Showing 78001 words to 81000 words out of 85584 words

Chapter 27 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf

27 Jul 2025

1495

yadda zango a ko ina ba sai k'asar
Cameroon, anan na share shekaru masu
yawan gaske ko sunan k'asata Nigeria ban so ji.
"A haka na cigaba da rayuwa ko zance aure bana yi, wannan shine dalilin da yasa ban yi
aure da wuri ba.
Cikin ikon ubangiji da k'udirarsa na waye gari ba abinda nakeso irin naganni a k'asata ta
haihuwa, haka na had'a 'yan kayana na baro, Cameroon dama bai tara komai ba illa tarin
wahala da k'uncin rayuwa.

"Lokaci da na iso gidanmu 'yan uwana kowa ya yi farin cikin dawowa ta, saidai ban tarar da
Dada ba Allah ya yi mata rasuwa shekaru bakwai da suka wuce.
Nayi kukan mutuwarta sosai saboda ita ce nake kallo a matsayin mahaifiya ta.
Anan na samu labari M Ardo yadawo daga k'asar waje ya yi kud'i na ban mamaki, yana d'aya
daga cikin masu kud'in Nigeria.
Alokaci da ake bani wannan labari jin nake yi tamkar zan had'e zuciya na mutu daga nan nasha
alwashi sai na dauki fansar abinda ya yi min.
"A wani yammaci ina zaune a k'ofar gida abin duniya ya taro ya yi min yawa sai ga wani
matashin saurayi ya zo mini, wai in zo mahaifinsa naso magana da ni ban yi gardama ba na bi
saurayin zuwa gidansu duk ban sanshi ba, muna zuwa ya yi min iso d'akin da mahaifin nasa
inda yake kwance yana jinya "Amina kinsan waye mahaifin wannan saurayi....?? Barrister A ta girgiza kanta.
Suraj ya share hawaye da suka zubo masa da tafin hannunshi, tare da fad'in Kabir ne
abokin Yaya M Ardo wanda tare da tallafinsa ne d'an uwana ya lalata min rayuwa, yana kuka
yana bani labari yanda aka yi suka yi min asiri.
"Alokaci da yake bani wannan labari sai kawai na tsince kaina da jin rashin imani na ratsa
zuciyata, ba abinda nake buri irin na bi hanyar da d'an uwana ya bi domin na dauki fansar
abinda ya yi min.
Duk rok'on gafara da Kabir yake min ban ko kalle shi ba kawai na tsince kaina da ficewa
daga d'akin, da taimakon abokina Hamza na samu wani shaharare boka ya yi min asirin da M
Ardo da kansa ya zo har Yola ya dank'a min kula da kamfaninsa da ke Yola.
Sannu-sannu bata hana zuwa saidai adad'e ba'a kai ba, kaman yadda naji malam bahaushe
yana cewa....sai gashi cikin lokaci k'ank'ani M Ardo ya yarda da ni ya zumduma ni cikin
dukiyarsa tsumdu.
"Gani yanda ya bani amana sai jikina yafara sanyi, ga kuma Maryama da ke jin kunya a duk
lokaci da muka had'u.
Ana ciki haka Allah ya had'ani da Zaituna wacce kyawo ta ne ya rud'ani zance gaskiya ina
matuk'ar son mace mai kyau duk da nasan a baya tayi sana'ar karuwanci a yanzu ta tuba, ba
wani aibu idan na aureta.
Na gabatarda da Zaituna a wurin M Ardo a matsayin wacce zan aura, kinsan me ya ce
Amina....??"
Nan ma girgiza kai barrister tayi ta zama speechless, saboda jin labari take yi kaman tatsuniya.
Cike da takaici uncle Suraj ya dauki handle cups da bottle d'in champagne da ke ajiye akan
center table d'in da ke gabansa, ya tsiyaya a two cups ya mik'awa barrister A guda bata yi
gardama ba ta kar6a saboda tana tsananin buk'atar abinda zata jik'a makoshinta da shi.
"Bayan kowane su ya jik'a nasa mak'oshi Uncle Suraj yana jujjuya cup d'in hannunsa tare da
kallon cup d'in kamar a cikinsa ne zai lalla6o labarin nasa da zai ya cigaba da ba ma barrister A.
Saida ya yi shiru few minutes kafin ya cigaba da cewa da "bud'ar bakinsa sai kecewa da
dariya ya yi cikin izza da izzgilancin nasa da ya saba yi min tun muna yara ya ce "dama nasan
sai hakan tafaru da kai Suraj, ba ka nace sai ka aure mace mai kyau ba wannan dai tsohuwar
karuwa ce kai da 'ya'ya nagari saidai ka gani a garemu. Ya k'arashe magana yana mai kwashewa da dariya, daga ni har Zaituna a sanyayye muka
fito daga office d'in shi har nayi nisa da office d'in ina jiyo sautin dariyar tasa, daren rana ban

