Showing 69001 words to 72000 words out of 85584 words
Chapter 24 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf
*Time:-10:00am*
Barrister A tana tsaye a kitchen tana ba ma 'yan aikinta umarni abinda zasu girka mata a
matsayin breakfast, suka jiyo wani shegen heavy knock ta Kalle Bintu ta ce "Bintu je ki gani
wanene ke min knocking da sassafe nan.
Bintu tana bud'e k'ofa taga momma a tsaye jikinta sanye da sleeping dress, sai d'an wani
siriri scarf da ta yane kanta da shi ta ce "ina kwana momma?"
Wulak'antattace kallo ta watsawa mata tare da sa hannayenta ta tureta gefe, ta shigo cikin falon
ranta a 6ace ta shiga kwalawa barrister A kira "ke Amina!
Amina!"
Kina ina fito ki fad'amin ubanda ya baki izzini dauke maryama daga gidanan?"
Jikin barrister ya dauki rawa ta zazzaro idanuwa cabdijam....wane munafuki ne ya fad'a mata
ni na dauke Maryama.
A fusace momma ta shigo kitchen d'in tashiga k'arewa Barrister A kallo mai cike da tsana, yayin
da barrister A ta tsareta da nata idanuwa ba alamar tsoro babu yabo ba fallasa ta ce "ina kwana
momma?"
"Ke saurara bak'ar munafuka alguguma har ni za ki nemi ki tonawa asiri, wallahi kiyi kad'an
fad'amin menene hujjarki na dauke maryama daga gidanan?"
Rolling idanuwa Barrister tayi hankalinta kwance ta ce "wai saboda kawai ki sami hujja momma
kika shigo min a hargitse.
ni wallahi na dauka ma gobara kika yi, Kalle kayan jikinki momma wannan sam bai dace
tsohuwa kamanki tana yawo da sleeping dress a farfajiyar gida ga katti bila adadin kiyi ma
kanki fad'a mana.
Ba ma wannan ba wane munafuki ne ya gayamiki ni ce na dauke maryama?"
Sororo da baki sake momma take kallon barrister A kafin tayi kwafa ta ce "kiyi katon kuskure
Amina kuma tabbas sai kiyi nadama mafi muni a rayuwarki, ki rasa wanda za ki k'aluballanta sai
ni tanuna k'irjinta da yatsa ta girgiza kai ba ki san wacece ni ba.
Shiyasa kika yi min kutse don tsabar iskanci kina tambayata wanda ya gayamin ke kika dauki
maryama to a Cctv camera naga lokaci da kika fita da ita ke da Teema da bak'in munafuki nan
Sa'eed.
"mtsss.....Barrister taja tsaki tare da fad'in wacece ke momma? Face bak'ar azzuluma
muguwa, kina matsayi mace kuma uwa amma bakida imani balle tausayi ko kad'an a zuciyarki.
kuma Cctv ki ya gayamiki k'arya ni ban dauki maryama, saboda haka don Allah ki fita ki bani
wuri banso haukar tsofa.
Nunata da yatsa momma tayi ta ce "Ni za ki gayawa maganar banza Amina?
"Ke uwata ce da ba zan gayamiki maganar banza ba, kisani momma Ubangiji yana ara
mana lokaci mu yi amfani da shi mu nemi duniyarmu da lahirarmu, amma wasu dolaye masu
6attaciyar dabara irinki, sai su yi amfani da lokacinsu su ci karensu babu babbaka.
momma ki sani ubangiji ya ara miki lokaci har na tsawon shekaru 28 kina shagalinki batare da
wani ko wata ya ce da ke uffan ba, a yanzu kuma lokacin naki ya k'are don haka bakida sauran
dabara kiyi amfani da d'an gajere lokaci da ya rage miki, ki tubawa ubangiji ki rok'e gafararsa da
wanda kika zalunta. Ki gyara abinda kika 6ata tun kafin lokaci ya k'ure miki. Matsowa momma tayi daff...da ita tadafa kafad'arta ta ce "karki damu da ni ki damu da kanki
domin komai zai iya faru da ke, na rantse da Allah idan har ba ki fad'amin inda kika 6oye
maryama ba sai na salwantar da rayuwarki.
