Showing 51001 words to 54000 words out of 85584 words

Chapter 18 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf

27 Jul 2025

1516

fita da ita yayin da barrister
sai magiya take mata don Allah.....baaba ki tsaya ki saurareni duk abinda kike zato akaina ba
haka bane ni ba muguwa bace, inaso na taimake Maryama she really need my help.....don
Allah ki d'an dakata koda d'aya daga cikin tambayoyina ne ki amsa min.
"Wulgata waje baaba tayi scarf d'inta da ya fad'i k'asa garin janta da Baaba ke yi ta dauko ta
jefa mata a fuska ta datse k'ofar da key wanda tun lokaci da ta budewa barrister A tashigo yana
rik'e da hannunta.
***---****----*******
Tana dawowa flat d'inta takasa zaune ta kasa tsaye, sai takai gwaro takai mari tanaso tasan
cikkake labarin maryama, wacece ita...?
ya akayi ta haukace...?
Kuma menene matsayin Baaba laraba awurin maryama...?
There's is lots of questions da take da buk'atar amsoshinsu, amma wa zata tambaya.
yini ranar gaba d'aya cikin tunani tayi shi gani taji sauki hannunta ga kuma tarin tunani dole tana
buk'atar, abinda zai d'ebe mata k'ewa sai kawai ta nufi kitchen ta doura dinner kasancewar Aliyu
bai cika cin abinci mai nauyi ba yasa ta dafa pasta, tayi miyar hanta da k'oda da had'in conslow
sai meat balls & patato da ya nuna ta juye a warmers ta jera a dining table, gani akwai sauran

lokaci kafin magarib tayi sai kawai ta shiga had'e lemon carrots tasaka a fridge domin ya yi
sanyi, agurguje ta nufi upstairs bedroom tayi wanka had'e da alwala koda ta fito anfara kiran
sallah, ta tsane jikinta da k'aramin towel sannan ta daura zani tasaka hijabinta na sallah tayi
sallah. "Tana gama sallar magarib ta shiga azkar kafin lokaci sallar isha'i ya yi.
Bayan tayi sallah isha'i ta mik'e ta linke pryamat da hijab ta adanasu ma'ajiyarsu, taja stool ta
zauna gaban mirror ta mulke fatar jikinta da lotion mai k'amshin gaske, ta gogawa fuskarta
powder kad'an ta k'awata lips d'inta da pink lispstick ta gyara gashin kanta tayi mishi style mai
kyau ta bude closet d'inta tayi tsaye tana k'arewa kayan da ke ciki kallo can dai ta zaro romper
red colour pants kawai ta sanya bata saka brazier ba rigar ta sauka iya rabin cinyoyinta, ta bi
lungu da sak'o na jikinta da pure royal & asarar alhub perfumes ta dauki k'amshi mai jan hankali
da tsinke zuciyar d'an-namiji tasaka gladiator shoe irin mai igiya nan da ake daurewa ta daure
igiya ya tsaya dai-dai gwiwar k'afarta, bata rufe gashin kanta ba saboda style d'in da tayi mishi.
"Ta sauko downstairs falo ta zauna a one sitter ta kira barrister z ta bata labarin maryama,
alokaci da barrister z taji labarin ta kad'u ba kad'an ba cike da zallan mamaki ta ce bebs wacece
wannan mahaukaciyar....?
Menene alak'arta da gidan....?
I don't know bebs.....nima I was shocked da naga matarnan daure da sark'ar har zuwa yanzu
abin ya kasa fita daga idona.
"Gaskiya al'amarin akwai rikitarwa ki daure bebs ki nemo cikkake labarin maryama, tabbas
akwai wani 6oyayye sirri a haukan nata.
ba ko shakka thats your wicked mother in law is behind of everything.....
"k'arfaffiyar ajiyar zuciya barrister A tayi kafin ta ce "kaman kin shiga tunanina bebs nima
zargin da nake yi akanta kenan, saidai banida kwakwarar hujja.
"Gaskiya ne yanzu abinda ya kamata ki yi ki cigaba da zuwa flat d'in a asirce har sai baaba ta
fayyace miki komai, domin daga bakinta ne za ki samu hujja wacce babu k'arya aciki.
"Haka ne bebs nagode da shawarwarinki sai da safe suka yi sallama.
Bata jima da gama waya da barrister z Aliyu ya dawo ya shigo da sallama dauke da bakinshi.
"Ta mik'e da sauri tana wanke shi da tsadadd'en murmushinta, tsaye ya yi yana kallonta
saboda kwalliyarta ba k'aramin gigita shi tayi ba, shu'umin kallonan nashi na k'asan ido yake
aika mata yayin da yake tsotsar lower lips d'inshi tsigar jikinta ya tashi yarrrrr.....tasaki
6oyayyiyar ajiyar zuciya. Yanufo ta walking majestically yana wani shegen smile na gefen baki, cikin sauri ta sadda
kanta k'asa gabanta na fad'uwa ya iso daff....da ita tana jin heart beats d'inshi, yasaka soft
hands dinshi ya d'ago face d'inta, yana kallon cikin idanuwanta yana mata shegen kallo still
yana lasar lower lips dinshi......Ba zata iya jure cigaba da kallon nashi ba, shiyasa ta runtse
idanuwanta gamm.....ya matsa fuskarshi daff....da nata kaman daga sama taji saukar tattausan
lips dinshi akan nata ya saki mata wani hot peg....wanda ya haddasa mata mutuwar jiki
zuciyarta ta cigaba da bugawa very past kaman zata zaga k'irjinta tafito, da kyar ta tattaro
raguwar k'arfin da ya rage mata ta matsa daga jikinshi kad'an da sauri ya rik'o waist d'inta da
hannayenshi biyu, ya motsata sosai yana sauke mata numfashinsa akan fuska, yana goga
karan hancinshi akan nata.
"Wani irin shock suke ji yana jansu saboda dukansu wannan shine first time da suka ta6a

