Showing 24001 words to 27000 words out of 85584 words

Chapter 9 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf

27 Jul 2025

1499

bud'e
idanun nata ta ce idan ba kada ra'ayi events d'in zan yi magana sai a fasa Yalla6ai.
Ta k'arasa magana tana kallon shi.
"Ya d'an shafo gashin kansa yana ta6e baki ya ce uhm....a'a kuyi kayanku dama ku mata ba'a
rabaku da bidi'a.
Tayi murmushi kawai ta rausayarda kanta gefe, kafin tadawo da ganinta akanshi ta ce hope za
kayi k'ok'ari kayi attending events din ko?"
Yalwatattacen murmushi mai narkarda zuciya yasaki, yana kallon kwayar idonta wani yarrr.....taji
yayin da sanyi ya ziyarce sassan jikinta batasan sanda ta lumsashe idanunta ba.
Cikin sanyi murya ya furta ya na iya dole na zo, kada nasake wani laifi saboda na fahimci kallon
mai laifi ki ke min.
A hankali tayi 'yar siriryar dariya mai ban sha'awa.
"Ya d'an gyara zamanshi yana kallon cikin idanuwanta ya ce kin ji sabon canji da aka samu
yanzu anan za ki fara zama kafin ki tare a Abuja.
Yalwatattace murmushi tayi kafin ta ce ni wallahi hakan ba k'aramin dad'i ya yi min ba.
Ta k'arasa magana tana sunne fuska.
Uhm....ya fa'da had'e da kallon tsakiyar idanunta ya ce dole ya yi miki dad'i saboda ba ki gaji
da cinyewa Abba tuwo ba.
Sosai maganar tashi tabata dariya ai kuwa ta dara har kana ji sautin fitar dariyar ta, ta.
Yadda take dariya ba k'aramin burgeshi ta yi ba har baisan lokaci da ya shagala da kallonta ba,
jikinta ya bata ana kallonta hakan yasa ta mayarda ganinta akanshi.
"Gani ta fahimci yana kallonta yasa ya waiyace ya mik'e da sauri yana kallon wrist watch da
ke daure a tsintsiyar hannunshi, yana mai cewa za mu wuce saboda yau zamu koma Abuja sai
ranar da za ku fara programs d'inku zan iso.
"Mik'ewa tayi fuskarta cike da murmushi ta ce Allah ya kaimu, ya Kuma kai ku lafiya ka
gaidamin da su mommy.
"Sai da ya nufi k'ofar fita sannan ya ce Amin!
Bayanshi tabi parking lot ta hango Jamal da Fadila, suna fira abinsu yadda yake tafiyarshi ta
k'assaita yasa har ta ci mishi suna tafiya side by side sosai suka dace da juna.
Suna shiri tafiya motar Barrister Z ta danno kai, cikin sanyi murya mai d'and'ano gaske,
Barrister A ta ce yalla6ai d'an tsaya ku gaisa da best friend d'ina Barrister Zarah.
Cak.....ya tsaya har Zarah ta k'araso wacce tun kafin ta iso take zuba murmushi, ta ce
sannunku!
Jamal ne ya amsa mata da yauwa Barrister ya hak'uri da Jama'a.
"Alhamdulillah!
Ashe na taki sa'a yau dai gani ga angon namu mai tsada ai na dauka sai na rubuta requested
letter zan samu ganinka.

"Sosa keyarshi ya yi yana murmushi kafin ya ce laifin k'awarki ne da bata dauke ni ta kaini
gidanki na kwashi gaisuwa ba.
Lokaci d'aya dukkaninsu suka yi dariya sannan suka gaisa fira suka d'an ta6a, daga bisani
suka yi sallama.
Bayan sun wuce s d'akin barrister A suka yi direct, nan suka bud'e sabuwar fira duk dai akan
Aliyu ne, Barrister Z da Fadila sai shawara suke bata, yadda za ta sami matsugunni a zuciyarshi
sosai tayi na'am da shawarar tasu.
***---****---****---***
*ABUJA*

Momma wacce abin duniya ya taro ya yi mata yawa, tarasa inda zata tsoma ranta taji sauki ta
kira Jarumi ko da wata mafita daga gareshi, sai ma lullu6eta da fad'anshi na raini wayo da ya yi
har yana had'awa da yi mata barazana mai firgitarwa, shiyasa tak'ara tsundumawa damuwa fiye
da ta farko ga kuma Daddy ya ce su had'a kayansu ita da yara gobe zasu wuce Yola. "Dole bata da za6i ta shiga had'a abubuwan da za tayi amfani da su, ita kanta tasan ba abu
mai yuwa bane ayi shagulgulan bikinan ba uwar ango, dole ta rarrashi zuciyarta ta danne
abinda takeji tashiga jama'a ayi da ita muddin bataso jama'ar duniya su saka alamar tambaya
akanta.
Washe gari jirgin safe suka biyo zuwa Yola.
"Girls d'inta sai murna da annashawa suke, bros d'insu zai yi aure zai kawo musu sister in law,
afakace momma take danna musu harara.
"Daga Airports gidansu suka wuce wanda uncle suraj ne ya yi picking d'insu.
Ta 6angare gidansu Barrister A shirye-shirye suke ba kama hannun yaro tuni 'yan uwa da
abokan arziki na nesa da na kusa sun fara cika gida, gani yadda gidan yafara haltsunewa yasa
barrister A da k'awayenta komawa gidan Barrister Z a can suke nasu shirye-shirye.
***---****---****
_RANA BATA K'ARYA_

