Showing 36001 words to 39000 words out of 85584 words
Chapter 13 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf
"Da sauri ya fice daga d'akin yana murmushin mugunta.
Fitarshi yasa tadawo da natsuwarta ta fahimci idan take, sosai mamaki ya rufeta da ta tuna
abinda ya kawota d'akinshi har bacci ya dauketa.
"K'ayattace murmushi ta yi ta d'an bige bayan k'eyarta, sai kawai take ji wani irin nishad'i ta jima
sosai tana blushing kamar wacce aka yi wa albishir da mallakar zuciyar Aliyu....lol.
Jin footsteps dinshi ya nufo d'akin yasa ta mik'e da gudu ta shiga bathroom, koda tafito har ya
shigo yana zaune akan resting chair closing his two eye's ta kalle shi asanyayye kafin ta dauki
hijab da praymat ta yi sallah, tana gama sallah ta ce "Ina kwana Yalla6ai?"
Ya bud'e idanuwanshi masu cike da bacci, saida ya yatsine fuska kafin ya ce banganshi ba.
Zaro manyan idanuwanta tayi masu kamar da an diga mata zaiba, tana kallonshi ba ki bud'e.
Kafin tayi magana ya katseta ta hanyar cewa tashi ki je had'a mana breakfast, idan kin kammala
ki zo ki tasheni.
Ta mik'e tana murmushi ta nufi k'ofar fita ya bi ta da kallo, tana ficewa ya sauke k'atuwar ajiyar
zuciya.
Ya haye bed had'e da switch off d'in bulb.
Ga mamankinshi a maimakon ya yi bacci sai ya tsince kanshi da tunaninta, tsawon lokaci ya
dauka kafin ya samu bacci ya dauke shi.
Tana bari d'akin ta shiga nata ta canza kayan jikinta, ta shiga kitchen a gaggauce ta had'a
breakfast, ta shirya table, sannan ta koma d'akinta tayi wanka ta shirya tsaf.....cikin atamfar
super exclusive d'ikin skirt and blouse kayan sun kar6i jikinta sosai tayi kyau na ban mamaki
tayi dauri d'an kwali Zarah buhari, ta kammala komai sannan ta nufi d'akinshi, ta samu ya tashi
har ya shiga wanka, ta isa ga gadonshi ta shiga gyarawa, tana cikin gyara gadon ya fito daga
bathroom sanye da bathrobe ta dauke kanta daga gefen da yake tsaye, tana gama gyarawa ta
fice daga d'akin.
misalin k'arfe 11:00 na safe suka bar gidansu zuwa Airports, Isah direba na sauke su ya yi
sallama da Aliyu saboda zai shi yi driving motar barrister A zuwa Abuja.
"Lokaci da flight d'insu ya yi landing direban Daddy ne ya dauko su.
Tun da suka fito daga Airports take kallon hanyoyin da direban yake bi, har suka iso Ardo
mansion.
Da gudu gateman da security d'in gidan suka iso wajensu, suna gaida su ta amsa fuska sake
har ma da wani d'an siririn murmushi.
Ta fito daga mota tabi bayan Aliyu sun iso flat dinshi ya ciro keys ya bud'e k'ofa suka shiga daga
ciki.
Gate man ya shigo musu da kayansu, cikin mintuna k'alilan ta d'anyi nazarin falon k'asa duk
abinda ke ciki kama daga cushion har zuwa painting falon white colour ne, kamar dai yadda
gidansu na Yola yake saidai wannan yafi na Yola had'uwa.
"Ki hau sama mana"
Muryarshi ta daki dodon kunnenta, ta juya cikin salon tafiyarta ta bi steps ta hau saman saidai ta
ja ta yi tsaye sakamakon rashin sani wane daga cikin k'ofufin da ta samu ne, nata.
Bata jima da tsayuwa ba ya shigo ya ra6ata ya nufi wata k'ofa ya bud'e, ta bi bayanshi.
Nan ma parlour ne ya sha kayan alatu na more rayuwa.
