Showing 42001 words to 45000 words out of 109746 words

Chapter 15 - SO DA BURI Book 2 by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

2924

mutum biyu zasu iya using dan hatta kitchen biyu ne)
Sai d’ayar k’ofar gefen hagu ta d’an gefe kad’an na d’auke da 7 bedrooms da 4 parlourns.

Mai girman Abba ya d’auka
Daddy kuma ya nufi d’ayar k’ofar (side d’in mutum d’aya wanda bai kai na Abba ba).

Suna shiga Hudan ta kusan daskarewa…
Dukda gidan chan estate d’in shima yana da double height ceiling amman ko rabin wannan bai kai ba, ga wata mahaukaciyar chandelier da tunda take bata tab’a tunanin akwai irinta ba, wasu irin kwayayene da suke k’ok’arin makantar da ita tsabar haske a gidan!
Waiting parlour yana a ta gefe a cikin wani d’an glass door
kafin ka k’arasa shigowa makeken main parlourn k’asa wanda girman parlourn zai iya cin set d’in manya manyan kujeru 6 ko bakwai!
Gefen dining daban, sai
wata had’add’iyar matattakalar bene doguwa da zata kaika sama.
K’aramin Kitchen d’in na ata gefen waiting parlour kana iya hango cikin shi dan bangon half ne bai kai har chan sama ba
Main kitchen d’in kuma yana ta gefen dining
Amman shi rufaffiyar k’ofa babba gareshi.
Akwai wasu k’ofofin still a cikin parlourn wanda take da tabbacin d’akuna ne.


Sama suka yi gaba d’ayan su,
Parlour ne nan ma biyu
d’aya a gefen dama d’aya a hagu masu masifar kyau, dukda basu kai na k’asan girma ba saboda double height ceiling d’in da aka yanka ya cinye kusan 1/3 d’in saman amman suma sun had’u sosai ba a magana!
pop kam kamar ka kirashi ya amsa ta jikin bango ta ceiling hatta k’afar bene shima ba
a barshi ya huta ba.

Wata matattakalar suka sake bi suka hau chaan sama.
Suna hawa suka nufi side d’in su Sudais, d’akunan su da parlourn su yayi matuk’ar burgeta.
Sudais yanata murna Shuraim kuwa miskili bai ce komai ba
Sudais shi a shirmen shi ya d’auka har da Huda, dan haka ya hau tsarawa
‘Za su d’auki d’aki daya ita kuma ta d’auki d’aya, sannan ya cewa Abba “ai da anyi mata nata gadon pink ba kalar blue ba”…’

Dariya dukkansu suka yiwa shirmen shi, kafin Abba yace “a’a ita nata d’akin daban ne bara in kaita in dawo ko?”
Yana shirin fita yaji Shuraim yace
“Abba yaushe Ummin zata dawo?
Gramma tace za kaje ka d’auko ta”

A lokaci d’aya duk suka d’auke wuta..
Gaba d’aya duk sai Hudan taji ba dad’i, yadda taga Abba ya had’e rai ne yasa ta kasa cewa komai
“Bana son yawan tambaya!”
shine abunda yace daga nan ya fice daga d’akin.

Ganin haka yasa itama Hudan tayi musu sai anjima ta fice..
Tanata kallon parlourn nasu har ta fita, ta jaa musu k’ofa ta rufe.

Sai a sannan Abba yace “tazo suje ya kaita d’akinta” yana mai kama hannunta.
A gefen parlourn da suke a ciki suka shiga wani dogon corridor, k’ofar tana achan k’arshe suna isa ya sa hannu ya zura key ya murza k’ofar ta bud’u! Sanna ya jaa hannunta suka shige ciki.

Set d’in kujeru biyu ne
Peach da black, sai wani d’an k’aramin dining mai mugun kayau mai d’auke da kujeru biyu a gefe, da wata had’add’iyar tv babba mai curve.

Wucewa sukayi suka shiga bedroom a nan ta sake shiga mamaki, gadon nata pink ne mai rumfa da net a jiki (princess tent) ga wasu had’add’un resting da coffee chairs guda bibbbiyu a kusa da tvn bedroom d’in, fad’ar had’uwar d’akin kawai sai wanda ya gani! Kawai.

