinta kuma yau ya d’unguma ga son ganin Mama
dan har yau Ummu tak’i d’aukar wayarta, wayar Sakina ma ta daina amsawa!
Tanaso ta tambaya amman kuma bata son zuwa k’asan dan haka ta yiwa Abban message.
Ba a fi mintuna uku ba, taga reply dinshi kamar haka
“Ok, no problem, but let it be tomorrow.”
Taso zuwa yau d’in, amman ta tura
“Thanks Abba ❤️”
Kawai, ta mik’e tayi sallah..
Yau basu wani zauna hira sosai ba,,ta dai fad’awa Sakina halin Auwal tace “Don taga yanata kallonta kar yazo mata da shirme”
Dariyan takaici Sakinan tayi kafin tace ,
“First, kin dai san akwai wanda naki dating, right?
Second, ga abunda ya yiwa Jalila sannan ya k’ulla makirci wai Ya Arshaad ne.
And third, wallahi ni bana son irin waennann mazan kwata kwata yana yinsa bai yi min ba at first sight!”.
Ajiyar zuciya Hudan tayi kafin tace “Duk cikin su Ya Arshaad shi ya fita daban i don’t know why.”
Murmushi Sakina tayi kafin tace “d’an halak, gashi yana kiranki.”
Tayi maganan tana mik’a mata wayar ta dake a hannunta.
Karb’a tayi ta amsa
bayan sun gaisa ta fara son sake bashi hak’uri amman sam yak’i yarda, a cewarshi bata laifi a gurinshi……..
Tun Sakina najin hiran su sama sama har bacci ya kwasheta bata san lokacin da suka gamaba.
Ranar ansha soyayya abun ba a magana dan sai wajen 2 tukunna suka yi hanging up, suka kwanta.
Bata samu magana da Sakina ba, kamar yadda ta yanke zata nemi shawarar ta jiya,
sai da suka sauk’o yin breakfast…
Suna zuwa suka tarar ba kowa dan haka suna zama Huda tace
“Daman akwai maganan da nake ta so muyi in mun gama shiryawa”
“Ok, akan me?”
Sakina ta fad’a tana mai d’an juyowa ta bata dukkannin attention d’inta.”
A hankali Hudan tace
“Ya arshaad ne, daman already ya yiwa su Abba maganan!
So yanzu jiya yace, wai ya nake gani,,jiya sun yi magana da Dad wai sun tsaida in anzo saka rannan za asa two months ne ba wani lokaci za a dauka mai tsawo ba!”
“Woow”
Sakina tace tana d’an zaro idanuwanta, kafin tace
“Amma hakan bai yi wuri ba kuwa?”
Da sauri Huda tace “nima dai abunda na gani kenan!
Amman dana nuna mishi tun kafin ma In furta sai naga kamar bai ji dad’i ba.
Wai shima yana so ya tafi wani course, so kafin a juya sabon session yake son samamun admission sai muje chan ni Ina degree shi kuma yana course din, nashi.”
Dai dai nan suka ji sauk’owar Abba, dan haka
a hankali Sakina wadda duk jikinta yayi sanyi jin za a rabata da best frnd d’inta
tace
“Anjima ma ji me su Mama za suce, in munje.”
Cikin girmamawa suka gaisheshi ya amsa da kulawa yana ce musu “ai da sun fara kawai”
Sai da suka kammala ya kalli Hudan yace “ki cewa Arshaad idan ya dawo a office ya zo, ku zo tare Ina son ganin ku!”
Da “to” ta amsa, shi
kuma ya tambaya ko “akwai abinda suke buk’ata zai fita shima” a hankali tace “a’a” sukai yi mishi a dawo lafiya, ya wuce.
Gidan shiru, daga su sai masu aiki…
Tun lokacin da Abba ya fita take nazari a kanshi, kamar akwai abunda yake damunshi, dan har sai da ta yiwa Sakina maganar…
Murmushi Sakina tayi kafin tace “Hudan he just knew you fa, kuma yanzu ana shirin aurar da ke, dole yaji ba dad’i mana.”
Jikinta itama duk sai yayi sanyi, ba abunda yafi d’aga mata hankali, irin barin k’asar da Ya Arshaad yace za suyi, ta san aure dolene dama wata rana za tayi shi, but bata tab’a kawowa nan kusa ba, kuma ba a k’asar ta ba.
Haka dai ta wuni ranar sukuku kana ganinta tashi d’aya zaka fahimci akwai abinda yake damunta!
Ko da Sudais ya shigo musu shi da Sakina suka yi ta shirmen su tana jin su k’arshema kwanciya tayi ta lumshe idanunta kamar mai bacci
Sakina kanta k’arfin hali kawai take yi tana daurewa, dan bataso itama ta zama moody kamar Hudan ta sake d’aga mata hankali.
Kafin Magriba Arshaad d’in yace mata zai dawo, so tana gani 6 yayi ta mik’e ta isa parlourn Abba.
Knocking tayi aka bata izinin shiga, a hankali da sallama ta tura k’ofar ta shige ciki.
Aiki ta sameshi yanayi tuk’uru
ga takardu da computer a gabanshi takardun duk a zuzzube.
Suna had’a ido yayi murmushi ya ture kayan aikin gefe ya bata dukkannin attention d’inshi bayan ya nuna mata gefen shi inda yake zaune a 2 sitter yace “ta zauna.”
Bayan sun gaisa ba tare da b’ata lokaci ba yace mata “Dad d’in Arshaad jiya ya kirashi akan maganarsu .....