"Ya nuna mata wata k'ofa can k'asan mak'oshi ya ce ga sasshenki anan, yak'arasa magana
had'e da mik'a mata key, ya shige d'akin da take tunanin shine na baccinshi.
"Ta kad'a kanta ta bud'e falon ta shiga ta wuce bedroom, ta ajiye jakkarta da mayafi ta shiga
gyara wurin saida ta gama, tanufi nashi ta gyara taji motsinshi a bathroom, agaggauce ta shiga
gyara d'akin koda yafito har ta kammala ta fice, ta gyara mishi falo, sannan ta sauka k'asa nan
ma ta gyare shi tass....ta shiga kitchen ta yi nazarinshi nan ma ta tsafta ce shi, gaba d'aya gidan
ya dauki k'amshi na fitar hankali.
Ta koma d'akinta ta yi wanka ta had'o da alwala, da yake lokacin sallar azhar ya yi ta yi sallah.
Sannan ta tsantsara simple makeup, ta dauko luggage d'inta ta ciro Arabian gown purple colour,
tasaka tayi rolling da white veil.
"Tana cikin fesa perfume ya turo k'ofa ya shigo shima ya sauya kayan jikinshi, zuwa white
chino trouser had'e da mandarin long sleeve, ya nad'e hannayen rigar.
"K'amshinta ya had'e da nashi ya k'ara k'amsasa d'akin.
Kallo d'aya ya yi mata ya dauke kai, tayi mishi kyau ba k'adan musanmman da tayi rolling da
white veil favorite colour d'inshi.
"Mu je flat d'in momma ki gaisa da su ga alama basu san mun iso ba.
Yana k'arasa magana ya juya ta biyo shi abaya tana k'arewa compound d'in gidan kallo.
A downstairs falo suka iske momma da Zee-Zee momma na waya yayin da zee-zee ke kallon
movie.
"Sallamar Aliyu ya dawo da hankalinsu akansu, zee-zee ta tashi cikin farin cikin tayi hugging
barrister A.
Lokaci da momma tayi arba da barrister ta ji gabanta, ya yi mummunan fad'uwa da had'ye wasu
mushirkai miyau.
"Barrister A ce tafara janye zee-zee daga jikinta, ta durk'usa ta gaida momma ta amsa cikin
fara'a saboda tsabar makirci hadda su rungume barrister tana fad'i welcome to the family my
daughter ya gajiyar hanya?"
Murmushin jin dad'i barrister A tayi duk tasan wannan welcoming da momma tayi mata bai
gansheta ba
Aliyu ya nufi one sitter ya zauna ya yi crossing legs d'inshi, shi ma ya gaida momma ta amsa
tana washe hak'ora.
"Sultan ashe kuna hanya?"
Uhm....!
Yafad'a kamar an mishi dole.
To miyasa jiya da dare da mu kayi waya ba ka fad'amin yau za ku zo ba?"
"Na manta ne!
Ya fad'a yana yatsina.
Kodai ka fad'awa Daddynka, ni ce da ka rena ba ka fad'awa ba?
Omg.....momma please banaso irin tambayoyin nan naki, sosai suke haifa min da ciwon kai.
Ya k'arasa magana yana turo miki.
"K'atuwar harara momma ta wulga masa afakace, a fili Kuma ta k'ikk'iro murmushin dole ta ce
haba gadangana don nuna damuwa na akanka laifi ne?"
"Wani shegen murmushi Aliyu ya yi kafin ya ce kai....momma na fahimci yau K'orafi ki ke ji, to
Allah ya ba ki hak'uri.
"Zee-zee ta rik'o hannun barrister A zo mu tafi matar Yaya d'akinmu mu yi fira, wallahi ina
cike da farin ciki zuwanki gidanan ba k'adan ba.
"Nasan ko Meenat idan tadawo daga school ta ganki, haukace mana za tayi, saboda tun
lokaci bikinku bakinta bai huta da zance ki ba.