tsintar kansu acikin irin wannan yanayin, daff....da kunnenta ya kai bakinshi cikin sexy voice ya
kira sunanta Aminaaaa......!
Yadda yaja sunan nata iskar bakinshi tashiga kunnenta yasa, saida ta hadiye yawu kafin ta
amsa da uhmm....!
Inaso lips d'inki kin bani izzini na tsotsa...?"
Ba k'aramin gigita brain d'inta kalamanshi suka yi ba, da kyar ta iya girgiza kanta.
"Ya shagwa6e murya cikin sexy tone ya ce please....Amina koda k'adan ne ba zan yi da yawa
ba.
K'arin bugawar zuciyarta ya tsananta ta d'an dafe k'irjinshi da hannayenta, hakan ne yak'ara
d'imauta shi ya matse waist d'inta sosai, kin amince Amina...?
Akaro na uku yasake tambayarta tayi nooding head saboda babu bakin magana gaba d'aya tayi
loosing control wani shauk'i take ji yana yawo a jininta bata dawo natsuwarta ba yasake
connecting soft lips d'insu ya shiga bata hot French kiss yayin da hannayenshi suke squeezing
bayanta, batasan lokaci da tayi rubbing hannayenta a bayanshi ba. "Hakan ya k'ara mishi k'arfin gwiwar cigaba da kissing d'inta tare da romancing all over her
body especially boobs d'inta da ya ji su very softly saura kirisss....numfashin barrister A yafita
daga gangar jikinta k'afafunta suka dauki rawa, kaman zata fad'i k'asa da sauri ya taro ta ya yi
hugging d'inta tightly kafin ya cire bakinshi daga nata. Alokaci d'aya suka saki zazzafar ajiyar zuciya, yana shisshinar neck d'inta closing his two eyes
sun dauki six good minutes ahaka sai saukar ajiyar zuciyarsu kake ji, daga bisani ya saketa ya
rad'a mata wifey.....muje ki had'amin ruwan wanka na d'ebo gajiya throughout a conference hall
na yini muna meeting ga 'yar uban yunwa da nake ji. "Kanta na kallon k'asa tayi murmushi acikin zuciyarta kuma ta ce "d'an duniya kawai saida ka
shanye min baki sannan ka tuna da kana jin yunwa, ka ji da shi wai ciwon ajali a d'an yatsa...lol
Ya d'ago fuskata yana mata sanyayye murmushi ya yi holding nose d'inta yana kallonta kafin
yasaki nose d'in nata ya yi kiss forehead d'inta ya haura steps, yana fad'in ke nake jira barrister
karki shanya ni.
"barrister A ta dauki few minutes tana jinyar dafin da Aliyu yasake mata, kafin tadawo
natsuwarta wani irin nishad'i mai cike da zallan farin ciki ya yi mata ziyarar bazata tadaka tsalle
had'e da furta....yessss!
Da sauri ta rufe bakinta kada ya jiyo ihunta class d'inta ya zube.
Hummm......ka ji su barrister bayan tagama shan mazankwaila.....lol.




Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:17 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*

08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO



*GIDAN RINA*


*29*




Koda ta isa d'akinshi har ya cire kayan jikinshi yana sanye da bathrobe, kallo d'aya tayi mishi ta
dauke kanta.
Ta wuce bathroom yayin da ya bi bayanta da kallo ta cika masa bathtub da ruwa masu
d'umi-dumi ta zuba turaren wanka aciki, tana fitowa ta ganshi tsaye bakin k'ofar bathroom.
Na had'a ruwan.
Tafad'a batare da ta kalleshi ba, ya yi murmushi ya ce nagode my wifey.
"Ta d'an murmusa tanufi kayan da ya cire ta linke su ta mayar a closet saboda basu yi dirty ba.
Boxer da vest dinshi ta saka su a laundry basket.
Kafin ya fito har tafice zuwa dining area tana cikin yi mishi serving ya iso taja mishi kujera ya
zauna, sosai yaci abincin nata sai santi yake hade da yaba mata.
Bayan sun kammala ya wuce bedroom dinshi ita ma ta wuce nata, ta sauya kayan jikinta zuwa
na bacci, sannan tanufi d'akinshi
Sosai ta kalleshi kafin ta ce "Yalla6ai koda akwai wani abinda da kake buk'ata nayi ma kafin na
kwanta...?
Hannunshi ya nuna akan gado had'e da furta bissimillah....je ki kwanta inda ina buk'atar wani