"Ture mata hannu Barrister tayi tare da kauda fuskarta tamkar abinda tafad'a bai firgitata ba,
ta matsa jikin kitchen cabinet ta jingina jikinta had'e da rungume hannayenta a k'irji cike da
natsuwa ta maida ganinta akan fuskar momma ta ce "Ikon Allah!
Wanda yafi gaban mamaki momma me na tare miki, da za ki zo min flat da sassafe ko breakfast
ban yi ba kina min barazana da mutuwa?"
Ni abinda yake bani mamaki ke nan da kike ashe za ki iya kashe mutu, to.....fad'amin mutum
nawa kika kashe sannan kuma mutum nawa kike da burin kashewa nan gaba?"
ta k'arasa magana had'e da takowa ta iso daff....da momma ta cigaba da cewa nasan ina
d'aya daga cikin mutane da kike da burin kashewa saboda ko yanzu kin fad'a sai kuma
maryama, to....amma ni abinda ban gane ba surukata shin har da mijinki m Ardo yana ciki
jadawalin mutane da za ki kashe....! Hannu momma ta d'aga da zumar ta wanka mata bahaggon mari, cikin zafin nama tayi
karaf....ta rik'e mata hannu cikin fushi da tafarfasar zuciya ta zuba mata manyan idanuwanta da
suka fara canza colour ta ce "Don't ever try to raise your dirty hand on me or else are will break
your bones zan manta da cewa ke kika haifi Aliyu understood?" Ta k'arasa magana had'e da wulgi da hannun momma.
Cikin tsananin 6aci rai irin wanda momma ta jima rabon da tayi irinsa, take kallon barrister A
kafin ta ce "Don't you dare to talk to me like thats Amina.
Shegen murmushi barrister tayi tare da fad'in oh....haka ne surukata to ya kike so nayi miki
magana?"
Baya nasan ke azzuluma ce, zaluncinki ba wai iya kan kishiyarki ya tsaya ba har da 'ya'ya da
kika haifa da cikinki.
kaicho ki momma kin ji haushi kuma inaso ki sa aranki yanzu na fara bankad'o ma'adanai
sirrikanki.
"Daga haka ta ra6a ta gefen momma ta wuce tana karkad'a mata mazauna ta haura upstairs
tashige bedroom d'inta.
Wani irin zufa ne ya karyowa momma tun daga tsakiyar gadon bayanta har zuwa dudduge
k'afarta, gashi night gown d'in jikinta silk ce nan take ta shar6e da zufa kaman an watsa mata
ruwa cikin tashin hankali marar misaltuwa ta baro flat d'in tanufi nata, a falo ta tararda Teema
zaune tana ganinta ta tintsire da dariya ta taso daga mazauninta ta nufo wajenta, ta shiga
girgiza kanta gashin kanta na wargajewa cikin wata irin rikitattaciyar murya ta ce "ki daina
wahalarda kanki momma na riga da na 6ata komai, bari na fad'a miki kad'an daga cikin abinda
na aikata ni ce nan na lalata asiri da kika yi ma Ya sultan kada ya kusance matarsa.
Ba iya wannan kadai ba ni ce na nunawa matar yaya inda kika binne layoyin da kika yi ma
Daddy asiri ya manta da maryama, ba iya wannan ba momma nice na fad'awa matar yaya za ki
kashe maryama.
Amma duk wannan abu da nayi momma, bai rage min jin rad'ad'in abinda ke kika aikata min
ba. momma kin 6ata min rayuwa kin cuceni me nayi miki da kika samarda ni ta k'azamar hanya
me nayi miki momma?
Da aurenki momma kika aikata zina kuma don tsabar rashin jin tsoro Allah, kika kawoni cikin
'ya'yan halak momma me zai faru da rayuwata idan har Ya sultan yasan cewa ni da shi ba
ubanmu d'aya ba, wane hali zee-zee da meena zasu shiga idan suka gano mahaifiyarsu ta
aikata zina har tasamar musu da k'anwa 'yar zina shin da wane ido za ki kalle Daddy ki fad'a
masa kin aikata zina da k'aninshi Suraj me kike tsanmani zai faru idan na sanarda wani ko wata
a cikin iyalan abind......
