Showing 78001 words to 81000 words out of 109746 words

Chapter 27 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2947

ta tsaya Sakina tai mata shine, eye lining..da
kyar ta yadda ta ja mata liner black a saman ido d’an kad’an, sannan tasa mata brown kwalli.
Ko dan bata saba yin kwalliyar ba ga kuma gyaran jiki da ta sha! Ya sanya
Inka kalleta ba lalle ka iya d’auke idonka lokaci d’aya ba.
Ita kanta Sakina ta kasa yin shiru da ce mata ‘kin yi kyau’.
Akwai wani sirrin da idanun Hudan yake dashi wanda bata tab’a gani a idon kowa ba, gashi kuma yau yasha liner da brown kwalli.

Wata zazzafar gown ta d’auko mata black, da ta ji silver stones, sai kyalli take yi.
Tun daga k’irjinta zuwa k’asan mararta a tsuke ne daga nan kuma yayi wani irin bajewa har k’asa.
Wani fitinennan tauban Sakina tayi mata wanda ya yi mata mugun kyau, sannan ta sak’ala mata wasu arnen silver sark’a da y’an kunne masu shek’i
da abun hannunsu da zoben sai silver takalmi ta bata ta saka.
Sannan ta d’auki set d’in kaya kala biyu suma duk English Wears kasancewar bata da wasu native masu kyau.
Kafin tace
“muje suna jira.”
Har ta kai k’ofa taji shiru, juyowa tayi tana kallonta tace
“Me ne kuma?”

Hararar ta tayi tukun tace
“A haka kikeson in fita da wannan matsarsen rigar?”
Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e kafin tace
“Hudan ana jiranmu, ga vail d’in nan a jakar nan na had’a In muka sauk’a sai in baki”

Ba don taso ba tabi bayanta suka wuce, dan ta san tunda ta nace tou ba zata bata ba sai sun sauk’an.
Ita kuwa Sakina batayi niyyar batan bane, ta gama rayawa a ranta ‘ko hoto d’aya ne sai anyi musu da wannan shigar’ ita tayi tauban d’in amman ba k’aramin tafiya yayi da imanin ta ba, dan haka bata ga dalilin da zai sa ta bata mayafi ta d’aura akai ba.

Suna sauk’a suka tarar da mai hoton har ya k’araso da yaranshi dan haka
suka fara……
Da kyar Hudan ta yarda ta tsaya aka yi kala uku da d’aurin daga su ta ware tayi rolling abunta.
Styles Sakina ta dinga d’aukowa a insta tana nunawa..
Auwal ne yaje har gida ya d’aukowa Arshaad kaya shima kala biyu!
Suite kalar kwanduwar kwai dark da kuma black d’in jamfa na yadi
Suite d’in yayi using a last pics d’in da suka yi
Ita kuma riga da skirt kalan suite d’in nashi tayi roling da black vail
Sunyi masifar yin kyau!.

Sai bayan Magrib aka kammala.
Sun yi hoton har da su Sudais
sannan aka yi da Auwal da su Sudais
Abun sai ya zama kamar event a tsakaninsu su shidda
dan har drinks da snacks suka d’auko suka d’an cicci suka yi videos a wayoyinsu...........

Masu hoto suna tafiya Abba yana dawowa..A parlourn ya samesu har Auwal suna zaune suna kallo.
Dai da mazan suka yi isha tukun suka zagaya gidan Daddy dukkansu aka yi dinner daganan kowa ya kama gaban shi bayan Arshaad ya karb’a ruwan adduar su......

Akwai maganar da yake so suyi da Aslam
amman takaicinshi yake ji shiyasa kawai ya rabu da shi ya nufi gida.. D’azu babu yadda bai yi da shi akan ya kawo mishi kaya kala biyu ba za ai pre wedding amman k’iri k’iri Aslam d’in ya k’i!
K’arshema da yayi ta kiranshi k’in d’aukar wayar yayi.

A parlour ya ga Aaima ita kad’ai tana shan tea akan dining, har zai wuce ta kawai, sai kuma duk yaji ba dad’i
tausayinta ya lullub’e shi, dan
haka ya koma ya ja kujerar kusa da ita ya zauna.

Bata ce mishi komai ba ta ci gaba da kurb’an tea d’inta.

Sai da ya zauna tukun ya fahimci ashe kuka take yi!
Dafe kanshi yayi ya furzar da iska kafin yace
“Ok, I’m sorry!
Kin b’ata min rain ne d’azu sosai Aaima..
Ba zai yiu ki tsani Hudan haka ba!
Za a samu matsala..Hudan ta zame
miki dole!
Ki ajjiye duk issues d’inku da ita aside, ki manta ki yafe
She’s about to become my wife!
Kar ki zama silar rusa zumunci da raba kan y’ay’anmu da naki in the future..”

