Showing 75001 words to 78000 words out of 85584 words
Chapter 26 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf
alamar you're finished. Da sauri momma ta sadda kanta k'asa tana jin wani masifaffen zafi da turiri a k'asan zuciyarta,
ta kuma sha alwashi ko ta wane hali sai ta dauki fansar abinda Jarumi ya yi mata.
Ba zai yu ba ita kadai sunanta ya 6aci a duniya dole su biyu ne zasu sha tsinuwa daga bakin
mutane duniya ba wai ita kadai ba.
Sannan wannan tozarci da ya yi mata iya saninta ba su shirya shi cikin tsarin plans d'insu ba,
wato nufinshi ita tun anan ya gama amfanin da ita shiyasa ya fallasata a idon duniya, hawayen
takaici suka zubu mata bata damu da ta goge su ba saboda wuta ce take ci a zuciyarta ba
kuma zata daina ruruwa ba har sai ta cimma burinta na gani bayan Jarumi da Barrister A domin
ita ce mutum ta farko da tafara challenges d'inta.
"Idanuwanta ne suka hasko mata wayar Meena da ta bari a gefen drawer gado, hannunta
har rawa yake yi ta dauki wayar, idan Allah ya taimake ta Meena bata saka security code a
wayarta, abu na farko da tafara yi shine calling d'in number Jarumi abin takaici wayar tashi a
kashe take. K'awarta Dijama ta lalabo ringing biyu zuwa uku tayi picking muryarta adak'ile ta ce ''Hello.....
Hello....Dijama!
Wa ke magana...?
Cewar Dijama duk da tagane muryar momma.
Ban so tsohon iskanci Dijama atsawon zaman da nayi da ke ko sautin tusa ta kika ji yaci ace kin
sheda ta balle muryarta.
"Allah ya ba ki hak'uri Zaituna ni sai yanzu na sheda ki, da farko naji muryarki tayi dususu
shiyasa ban gane ki ba.
Zaituna wani mugun abu naga yana kara kaini gidan rediyo da gidan television ke har ma da
kafaffen sada zumunta, shin ke ce da kanki kika aikata wannan mugun aikin ko kuma ussaina ki
ce....?
Mtssss.....momma ta bata amsa da dogon tsaki tare da cewa uwata ce ta aikata ba ussaina ta
ba, look.....Dijama ban kira ki ba don tambaya da bada amsa ba na kiraki ne don ki taimaka min
ki zo ki fitarda ni daga asibiti nan, tun kafin ciwo na gaskiya ya kamani.
Uhmm.....cewar Dijama har tana ta6e baki kina wane asibiti ne....?
"National Hospital a room 9 ki zo min da kaya nasaka saboda ni da wanda yake tsirara duk
d'aya.
"To.......shikenan gani nan zuwa ki zama ready kada gari taimako ni ma a zuba ni a Median.
Mtsss.....momma ta ja tsaki tare da hanging up.
*FEW MINUTES AGO*
Dijama ta parker motarta a parking space d'in asibiti, ta fito cikin sauri ta nufi cikin reception d'in
asibiti ta bi corridor da zai sada ta da room d'in da momma take kwance, ta tura k'ofa ta shiga
momma tana ganinta tayi zubur ta mik'e zaune tun kafin Dijama ta zauna ta ce "Bani kayan na
saka banso yara nan su shigo su ganki. "A yatsine ta bud'e handbag d'inta ta ciro brown jallabiya ta mik'a mata, tasaka jikinta har rawa
yake yi ta yanne kusan rabin fuskarta da mayafin rigar.
"Har suka fice daga d'akin zuwa parking space ba su ci karo da idon sani ba.
***----***---*****----**
*MADALLAH VILLAGE*
Barrister A ta gallawa Uncle Suraj harara tare da fad'in wallahi da sannu Allah zai toni asirinka
uncle, sai ka girbi abinda ka shukka da hannunka mugu bak'in azzalumi.
