Showing 48001 words to 51000 words out of 85584 words

Chapter 17 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf

27 Jul 2025

1494

"Har zuwa lokaci she can believe Aliyu ne shin me ya kawo wannan sauyin da sauri haka?"
Ta Kalleshi irin kallon mai ratsa jini da 6argon jiki ta motsa pink lips dinta with so much
excitement ta ce thank you so much my humble husband for caring.
D'an hararanta ya yi yaja karan hancinta ya ce banaso shirme duk abinda nayi miki tamkar
kaina nayi ma don haka karki sake godemin.
"Sai kawai tayi murmushi.





Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:14 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE

IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*


*27*


Momma tafito cikin shirinta na zuwa ganin Jarumi.
sai sauri take yi kaman mai shirin bari gari, tun kafin ta k'arasa parking lot tayi unlock d'in
motarta da car key da ke rik'e da hannunta.
Ta shiga motar tayi reverse ta nufi gate maigadi ya bude mata gate tafice da wani irin gudu na
ban mamaki, western dreams hotel ta nufa saida tayi 6ada kama ta hanyar saka face mask za
ka dauka saboda cutar corona ne, yasata amfani da shi ta rufe kwayar idanunta da black shade,
sannan tafito daga mota ta shiga reception shigowar text message taji a wayarta _ina room
247_
Tana gama karanta text message d'in ta nufi corridor da zai saddata da d'akin.
"Tun kafin takai da yin knocking ya bude mata k'ofa, tashigo yau d'inma fuskarshi a rufe take
da face masks mai siffar lion tana shigowa ya maida k'ofa ya rufe.
Tana dosana bombon d'inta gefen gado tana jin saukar wani mushirikin mari, saida tanemi ji da
ganinta tarasa kafin tayi wani yunk'uri ya tureta tafad'i kwance akan gado ya bita ya haye ruwan

cikinta.
"And then....he started removing her clothe ya yi mata naked ya tsaya yana kallon nakedness
d'inta.....he wearing a wicked smile duk lokaci da yaso yaci zarafinta kwanciyar wulakanci yake
da ita cikin muryar kuka momma ta ce don Allah Jarumi kayi hak'uri....don't treat me like this"
"Ya d'ago da fuskarshi da ke lullu6e da masks ya ce "you made a huge mistake na sanarda
wani sirrina don haka ina da damar da zan yi treating naki yadda nakeso.
"Tana ji tana gani ya shiga sarrafata kuma irin na mugunta d'inan ga momma jiki yafara nauyi
dama makeup ne yake 6oye tsofanta....lol.
Haka ya Jarumi ya cigaba da shagalinshi ita kuma tana kwance kaman gawa saida ya yi son
ranshi, sannan ya barta abin takaici ta tashi ta tsinto tufafinta da ya zubar a k'asa tasaka.
"Cikin kaukausar murya yafara magana wato yanzu na fahimci reni yafara shiga tsakanina da
ke Zaituna, kin manta waye ni da Kuma abinda zan iya aikatawa idan mutum ya kuskure min.
Zan miki gargadi na k'arshe wallahi.....wallahi Zaituna kinji na rantse idan kika sake plans dina
na tsawon shekaru masu yawa ya rushe ki saka aranki kin zama gawa.
"Da mugun tsoro momma take kallonshi, shi kuwa ko a jikinshi ya cigaba da zazzaga mata
ruwan bala'in.
Tunda na fahimci kwakwalwarki batada amfani na canza plans d'ina ba kuma zan sanarda ke
ba, saidai na baki umarni ki bi idan kuma kika kuskure sai na lahira yafi ki jin dad'i tashi maza ki
6acemin da gani tsohuwar banza tsohuwar kilaki.
"Ta tashi jikinta yana rawa ta dauki car key d'inta tafice cikin wani irin tafiya kaman wacce tayi
tangard'e.
"Tana shigowa main parlour ta iske Daddy tare da Teema zaune yana sauraren shirmeta,
suna arba jikinta ya dauki mugun rawa kaman daga sama taji sautin muryarshi yana cewa
"Zaituna daga ina kike?"
"Cikin rawar murya tafara magana abinka da marar gaskiya Du.....biya.....
Dubiya?"
Ya tambaya sounding very angry momma ta gyad'a kanta.
"K'arya kike yi Zaituna ba daga dubiya kike ba, koma daga ina kike Allah yana ganinki.
Daga haka bai k'ara furta uffan ba ya dawo da ganinshi akan Teema.
"Momma tayi shiru saboda babu bakin magana, jikinta sanyi lak'asss.....ta nufi upstairs yayin
da Daddy yabi bayanta da kallo yana jin wata irin tsanarta tana haurowa a k'asan zuciyarshi.
*****---****----*******
"Tun daga dowawarsu daga asibiti yake zaune a gida bai sake fita ba, sai kulawa ta
musanmman yake bata.
"Ko motsi kadan tayi sai ya tambayeta hannu ne?"
Ita kuma ta gyad'a kanta har wani sabuwar shagwa6a ta tsiro da shi ta dinga matsar hawaye
k'arya.
"sallah kadai ke fitarda shi daga gidan, lokaci da ya dawo daga sallar isha'i ya bi ta flat d'in
momma domin ya sanarda ita barrister A ta k'one.
"Koda ya shigo bata falon k'asa sai kawai ya nufi bedroom d'inta da ke upstairs ya sanarda ita,
ba yabo ba fallasa tayi mishi fatan Allah ya bata lafiya ba.
Falon Daddy ya wuce ya isa ga kujera ta kusa da wacce Daddy yake zaune ya zauna yana
gaidashi "Daddy barka da hutawa!