abu zan tashe ki.
Sosai ta dubeshi tana d'an siriri murmushi kaman za tayi magana sai kuma tafasa, ta nufi
gadon ta kwanta tana kallonshi ya kashe bulbs ya kunna diff one ya dauko laptop d'inshi yana
tura wasu bayanai tsawon lokaci ya dauka kafin ya rufe laptop d'in, atunaninshi ya dauka tayi
bacci shiyasa ya mik'e ya nufo gadon ahankali, tana jin lokaci da ya hau gadon ya kwanta kusa
da ita ya kalleta duk da d'akin baya da wadattace haske hakan, bai hana shi ganin kyakyawar
fuska da surar jikinta ba, ya kai hannunshi ya shafa gefen neck d'inta ahankali kaman mai
shafar jikin jinjiri tana jinshi amma tak'i tayi wani kwakkwaran motsi da zai gano ba bacci take yi
ba.
Ya d'an matsa ya yi hugging nata tightly yana shak'ar k'amshin perfumes d'inta ya rasa gane
wane irin perfume take shafawa, yana matuk'ar son k'amshinta tunda yake bai ta6a jin irin
wannan k'amshin ba, sai a wajenta wato ita komai nata na musanmman ne ya lumshe
idanuwanshi tare da sauke sanyayyar ajiyar zuciya sai dai kuma baya tunani zai nemi kusantar
ta nan kusa zai daure har su fara son junansu sai ya barje shagalinshi atsanake.
Da wannan tunanin bacci ya dauke shi yayin da mamakinshi ya lullu6e barrister A yau gata
kwance the same bed da Aliyu yana kuma rungume da ita yana bacci, tabbas duk abinda
hak'uri bai ba ka ba rashinsa ba zai ba ka ba.
Gashi yau a sanadin hak'urinta tafara winning zuciyar shu'umin Aliyu tayi murmushi tare da
ajiyar zuciya tak'ara shigewa jikinshi daga bisani bacci ya dauketa.
***----****---****
Washe gari bayan sun kammala breakfast zai wuce office tayi mishi rakiya zuwa parking lot ,
suna tafiya side by side hannunta rik'e da briefcase d'inshi ya kar6i jakka nashi ya matsota sosai
ya sauke mata peg a forehead, har ya gangaro zuwa lips d'inta anan kam ya jima kafin ya
saketa ya shiga mota yana fad'i bye wifey please take care of yourself. Tana kallo har motarshi tafice daga gidan, sannan ta juya zuwa flat d'in Maryam a barandar
wurin ta tsaya kafin ta yafito d'aya daga cikin housemaids da saurinshi ya zo, cikin daure fuska
ta ce "inaso nan da one hour wurinan ya zama very neat indan ka sake naga dirty a bakin flat
d'inan you will be fired understood....? "Yes ma'am!"
oyaa....go your time is started now.
Da gudu ya juya bai wuce three minutes da barin wajen ba sai gashi tare da wasu maids gudu
biyu suka zama su uku, ta koma gefe tayi folding hannayenta a k'irji tana kallonsu kafin ka ce
kwa6o har sun fara shara jin motsin mutane had'e da shara yasa Baaba laraba bude k'ofa ta
lek'o gani abinda ke faru yasa ta dauki dogon salati, ta k'arasa fito da gangar jikinta waje tayi
arba da barrister A tana tsaye sai faman commanding 'yan aikin take yi da mugun sauri har tana
had'awa da tuntu6e Baaba laraba ta nufeta, tana fad'in 'yarnan ki dubi girman Allah ki rufawa
mana asiri ki kuma rufawa kanki, banaso abinda zai ta6a numfashinmu ke kuma ya ta6a
lafiyarki muddin ba ki daina shiga sabgarmu ba har abinda bana tunani zai iya faruwa.
"Har ta dasa aya azanceta barrister tana kallonta, daga bisani ta gyara tsayuwarta ta
fuskance Baaba da kyau ta ce "ki kwantarda hankalinki Baaba ki tattaro natsuwarki ga baki
d'aya ki saurareni, ban shigo rayuwarku don na cutarda ku ba asalima ni taimakonku nakeso yi
Baaba na rok'e ki ki barni nayi aikin lada. Baiwar Allah nan tana buk'atar taimako ki barni na taimaka mata.