runtsa ba. washe gari na had'u da Zaituna na gabatar mata da burina naso ta aure M Ardo mu
kwashe dukiyarsa saboda ita ce take saka shi izzgilanci da girman kai.
"Da yake ita ma wata shasssha ce batare da wani dogon nazari ba ta amince, daga nan
muka wuce wajen wani boka a wani kauye da ke minna ta jahar Niger state shine ya yi mana
asirin da M Ardo ya aure Zaituna.
Lokaci da muka gano Maryama tana da juna biyu mun je wajen boka da zumar ya lalata
cikin, ya ce ba makawa sai ta haife shi.
Sai muka buk'ace ya yi mata asiri ta haukace.
Lokaci da Zaituna ta haihu 'ya mace saidai bata zo da rai ba sai muka taki sa'a M Ardo yana
Lagos, abin mamaki sai ga maryama ta haihu duk da cikinta alokaci yana da watani takwas.
Ashe twins ne a cikin nata kuma duk maza shiyasa ta haihu a watani 8 saidai ita ma d'aya bai
zo da rai ba.
"Na cewa Zaituna ta dauke d'an Maryama ta mayar nata ta dauki gawar 'yarta mace ta ce ita
ce maryama ta haifa, tasa a binne d'an Maryama wanda bai zo da rai ba.
"Hikima ta tayin hakan shine ban so M Ardo ya ta6a alfahari da cewa maryama ta ta6a haifa
masa d'a namiji, dama burinsa Maryama ta haifa masa magaji.
mune muka yi ma Aliyu asiri da yasa ya tsani aure da mata, a dalilin boka ya gayamana muddin
mu kayi sake Aliyu ya yi aure ba za mu cimma burinmu na mallaka dukiyar M Ardo ba.
Labari ya canza daga lokaci da M Ardo ya nemo masa aurenki, mu je wa boka da buk'atar ya
wargaza aure kaman yanda ya saba yi mana a baya sai cewa ya yi tabbas sai Aliyu ya aureki
domin ya ga rabon 'ya'ya atsakaninku saidai kada mu sake Aliyu ya kusance ki, daga lokaci da
ya kusance ki komai namu zai tabarbare sai gashi hakan tana shirin faru Ni da Zaituna mun kasance muna aikata Zina yanzu haka ina da 'ya a tare da ita.
"Barrister A ta katse masa hanzari ta hanyar cewa "Ai nasani ko ba Teema mai aljannu k'arya
kake nufi ba, tuni nagano 'yarka ce uncle Suraj.
Cikin kad'uwa uncle Suraj yake kallon barrister A, ita kuma sai murmushi take zabga masa.
Nasan kana so kasan ta wacce hanya na bi nagano Teema 'yarka ce....?
Amsar ita ce ta cikin baccin Teema.
Bacci kuma....?
Uncle Suraj ya maimaita cike da mamaki.
Kwarai kuwa ta baccinta wanda ko ita kanta Teema batasan na sani ba, ranar da Aliyu ya yi
tafiya zuw Lagos ina jin tsoro kwana ni kadai sai na nemi Zee-zee da Meena su zo su tayani
kwana amma sai momma ta hana su.
Sai kawai na gayyato 'yan aikina da su zo mu kwana tare har na rufe k'ofa sai naji knocking
koda na bud'e k'ofa sai naga Teema, kamar yadda tasaba yi pretending d'in iskokanta hakan
tayi min ta wuce ni batare da ta ce da ni uffan ba, ina kallonta ta haura upstairs na bi ta da sauri
tana zuwa ta bud'e bedroom d'ina ta shiga ta kwanta kan gadona, sai lokaci ta ce da ni matar
yaya na zo na tayaki kwana ne.
Nayi mata murmushi tare da cewa nagode Teema.
Bata dauki dogon lokaci ba tafara bacci ni kuma na dauko laptop dina domin nayi wani aiki,
Teema tana cikin mutane da ke bayyanar da damuwarsu ta cikin baccin da suke yi. Can tsakiyar
dare baccinta yafara nisa sai tafara kuka ta na fad'in momma kin cuceni Me nayi muku ke da
uncle Suraj za ku samar da ni ta k'azamar hanya Allah ya isa tsakanina da ku ba zan ta6a yafe