Murmushin takaici Aaima tayi
ta ajjiye cup d’in hannunta kafin tace
“Do you know what the funny thing Is?”
Bata jira jin mai zai ce ba, tace
“Ya Arshaad ban ma san za ka yi aure ba!
So i think ba ni ce zan zama silar raba zumunci ba! Kai ne!
Infact ka riga ma ka raba dan
wallahi ba k’aramin haushi na ji ba ba zan b’oye maka ba
Iya wannan banzatar dani d’in da kayi ya isa zumunci ya samu tangard’a!”

Cikin son fahimtar da ita yace
“Aaima, an saka date d’in a k’urarren lokaci
I have a lot to discuss with you, inaso In ganar dake abubuwa da dama kafin In sanar dake shiyasa kika ga ban fad’a miki ba!
Issues d’in are all tied up
In na gaya miki zan yi aure dole za ki buk’aci Mammy! anan ne kuma za a samu case, na sani.
But I was planning inje in d’auko ki a week b4 daga nan in miki bayani ta yanda zamu fi fahimtar juna..
Mu uku ne kawai Aaima
kece mace dan Allah kar
ki fara irin haka tun yanzu, please..”

Ajiyar zuciya ta sauk’e, kafin ta kalleshi eye to eye, babu alamun wasa ko tsoro tace
“Wallahi!! Muddin Hudan zaka aura to tsakanin mu ba zai yi kyau ba!.”
Tana gama fad’in hakan ta mik’e ta bar mishi wajen a fusace…

Sai da ta kai stairs tukunna ta juyo tace
“Ya Aslam bashi da lafiya,
Yana side d’insu ana k’ara masa ruwa.
Kaje ka kula da shi pls, shi kad’ai ne, ni kuma yak’i yarda In zauna da shi, sai amai yake yi.”
Har tayi gaba kuma sai ta sake juyowa tace
“If Hudan permits.”
Bata sake juyowa ba tayi sama abunta.

Ya dade a wajen, tukun ya mik’e ya je ya watsa ruwa ya sa pyjamas ya nufi gidan su Aslam d’in:

Direct d’akin sa ya wuce
bayan ya bawa Gwaggo Asabe ruwan adduar.


Akan gado ya ga cannula da bandage da alamun wadda aka saka mishi ce ya cire!
Yana shirin fara neman shi ya jiyo shi a toilet yanata shek’a amai.
Toilet d’in ya nufa ya tura k’ofar ya shiga..
Sai da gabanshi ya fad’i ganin yanda duk Aslam d’in ya fita daga haiyyacinshi cikin wuni guda tak!.

Taimaka mishi yayi suka fito bayan ya yi brush ya wanke fuskarshi.
Yana kwantar da shi ya d’auki waya ya kira Doc..
Bayan ya ajjiye wayar, cikin sanyin murya yaji Aslam d’in yace
“Yanzu fa Doc d’in ya tafi, wanne kuma ka kira?”

Banza Arshaad yayi da shi
kawai yaci gaba da had’a mishi tea d’in da ya fara.

After kamar 20min haka, Doc d’in suka shigo tare da Gwaggo Asabe….
Sai da ta sa baki tukunna ya yarda ya tsaya aka sake duba shi, dan shi already ya riga ya san me yake damunshi tun kafin zuwan first Doc d’in
kuma baya so Arshaad d’in ya sani…
Ba yadda ya iya shiyasa kawai ya kyalesu, bayan y’an gwaje gwaje Doc d’in ya tabbatar musu da ‘jininshi ne ya hau sai kuma fever mai zafi da ta ke damunshi.’

Gwaggo Asabe har da kukanta take ce mishi
“Jikin Mommyn fa yanzu da sauk’i Alhamdulillah
Gashi kusan satinshi biyun a gidan amman shiru bata yi komai ba! Ta warke sosai fa, ita abun har mamaki ma yake bata, amman in ta tuna yadda aka duk’ufa akan neman lafiyarta ta hanyar kad’aita Allah shi kad’ai da taimakon ayoyin shi, sai ta ga ba abun mamaki bane ba!”
K’arshema cewa tayi “ya taso suje ko da ta window ne ya lek’a ya ganta, in ba fad’a maka akai ba ba zaka tab’a yarda ma ta tab’a yin rashin lafiya ba! Har waya fa suke yi da Dad”.
Shiruu, kawai Aslam d’in yayi a zuciyar shi yana godewa Ubangiji, sannan yana adduar Allah ya kawo ranar da zata warke baki d’aya su zauna inuwa d’aya shi da ita…..