musu iya magana suka ce saidai uwar d'iya taji kunya, daren yau da misali k'arfe 9:00pm za'a yi
Fulani night tun wayewar gari ake yi wa barrister A gyaran jiki daga ciki har da k'umshi na zane
lalle baki da ja, abinka da farar fata lalle ya yi dass....a fatar hannunta da k'afafunta duk wannan
shirye-shirye da suke hankalin barrister A atashe yake, sakamakon rashin jin d'uriyar ango tun
daga ranar da ya zo ko a waya bai kirata ba.
Sai ma ita ce ta kirashi sakamakon alert na mak'udan kudad'e da ta gani daga gareshi, kiran
nata ma k'in d'agawa ya yi sai d'an guntun text da ya turo mata I'm busy I'll call you later, bai
kuma kirata ba hakan ba k'aramin kada mata anta jikinta ya yi ba, har yamma lis bata ji daga
Aliyu ba zai zo ko ba zai zo ba, sosai tasha jinin jikinta.
Kasa hak'uri tayi taja Barrister Z agefen ta kora mata bayanin damuwarta, shiru Barrister Z tayi
kafin ta ce ko za mu kirashi ne da sauri Barrister A ta girgiza kai, ba za mu kirashi ba saboda zai
dauka kamar na damu da shi ne.
Ya zo ko kar zo duk uwarsu d'aya ubansu d'aya awurina duk irin zaman da ya tanada mana shi

za muyi, koda sonshi zai yi ajalina ba zan ta6a zubarda ajina na bishi ba.
Karki ce haka Minal komai na duniya a hankali ake binshi sai ka ga ka ci ribar abin.
Cewar barrister Z.

"Ba za ki gane ba Zarah duk aure da aka gina shi ba soyyayya dama hakan zai faru.
murmushi barrister Z tayi ta kuma rik'o hannun barrister A, karki matsantawa kanki da yawa
bebs Allah ya na tare da mu, insha Allah komai zai tafi yadda mu ka tsara.
Nodding head kawai barrister A ta yi.

Misali k'arfe 8:30pm amarya ta sha makeover cikin kayan Fulani na sak'i royal blue in colour, ba
k'aramin kyau kayan suka yi mata ba musanmman yadda wuyanta ya sha sark'a tsakiya na
duwatsu masu launi dabam-dabam sosai ta fito bafullatana.
Yayin da k'awayeta su ma sun had'e cikin kayan Fulani saidai nasu farare ne.
Tuni motoci suka fara daukar mutane zuwa hall d'in da za'a yi events d'in.
Har zuwa lokaci barrister A bata ji daga Aliyu ba, sai k'ok'arin danne abin take a ranta saboda
bata so mutane su farga su gano halin da take ciki.


_Fans ba yawa Just to manage_


Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:55 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*

*16*

Daga ita sai fadila ne a cikin mota har suka iso hotel d'in zuciyarta a cakud'e, direba nayi
parking k'awayeta suka lullu6e motar.
lokaci da take k'ok'arin fitowa daga mota barrister Z ta kutso ta matsa daf da ita ta rad'a mata,
Aliyu yafi almost 10 minutes a mota yana jiran zuwanki.
"Ajiyar zuciya ta sauke wani irin dad'i ya ziyarceta, tana gama fitowa Aliyu ya fito daga nashi
mota sanye cikin tsadaddiyar shadda fara tass....kanshi sanye da hula zanna bukar, lokaci da
suka had'a idanu ba k'aramin kyau ya yi mata ba.
Yayin da shi ma yake yaba tsan-tsa kyau da ta yi.
"D'an siriri murmushi ya saki mata, ta mayar mishi da martani har da k'arin lumshe idanu.
Saboda murmushi nashi ba k'aramin awon gaba da ruhinta ya yi ba.
Ga mamakinta ya na k'arasowa kusa da ita ya rik'on palm d'inta cikin nashi, sai kuma ta
kawarda mamakin nata sakamako tunawa da ta yi Aliyu wayayye ne ya kuma wadatu da ilmin
zamani, don ya rik'o tafin hannunta baya nufi komai a wurinshi.