Still toilet d’inta ya nufa da ita don ya nuna mata…
Ta closet suka bi kafin su isa cikin toilet d’in
A nan kuwa ta saki baki, wajen wanka har uku shower da wani had’add’en jacuzzi, sai kuma wani makeken bathtub da mutum hud’u ma za su iya shiga su kwanta kamar gado
da
Showers a jikinshi ta ko ina.
Ba abunda yafi bata mamaki irin wutan pop da take gani na sama, da taga yana ratsowa ta k’asan toilet d’in toilet d’in ta ko wanne angle.

Bata gana dawowa dede ba ,
taji Abba yana cewa
“Duk abunda bai yi miki ba ki fad’a sai a chanja! Munata sauri ba a samu anyi komai a nutse ba, so if you need anything just say it sai a chanja miki ko a siyo, an d’an zab’a miki kad’an jiya
kayan suna mota mostly abaya ne da shoes da sauran y’an abubuwa, zan kawo miki tab zuwa anjima, sai kiyi shopping duk abunda kike buk’ata, in kuma a furnishing akwai abunda kikeso ki fad’a shima sai a kawo.”

Ita dai mamakine ma ya hanata yin magana, wai
A nan d’in amman still ana tambayanta ko akwai wani abun da takeso a kawo!

Girgiza kai kawai tayi, kafin tace
“Abba na gode komai yayi Allah ya k’ara Arzik’i. “

A hankali ya dafa kanta yana mai jin tsananin kaunar y’ar tashi tana ratsa ko Ina na jikinshi sannan ga tsananin tausayinta da ya hanashi sukuni!
Ji yake kamar yaje ya kama Usman yayita dukanshi har sai yaga baya numfashi tukunna ya kyaleshi!
Jiya yanda yaga rana haka yaga dare tsabar bak’in ciki…
Jin yadda zuciyarshi ta fara tafarfasa ne yasa ya kawar da tunanin yace
“Ki huta bara a kawo miki tab d’in da kayan, anyi order abinci shima na san kafin ki gama freshining up ya zama ready sai ki sauk’o muci ko?”

D’aga mishi kai kawai tayi ta kasa d’ago kanta, saboda kwallar da ta tarar mata!
Dan
tana ganin inda aka kawota a matsayin mallakinta Mama ce kawai ta fad’o mata……

A tare suka fito daga toilet d’in suka shigo d’aki.

Ganin Abba yana shirin fita yasa tunanin ta ya katse tayi saurin cewa
“Abba”

Juyowa yayi yana kallon ta.
A hankali ta k’arasa wajen da yake sanna tace
“Dan Allah Mama, mun yi waya da Sakina tace min Maman tana asibiti tun shekaran jiya”ta k’are maganan hawaye na zubowa daga idanunta.

A hankali ya kama hannunta suka k’arasa bakin gadon suka zauna sannan yace
“Zan kaiki wajenta anjima da daddare.
Ki daina kuka”
Da sauri tasa tafin hannunta tana share hawayen duka biyu.

Kallonta yayi tukunna yaci gaba
“Amman idan kinje, inaso ki yi promising d’ina zaki dawo, 30 minutes kawai za kiyi, zan
jiraki a mota!
Ku gaisa ki dubata daganan kice musu kina zuwa, in
kin fito sai mu dawo.
And karkice musu ni na kawoki”.

Da sauri ta d’ago ta kalleshi kafin tace
“To ai kamar na yaudaresu ne idan nayi hakan, kuma Mama ba zata ji dad’i ba.”

Mik’ewa yayi kafin yace
“Shine ni kuma zaki yaudareni ki tafi kik’i dawowa ko?”

Kuka ta fashe da shi….saboda daman ta san ko da ace ta yarda zata dawo d’in su Mama ba za su barta ba!.

A hankali yace “Hudan nima mahaifinkine kamar Maman ki, na san ba lalle ki fahimci komai ba, amman inaso ki san cewa ‘ban tab’a k’in ki ba’ Yadda Mahaifiyarki take sonki nima haka nake sonki, kina gani a gabanki na hukunta waenda sukayi nasarar raba ni dake!.
Ba zan tab’a yarda in barki ki koma gidan da kika taso ba, dan duk halin da kike ciki a gidan na sani.
Idan kin yarda kullum idan kina so to za kije ki dinga duba Mamaki, amman Hudan ba zan sake bari kiyi nesa dani ba..
I want to take care of you
Make it up to you
Make you forget all the sufferings that you go through.
Amman
hakan ba zai tab’a faruwa ba, sai da had’in kanki! Ba zan
b’oye miki ba har ga Allah banji dad’in yanda kike yi mini ba kwata kwata Huda, it’s like kamar ma bakya farin ciki da ganina, komai ke kawai Mamanki!
Ko maganan 10 minutes ban tab’a yi da ke ba!
Yanzu ma kalli yadda kike yi
min kukan in maidake wajen ta kamar irin na satoki d’innan?”
Ya k’arashe maganar a hankali.