A d’akin suka zauna bayan Doc ya tafi, shi Aslam har haushi ma suka fara bashi dan sai kace wani jariri haka suka maidashi wai duk dan Doc yace kar a barshi da damuwa ko loneliness.
Sai wajajen 11 Arshaad ya k’arasa karatunshi shi da Aslam da Gwaggo Asabe tukun yayi musu sallama ya tafi bayan ya tabbatar Aslam din ya sha maganinshi.

Dariya Arshaad yake bawa Aslam, shi ala dole fushi yake yi dashi wai akan yak’i fad’a mishi damuwarshi dan
ko kallonsa ma baya yi
amman kuma shi yayi jinyar shi yanzu.



Arshaad, ya fito kenan a babban parlourn suka had’u da Jalila, yayi matuk’ar mamakin ganin yanda ta rame. Bai kula ta ba ya d’auke kai kawai ya yi wucewarshi, ga mamakinshi shi kawai yaga tasha gabanshi ta tsaya.

Tamke fuska yayi kafin ya tsareta da lumsassun dogayen idanuwanshi
cikin dakakkiyar murya yace
“Jalila!”

Jin yanda ya kirata, da yanayin data ganshi ya mugun tsoratata dan haka ta kasa magana ta kasa cewa komai
chaaan! Kuma sai
ta hau kame kame tana wasa da y’an yatsunta
“Em, Ya Arshaad wai dagaske Gwaggo Asabe take?”

“Da gaske take me?”

“Maganar aurenku kai da Huda…”
Sai kuma ta fashe da kuka.

Da mamaki yake kallonta
kafin yace
“Eh”
Kawai ya juya ya fita
dan ya san indai ya ci gaba da tsayuwa Inuwa d’aya da ita tou tabbas za a samu matsala!
Ya san babu kyau ka tsani d’an uwanka musulmi but he cant help it! Wallahi tunda yake a rayuwarshi bai tab’a jin
tsantsar tsagwaron tsana kalar wacce yake yi wa Jalila ba.

Da gudu tayi hanyar d’akin ta
tana zuwa ta dannawa Umma kira!
Ko gaisawa bata bari sun yi ba ta fara magana
“Umma, Huda aure zatayi!
Ya Arshaad zata aura.
Umma wallahi mutuwa zan yi in ya aureta
Umma dan Allah kiyi wani abun, wallahi ina sonshi.”

Cikin katseta Umma tace
“Dalla malama ki tsaya ki nutsu kiyi min magana yanda zan fahimceki”

Cikin kukan jalilan ta hau yi mata bayani tiryan tiryan akan
yadda taji Gwaggo Asabe
suna maganar auren ita da wata mai aiki satin baya daya wuce
data tambayeta kuma ta gasgata mata hakan
sannan yanzu ma Arshaad d’in ya sake tabbatar mata.

Cikin b’acin rai Umman tace
“Kece ai Jalila
da shegen son abunki!
Nace miki ki kawo kud’i kin k’i ki bayar ya kikeso in yi?
Babanku ma yanzu haka baya nan ya gudu saboda ba zai iya rayuwa ba Maryam ba!
Ga Ja’afar ba lafiya!
Ga Junaidu ya b’ata!
Matsalalo gasu nan burjik sunyi mana yawa
ke kuma kin matse bakin aljihu ya kike so inyi???.

Ni kaina sai na mutu dan bak’in ciki in dai Huda ta auri Arshaad d’innan ba ke kad’ai ba!
Haba dan Allah mana sai kace
su kad’ai Allah yake so??
Baban ta mai kud’i sannan ta auri mai kud’i!
Inaa, ba zai yiu ba
gaskiya!”
Umman ta k’arashe maganar
cikin tsananin tashin hankali.

Cikin kuka Jalila tace
“Umma yanzu meye abun yi?
Dan Allah karta aure min shi
wallahi Umma ina son Ya Arshaad
sosai.”

Ajiyar zuciya Umman ta sauk’e kafin tace
“Ki bani kud’i!
Ki turo kud’i!
Ki zuba mini ido kawai,
shine abun yi.”

A hankali Jalila ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“Tam shikenan,
Ta accnt d’inki ko?”.
“Eh”
Kawai Umman tace
saboda tsantsar tashin hankalin da take ciki
ba zai iya barinta tayi magana sosai ba.

“Tam” kawai Jalila tace
ta kashe wayar
daganan ta tura mata ragowar kud’in accnt d’inta
da ta ishi Auwal, ya tura mata da kyar..............