"Duk abinda zan fad'a 'yarnan baza ki gane ba saboda haka ina gargadinki da ki daina zuwa
nan.
Kafin Barrister A tayi magana suka ji muryar momma tana fad'ar da kyau isasshiya wato ke
kissa da munafuci ne suka kawo ki gidanan ba zaman aure ba.
To kisani idan kinason kanki da lafiya, karki kuskura ki yi tako sak'a da ni domin baza ki ci riba
ba.
Tun daga lokaci da tafara magana jikin Baaba laraba ya dauki rawa wani fitinane tsoro ya
lullu6eta, yayin da barrister A take kallonta tana wani shegen murmushig ta nisa had'e da cewa
"Allah ya huce zuciyarki momma wace ni da zan yi takon sak'a da ke, kawai dai amatsayina na
surukar gidanan nima ina da 'yanci da zan yi abinda nakeso in fact ni banga abin tada jijiyoyin
wuya anan ba.
"Ke.....!saurara marar kunya fitsarariya karki sake ki gayamin maganar banza.
Haba! Mo.....!
Ya isa nace banaso nasake jin koda kalmar hak'uri ce daga bakinki.
Shiru barrister A tayi tana kallon ikon Allah wanda yafi gaban mamaki.
Momma ta juya wurin Housemaids da ke tsaye cirko-cirko cikin tsoron irin hukunci da za ta
dauka akansu, ta daka musu razananiyar tsawa maza ku 6ace min dagani kuma jira
makomarku a gidanan, tunda har zan aza doka ku karyata.
"Hak'uri suka shiga bata d'aya daga cikin Housemaids d'in mai suna Sa'eed ya nemi ya kare
kansu ta hanyar cewa ba laifinmu bane, ma'am saka mu tayi ta ce idan ba muyi ba zata kore
mu aiki don Allah ki taimaka mana.
"Dallah...rufe min bakinka an gayamuku har ita d'in tana da matsayin da zata kore ma'aikaci
agidanan.
Jikinsu na rawa suka tattara mop da bucket had'e da tsintsiya, suka bar wurin.
Momma tadawo da ganinta akan Baaba laraba sai taga wayam....batasan lokaci da take
zazzagawa housemaids fad'a ita kuma Baaba ta sulale ta datse k'ofarsu, da key ta barshi a jikin
k'ofar saboda tasan momma tana da spares key na flat d'in yanzu kuma duk tsabar masifarta ba
zata iya shigowa ba, balle ta d'aga musu hankali. "Da taga Baaba ta gudu tadawo kan barrister A tana fad'i to bak'ar munafuka ki bud'e
kunnenki da kyau ki saurare ni, daga yau sai yau karna sake gani k'afarki anan wuri ki tsaya iya
apartment dinki bakida hurumin zuwa wajenan.
"Ya motsa fuska barrister A tayi ta ce "momma yanzu laifi ne don na taimaki wanda ke neman
taimako?"
"kinga Amina ni ba tsara ki bace da za ki yi min titse, ina gargad'inki da babban murya da
kada ki sake rud'in kurciya ya rud'e ki, yi min katsalanda a al'amurana.
"Banyi nufi nayi miki katsalanda ba momma gani nayi anbar baiwar Allah nan a cikin k'azanta,
don kawai Allah jarabce ta da cuta shine za'a barta a wulak'ance wannan bai dace ba.
Duk yawan ma'aikatan gidanan ace anbar flat d'inta da k'azanta ki yi tunani momma duniya
zata zage ki.
"Matsowa kusa da ita momma tayi ta shiga k'are mata kallo kafin tayi kwafa ta ce "lalle Amina
ba kisan wa kika ta6o ba shiyasa kike da courage d'in musanya yawu da ni.
Allah ya ba ki hak'uri momma idan akan aikin Allah ne bana fargaba ta6a koma waye
ballantana, nasan alkhairi na ta6o.

"Shikenan za ki san ni kika yi ma rashin kunya bari wanda ya ajiye ki ya dawo, sai nanu miki
ruwa ba sa'ar kwado bane tunda ke bakida tarbiyya bakisan yadda ake daraja uwar miji ba.
Daga haka ta juya tanufi k'ofar maryama ta dinga heavy knock kaman zata k'arya k'ofar sai
surfawa Baaba laraba zagi ta uwa ta uba take yi, yayin da Baaba tana ji tayi biriss...da ita.
Barrister A tana tsaye kaman andasa ta sai kallon momma take yi, da momma tagaji da
knocking k'ofar ta juya ta nufi flat d'inta tana mai cigaba da bambamin fad'a.
Barrister A tayi ajiyar zuciya had'e da fad'in "cab....lalle ma momma tunda yanzu na fahimci
abin naki ba rawa ba tumami mu zuba ni da ke, sai na fitarda baiwar Allah nan daga k'agin da
kika jefata.
Ba don ke kika haifi Aliyu ba da yau nayi miki rashin mutunci na nuna miki 'yar zamani ce ni.
"Dole ta kama hanya ta koma flat d'inta amma da kudurin sai ta binciko matsayin Maryama
agidan.
****----*****----****
Daddare suna zaune a downstairs falo kowane su yana aikin gabanshi, yayin da Aliyu yake
kallon basketball da ake haskawa a allon television.
Barrister A kuma tana sarrafa laptop can ta d'ago tana murmushi ta ce "Yalla6ai ina fatan ba ka
manta ba ranar Monday zan fara zuwa office....?
Shima d'agowa ya yi yana yatsine fuska, ya ce "uhm....ke nan murna kike yi za ki fara cud'anya
cikin wasu maza, gaskiya Amina ba zan 6oye miki ba ina da tsananin kishi sai kin kula ta yadda
za ki dinga mu'amala da abokan aikinki, banaso yawan cud'anya da maza ki kiyayye banso mu
fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login