"Ko kad'an fuskar uncle bata nuna ya ji zafin kalamanta ba, sai ma wani shegen murmushin
da ya yi ya d'aga pistol d'in hannunshi ya yi pointing d'inta cikin kakkausar murya ya ce "Za ki
zauna ko sai na har6e ki ne...?
Sai da tasake zuzzuba masa harara kafin ta zauna tayi bala'in daure fuskarta ta ce "Na zauna
sai ka yi gaggawar fad'amin uban me zan maka da ka satoni mugu kawai mai fuska biyu...?
"Numfasawa ya yi tare da gyara ya zamanshi ya ce "ina fatan kina da labari halin da in laws
dinki suke ciki....?
Dama ka satoni ne don ka sanar da ni halin da suke ciki...?
Cewar barrister tana aika masa da wani mugun kallo.
Cikin kwanciyar hankali ya ce "ah'a......ba ko d'aya.
To kayi gaggawa sanar da ni dalilinka saboda banida lokacin 6atawa tare da kai.
"Barrister kenan ki bi ni ahankali saboda duka mutanen ki suna k'ark'ashin ikona, ba ki da
zabi sai abinda na za6a miki.
"Zaro idanuwanta tayi cikin kad'uwa ta ce "me kake nufi da wannan kurman zance naka....??
Murmusawa ya yi tare da mik'ewa tsaye ya nufo wajenta, yana mai cigaba da murmushi da
sauri ta tashi tsaye muryarta tana rawa ta ce "kar ka sake ka matso ku sa da ni.
Dariya ya kwashe da ita tare da fad'in ki biyo ni domin ki sami amsar tambayar da kika yi min
saboda ni ma banida lokaci 6atawa wajen amsa miki tambayoyin ki.
Mtsss.....ta ja tsaki ta bi shi abaya kaman kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Upstairs ya nufa haka ta dinga bin shi har zuwa k'ofar wani d'aki da ke rufe, ya yi using d'aya
daga keys d'in hannunshi ya bud'e k'ofa.
Da fuskar barrister Z tafara cin karo da ya ke tana facing k'ofa tana d'addaure, da igiyar akan
robber chair. "Cikin firgici da tashin hankali barrister A ta bangaje uncle Suraj tak'arasa
wajen Barrister Z ta durk'usa tare da cire mata salatif da aka rufe mata baki da shi.
Kafin tayi magana ta hango malam shima adaure kama barrister Z, sai kawai ta mik'e tsaye ta bi
d'akin da kallo maryama da Baaba laraba idanuwanta suka hasko mata su adaure, yayin da
Sa'eed yake daure duk fuskarshi ta kumbura jini ya bushe a gefen bakinshi da alama ya daku
ba kad'an ba. Gaba d'aya jikin barrister A ya dauki rawa kaman mazari, a fusace ta nufi Uncle Suraj da ke
tsaye ajikin k'ofa yana zabga mata murmushi sai kace wanda ya aikata abin k'irki.
"Kai mahaukaci ina ne uncle?"
Me wad'annan bayin Allah suka yi ma da za ka kawo su nan??"
Bebs.....uncle Suraj yana yi ma momma aiki ne.
muryar barrister Z ce ta d'aki kunnen barrister A wacce ta Juyo da sauri cike da zallan mamaki
tacce momma kuma??"
Kwarai kuwa tare suke.
Uncle ya girgiza kanshi tare da fad'in point of correction Barrister Zarah....Zaituna tana min aiki
ne ba ni ne nake mata aiki ba yaushe tsohuwar kilaki kamar Zaituna take da matsayin saka
Jarumi kamata aiki.
Harararshi barrister A tayi tare da fad'in dallah malam ka rufe min bakinka....ka bar ni nayi
magana da k'awata.