muku ba.
Alokaci na firgita had'e da gigicewa ba kad'an ba da farko na dauko ko iya shegen ta ne, na
iskoka sai na isa daff.....da ita na aza hannuna a k'ofufin hancinta sai naji saukar numfashinta
tabbas bacci ne take yi kuma ya yi nisa sosai.
"Ka ji ta yanda aka yi nasan Teema 'yarka ce.
Uncle Suraj ya saki murmushi ya ce gaskiya you're very smart barrister A kwakwalwar ki tana ja
sosai.
Dariya tayi tare da ajiye cup d'in hannunta ta ce "Uncle kenan ai ba banza ba Abba na yana
ce saida ya ga na zama cikkakiyar lawyer
Abban ki ya ci a bashi award domin gashi ta sanadin mayarda ke lawyer kina bankad'o sirrika
mutane.
"Dariya barrister A tayi tare da fad'in gaskiya ya chanchanci abashi abinda ya fi award
saboda, ga shi a sanadinsa zai cuto rayuka da yawa daga halak'a daga ciki kuwa har da kai
Uncle.
Uncle Suraj ya girgiza kanshi tare da fad'in karki yi gaggawa Barrister A ki d'an takata
kad'an.
Saboda mijinki Aliyu da kike gani ba d'an Zaituna bane Maryama ce ta haife shi kinga ya
kamata ki san irin hatsarin da uwar mijinki ta ke ciki.
Ga mamakinsa sai ya ga tayi murmushi tasake kur6a champagne d'inta, ta ce "kwarai kuwa
nasan da hakan nagano hakan ne kusan kwanaki biyu da suka wuce a dalilin cindo[6th finger]
da ke hannun maryama, wanda Aliyu shi ma yana da shi duk da kun cire nashi tun yana jinjiri
saboda kada a gano d'an maryama ne amma ta6o hannunshi ne ya toni asirinku nagano shi d'in
d'an Maryama ne ba Zaituna ba.






Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:30 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


_LAST PAGE_

*Ban yi editing ba ku yi hak'uri da errors d'in da za ku ci karo da su*

*40*


*NNAMDI AZIKIWE INTERNATIONAL AIRPORT ABUJA*


Flight d'in da Aliyu ya shigo ya yi landing a Nnamdi azikiwe international airport abuja, batare
da ya kira direban shi ba ya bi taxi zuwa hospital d'in da aka kwantar da Daddy.
Koda ya iso Daddy ya farfad'o rana d'aya duk ya zabge ya yi wata bak'ar ya rama, kaman
wanda ya shekara yana jinya abin gwanin ban tausayi.
"Cikin yana yi na kariyar zuciya Aliyu ya isa gareshi ya rungume shi tare da fashewa da kuka
kaman k'aramin yaro, gani hakan yasa su Zee-zee suka shiga taya shi.
Cikin muryar kuka Zee-zee ta ce "Ya Sultan momma ta gudu an neme ta sama da k'asa a
hospital d'inan an rasa.
A fusace Daddy ya katseta ta hanyar cewa "Zainab ba nace kar ku sake yi min zancenta
anan wuri ba.
Kayi hak'uri Daddy insha Allahu.....ba za'a sake ba Zainab ki bashi hak'uri.
Cewar Aliyu yana kallon Zee-zee.
Kusa da shi Zee-zee ta matso tare da rik'o d'ayan hannunshi tayi k'asa da murya tare da fad'in
ka yi hak'uri Daddy ba zan sake ba.
Kafin Aliyu ya sake yin magana Abban Barrister A Alhaji Abdallah Barkido ya ban ko k'ofa ya
shigo yana muzurai, kaman wani tsohon Soja.
Ummi da twins suna biye da shi kowane su daga ni yaci kuka har ya godewa Allah, Cikin sauri
Aliyu ya ta shi daga jikin Daddy yana share hawayenshi ya ce "Sannu da zuwa Abba...?
Wani mugun kallo Abba ya watsa masa cikin kakkausar murya da hargowa ya ce "kai.....ina 'ya
ta.....?"
Aliyu cikin kad'uwa yake kallon Daddy zuciyarshi na bugawa da k'arfin gaske, ya furta Abba