"Suna shiga hall Siblings sisters d'inshi suka mik'e suka nufo su, sosai Barrister A ta burge su
musanmman Meena da ta k'asa 6oyewa saida ta furta ta hanyar cewa wow....tubarakallah
masha Allah you're so beautiful sister in law.
Kalamanta ya sa barrister A ta gano sister din Aliyu ce ta yi mata murmushi had'e da furta
thanks!
You're highly welcome.
Cewar Meena.
Wurin da aka tanada domin su suka zauna aka soma gabartada da programs d'in, anyi rawa an
kuma zuba naira ba kad'an ba sai around 12:30am aka tashi kamar yadda suka shiga hall rik'e
da hannu juna haka suka fito har mota ya rakata, duk wanda ya ga yadda yake bata kulawa zai
dauka akwai soyayya mai k'arfin gaske atsakaninsu. Da kanshi ya bud'e mata k'ofar mota tana murmushi ta zauna ta dube shi cike da kulawa ta ce
"Good night!
Saida ya haskata da tsadadde murmushinsa sannan ya amsa da "Good night nd have a nice
dream.
Yatsunta ta guda biyu ta d'aga mishi had'e da furta bye da haka direba ja mota suka tafi, ya kalli
Jamal da ke tsaye a gefe yana kallonshi ya ce mu tafi ko?"
Suna tafiya Jamal ya ce gaskiya abokina ka yi dace da mata kyakyawar gaske ba ko shakka za
ku haifa mana kyawawan yara.
Aliyu ya yi dariya marar sauti ya ce ni fa har yanzu ban ji son barrister a zuciyata ba, ga kuwa
zai yi matuk'ar wahala ku sami yara.

"Jamal ya ja tsaki mtsss.....kafin ya ce wai kai wane irin tintirin d'an iska ne me zuciyar dutse?"
Ba zaka gane ba Jamal shi so ba mutum yake dasa shi a zuciya ba, Allah ne yake jarabta d'an
Adam da shi.
Murmushi Jamal ya yi ya ce zancenka haka yake, amma akwai sakawa rai idan har ka sakawa
ranka soyayyar barrister ba za'a dauki dogon lokaci za ka afka a sonta, ko don kyau halinta.
"Girgiza kai kawai Aliyu ya yi sakamakon yadda ya fahimci duk abin da zai fad'a ba lalle bane
abokin nashi ya fahimce shi ba shiyasa ya ja bakinshi ya tsuke.
***---****---****
*WASHE GARI*

Akayi mother night wanda har iyayyensu sun je, sai lokaci momma ta ga barrister A duk da girls
d'inta sun ba ta labarin kyawonta har da nuna mata pics d'inta, tsabar takaici ya hanata kallon
pics d'in.
Sosai momma ta firgita lokaci da ta yi arba da barrister A cikin wedding gown golden in colour,
kanta dauke da bridal turban Royal blue colour, yayin da Aliyu ke sanye da farar shadda as
usual sai dai ta yau babbar riga ce kamar yadda ya rik'o hannunta a events d'in jiya haka ma
yau suka shigo, ba k'aramin kad'awa hanta cikin momma ta yi ba. Ba abin da take sai zufa K'awarta Dijama ce, tadawo da ita natsuwarta ta hanyar cewa lafiya
Zaituna duk sanyi Ac da ke wurinan naga ke sai had'a gumi ki ke?"
Wasu yawu masu masifar d'aci ta hadiye tashiga kame-kame uhm....uhm.....lafiya qalau kawai
sanyi wuri ne bai wadace ni ba.
Ta6e baki Dijama ta yi had'e da yatsine fuska kafin ta furta kedai ba kya rabuwa da zance wofi,
ko munafuki ba zai ce wurinan da zafi ba.
"Batare da momma ta kula ta ba gaba d'aya hankalinta ya raja'a da kallon Aliyu da barrister
A, da ke ta faman zabga murmushi suna gaisawa da jama'a bata ankara ba har suka iso gunta,
zazzak'ar muryar barrister A mai shegen dad'i ta dawo da ita hankalinta da kyar momma ta iya
controlled kanta, ta amsa gaisuwar da Barrister A take mata. "Tsabar kwarewa da bariki yasa momma ta mik'e ta had'e su duka ta rungume, sai faman
zuba musu albarka take sosai Barrister A ta ji dad'i a tunaninta uwar mijinta na sonta, har suka
nufi high table suka zauna momma ta na cikin tashin hankali saboda har ga Allah ba ta dauki
za ta ga barrister A haka ba. kyawo da wayewar yarinya suna neman zuzuta tunaninta. Lokaci da mc ya umarce ango da amarya su fito filin domin su taka rawa, gudun abin fad'a
yasa momma ta fito tana yi musu lik'i ita ma Ummi ba'a barta a baya ba.
"Kud'in da Abban barrister A ya zuba fad'arsu ma k'auyanci, ne gudan aure shalele shi dole
naira ta koka.
Kasancewar events d'in yau ya kera na jiya yasa sai around 1:30am aka tashi, yau ma sai da
Aliyu ya raka barrister A a wajen mota sannan suka yi sallama.
A washe gari misalin k'arfe 2:30pm ana gama sallar juma'a aka daura auren Aliyu da barrister
A akan sadaki naira dubu 100, daurin aure da ya tara duban jama'a.
Misalin k'arfe 5:00pm Ummi ta shirya walima ta musanmman a gidanta, wanda mata manya
suka halarci wurin anyi wa'azi mai shiga jiki akan zamantakewar aure daga bisani aka ci abinci
serve yourself duk abin da ranka yake so za ka ci idan za ka wuce abaka jakka mai dauke da
pic d'in ango da amarya, acikin jakka har da atamfa ak'allan kud'inta za su kai 6k.