Bayan Arshaad ya tafi sun d’an tab’a hira tukunna Gwaggwo Asaben tace “itama bara taje ta bawa Mommy maganin nata ta sha ta shaafa dan yanzu ita take yi da kanta”
Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace
“Ka zo muje kaga jikin nata mana”.

Ahankali ya girgiza kai kafin yace “Gwaggo na san da sauk’i tunda gamu waje d’aya amman lafiya,
kuma kin ce tayi garau yanzu
to ai
Alhamdulillah!
Inaga ba sai na je ba, kar
muje a samu matsala.”

Shiruuu, Gwaggo tayi..
Ita har ga Allah so take Aslam d’in yaje ya ga Mommy watak’il In ya ga ta warke shima ya samu ya rage damuwar da ta hau kanshi.

Amman tunda taga baya so bara kawai ta kyaleshi.

Ganin dayayi kamar bata ji dad’in musun da yayi mata bane yasashi mik’ewa kafin yace
“muje to”

Murmushi ta saki tace
“Yauwa d’an albarka, muje.”

Itace a gaba shi a baya
Haka suka nufi saman ba don ranshi yana soba gashi k’irjinsa In banda dukan uku uku ba abunda yake yi.
Wutar parlourn a kashe suka tadda, suna k’ok’arin kunna flash d’in wayoyin su haske ya gauraye ko Ina!
Bata lura da shi ba tace
“Yanzun fa nake shirin kiranki na jiki yau duk shiru!
Sai kuma nace bara in yi wanka kafin ki zo, kin ga
banma ida shiga d’akin ba naji motsinki.”
Tana maganar tana tahowa garesu.

Aslam mutuwar tsaye yayi!
Dukda a cikin zuciyarsa hamdala yake yi na ganinta a hakan, amma kuma bayaso suyi ido biyu dan bai san ya zata kaya ba!
Hakan ne yasa shi fara ja da baya dan barin wajen
Ita kuma kamar ance ta d’ago karaf! Suka yi ido biyu da ita......

Ta k’uraa mishi idanu ko kiftawa bata yi
tana kallonshi kamar da mamaki akan fuskarta…

Lura da hakan da Gwaggo Asabe tayi ne wadda itama ba k’aramin firgice ta shiga ba ya sanya ta daure taje ta fara jan hannunta tana
“Muje ga tofin naki kisha In kin fito wankan sai ki shafa ko?”

A hankali suka ji Mommy tace
“Aslam!”
Aslam wanda already ya juya da niyyar tafiya har ya d’aga k’afar shi jin ta kira sunanshi ya sanyashi dakatawa ba tare da ya sauk’e k’afar shi ko ya juyo ba!
Sai da ta sake cewa
“Aslam”
Tukunna ya ajjiye k’afar ya juyo yana kallonta da idanuwanshi da suka rine lokaci guda!.

Dafe kanta tayi da k’arfi, ta runtse idanuwanta kamar mai son tuno wani abun…

Ganin haka yasa Gwaggo Asabe ta sake kamo ta kafin ta ce mata
“Muje ki huta dan Allah”
Sannnan ta baya ta yiwa Aslam d’in alamar ya tafi da hannunta.

A hankali Mommy ta bud’e idanunta tana sake kallonshi
kafin tace
“Asabe me ya faru da ni?
Kin ce nayi rashin lafiya
meye ne ya sameni?
Na shekara nawa?.
Kinga fa Aslam
kina ganin abunda nake gani kuwa?
Shekara ta nawa a kwance?
Dan Allah kimi.....”
Gigitacciyar rungumar da Aslam wanda ba suba tahowarshiba
yayi mata ne ya sanya ta kasa k’arasawa…
Tana shirin yin magana taji Gwaggwo Asabe ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi cikin kukan banda kalmar
“Alhamdulillah!”
Ba abunda take ta nanatawa.

Da kyar Mommy ta iya b’amb’aro Aslam daga jikinta,
a hankali da hawaye sharkaf akan fuskarta ta shafa fuskarshi wadda ta koma jajir kafin tace
“Loosing memory nayi ko?”
Ta fad’i hakan
tana mai fashewa da kuka.