"Teema ma za tayi farin cikin ganinki.
Barrister A tayi murmushi ta sace kallon Aliyu, karaf.....suka had'a idanu ya kashe mata idonshi
d'aya batasan lokaci da ta lumshe golden eyes d'inta, daga bisani ta bud'e su fesss......akanshi
tayi mishi k'ayatattce murmushi, sannan ta bi bayan Zee-zee har suka shige d'akin idanuwan
Aliyu suna kanta. "A lokaci da za'a auna Bp momma za'a iske ya haura d'ari biyu da tamani, tsabar kad'uwa
gani abinda Aliyu yake yi wa barrister babban tashin hankalinta bai wuce mayatattace kallon da
ya bi ta da shi ba.
"Da kyar ta tattaro 'yar raguwar natsuwarta ta had'a da k'arfin hali ta dube Aliyu da
idanuwanta ba bu komai ciki face tashin hankali.
"Sul....tan....!
Ta kira sunanshi cikin rawar murya.
Na'am!"
Ya amsa yana kallonta.
Da fatar kana zaune lafiya da iyalinka?"
"Lafiya qalau momma ba wani matsala.
Shiru ya biyo baya jikin momma ya yi sanyi tana so ta tambayeshi yana had'a shinfid'a da
barrister, tana jin tsoron amsar da zai bata.
"Sai kawai tayi ta maza ta gyara zamanta, tana mushirikin murmushi ta ce ina fatar kana
sauke hakkinta yadda ya kamata?"
Kallon mamaki yake mata sai kuma ya murmusa tsaff....ya gane idan ta dosa sai ya ce sosai
ma kuwa momma duk abinda takeso ina mata.
"Gaban momma ya cigaba da dukan tara-tara babban tashin hankalinta bai wuce asiri da
Jarumi ya bata na kashewa Aliyu mazak'uta, sai gashi Aliyu yana fad'a mata yana shagalinshi
to.....ina zance asiri da suka yi mishi ana nufi ya karye.
"Gani yadda ta k'ura mishi idanu ba ko kaftawa yasa ya ce lafiya momma naga kin tsareni da
ido, kuma kinyi shiru?"
"Ta shiga kame-kame daga bisani ta yi nasarar cewa anyya kuwa Gadanga kana had'a
shinfid'a da yarinyar nan?"
Sam banga jikinta ya nuna hakan ba.
Tafad'a tana tsare shi da idanu, sosai wannan tambayarta ta tabashi haushi da takaici ya 6ata
fuska ya ce ki tambayeta momma za ta fad'a miki ko yau kafin mu baro Yola muna tare a d'aki
d'aya.
"Please....momma ki daina irin wannan bincike bashida amfani, ni fa ba k'aramin yaro bane
duk wani hakke aure nasani.
Kuma ina k'ok'arin sauke shi.
"Ni zan fita sai na dawo."
Ya k'arasa magana had'e da mik'ewa.
A dawo lafiya!
Cewar momma cikin yana yi na tsoro.
"Kaitsaye d'akinsu Zee-ze ya wuce ya tararda su suna fira yayin da Teema na kwance a jikin
barrister, sai wasa take da dogon bak'in gashinta.
"Sosai hakan ya yi mishi dad'i saboda yana k'aunar siblings d'inshi ba kad'an ba
miskilancinshi ke hanashi nuna musu hakan.
"Tsaye ya yi a bakin k'ofa yana kallonsu da girar ido d'age, Teema na arba da shi ta sha jinin
jikinta saboda Allah ya zuba mata tsoronshi.
"Zan fita"
Yafad'a k'asan mak'oshi.
Atsanake tad'ago tana fad'i adawo lafiya Allah ya bada sa'a!
Amin nagode!
Har juya ya sake waigowa ya ce Zainab ba abinci agidan naku ne da ba ki kawo mata ba?"
Ko tsabar rashin iya tar6o guest ne?"
"Cike da tsoro Zee-zee ta ce Yaya kasan momma bata bari adafa abinci da yawa.