Gaba d’aya Hudan sai taji jikinta yayi sanyi,
tabbas bata kyauta ba! Ya kamata ta nuna mishi shima Mahaifinta ne tunda gashi ata dalilinta har gidansu ya bari da shi da d’an uwansa don kawai ya zauna a tare da ita….
Tunaninta ne ya katse jin yana cewa
“I’m sorry Hudan dan unless you promise me ba zan tab’a barinki ki je ki ganta ba.”

Shiruu, d’akin ya d’auka kafin yaji tace
“Tam”.

Kallonta yake yi, kamar zai ce mata wani abun kuma kawai sai ya juya ya fita.

Kamar yadda ya fad’a haka aka kawo mata kayan da ya ambata..
Ita dai Hudan mamaki ta shiga yi dan bata ga kuma abun k’ari ba anan, komai akwai hatta inner wears sai dai kawai kamar ba za suyi mata ba, dan haka ta d’au tab d’in ta hau shopping…
Sai da ta hau d’in kuwa tukunna tayita gannin abubuwa dan haka ta zazzab’a, bayan ta gama ta rufe ta ajjiye.

Tana idar da sallar Magrib ta sauk’a k’asan kamar yadda Abban yace mata.

Bata samu kowa ba, amman dai ga uban abinci nan shak’e a kan dining d’in
wajen kala nawa..
Ga kuma wata maid cikin uniform sai kai komo take yi tsakanin kitchen da dining d’in tana jera su plates.
Bata yi minti uku a zaune ba, suka shigo daga masallaci…
Su Sudais ne suka fara shigowa, Sudais yana ta tsallen tsallenshi, Shuraim kuwa ya mazee, kallonsu take tana mamakin kamanninsu dan ita kam miskilancin Shuraim ne kawai yake sawa take iya gane su..
Tana murmushi tanata kallonsu tana jin tsananin k’aunarsu a ranta
su Abba ma suka shigo dukkansu, har a Auwal wanda Daddy ya matsawa akan dole sai yazo sun gaisa da cousin d’inshi! Sai kumbure kumbure yake yi, ba wanda yabi ta kanshi haka nan suka shigo abunsu ana d’an tab’a hira kowa yana fara’a banda shi.

Suna shigowa da Daddy suka fara had’a ido dan haka ya yafitota da hannu.

A hankali cikin nutsuwarta ta nufi dogon dining d’in mai kujeru kusan ashirin
inda taga sun nufa
kamar an tsamota a ruwa a haka ta k’arasa wajen,
Abba ne da kansa ya jaa mata kujera ta zauna, ita har kunya take ji yadda ake wani lallab’a ta ana janta a jiki musamman ma Abba yadda yi mata kamar ya goya ta yayita zagaye garin da ita.

Cikin ladabi ta shiga gaidasu suka amsa, su Aslam kuma tayi musu jimla tace “ina wuninku”
Aslam ne kawai ya amsa mata,
a hankali ta d’ago ta kalle setin da Arshaad yake taga ya wani had’e rai ya d’auke kai ko inda take bashi da niyyar kalla ma!
Nan kuwa ta k’ule, tana mamakin shi, a ranta tace “tabarmar kunya yake son nad’ewa da bori!”

A take ta d’auke kanta itama bata sake kallonshi ba, tana jin haushi da wani tuk’uk’in kishin dake sake taso mata.

Tana cikin wannan tunanin taji Daddy yace,
“Sorry dota mun barki ke kad’ai ko?
Za kini shiru kam, gashi Aaima na school, ya kamata a nema miki Abokiyar hira gaskiya!in ba haka ba bazaki ji dad’in zaman ba kwata kwata
tunda su Sudais suma islamiyyarsu da boko a had’ene sai pass 5 suke dawowa.”

Da sauri cikin tarar numfashinsa Auwal yace
“ai daman da ace Ummi tana nan ba a kaita cell ba to da zata ji dad’in zama sosai, gashi Gwoggwo Asaben ma da naga kamar sun d’an saba itama ta saka an baro inda take!
Dole ta sha zaman shiru kuwa ai!.”

