Showing 3001 words to 6000 words out of 85584 words

Chapter 2 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf

27 Jul 2025

1498

BIKIN FARAR KAZA BALBELA BA SAI ANBATA GORON GAYYATA BA, KAR DAI
KU MANTA WADANAN MARUBUTAN DAGA KUNGIYAR NAN MAI ALBARKA KUMA
HASAKKAKU WATO *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* *ALK'ALUMA SHIDDA AMANA*

_GA MAI BUK'ATAR KARANTA WADANNAN K'AYATATTUN LABARAI ANYI MASU KUDI NE
AKAN NAIRA DARI BIYAR 500 KACAL GUDA SHIDDA, MAI SON GUDA D'AYA ZAI BIYA 200
MAI SON BIYU 350 MAI SON HUDU ZAI BIYA 400_

*SAI KU TUNTUBE MU KAMAR HAKA*

FIRST BANK
3120641551
SAFIYA MUSA GALADANCI
SHAIDAR TURA KUDINKA GA WANNAN NUMBER
08103943903

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
ZENITH BANK
2255398727
AMINA JIBRIL
SHAIDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER
08166177830

GA MASU TURA KATIN WAYA MTN AKE BUKATA ZAKA TURA GA WANNAN NUMBER
08039424298 SHAIDAR BIYAN KATINKA GA 07084161619

KADA KUBARI A BAKU LABARI!!!

DOMIN K'ARIN BAYANI
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
07084161619
08103943903
08166177830


Jeeddah Aliyu

[7/26, 11:34 PM] Jiddah Aliyu: *GIDAN RINA*

Na Jeeddah Aliyu



*FREE PAGE*

*2*

Isowar Barrister Zarah Ladan ya yi dai-dai da tana lumshe idanunta, daga bisani ta bud'e su
key ta mik'a mata batare da ta yi magana ba.
"Barrister Zarah ta kar6i key d'in saboda ta fahimce me k'awartata take nufi.
sit d'in direba ta zauna yayin da Barrister Barkido ta zauna gefenta, har lokaci da damuwa akan
fuskarta.
Saida Barrister Ladan ta kalleta na wasu 'yan dak'ik'u ta gargiza kai, sannan ta ja mota.
"Bayan sun hau titi barrister ladan ta dubi barrister Barkido sosai sannan ta yi concentrated
tuk'i da take.
"Meke damunki bebs naga tsananin damuwa akan fuskarki?"
Barrister Barkido ta d'an ja tsaki tare da sauke ajiyar zuciya, ta ce ki bari kawai bebs yau
kwata-kwata bana cikin natsuwa Allah ne kawai yanufi za mu yi winning case d'inan.
"Uhm! Gaskiya ne amma meke damunki ne?"
"Ta d'an gyara zamanta ta fuskanci Barrister Ladan sosai, ta ce abubuwa da yawa, za ki yarda
ida nace da ke daren jiya ban runtse ba, yadda naga rana haka naga dare.
sai juyi nake yi akan bed har asuba.
"Gaba d'aya Barkid'o ya d'aga min hankali, har na rasa inda zan sa kaina.
"D'an waigowa Barrister Ladan ta yi ta zubawa Barrister Barkido ido gani yadda damuwa
tak'ara bayyana k'arara, akan fuskarta ita ma sai ta ji ba dad'i saboda amintaka da shak'uwar da
ke tsakaninsu tasamo asali tun suna yara.
''Ta nisa tare da girgiza kanta ta ce ko ba ki fad'a ba nasani bebs, saboda the whole week
d'inan ba ki cikin hayyacinki, nishad'i da walwala sun k'aranta agareki na zuba miki ido ne
nagama karantarki.

"Now tell me what's exactly wrong with you....?
Sassanyar ajiyar zuciya Barrister Barkido ta sauke, sannan ta d'an yatsina fuska wanda d'aya
daga cikin d'abi'unta ne wanda wasu mutane masu karancin fahimta suke mata kallon tana da
wulaqancin.
"Ta ce wallahi bebs komai ya dagule min, ki taimakeni da shawara.
"Inajinki!
Cewar Barrister Ladan.
"Shin ko kinsan yau za'a zo neman aurena daga Abuja?"

whats!