Mak'e kafad'a ya yi tare da ta6e baki.
barrister Z ta ce
lokaci da jirgin mu ya yi landing dama nace miki zan kira ki da zaran mu iso, kafin na kira ki sai
kawai ga Uncle Suraj ya ce "ke kin ka aiko shi ya yi picking dinmu, kasancewar nasan
matsayinshi a gidan da kirkin shi da kike fad'a yasa ban 6ata lokaci wajen dogon nazari ba na
umarce malam muka shiga motarshi daga nan ba mu sake sani idan kanmu yake ba, sai daga
baya muka dawo hayyacinmu muka tsince kanmu anan a d'addaure kuma anan muka tararar
da Maryama da Baaba har ma da Sa'eed.
"Uncle ya shafi gajeren gemunsa ya tanko zuwa gaban barrister Z ya duk'a ya dauki salatif
d'in da barrister A ta cire mata, yana fad'in to fad'i ba'a tambayeki ba labarin ya isa haka.
Na fahimci idan na zuba miki ido sai ki cinye min lokaci da labarai.
Ya nufi wajen barrister A ya tank'e hannunta ya jata zuwa waje, ya yi wulgi da ita ta fad'i k'asa
cikin rashin imani ya murzawa k'ofa key ya rufe.
Barrister A ta mik'e da sauri ta rik'o gefen rigarshi tana rok'onshi don Allah Uncle Suraj kayi
hak'uri ka saki bayin Allah nan.
Me suka yi maka ne?
Batare da ya tanka mata ya nufi steps yana takawa ahankali, arud'e ta bishi har tana had'awa
da tuntube uncle.....please ka zo ka bud'e su musanmman malam a haife ya haifeka.
Ya k'arasa sauka k'asa ya nufi kuejarar da yake zaune ya zauna, sai wani karkad'a k'afafu
yake yi da gudu tak'araso ta zube gabanshi tana mai cigaba da rok'onshi, gani ko matsowa bai
yi ba balle tasa ran zai kar6i buk'atarta.
"Gani yanda ya yi banza da ita yasa ta mik'e tasoma zazzaga masa kwadon bala'i da masifa
nan ma kamar ba da shi take ba.
"Gani yak'i tanka mata yasa ta sassauta murya ta ce "zUncle laifi me muka yi maka ne da ka
kawo mu wannan wuri...?
Ya gyara zamancshi tare da yi mata shegen murmushin nan nashi, ya ce "yanzu kika yi
tambaya mai amsa sai ki nemi waje ki zauna domin ba zan ba ki amsa kiyi min tsaye aka ba.
"Batare da gardama ba ta zauna k'asa akan tiles tana kallonshi.
Na sato ki ne saboda kina so ki taimakawa Maryama, nayi kidnapping d'in barrister Z da kakan
ta saboda suna so su taimaka miki Maryama ta dawo hankalinta na sato Sa'eed ne domin inaso
ya sanar da ni duk wani shirinki akan Maryama.
"Me Maryama tayi maka ne da ba ka so samuwa lafiyarta?"
Saboda ta chanchaci ta dauwama a haukace, shine hukunci azzuluma mayaudariya irinta.
Maryama ita da mijinta mugaye ne duk abinda na zama a yau su ne sila.
Barrister A ta galla masa harara tare da fad'in uncle banso wasa da hankali idan za ka yi
magana Just go straight forward ka ce ba momma kake yi ma aiki ba, ita ce take maka aiki
kenan da hannunka a haukan maryama...?
Murmushi ya yi tare da fad'in kwarai kuwa hatta abinda ya faru da Zaituna a yau ni ne na
shirya shi.
"Saboda me Uncle an maka wani laifi ne da ka za6i ka tarwatsa farin ciki iyali guda....?
Kafin na tartsawa musu farin cikin su ne suka fara tarwatsa min nawa, duk abinda na aika a
yanzu daukar fansa ne akan d'an uwana M Ardo.