Dakatawa Abba yayi da zuba mata abincin da yake yi ya rik’e serving spoon d’in kawai still yana kallon plate d’in!
Yana mamakin Auwal!!
Wato rashin kunyar tashi yau ta hauro kanshi kenan, a gabanshi haka yake zuba mishi magana…..
Yana shirin yin magana yaga Daddy ya taso ya nufi Auwal d’in a zuciye, da sauri Abba ya mik’e ya rik’e shi haka ma Aslam ya mik’e yana cewa
“Daddy dan Allah kayi hak’uri ka kyaleshi.”
Arshaad kuwa ko motsi bai yi ba dan shi kam tasa kad’ai
ma ta isheshi, ba k’aramin k’ok’ari yake ba wajen share Hudan da yake yi, gashi tunda ya zauna yake d’an satar kallonta amman yaga kamar ma ko inda yake bata son kalla!.

Cikin fushi Daddy yace
“Dan uban ka iskanci naka yau a kanmu zai k’are?
Auwal wallahi zan yi mugun sab’a maka fa!!”

Cikin katseshi Abba yace “ya isa haka Daddy ka kyaleshi kawai! Dan Allah”

Cikin rashin jin dad’i Aslam ya cewa Auwal d’in “you can leave, tunda ka ganta gashi har kun gaisa ma.”

A fusace Auwal ya kalleshi, yana shirin yin magana Daddy ya daka mishi tsawa yace
“Get out akace!! Stupid boy kawai!!!”

Fuu!! haka ya tashi ya fita kamar zai tashi sama.

Daddy da kyar ya koma wajen zaman shi ya zauna gaba d’aya guiwanshi a sace! Ya so ace a kusa da Auwal ya zauna yau da sai ya sauya mishi kamanni ya nuna mishi still da ragowar k’arfinsa shima har yanzun, dan yaga alamun Auwal d’in ya kawo k’arfin da yawa shiyasanya yakejin kanshi a sama kamar yafi kowa!.

To dai dinner d’in haka ta wakana babu dad’i,,kowa da abunda yake damun ranshi.

Sai wajen 9 Aslam da Arshaad suka yi musu sallama suka tafi, bayan an yanke yin wata sauk’ar gobe amman sai dare za a kammala,
kowa zai yi izu biyu bayan sallar farilla sai su tafi da ruwan addu’ar a shafa mata .


Suna fita Abba ma yace mata “ta d’auko hijabinta ya kaita ta duba Mama”
Murna a wajen Hudan ba a magana dan da gudu ta haye benayen, bata yi minti uku a saman ba ta sauk’o sanye da hijab har k’asa wanda ta gani a cikin kayan da aka bata.

Ya lura da yadda jikinta har karkarwa yake yi, shiyasa bai b’ata mata lokaci ba yace “suje”.
Da sassarfa ta shige motar.
Shi dai Abba kallonta kawai yake yi, tabbas Hudan da shi take kama komai da komai amma idan tana wani abun sai ya dinga ganinta kamar Maryam!!!
Wani d’an murmushi ne ya sub’uce mishi, a hankali cikin sanyin jiki ya murza key ya tada motar ya nufi gate.

Masu gadin gidanjensu na chan estate su suka d’auko suka taho dasu..
Suna Isa gate d’ayan ya ajjiye rediyonshi a kan dogon bencin da suke zaune su wajen biyar harda driver da mai wankinsu da gyaran fulawar, yaje ya bud’e musu makeken gate d’in, suka fice.

Tunda suka fita Huda ta kasa sukuni, tsabar zumud’i, gani takeyi kamar Abba baya gudu, har d’an tasowa take yi ta d’an lek’a gaban titin ta gaban glass d’in motar..
Dariya ta bashi sosai dan haka yace “Gani kike kamar bana gudu ko?”
Ya fad’a yana dariya sannan ya k’arawa motar wuta…
Itama murmurshin tayi ta koma ta zauna da kyau a mazaunin ta.

Tafiyar minti ashirin ce ta kaisu AKTH emergency, dan ma sun d’an tarar da go slow a hanya.

Tana shirin fita taji yace
“You promised Hudan, right?”

A hankali ta d’aga mishi kai, sannan tace
“Na gode sosai Abba”
sannan ta fita.