*9:45pm*
k'anwar Abba ta fito da barrister A lullu6e cikin farar lafayya ko fuskarta ba'a gani, ga wani
k'amshi na musanmman da take yi direct setting room d'in Abba aka wuce da ita sosai Abba ya
yi mata nasiha, daga bisani ita ma Ummi tayi mata.
"Abin mamaki Ummi nagama mata nasiha Abba ya rik'o hannunta ya kalli k'anwarshi mai suna
Maimuna ya ce mu je Maimuna ki rakani na kai, 'yata d'akinta.
Jin furucinshi yasa mamaki ya rufesu sanin halinshi da suka yi yasa ba su tambaya ba, dole
Maimuna ta mik'e tana rik'e da barrister A wacce ke ta faman shasshak'ar kuka, Abba da kanshi
ya yi driving da suka iso gidan, har cikin bedroom d'inta ya kaita sannan ya yi mata sallama ya
fito, sai daga baya k'awayeta suka iso wanda sosai abin da Abba ya yi yai matuk'ar burgesu.


Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:59 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*

*17*

Misali k'arfe 10:30 na dare ango Aliyu ya iso tare da tawagar abokanshi, bayan anyi wasa da
dariya kowa ya kama gabanshi, Aliyu yana dawowa daga raka su ya rufe k'ofar main parlour ko
kallon d'akinta bai yi ba, ya nufi master bedroom d'inshi da ke upstairs.
"Gyagyad'i tafara daga zaune hakan yasa ta tashi da kyar saboda tsananin gajiya ga Kuma
bacci da ya cika idanuwanta.

Ta cire kayan jikinta ta maye gur6insu da wata pitch colour nightgown wacce ta tsaya iya
gwiwarta, ta tufke gashinta wurin d'aya tabi lafiyar gado bata matsantawa kanta da dogon tunani
ba, shiyasa barci ya yi sauri dauketa.
"Washe gari sai misali k'arfe 11:00 na safe ta falka inda Allah ya taimaketa tayi sallar asuba,
agurguje ta gyara bedsheet ta kunna burner ta zuba turaren wuta d'akin ya dauki sanyayye
k'amshi sannan tanufi bathroom tayi wanka.
Simple makeup tayi fuskarta sai glowing take yi.
Tasaka wani tsadadde lace jikinshi marrow colour anyi mishi Zane flowers baby pink da sky
blue style d'in doguwar riga sosai kayan suka k'awata kyakyawar surar jikinta, tasaka half cover
baby pink in colour bata daura d'an kwali ba sai tayi using d'an siriri veil ta yane dogon bak'in
gashinta. Jikinta na fitarda k'amshi na musanman, ta dauki wayoyinta had'e da burner ta nufi
parlounta nan ma ta k'amsashi, daga bisani ta sauko downstairs parlour komai na parlour White
colour ne.
Tayi tsaye tana kallon tsari parlour ta gyad'a kanta a zuciyata tana yaba yadda Aliyu yake
matuk'ar so White colour.
Burner ta jona ta sake zuba turare ta shiga arranging throw pillows d'in da ke kan kujeri.
"Daga bisani ta nufi kitchen tasaki murmushi hatta da kitchen cabinet fari ne tass....ta lek'a
store cike yake taf da foodstuffs iri dabam-dabam.
Ta dawo parlour ta zauna akan one sitter ta dauki phone d'inta ta bud'e data, ta shiga handle
d'inta na Instagram tana karanta comments d'in well-wishers, hanci da dodon kunnenta suka ji
footsteps da k'amshi desingner perfumes d'inshi gabanta ya shiga dukan tara-tara.
"Kasa d'agowa tayi har ya k'araso cikin parlour ya sha ado da dakakkiyar shadda fara sai
walk'iya da daukar ido take.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login