Teeema......da mugun sauri momma ta rufe mata baki had'e da kiran sunanta, don girman Allah
Teema ki rufamin asiri kada ki fad'i wannan magana nasan ban kyauta miki ba amma ya na iya
da k'addara.
Teema wacce ke gunji kuka kamar ranta zai fita ta gantsarawa momma cizo ga hannu babu
shiri momma tasaki mata baki.
Teema ta durk'ushe k'asa tasaki wani irin kuka mai ciwo cikin murya kuka ta ce Allah ya isa
tsakanina da ke momma Allah sai yasaka min wallahi ba zan ta6a yafe miki ba.
Ta k'arasa magana had'e da mik'ewa tanufi wata flower vessel na glass ta jefata jikin plasma,
ta tararatse ta bi duk abinda ya kai hannunta tana kuka tana farfasawa, da gudu bala'i Zee-zee
da Meena suka fito daga bedroom dinsu cikin tashin hankali suka yi kan Teema had'e da
rirrik'eta. Sai cewa take ku barni na lahanta kaina ko zai rage min ciwo da nake ji a zuciyata.
"Haba Teema.....haba wannan wane irin tashin hankali ne, har sai yaushe za ki daina d'aga
mana hankali a gidanan...?
Cewar Zee-zee tana girgiza kafand'u Teema.
Cikin muryar kuka Teema ta ce har sai lokaci da momma ta bud'e bakinta tafad'awa duniya
wacece ni, da kuma irin rayuwar da ta za6a min anan gaba.
Ta k'arashe magana had'e da ture su ta 6alla da gudu ta shige d'aki ta rufo k'ofa har da su
murza key.
"Cirko-cirko suka yi tare da kallon-kallon atsakaninsu, su Kalle momma ta Kallesu Meena ce
ta kawo k'arshen shiru nasu ta hanyar cewa momma me kuma kika sake yi ma Teema?"
"Saida momma tayi ajiyar zuciya kafin ta ce "Ba abinda nayi mata matsiyata iskokanta ne
suka motsa, amma ni me zan mata.
"Wannan karo Zee-zee ce tayi magana kwata-kwata ban yarda da wannan al'amarin naki ba
momma, a koda yaushe iskokan Teema suka tashi duk yawan mutane gidanan ba su tsinewa
kowa sai ke, yau kuma da kunnena naji Teema tana miki Allah ya isa kai.....ina momma wannan
lamarin naki akwai lauje cikin nad'i Zee-zee ta k'arashe magana tana girgiza kanta. "Momma batasan abinda zata ce da su ba, gaba d'aya noti kanta ya kwance shiyasa ta bi ta
gefensu ta shige bedroom d'inta
***---***---****----**
Jirgin da Daddy ya biyo daga Lagos zuwa Abuja ya yi landing a Nnamdi Azikiwe international
airport Abuja, Daddy yana fitowa daga jirgi ya kira direbanshi ya zo ya yi picking d'inshi suna
cikin tafiya bisa hanyar zuwa gida message ya shigo wayarshi sai kawai ya tsince kanshi da
fad'uwar gaba, ya bud'e sak'on yayin da gabanshi ke cigaba da fad'uwa *_idan har kanaso
kasan wacece matarka Zaituna Ka yi gaggawa ka zo western dreams hotel room 126_*
Rass....rasss....! Sautin da ke fita daga k'irjin Daddy zuciyarshi sai halbawa take da k'arfin
gaske, ya bud'e baki da kyar ya ce da direbanshi ya wuce da shi western dreams hotel.
Jeeddah Aliyu.
[7/27, 12:25 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*38*
Barrister A tayi wanka ta shirya ta nemi wuri ta zauna tana jiran barrister z ta kirata, ta ce sun
iso tazo tayi picking d'insu har k'arfe 12 noon ya yi bata ji daga gareta ba.