Mtsss.....ya ja tsaki had'e da barin d'akin yana cewa ki tabbata kin gayawa chef Emmanuel ya
girka mata abinda za ta ci.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:02 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
Not edited!
*23*
Yana k'arasa fita zee-zee ta kalleta tana dariya ta ce gaskiya matar Yaya Yayanmu yana ji da
ke, Allah yasa kema haka ki ke ji da shi.
'Yar siriryar dariya tayi ta ce sosai ma kuwa.
Momma wacce tun fitar Aliyu take la6e tana sauraren firar tasu, ta zaro manyan idanuta tana
huci, bankad'o k'ofar tayi ba ko sallama ta bi su da kallo.
Gani yadda suma suke kallonta yasa ta wayace ta ce Emmanuel girkin Alhaji zai doura yanzu,
Zee-zee ta bi ki ku je flat dinku ta tayaki ki girkawa mijinki abinda zai ci.
"Da sauri Zee-zee ta d'ago tana kallon momma cike da zallan mamaki, ta ce "momma yaushe
na iya girki da har zan tayata?"
ki bar Emma ya dafa mata koda noodles ne.
makirin murmushi momma tayi kafin ta ce "miye amfaninta idan bata girkawa mijinta abinci ba?"
Idan ke ba ki iya ba ai ita ta iya
daga yau ki fara girkawa mijinki abinci kinji my daughter?"
Ajiyar zuciya barrister A tayi tana mai cigaba da kallon momma tana karanta yana yinta.
"Har zee-zee za ta sake yin magana barrister A ta katseta da sauri ta hanyar cewa, to
momma!
"Momma tayi murmushin mugunta saboda ganinta barrister A ta taso gidan huta uwa-uba
yana yin aikinta yaushe take da lokaci shiga kitchen har ta iya wani abu wai shi girki.
Atunaninta tun daga wurin girki za su fara samun matsala da Aliyu saboda ta san halinshi da
tsirfa, ba ko ne irin abinci yake ci ba.
Saboda haka shiyasa tayi amfani da wannan damar tafara aiwatar da nufinta akansu.
"Shikenan my daughter tashi maza ku tafi ki had'awa yarona delicious, yana ci kunnenshi na
motsi.
Ta k'arasa magana tana washe hak'ora na kissa da kissisina.
Hannun Zee-zee barrister A ta rik'o zo mu je Zee ki tayani kema daga yau ki fara learning.
"Ni ma zan je matar Yayanmu!
Cewar Teema tana sosa gashin kanta.
Kafin barrister A tayi magana har momma ta rigata cewa kema bi su ki koya.
"Har suka fice daga d'akin momma tana murmushinta na zallan mugunta.
Da suke iso compound idanuwan barrister A suka hango apartment d'in Maryam, ta k'urawa
wurin idanu tana mamaki yadda aka bar barandar wurin tayi k'ura, musanmman da tayi la'akari
ko ina na gidan tsaf-tsaf yake idan ka cire wurin.
Ajiyar zuciya ta yi ta kauda ganinta suka k'arasa flat d'inta.
A falon k'asa suka zauna zee-zee ta had'a kayan kallo, suna cikin kallo aka yi kiran sallar
la'asar, har barrister A tayi sallah ta dawo bata ga alamar Zee-zee da Teema zasu tashi suyi
sallah ba.
Sai tunanin dukansu suna period ne, don haka ta share su suka cigaba da kallonsu.
"K'arfe 5:00 ta buga Zee-zee ta kalli barrister A ta ce matar Yaya kin ce sai kin yi sallah, za
mu doura girki gashi har 5:00 o'clock ya yi.
"Barrister A tayi murmushi tana fad'i ko za mu fara girki nan zee-zee saidai gobe, saboda na
duba a store ba foodstuffs, kinga zuwa gobe Yayanki zai siyo.
"Shikenan matar Yaya bari na je sai na fad'awa momma tunda ita store d'inta akwai sai, tasa
akawo muku.