wacce 'ya....?
"Wacce 'ya kake tambayata Aliyu to a ubanka nace ta ubanka. Aliyu....billahilazi idan ba'a ku
fito min da 'yata za'a yi babban tashin hankali, da yafi wanda kuke ciki gayyar tsiya masu abin
kunya saboda wannan abin kunyar naku yasa kidnappers suka yi garkuwa da 'ya ta.
Sosai Aliyu ya tsorata da jin abin da Abba yake fad'a.
Daddy ne ya yunk'ura ya tashi tsaye da kyar ya nufi Abba yana cewa "don Allah Alhaji Abdallah
ka zauna ka yi mana bayani a natse.
Aliyu ma da kake gani yanzu-yanzu nan ya iso daga Lagos, ga dukkan alamu bai da masaniya
akan abinda kake tuhumar mu da shi.
Mtssss.....Abba ya ja tsaki tare da buge hannun Daddy da ya rik'o shi, ya ce "Wallahi ba zan
zauna ba M Ardo har sai kun fad'a min inda 'yata take.
Khalid ne ya dauko kujera ya kama Abba ya zaunar da shi, ya durk'usa gabanshi ya yi k'asa
da murya ya ce "ka dubi girman Allah Abba ka kwantar da hankalinka duba da yana yin da
mutane nan suke ciki ya isa ya zama sheda basu da labari akan Kidnapped d'in Ya Minal.
Saura kirisss.....numfashin Aliyu ya fita daga gangar jikinsa, wani irin duhu ya maye ganinsa,
da kyar ya iya d'aga k'afafunsa ya isa wajen da Ummi da Khalil suke tsaye zugun!
Ya ce Ummi me ya sami Amina ni dai nasan nayi waya da ita safe bata gayamin ko nan da
k'ofar gida zata fita ba to....ya akayi kidnapped d'inta?"
Shin kidnappers d'in sun kira Abba nawa suka buk'ace abasu...?
Ajiyar zuciya Ummi tasauke mai k'arfin gaske tare da ba shi labari kamar yanda Abba ya
sanar da ita, hankalin Aliyu ya yi mugun tashi duk ya bi ya rud'e.
Gani haka yasa Abba ya d'an sauk'o da kanshi ya sake basu labarin yanda al'amari ya faru,
Teema ta d'ago kanta da ke duk'e a k'asa ta kalle su tare da fad'in nasan inda take.
Cike da zallan firgici suka zuba mata idanuwa, Aliyu kam tashe ta tsaye ya yi, ya ce "tana
ina Fateema fad'a min matata tana ina....?
Teema ta ce tana inda ta 6oye umma Maryama gidan Ya Jamal.
Daga nan ta shiga ba su labari abin da tasani.
jikin Aliyu yana rawa ya kira wayar Jamal saidai kashhh....a rufe take, nan da nan hankalinsa
ya k'ara tashi.
Don haka gaba d'ayan su suka had'u suka dunguma zuwa gidan Jamal hatta Daddy ba'a
barshi ba.

*JAMAL*

Jamal da matarsa suna baro Nimzamia hospital, Suka nufi gidan yayar shi aunty Sakina da ke
zone six.
A falonta suka isko ta cikin tashin hankali ya bata labari abinda ke faru saboda lokaci da Uncle
suraj da boys dinshi suke dukan shi, ya gane Uncle shiyasa ya zo ga Aunty sakina ya da ta
taimaka musu, kasancewarta k'awar Nafisa matar uncle Suraj ta tuntube ta taji ko tana da
masaniya akan abin da mijinta yake shirin aikatawa. "Sakina tana kiranta batare da gardama ba gayamusu ta ta6a dauk'ar wayar Jarumi da
momma ta kira alokaci yana wanka anan ta ji ta'asa da suke k'ulawa, tun daga lokacin take
bibiyarsa a 6oye yanzu haka tana cikin abuja su had'u a bakin Emmaculete hotel, anan tayi

masauki zata musu jagora zuwa madallah village inda take da tabbaci Suraj ya 6oye su
maryama a poultry house d'in shi.

*MOMMA*

Dijama da momma suna zaune a bedroom, Dijama ta kalle momma ta ce kin bani mamaki
Zaituna ya aka yi kika bari shed'an da son zuciya suka d'ebe ki kika aikata wannan mummunan
aiki..?
Yanzu duk karuwanci da muka yi abaya bai isheki ba sai da kika aikita zina da aurenki,
to...gashi nan abinda son zuciyarki ya jawo miki wannan kayan kunya har ina.
Ta k'arashe magana tana kya6e baki.
Cike da takaicinta momma ta ja tsaki mtsss....ta nemi gefen gado ta kwanta tare da lumshe
idanuwanta. Dijama ta kad'a kai kana ta nufi bathroom ta bud'e ta shiga momma nagani haka ta
dauke key d'in motar Dijama ta fice da gudu-gudu, kaitsaye gida ta nufa cikin yana yi na tashin
hankali ta danna horn Daniel ya bud'e mata gate, ta shigo. "Agaugauce ta shiga sasshen ta dauki ATM d'inta tasake ficewa saida ta fara tsayawa a bank
tayi withdrawing d'in mak'ud'an kud'i, sannan ta dauki hanyar madallah village cike da mugun
nufi
Uncle Suraj ya saki k'ayatattace murmushi tare da fad'in tun da kin ri ga da kinsan dukan
sirrina, bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login