Ta kira wayarta yafi a kirga sai kawai taji matar nan mai zazzak'ar murya tana fad'in wayar a
kashe take.
"Da sauri ta mik'e tsaye tafito compound ta yafito Daniel da hannu ta tambayeshi ina Sa'eed
ya ce mata tun jiya yalla6ai Aliyu ya aike shi poultry house d'inshi da ke suleja ya kai ma
manager sak'o, jiya bai samu zuwa ba shiyasa yau ya tafi tun da sassafe amma shima ya yi
mamaki abinda ya hanashi dawowa har yanzu. Sai kawai ta tsince kanta da fad'uwar gaba mai tsanani, da sauri ta juya flat d'inta babban
takaicinta bai wuce contact d'in Jamal da bata da shi ba.
Gani zata 6atawa kanta lokaci da fargaba yasa ta haura sama ta dauko handbag da makullin
mota, har tayi reverse ta fita daga gidan tana jin fad'uwar gaba kaitsaye gidan Jamal ta nufa.
***---****----****--***
Direban Daddy yana danno mota a western dreams hotel.
Daddy ya jin fad'uwar gabanshi ya k'aru fiyye da farko, direban ya yi parking ya fito ya bud'ewa
Daddy k'ofa yayin da Daddy bai ma san sun iso hotel d'in balle yasan direban nashi yana bude
masa k'ofa.
Gani shiru nashi ya yi yawa yasa direban ya d'an sunkuya had'e da tura kanshi cikin motar kana
ya ce "Alhaji mun iso!
Firgigit......! Daddy ya yi kaman wanda aka tadda daga bacci ta hanyar watsa masa ruwa musu
masifar sanyi.
Cikin mutuwar jiki Daddy ya zuro k'afafunshi k'asa kafin ya yunk'ura ya fito da gangar jikinshi
waje.
"Batare da Daddy ya kalle direbanshi ba ya ce "Ka zauna a mota ka jirani ina zuwa.
Yanda yake tafiya kawai zai tabbatar maka da baya cikin natsuwarsa, yana zuwa bak'in k'ofar
d'akin ya taka birki almost 3 minutes yana tsaye shi bai yi knocking bai kuma juya inda yafito ba.
Can ya ga wankin hula zai kaishi dare ya yi kasada ya daura hannunshi, a jikin k'ofar ya shiga
knocking ahankali.
Jarumi da ke haye da ruwan cikin momma ya dakata da abinda yake yi, ya tsurawa k'ofar
idanu, yayin da Daddy bai fasa knocking d'in ba.
"Cikin tsanani gajiya Jarumi ya mirgina gefe ya kwanta yana sauke numfashi, batare da ya
kalle gefen da momma take ba ya ce "Zaituna ina gani room service ne ya kawo abincin ki tashi
ki kar6o.
Batare da ta furta uffan ba ta mik'e da kyar saboda ta gurzu a wurinsa ba k'adan tsirara
haihuwar uwarta ta mik'e, ta dauki bathrobe tasaka ta nufi k'ofa wacce har zuwa lokaci Daddy
yana cigaba da knocking d'in hankalinta a kwance tayi unlock d'in k'ofar saboda sam bata kawo
tunani yau ce ranar da zata kasance ranar tonuwar asirinta ba, tana bud'e k'ofa idanuwanta
suka sark'e da na Daddy wanda ke tsaye sai faman tattara babbar rigarsa yake, ga kuma
matsananci fad'uwa gaba da yasaka shi agaba, saura kirisss.....numfashin Momma ya fita daga
gangar jikinta yayin da duhu ya mamaye gani Daddy kwakwalwarsa ta daina aiki ta tsaya
cak.....tsananin rud'ewa da tashin hankali marar misaltuwa ya sanya momma ja da baya,
muryarta na rawa da kyar ta had'a ruguwar jarumta da ya rage mata ta shiga had'a kalma da
kalma tasha bak'ar wahala kafin tasamu ta had'a. kalmar Al....ha..ji...!