Da kyar security suka barta ta shiga bayan tayi ta nacin ce mishi Mamanta ne a kwance, Allah ya taimaketa, wanda yake gadi ne a wajen ranar da suka kawota ita da Aslam, kuma d’azu tabbas yaga Maman nata an fito da ita tana d’an zagaye, shiyasa ma ya barta ta shiga, don ya tunata tun ranar da suka zo ita tana kuka shi kuma yanata mamakin had’uwar Yarinyar, hakanan yaketa ganin hoton fuskarta a zuciyarshi amman ya san ko hauka yake ba zai ma yi tunanin tunkarar ta ba.


Dube dube ta hau yi bayan ta shiga, da kyar da sid’in goshi ta hango su…
Mama da Ummu a kan gadon a zaune suna magana da alamun mai matuk’ar mahimmanci ce sai Sakina ita kuma a gefe kan kujerar mai jinya da waya a hannunta.


BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
41

Basu ga tahowarta ba, kawai suka ga an afka kan Mama da gudu an rungumeta!
Kukan da ta fashe dashi ne yasa suka gane itance, da sauri Sakina ta d’ago ta, ai
kuwa tana ganinta tayi hugging d’inta tana dariya.

Ummu itama murna kamar tayi me, Mama kuwa ba a magana.

Ummu ce ta zare Hudan daga jikin Sakina sannan ta d’an muskuta ta ajjiyeta a tsakiyar su ita da Mama.
A hankali Mama tasa hannu ta shafa fuskarta tana hawaye, da sauri itama Hudan ta goge mata hawayen tace “ki bar kuka Mama, i missed you so much, kwana biyun nan ji nayi kamar shekara wallahi”
Ta fad’a tana sakin wani kukan, sannan ta kwanta jikin Mama.

Sakina ce ta d’aka mata duka a cinya kafin tace “dalla Malama d’agata, kin wani zo sai kuka kike yiwa mutane salon ki karya mana zuciya muma mu biye ki! To Mama dai ance a daina sakata a damuwa dan haka sai kiyi k’ok’arin tashi ki ware garau ki bar wannan tab’arar.”

Da sauri ta d’ago tana goge hawayen da suka k’i tsayawa, da kyar kuwa ta tsaidasu, ta d’an harari Sakina tana murmushi
sannan juya tace “ina wuni Mama, ya jikin ki?”

Da murmushi Maman tace
“Alhamdulillah”

Sannan Huda ta juya ta gaida Ummu, wadda itama ta amsa mata cikin kulawa
sannan tace “ya mutanen gidan naku?”
A hankali Huda tayi k’asa da kanta tace
“Alhamdulillah”

Sakina ce tace “a estate d’in kike? Family house d’in nasu kamar estate ne kowa da kowa ko?”

Numfashi Hudan ta fesar tukun tace “Eh, nan aka kaini da farko, amman yanzu dani da Abba da Daddy da Ya Auwal mun tashi mun koma wani gida a baya.
Saboda Granpa yace ‘Abba sai dai ya zab’a, ko ni ko su!’.”

Cikin mutuwar jiki Sakina tace
“Shine ya zab’e ki kuka tashi?”

Da “eh” ta amsa, kafin tace “Har da d’an uwanshi ‘Daddy’ shima muka tashi, sun yi fad’a sosai jiya da Granpa d’in.”
Tana shirin sake yin magana Mama tace
“Kuka tashi as in how??
To ai yayi ta banza ne, dan ke kam kin zo kenan!!
Ya aka yi kika fito? D’azu su Kaka suke gaya mana kalar rashin kunyar da yayi musu ai!
Yanzu haka takardun shiga kotu ake had’awa!…”

Cikin rashin jin dad’i Ummu tace “Mama dan Allah ki daina biyewa su Abba Modu kina k’ara tunzurasu!
Kina ji fa bawan Allahn nan har gidansu ya bari, saboda ita!.

Ko fa anje kotun nan na fad’a miki bamu da nasara saboda
kamar yadda Abba Madun yace d’an uwanshi( Daddy) ya fad’a musu d’azu ‘ko a iya case d’in Baba aka tsaya dole a bashi Hudan!!’
Ballantana kuma idan aka duba yanayin standard of living! Shi (Abba) yana da aikin da zai iya kula da ita ke kuma.....”
Shiru Ummu tayi ta kasa k’arasawa ganin yanda Maman ta kafeta da idanuwa.
Cikin jan numfashi Maman tace “Ki k’arasa mana! Ni kuma bani da aikin yi, bani da komai ko?.”
Sai kuma tace
“Bari kiji idan su sun yi amfani da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login