Are you serious?

Sake yatsine fuska ta yi fiyye da farko, tare da d'aga girar idonta.
"Bebs ba ki da kirki shine sai yanzu ki ke fad'amin.
"I knew bebs za ki ce haka da farko ban dauki abin da mahimmanci ba sai gashi abin is
getting serious but am sorry.
''Shikenan bebs na hak'ura amma yaushe ki ka yi boyfriend da ban sani ba?"
"Uhm! Da zan yi boyfriend you're the first person da za ki fara sani.
"Bebs am confused kin k'ara jefa ni a duhu, taimaka fito da ni haske.
"Murmushi Barrister Barkido ta yi wanda yak'arawa kyakyawar fuskarta ma'abociyyar kwarjini
kyau, ta ce Barkido ne ya yi min miji.

"What's?
Barkido kuma oh my god!
That's old man ba zai bar mutane su huta ba.
"Mak'e kafad'a Barrister Barkido ta yi alamar ni ma shi nagani.
Abin takaici bansan waye mijin ba kuma aure ba zai wuce 2 months ba.
"Cabdijam!
Lalle this time Barkido ya zo mana da Babban al'amari, amma Bebs miye mafita?"

"I don't know bebs ki nemo mafita before Zuciyata ta buga, kinsan kuma idan zuciya ta buga
bebs mutuwa ake yi.
Tak'arasa magana cikin kalar tausayi.
"Dariya Barrister Ladan ta yi ta ce kwantarda hankalinki k'awata kamar kin yi bako ya mutu.
"Mtcwww!
ta ja d'an siriri tsaki
Da ace bako zai mutu da sai na fi kowa murna da farin ciki, kinga abin ya zo min da sauki.
"Wane bako Ki kewa fatan mutuwa?"
Wanda zai zo neman aurena mana.
Sosai Barrister Ladan ta ke dariya saida ta yi mai isarta kafin ta ce, Bebs please mu koma
zance mu na farko karki fasamin ciki da dariya.
"Shiru suka yi na d'an lokaci kafin Barrister Ladan ta ce ba za mu yi sauri yanke hukunci ba,
k'awata har sai mun had'u da shi idan ya yi miki falillahi hamdu.
"Idan kuma bai yi min ba?"
Barrister Barkido tafad'a tana mai kafeta da ido.
Alokaci za mu nemo mafita sai mu koreshi cikin sauki, kamar yadda mu ka yi wa na baya.
"Ba za ki gane ba Zarah a wannan karon har rantsuwa Barkido ya yi akan lalle sai na kar6i
mutume amatsayin mijina.
Kinga kenan zance mu koreshi ma bai taso ba.
"Inna lillahi wa'ina illahim raji'un....ban zace abin ya kai haka ba, yanzu dai mafita guda d'aya
ta rage mana dole ne mu duk'ufa addu'a da sadaka Allah ya yi mana kyakkyawan za6i, domin
shi kadai yasan abinda yafi dacewa da bawansa.
"Haka ne Bebs amma mazanan suna bani tsoro ko zance aure banaso anayi min, sai gashi

kwantsa lokaci da ban yi zato ba ya riskeni.
"Ki daina jin tsoro minal saboda ba duka gaba d'aya maza suka taru suka lalace ba har gobe
akwai nagari akwai bata gari.

"Uhm! Bari kawai Zarah ko iyayyenmu kina kallo yadda suke gwagwarmaya da halin d'iya maza,
balle mu da mu ke tasowa wallahi da iyayyena za su kyalleni da zan iya rik'e kaina batare da
aure ba.
"Allah ya kiyayye bebs ba ma fata ki k'are rayuwarki batare da kin aurarda jikokinki ba.
Barrister Barkido batasan lokaci da dariya ta subuce mata ba, ta ce kai Zarah ba ma 'ya'yana
ba.
Eh! mana.
Ita ma tafad'a tana tayata dariya.
Nan take Barrister Barkido ta ji hankalinta ya kwanta damuwar da ta ke ciki ta ragu, shiyasa
batada k'awa da ta wuce Zarah saboda duk lokaci da shiga matsala ita kadai take tunk'ara.
"Haka suka cigaba da tattauna zance har Barrister Zarah ta iso k'ofar gidanta, nan suka yi
sallama Barrister Barkido ta ja motarta ta nufi gida zuciyarta wasai babu saura damuwa.
****----*****-----***
*WAIWAYE ADON TAFIYA*