Jarumi da ke kwance daga shi sai boxer saboda bayan tanufi k'ofa yasaka boxer d'in, dalili
kuwa yasan dole room service d'in ya shigo don haka bai kamata ya ganshi naked ba.
"Cikin wani irin yana yi Daddy ya bi bayanta yayin da idanuwanshi suka sauka akan Jarumi,
cikin tashin hankali yake kallonshi gani haka yasa Jarumi ya mik'e zubur.....da zumar ya ture
Daddy ya gudu, cikin zafin nama Daddy ya cafke dantse hannunshi ya kuma fizgo shi da k'arfi
har ya yi nasarar tureshi bisa gado, Momma wacce ke gefe tsaye ta kurma mashahuri ihu
sakamako yanda taga Daddy yana dambe cirewa Jarumi masks, kururuwa take yi da dukan
k'arfinta shiru nata ya tsaya ne cak....adai-dai lokaci da Daddy ya yi nasarar yaye face masks
d'in, fad'uwar gabanta ya k'aru a dalilin fuskar da take kallo wacce tsawon rayuwarta bata ta6a
koda mafalkinta ba, kafin tayi yunk'uri tambayarshi waye shi ya akayi ya rikid'e ya zama
Jarumi?"
Shin ko Jarumi yana canza launi ne ko kuma yana da sihiri da yake canza kamanu, idan kuwa
haka ne tabbas ya cuceta me zata cewa Daddy ta tabbata koda zata mutu tasake dawowa
duniya ta cewa Daddy abokin fasik'ancinta d'an uwanshi ne Suraj Ardo ba zai ta6a yarda ba.
Daddy yana cire masa face masks ya koma gefe yana kallonsa da idanuwanshi da sukai jajir,
yayin da numfashinsa ya shiga daukewa yana dawowa ya misalta shekarun abokin fasik'ancin
momma wanda ko d'anta Aliyu ya girmeshi nesa ba kusa ba, saidai ya zo tsaran Meena ba ma
Zee-zee ba. "Cikin mugun tashin hankali momma ta nufi wajen duplicate d'in Jarumi, kafin ta aika masa
tambayar da ke nuk'urk'usar zuciya da kwakwalwarta kafin tayi wani yunk'uri 'yan Median suka
bankad'o k'ofa suka cika d'akin kowane su yana k'ok'arin daukar abinda zai watsawa duniya.
"Gani haka yasa Daddy ya k'ara firgita, numfashinsa ya tsaya cak....ya sulele k'asa ya some.
Momma tafasa ihu tayi kanshi tana jijjiga shi yayin da press sai ya k'ara cika d'akin suke, kamar
turo su ake yi yayin da wasu nan take suka watsa akan social Median, asirin uwargida M Ardo
ya tonu an kamata tana fasik'anci da d'an cikinta, wasu maganganu ba dad'i ji.
Yanda momma taga flash d'in camera yana shawagi ta ko ina akanta, yasa tayi suman k'arya.
Ma'aikatan hotel d'in ne suka kira ambulance aka turo Daddy da momma akan gadon daukar
marar lafiya, sai lokaci direban Daddy yaga abinda ke faruwa.
Alokaci da ake k'ok'arin fitowa da Daddy da momma duplicate d'in Jarumi ya sami hanyar
guduwa.
Kaitsaye national hospital akai nufa da su har a can....basu tsira daga Median ba saboda biye
suke da su har lokaci da aka shigarda su d'akin taimakon gaggawa.
"Bayan kowa ya kama gabansa manager hotel d'in ya tsinto kayan momma ya rufe d'akin.
Jin kad'an da fitarshi Jarumi uncle suraj ya fito daga ma6oyarsa bathroom, ya dinga kwasa
dariya kaman wani motsatsi.
Saida ya yi mai isarsa ya nufi k'ofar fita ya ciro key daga aljihunshi ya bud'e y k'ofa, ya lek'a
ya ga babu kowa a corridor ya fito abinsa zuciyarshi fara tass....yau burinsa na daukar fansa
akan d'an