Yayi mata bayani dai dalla dalla kamar yadda Arshaad yayi mata jiya”
Kafin ya k’ara da cewa
“Kina son shi!
In ba kya sonshi ki fad’amin, ba zan bari ki auri wanda ba kya so ba!”
Just say watever it is that you feel towards him ko friendship ko love ko ma meye just feel free to tell me”
Ya k’arashe maganan yana kallonta da dukkan hankalinshi.
Shiruuu, tayi tana d’an jin kunyar cewa Abban tana son shi k’iri k’iri, dan haka tace
“Abba mun ma shirya mun daina fad’an, duk abunda kuka yanke dai dai ne.”
Ya fahimceta sarai amman yace “Kina sonshi kenan? Za ki aureshi?”
A hankali ta d’aga kanta, sannan tayi saurin rufe idonta da tafun hannunta.
Murmushi yayi,
bai ce komai ba, daga nan
d’akin ya d’au shiru.
A hankali Hudan ta aro jarumta kafin tace
“Daman Abba akwai wata magana danake ta so in rok’e ka”
Kallonta yayi kafin yace
“Un hm, Ina jinki”
A hankali tace “akan su Ummi ne
Abba dan Allah ka..”
Tun kafin ta k’arasa yace
“Maganan ya fita a hannuna tun tuni, so karki sake min maganan bana son ji.”
Ganin da tayi kamar ranshi ya b’aci ne yasa tace
“Sorry Abba”
A hankali ya sauk’e ajjiyar a zuciya kana yace
“It’s okay”
Dai dai nan suka ji ana knocking!
Izinin shigowa ya bada, hakan ya sa ya turo k’ofar a hankali ya shigo…
K’amshin turarenshi ne yasa ta ganeshi!
Me kuma ya zo yi?
Ta yiwa kanta tambayar a cikin ranta.
Bata gama wannan tunanin ba, ta ji muryar Arshaad yana sallama alamun tare suka shigo.
Rashin nutsuwar da takan tsinci kanta a ciki ne ya ziyarceta a take, lokaci guda!.
Akan kujerun suka nemi wajaje suka zazzauna.
Sai da suka gama gaisawa da Abban tukun ta juya ta gaidasu
A hankali Aslam yace
“Lafiya Alhamdulillah”
Arshaad kuma yana d’an murmushi ya d’aga mata gira d’aya yace “fine” a hankali.
Murmushi tayi itama ta maida kanta k’asa.
A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi kafin ya bud’e yace “Abba, Arshaad yace wai akwai meeting inzo kana son ganinmu”
Murmushi Abba wanda ya fahimci Arshaad d’in
yayi kafin yace
“Ni shi kad’ai na kira, sai dai kuma na lura har kunyar surukai ta fara shiga tsakaninmu tunda gashi sai da ya nemo d’an rakiya.”
Murmushi Arshaad d’in yayi ya sunkuyar da kanshi k’asa yana danna wayarshi dan gaskiya Abban ya fad’a sam bai san daliliba amman wata kunyarshi yake ji kwana biyun nan.
D’an murmushi kad’an Aslam d’in yayi yana mai sauk’e ajiyar zuciya.
A hankali Abba ya sauk’e ajiyar zuciya shima kafin yace
“Mun gama magana da Huda saura kai”
Har zai fara magana sai kuma ya juyo yace
“Daughter akwai wani abun da kike son sanar dani ko shikenan?”
A hankali tace “ba komai Abba duk na fad’a
kawai dai maganar zuwa wajen Mama ne, k’arfe nawa?”
Murmushi yayi yace “bayan isha zan kaiki ku shirya ko?”
Da “to” ta amsa tana murmushi kafin ya sallameta tayi musu sallama, ta wuce.
D’an gyaran murya Abba yayi kafin yace
“Arshaad!”
Jin yanda Abban ya kirasa yasa Arshaad d’in d’agowa yana kallonshi with full attention.
“No need na In tsaya tamabayar ka ko kana son Hudan tunda gashi duk ka fad’a mana ko? But inaso In sake tabbatarwa tunda kaga shi aure ba abun wasa bane, sannan kuma inaso ka tsayar da kanka da hankalinka waje guda kafin a gama magana, dan naji Dad yana cewa 2 months kawai za a saka bikin saboda tafiyarka!
So kaga kar aje abu ya taho kuma kuzo ku fara inda inda, bayan ba wannan lokacin.”
D’an tari kad’an Aslam yayi, kafin ya mik’e tsaye yace
“Abba Ina zuwa, i’m thirsty”
Bai jira jin me zasu ce ba ya fice daga parlourn ya sauk’a chaan k’asa.
Yana fita Abba ya ci gaba da cewa
“Sannan magana ta biyu!
Why do you hide Hudan away from me??
Meye shirinka?
Bana so ka b’oye min komai”
A hankali Arshaad ya lumshe shanyayyun Idanunshi, kafin ya bud’e su ya d’aura akan Abban sannan ya fara magana “Abba ba 2 months ba, ko nan da 2 days ne aka yanke ranar aurenmu, I’m ready in auri Hudan dan ita nake so, so na tsakani da Allah,
Ita nake son aura in rayu da ita har abada, na yanke wa kaina wannan decision d’in 3 years ago and I don’t think akwai rana d’aya dana tab’a jin tunanin sauya decision d’ina.
Magana ta biyu kuma
Tabbas na fahimci wacece