*WANENE ALIYU?*
Aliyu Muhammad Ardo shine cikkakke sunanshi, fari ne tass!
Mai matsakanci tsawo yana dogon hancinshi, akan zagayayyar fuskarshi ma'a6ociyya kwarjini.
"Aliyu miskili ne na bugawa a Jarida daily trust shiru-shiru yake bayaso yi doguwar magana
yana da zafin zuciya matuka ga sauri fushi da kamar kububuwa.
Aliyu sunan Kakanshi na waje uba yaci shiyasa ake kiranshi da sultan.
"Mahaifinshi Alhaji Muhammad Ardo haifaffen gari Yola ne ya yi ilmin addini da na boko, saidai
boko ya fi k'arfi sosai shiyasa ya dusashe na addini.
"Alhaji Muhammad Ardo mahaifinshi Aliyu Ardo a wanchan lokaci mai arziki ne, sosai, ya yi
suna har a kudanci Nejiriya k'arin abin ga kuma sarautar da yake da.
"Yana da matan aure har guda hudu da sad'aka guda uku, shiyasa yake da tarin 'ya'ya har
talatin da biyu.
Muhammad Ardo mahaifiyarshi Fatima ita ce mata ta biyu, tana da 'ya'ya bakwai ahalin yanzu
uku su mutu saura hudu sai d'an kishiyarta Suraj wanda take riko, mahaifiyar Suraj ta rasu tun
daga haihuwarshi alokaci Fatima tana goyon Muhammad sai ta kar6i suraj ta cigaba da
shayarda shi, idan ba fad'a maka aka yi ba ba za ka ta6a sani ba ita ta haife shi ba. Muhammad shine d'anta na uku.
"Alhaji Aliyu ya mutu kusan shekaru ashirin da biyar kenan da rasuwarsa.
Matanshi da sadakunshi, da wasu daga cikin 'ya'yanshi sun rasu.
Mahaifiyyar Muhammad tana d'aya daga cikin matan Ardo da suka rasu.
"Duk da haka da yake akwai tarin jikoki shiyasa har yanzu Family din yake da yawa.
Alhaji Muhammad Ardo ya yi karatu boko sosai wanda har ya kaishi da zama Ambassador a
England a lokaci matarshi d'aya Maryam tsawon shakaru goma sha biyar da aurensu, Allah bai
bata haihuwa ba.

"Da suka dawo Najeriya ya shiga business har ya yi nassarar bud'e kamfanuni da dama
arewaci da kudanci Najeriya.
Yana d'aya daga cikin manyan masu kud'in Najeriya.
Yana da gidajen man fetur billa adadin da manya-manya malls a Abuja da Lagos, Alhaji
Muhammad Ardo mutum ne mai kafirin neman kudi.
Shiyasa d'ansa tilo Aliyu ya gadesa ba abinda yasani illah neman duniya.
"Lokaci da Alhaji Muhammad Ardo yadawo da England ya had'u da Zaituna Wanda
k'aninshi Suraj ya had'a shi da ita.
[7/26, 11:35 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- RUYUWATA