Nayi amfani da Zaituna ne kawai don na taka ta domin cimma burina.
*LABARIN JARUMI UNCLE SURAJ ARDO*
Uncle Suraj ya gyara zamanshi tare da fad'in "Sai ki karkad'e kunnenki da kyau ki sha labari,
kuma duk abinda zan fad'a miki na rantse da ubangiji da ya busa min numfashi babu k'arya
acikinsa.
Karo na farko da barrister A ta ji wata 'yar natsuwa ta saukar mata, saboda ta k'agu ta ji laifi
da M Ardo da Maryama suka aikata masa da har ya za6i ya jefa rayukansu cikin mummunan
hali, ga kuma wasu bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba. kaman ita da su barrister Z yana so
ya shafe su. "Nan da nan annurin kan fuskar Uncle Suraj ya dauke chakk.....kamar an yi ruwan sama an
dauke, saida ya dauki tsawon lokaci kafin ya ce
kaman yanda kika
sami labari ni maraya ne, mahaifiyata ta rasu kuma ni kadai ta haifa.
A yanda na samu labari da ga bakin Dada ta ce ko ganina bata yi ba Allah ya kar6i ranta.
Dada wacce ta maye min gur6in mahaifiyata ta shayar da ni tare da d'anta M Ardo alokaci bai
wuce shekara d'aya ba.
Tun kafin na fara wayo nake shan gori da hantara daga d'an uwana M Ardo, a koda yaushe
yana kirana da marar sa'a a rayuwa wanda tsabar rashin sa'ar sa ko nono mahaifiyarshi bai sha
ba.
sai na kishiyar uwa ya sha ya kan ce da ni ba don shi ba da tuni na bi uwata k'iyima.
Lokaci da na fara wayo na fahimci idan maganganu shi suka dosa, duk lokaci da ya ce da ni
haka sai na fashe da kuka naje wurin Dada na sanar mata.
ta rarrashe ni da kalamai masu dad'i, shi kuma tayi masa dukan tsiya.
Dada tana matuk'ar k'aunata zan iya cewa fiyye da 'ya'yan cikinta, kuma duk cikin 'ya'yanta idan
kika cire M Ardo kowane su yana so da k'aunta.
M Ardo ya tsane ni tsana mai tsananin gaske wacce har takai yana hassadan cigaba na, ban
tabbatar da hakan ba sai lokaci da na had'u da Maryama.
"Barrister A ta katse shi da sauri ta hanyar cewa wacce Maryama....?
kaitsaye ya ce Maryama mahaukaciya uwargidan M Ardo.
Barrister A ta girgiza kanta cike da d'ibin mamaki ta ce "cigaba ina saurare ka.
"Na had'u da maryama a Ahmadu Bello university Zaria[ABU ZARIA] shekarar 1972 kusan
kusan shekara 48 kenan.
Alokaci ina karatun degree na ina shekarar k'arshe ita kuma tana shekarar farko, department
d'inmu d'aya kasancewar mu mun fito gari d'aya wato Yola yasa muka fara zumunci daga
karshe alak'ar mu ta tashi daga zumunci zuwa zazzafar soyayya mai k'arfin gaske ina matuk'ar
k'aunar Maryama Kaman numfashina haka ita ma take sona. Ban ta6a tsanmani akwai wani mahaluk'i da zai iya raba Maryama da soyayyata ba koda
mahaifanta ne, ashe gajeren tunanina ne ya bani hakan.
Na kammala karatu na cike da nasara ba al'afahari ba duk yawan 'ya'ya Ardo ba wanda ya
kai basira ta, Allah ya albarkace da ni kwakwalwa mai sauri rik'e abu komai girmansa ko kuma
k'ank'ata shi zan iya cewa wannan baiwar ita ce tak'ara jayo min zazzafar kiyayya daga d'an
uwana M Ardo, saboda ina kammala karatu mahaifinmu Allah ya jik'ansa. Amin summa Amin!