Rasa wanda zai rarrashi wani akayi tsakanin ita da Gwaggo Asabe..
Aslam kam banda ajiyar zuciya ba abunda yake sauk’ewa!
Shi kanshi yau
so yake hawaye ya zubo ta idanunsa amman abun ya gagara!
A hankali ya cika mata hannunta dake cikin nashi
ya dan jaa da baya kafin ya seseta gabas ya durk’usa yayi sujjada!
Da sauri itama Gwaggwo Asabe tayi sujjjadar, ita kam
Mommy tsayawa tayi tana kallonsu tana hawaye da mamakin abunda ya sameta haka…
….Wani abun mamakin still shine yanda ta kasa tambayar inda Aslam d’in yake har sai da ya baiyyana a gabanta!
Wanne irin loosin memory tayi haka ita kam? Aslam wanda ta san shekarunshi basu wuce 12 ba shine yanzu haka wanda ta tabbatar yafi 30!
Daman tun kwanaki 7 da suka wuce tayi noticing yanda Gwaggo Asabe tayi aging da kuma ita ma kanta!
Mai ya faru?
Wanne irin ciwo tayi haka?
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Allahumma ajirni fi musibati…
Take ta maimaitawa
cike da rud’ani da alajabi
gaba d’aya kwanyarta ta cunkushe............


A hankali Aslam ya mik’e ya kama hannunta suka shiga d’akinta ya zaunar da ita kafin yace
“Ina yake miki ciwo, yanzun?”
Murmushi tayi ta shafa fuskarshi a hankali tace
“Ba ko ina”
Sai kuma ta sake fashewa da kuka.
Hugging d’inta kawai yayi yana tapping bayanta.
A hankali ya d’auko wayarshi, ya hau kiran Dad video call, bai damu da time ba.

D’auka Dad yayi suka gaisa yana tambayarshi “ya shirye shirye na bikin su Arshaad?”
A hankali Aslam
yace “Alhamdulillah”
Sai kuma ya gyara zamanshi ya matsa kusa da Mommy ya kamo hannunta cikin nashi
ya d’an kalleta yayi murmushi yana ganin yanda ta k’urawa Dad d’in ido, kafin ya juyo ya kalli Dad shima yace
“Alhamdulillah Dad..”
Bai ida rufe bakinshi ba, yaji Dad d’in ya saka kuka, cikin kukan shima yace
“Alhamdulillah!
Alhamdulillah!!
Alhamdulillah!!!”
Sannan yace “Aslam ganinan zuwa yanzun nan, in shaa Allah”
Da sauri Aslam d’in yace
“No dad, kabari sai gobe yanzu dar....”
Kit! Dad ya kashe wayar ba tare da ta tsaya jin maganar Aslam d’in ba.

Anan aslam ya zauna, ya rik’e mata hannu gam kamar ance za a kwace mishi ita!
Sai kallonta yake yana murmushi yana sauk’e ajiyar zuciya in yaji hakan bai mishi ba yasa hannu yai hugging d’inta.

Ita ma Gwaggo Asabe a daren ta kira Yaranta duk biyun ta fad’a musu halinda ake ciki,
murna a wajensu ba a magana, suka ce “in shaa Allah, za su tambaya.
Za su taho suma in shaa Allah.”

A haka Mommy ta sha addu’o’i ta shafa da hannu d’aya dan Aslam yak’i cikata, Gwaggo Asabe tana musu dariya tana kuka at the same time.


Ko cikakkiyar awa biyu Dad bai yi ba, sukaji tsayawar mota.

Aslam ne yace “Oh Dad, dana sani da ban fad’a mishi ba.
Waye ma ya d’auko shi a airport d’in sai Allah
tunda gashi bai kira ni ba.”

Murmushi Gwaggo w tayi kafin tace “ai ko kaine a matsayin shi na tabbatar sai ka zo”
Murmushi shima yayi kafin yace “Kuma fa hakane”

Cikin minti goma ya iso cikin d’akin!
Yadda ya gansu a zaune ne yasa hawayen da yake ta koma run yaga ya danne
suka samu nasarar zubowa.
A hankali ya k’araso ya had’asu waje guda ya rungume ..
Shi kuka Mommy da kanta ya d’aure da komai kuka Gwaggo Asabe ma kuka
Da kyar Aslam wanda duk ya fi su son yin kukan ma
ya samu ya lallashesu,
daga nan aka hau murna
k’arshe dai ba wanda ya runtsa a cikinsu har asuba.

Kafin gari ya gama wayewa kuwa, labari yaje kunnuwan kowa a estate d’in, har su Abba.

Daga masallaci Arshaad ya biyo Aslam suka zo tare dan ya ganewa idanuwanshi, ai kuwa shima har da kukan shi na tsananinfarin ciki.

Haka shima Auwal yazo da daddare tare da Daddy da Abba duk a b’oye kar e ya gansu.
Sun ji dad’in ganinta kuwa, sukayi barka suka tafi .

Mommy kuwa tunda aka bata labari sannan taga su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login