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*







*FREE PAGE*

*3*

Zaituna cikkakiyar 'yar duniya ce Mai lasisi a hannu, asalinta 'yar k'asar nijar ce iyayyenta sun
mutu tun tana da karanci shekaru.
"Hannu k'anwar mahaifinta Adama ta taso ba k'aramar azaba k'anwar mahaifin nata take
gana mata ba, Adama muguwa ce ta k'arshe lokaci da Zaituna ta kai shekara goma sha biyar,
ta aurarda ita ga wani tsoho mai mata uku ita ce cikon ta hudu.
''Tun daga lokaci rayuwarta tak'ara shiga garari saboda mijin nata Rudda ya fi Adama
mugunta nesa ba kusa ba.
Dukan mata yake kamar ba zai barsu da rai ba, yana d'aya daga cikin dalillai da yasa Adama ta
bashi aurenta don tasan azaba za ta sha ba kadan ba.
"Ga kuma matsalar kishiyoyinta kasancewar sun fi ta shekaru, sai su dinga had'e mata kai.
kullum sai sun kulla mata makircin da Rudda zai daketa saida tadawo tamkar ta6arya kir6a
sakwara saboda duka.
"Ana cikin haka tasamu ciki duk da cikin da take dauke da shi, bai fasa lakada mata duka ba.
"Cikinta yana da wata bakwai ya daketa kamar yadda yasaba hakan ne yasa ta haifi bakwani,
d'a namiji yaro yana da wata d'aya kachal a duniya.
Atsakiyar dare, Rudda ya nemeta tak'i yarda ya rufe ta da duka sai dukanta yake tana ihu, duk
yawan matan gida da gayya 'ya'yansu ba wanda yakawo mata dauki.
"Da Rudda ya gaji da dukanta sai kawai ya shak'e mata wuya sai kakarin mutuwa take, gani
zai kasheta abanza yasa tashiga lallu6e abinda za ta kwace kanta da shi, cikin sa'a ta ci karo da
wuk'a daure a k'ugunsa cikin zafin nama ta zaro ta cikin kube, ba tare da dogon tunani ba ta
da6a masa a ciki. "Yafad'i k'asa yana kugi gani yadda jini ke malala yasa ta buga ihu tafice da gudu tanufi
dakuna kishiyoyinta, tana neman taimakonsu.
"Gani halin da mijinsu yake ciki suka fara ihu yayin da 'ya'yansu suka rufe Zaituna da dukan
mutuwa.
"Allah ya taimaketa ta kwace daga hannunsu ta 6alla da gudu bala'i ta yanki daji, ba ta ko bi
takan bakwani yaronta ba wannan shine sanadin zuwanta Nigeria da farko Lagos tafara yadda
zango ana ta hadu da k'awarta Dijama suna aikin wanke-wanke wurin wata bayarba mai siyarda
abinci. "Gani yadda Zaituna take da kyau da diri yasa maza suka fara nemanta da lalata, da farko ta
k'i amincewa saida Dijama tai mata huduba sannan ta amince.
"Sannu-sannu idanunsu yana bud'ewa suna k'ara wayewa, da tafiya tai nisa sai suka koma
gidan karuwai suka kama d'aki.
"Cikin lokaci k'alilan Zaituna ta zama k'ursugumar karuwa.
Shekaru sun tafi customers suka fara yi musu wuya, sai suka yi kaura zuwa garin kaduna anan
ta hadu da Alhaji sambo ya nuna yana sonta da aure nan take ta amince.
"Dijama ta nemo wani malami ya zama waliyin Zaituna aka daure musu aure ta tare gidan
mijinta Alhaji sambo, anata gajere tunani tun da tafi uwargida Alhaji kyau nesa ba kusa ba dole
ita ce mowar gida.
Da yake Uwargidan Alhaji Sambo ita ma ba kanwa lasa bace, ta tsare gaba ta tsare baya shi
kanshi Alhaji tsoronta yake saboda bata bar shi a banza ba.