Cewar Barrister A tana mai talla6e kumatunta.
Yayin da Uncle Suraj ya cigaba da cewa duk wani kasuwanci na mahaifinmu a wancce lokaci da
ni ake tafiyar da shi, duk wani sirri na dukiyar mahaifinmu ba wanda ban saniba.
M Ardo hassada da bakin cikina kaman zasu kashe shi saboda haka ya kudurta anniya duk
wani farin cikina, sai ya yi awon gaba da shi.
Sai ya fara bin bokaye da malaman tsinbu duk don a shiga tsakanina da mahaifina ya cire ni
daga cikin kasuwancin sa, tsafi gaskiya mai shi sai gashi na wayi gari duk abinda na ta6a sai ya
lalace, sannu-sannu na fara janyowa mahaifina asara wacce yana daff....da afkawa kariyar
arziki da mahaifina ya fahimci abin daga gareni ne sai, ya fara daure min fuska baya so ganina ya tsane
ni daga k'arshe sai cewa ya yi na daina zuwa kasuwa har sai ya nemi ni, abin mamaki yana cire
ni daga dukiyarsa sai gata dawo tana hab6aka fiyye da farko, ban gama jinyar kora da
mahaifina ya yi min ba sai ga wani sabon al'amari maryama za ta aure d'an uwana M Ardo ba ni
ba.
Ranar nayi kuka kamar raina zai fita
Dada ce kadai mai rarrashi na, ba k'aramin fushi Dada tayi da M Ardo a dalilin ta ce ya hak'ura
da auren Maryama saboda ni ne nafara neman aureta, amma sai ya k'ekyashe k'asa ya ce
Allah ya kashe shi babu wanda ya isa ya raba shi da maryama.
inaji ina gani M Ardo ya aure Maryama, kuma ba wanda ya nuna masa kuskure sa saboda
malamin shi ya riga ya rufe masa bakin mutane ba wanda zai iya tanka masa.
Washe gari da aurensa da maryama ya zo ya same ni a d'akina da ke soro gidanmu, cike da
izzgilanci yake kallona kafin ya ce "Suraj dama na gayamaka bakada sa'a a rayuwa amma ba
ka yarda ba, sai gashi ka fara ganin zahiri da kanka.
"Yanzu duk abinda ka mallaka ya dawo nawa, hatta maryama da kake hauka akanta, yanzu
tawa ce kad'an ka fara gani daga cikin k'iyayyar da nake maka.
Tsabar takaici da wuta tsanar sa da ke ruruwa a zuciyata ya hanani tanka masa, har ya gama
tsoki burutsun sa ya fita, kawai dai ina ta sharar hawaye barrister A kiyayyar 'yan uba bala'i ce
da kukana nasame Dada na kwashe duk abinda yafaru na sanar mata, ita kuka ni kuka daga
k'arshe dai ita ce ta lallashe ni ta kama shanunta da ke k'iwo ta sayar ta bani kud'i na ja jari, na
fara kasuwanci saidai kashhh....ban maida watani uku ba duk yawan kudin suka lalace,
kasuwancin ya rushe.
"Ina cikin wannan halin muka waye gari mahaifin mu ya rasu, bayan an raba gado an ba wa
kowane mu hakkinsa a dare da ba zan ta6a mantawa ba sai ga M Ardo ya zo min shi da
abokinsa Kabir, cike da izza da zallan izzgilanci ya umarce ni da na mallaka mishi nawa gado
ba musu balle gardama na tsince kaina da dauko masa takardun dukiyata na ba shi, ya kalle ni
yana dariyar mugunta ya ce "Suraj!
na ce na'am Yaya!
Ya ce inaso ka shiga duniya kayi nesa da nan karka dawo har abada, nan ma sai na tsince
kaina da cewa to.....Yaya.
washe gari ko sallar asuba ban yi ba na had'a kayana ban