"Ba sai kin fad'a mata ba maybe fitarnan da ya yi zai dawo da su.
Daga haka su ka cigaba da firarsu har meenat ta dawo daga school, ta shigo da murnarta na
gani matar yayan nata.
"Lokaci sallar magarib ya yi still barrister A ce kawai tayi sallah, sosai abin ya daure mata kai
matuk'a ana nufi su duka uku suna menstruation period.
Sai kuma tabar tambayar k'asan zuciyarta.
Saida momma ta kira wayar meenat sannan suka koma flat dinsu, amma ba don ransu yaso ba
sun so tabarsu sai Aliyu ya dawo.
"Bayan tafiyarsu barrister A ta haura sama tayi wanka, ta shirya cikin California candy strip ba
k'aramin kyau rigar tayi mata ba.
Zanin ta doura akan rigar sakamakon tsagar da rigar take da a side by side, tayi sallar isha'i
tana gama sallah ta cire zanin ta like ta mayar a closet ta fice zuwa downstairs falo.
"Misalin k'arfe 9:00 na dare Aliyu ya murd'a k'ofa ya shigo cikin sallama, ta mik'e tsaye tana
amsa mashi tare da yi mishi sannu da zuwa, sannan ta isa wajen shi ta kar6i ledojin da ya shigo
da su.
"Ya amsa gaisuwarta yana kallonta kallo ne irin na kwalliyarki ta ban sha'awa, d'an zaman da
ya yi da ita akwai abubuwa da dama da ta mallaka da ke matuk'ar d'aukar hankalinshi, abu na
farko ta iya kwaliyya ko yaya ta sanya kaya sai sun kar6i jikinta, sun fito da kyakyawar surarta.
"Hakan na dauke mishi hankali ba kad'an ba.
Gashi ta iya tafiya ta jan hankali duk lokaci da take tafiya yana lura da yadda take rausaya,
ga66o6in jikinta na motsawa especially hips da boobs d'inta.
Idan kuma ya tsareta da lulu eye's dinshi, k'irjinta da fuskarta suna daukar hankalinshi, idan
kuma ya kusanceta k'amshinta yana tafiyarta ruhi da gangar jikinshi, saidai yak'i bari ta gano
hakan sau da yawa yana satar kallonta ne batare da saninta ba.
Tana zuba sanyayye murmushinta mai tsada ta wuce kitchen da ledojin da ta kar6a daga
hannunshi, ta duba abinda ke ciki kayan tea ne had'e da bread sai shawarma , ice cream da
kuma gassassun kaji sai k'amshi ke tashi.
Sai leda ta k'arshe mai dauke da tambari chicken republic restuarent, plates da spoons had'e
glass cup ta dauko ta wanke, ta juye abinci ta kuma doura kajin sama plate ta nufi falon ta
tararda ya haura sama, tasan wanka zai yi ta koma kitchen ta dauko drinks da ruwa.
'Bata jima da zama ba ya fito sanye da wandon pajama as usual ba riga, ya zauna a tsakiyar
rugs carpet, ya mik'e kafafuwanshi hannunshi ya kai ya dauke remote control ya canza channel.
"Ta kalleshi tana yaba fad'i da girman k'irjinshi a zuciyarta cikin wani shegen voice mai dad'i ta
ce "Yalla6ai ga abinci yanzu za ka ci ko sai zuwa anjima?"
"Ya Kalleta atsanake ya mayarda ganinshi akan Tv ya ce "Tunda na fita banci komai ba sai
coffee kawai, ko ke bakya ji yunwa ne?"
Murmushi tayi ta ce "inaji mana saidai ba sosai ba kaman kai.
Naso nayi girki kafin ka dawo koda na duba store ba foodstuffs"
Murmushi ya yi tare da girgiza kanshi yana cewa "barrister kenan ya za'ayi ki samu foodstuffs
anan saidai a apartment d'in momma.
Idan nayi wanka na fita tun