"Zama yak'i dad'i tsakani Zaituna da kishiyarta, ita da kanta tanemi Alhaji Sambo yasaketa
saida suka kai ruwa rana kafin ya amince yasaketa d'in.
Bayan ta kashe aureta da Alhaji Sambo ta ji ba za ta iya komawa, k'azamar sana'arta ta
karuwanci ba ta ja jari da kud'in da take tarawa a asusunta na banki.
Ta shiga safarar tufafi na mata da na zama daga Dubai, gani haka yasa k'awarta Dijama ta
watsarda karuwanci ta aure wani Alhaji Yusuf da ke zaune a garin Abuja, wannan shine dalilin
Zaituna na sake kaura zuwa babban birnin tarayya Abuja tanemi gida a unguwar Garki ta kama
hayya. "Yayin da mijin Dijama ya bata jari mai kauri ta zuba a kasuwancin Zaituna, cikin d'an lokaci
kad'an suka bud'e manya shaguna har guda biyu.
Lokaci ya mik'a sosai har Dijama ta kai ga haihuwa, wannan ne ya sakawa Zaituna tunanin
sake yin aure kwatsan Allah ya had'ata da Suraj Ardo, da farko ya nuna zai aure ta ko ya akayi
auren ya juye kan d'an uwanshi Muhammad, Alhaji Muhammad Ardo aminine awurin mijin
Dijama. "Batare da dogon bincike ba ido rufe da zugar Suraj Alhaji Muhammad ya aure Zaituna, irin
aurenan na bariki.
Da yake uwargidansa Maryam mace ce mai hak'uri gaske da kauda kai sai zaman nasu ya yi
dad'i.
"Wata Zaituna biyu a gidan tasami ciki, ashe ita ma Maryam tana da shi 6oyewa ne kawai ta yi
batare da tafad'awa kowa ba.
'Sa6ani Zaituna da gaba d'aya dangin mijinta ba wanda baisan tana da ciki ba, farin ciki
awurin Alhaji Muhammad ba kama hannun yaro.
"Cikin maryam yana da wata hudu ya bayyana saboda tsananin girmansa, sai lokaci
Muhammad yasan tana da ciki ranar kamar zai yi hauka saboda murna da farin ciki.
"Gaba d'aya kulawarsa da tattalinsa suka koma kan Maryam, hakan ba k'aramin bak'antawa
Zaituna ya yi ba.
"Cikin Maryam na da watani shidda ta had'u da lalura ta6in hankali, duk wani asibiti na masu
ta6in hankali, Muhammad yakaita abin yaci turo dama ciwo ke shiga farat d'aya sauki kuma ya
na zuwa ahankali.

"Rayuwar Maryam gwanin ban tausayi ga ciki ga hauka, ko yaushe k'ok'arin take ta gudu,
ba yadda dangin Muhammad ba su yi da shi ba akan yakai Maryam Mental asylum amma yak'i
amincewar da shawararsu.
Aganinshi Maryam bata chanchanci hakan daga gareshi ba, ya tabbata da shine ya had'u da
lalura irinta ta ba za ta gujeshi ba.
Za ta zauna da shi har k'arshen rayuwarta saboda haka ya za6i zai cigaba da zama da ita har
zuwa lokaci da Allah zai bata lafiya.
''Gani halin da Maryam ta tsince kanta aciki yasa Zaituna ta yi laushi, tagano rayuwar d'an
adam ba'a baki komai take ba.
Tadawo tana bata kulawa ta musanmman duk da kowace daga cikinsu cikinta ya tsufa, wani
ikon Allah rana d'aya suka haihu Zaituna ta haihu da safe d'a namiji kyakyawan gaske.
"Yayin da dare na zagayowa Maryam ta haifi 'ya mace saidai bata zo da rai ba, ranar
Muhammad har kuka sai da ya yi ranar sunna d'a Zaituna ya zagayo aka saka masa Aliyu.

Daga lokaci haihuwa ta budewa Zaituna ta haifi Zainab, shekarar Zainab biyu kachal ta haifi
Amina sai auta Fatima.
"Fatima tana fama da lalura ta shafar jinni tun tana yarinya take fama da ciwon wanda har
zuwa yanzu ana nema mata magani duk tsawon wannan lokaci Zaituna ba ta waiwayin
K'asarsu Nijar ba.
******------*****-----

Family Alhaji Usman Barkido family ne mai girman gaske, wanda girmansa yasa duk wanda
yake cikin garin Adamawa yasan da wannan family kasancewarsu jinin sarauta.
"Alhaji Usman Barkido yana da 'ya'ya da tarin jikoki, saidai duk yawan 'ya'yanshi bai yarda
sun yi aure ba daga daga tsatso shi ba, don haka tun daga kan 'ya'yanshi mata har zuwa maza
aure had'i yake musu.
"Wannan al'ada ta shi hatta jikokinshi ba su tsira ba, namiji ko mace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login