"Ya amsa da yauwa sultan ya jikin matarka?"

Taji sauki Daddy!

Madallah ka kula da ita sosai.

"Insha Allah Daddy!
Daga haka suka yi shiru yayin da Aliyu yake karantar yanayin mahaifin nashi, sai yaga kamar
akwai damuwa atattare da shi ya ce "Daddy naga kamar akwai abinda ke damunka,
musanmman lokaci da na shigo sau uku ina sallama kafin ka ji kayi nisa a tunani "don Allah
Daddy meke damunka?"
Asanyayye Daddy ya yi murmushi ya kalle d'an nashi ya ce "ba komai sultan gajiya ce kawai.
Kallonshi kawai Aliyu ya yi amma ba don ya yarda ba, ya mik'e had'e da cewa sai da safe
Daddy!
Har ya kai bakin k'ofa Daddy ya kirashi sultan...!
Na'am Daddy amsa had'e da juyowa.
Zo nan.
Daddy ya yafitoshi da hannunshi na dama.
''Dawowa ya yi ya zauna inda ya tashi yana kallon mahaifin nashi atsanake.
"Sultan inaso kayimin wani alk'awali ko bayan raina bazaka warware shi ba.
"Inajinka Daddy!
Cewar Aliyu cike da fargaba jin abinda mahaifin nashi zai fad'a.
Sultan inaso kayi min alk'awali komai runtse bazaka rabu da matarka ba, za ka zauna da ita
cikin dad'i ko akasin hakan.
Murmusawa Aliyu ya yi yana shafar gemunshi ya ce "Daddy idan wannan ne bakada matsala
da ni, nayi maka alk'awali komai wuya komai dad'i ina tare da Amina.

"Masha Allahu.....yarona naji dad'i wannan furuncin naka Allah ya yi maka albarka, ya baka
ikon rik'e alk'awali.
Aliyu ya amsa da ameen summa ameen!
Cike da farin ciki Daddy ya ce tashi ka tafi ka gaida min da ita, kafin na shigo da safe na dubata.
Za taji Daddy!
Ya tashi yafice.
Lokaci da ya shigo bata falon k'asa sai kawai ya wuce d'akinshi ya yi wanka, ya shirya cikin
pyjama saidai bai rufe bottoms d'in rigar ba sai uban k'amshin dolce & gabbana perfume yake yi
kai tsaye bedroom d'inta ya nufa alokaci har tayi wanka tana sanye da cotton night gown mai
d'an siriri hannu wacce da kad'an ta wuce cinyoyinta. "Yana tura k'ofa ta d'ago suka had'a idanu ya yi tsaye jikin k'ofar, yana aika mata da shu'umin
kallo.
Kasa jure kallon nashi tayi sakamakon wani irin bugawa da zuciyarta ke yi.
Ya k'araso ya iso gabanta ya durk'usa, ta shak'i dadd'add'en k'amshin turarenshi wanda gaba
d'aya ya lullu6e k'ofufin hancinta ta lumsashe idanuwanta. Hannunta mai ciwo ya rik'o yana

kallon ciwo, kafin ya dawo da ganinshi akanta cikin tattausan lafazi ya ce "ya kike jin hannu
yanzu?"
Rausayarda kanta tayi tana kallon wani gun daban, ta ce da sauki.
"Murmushi ya yi had'e da mik'ewa tsaye batare da dauke idanuwanshi akanta ba ya ce "tashi
muje kici abinci.
Nagode Yalla6ai amma bana jin yunwa.
Tafad'a had'e da sadda kanta k'asa.
"Ya 6ata fuska sosai alamar ranshi ya6aci, duk da haka sai ya tsince kanshi da controlling anger
nashi ta hanyar sassauta murya alamar rarrashi ya ce "ki daure Amina ko kad'an ne kici idan
baki ci ba, bazan zan ji dad'i ba.
Yadda ya yi magana ya yi masifar burgeta tayi murmushi had'e da mik'ewa ya wuce gabanta ta
bishi abaya.
"Da kanshi ya yi mata serving da yake ga hannunta na dama ta k'one sai ta rik'e spoon da
hannun hagu, saidai bata taji dad'in rik'on spoon d'in ba.
"Gani haka yasa ya kar6i spoon daga hannunta ya shiga feeding d'inta, goganyar taku ta
bud'e ciki ta narki abinci kaman ba ita bace ta ce ta k'oshi.
ragowar abinci da ta rage ya ci sai faman kallonshi take yi idan ya d'ago suka yi four eyes,
tasake mishi murmushi shima ya mayar mata da martani murmushin nata.
Yana kammalawa ya tattare plates ya kai kitchen.
Ya nufo cikin falo idan ya hangota zaune maganinta ya dauko da bottle d'in ruwa, ya bata tasha
sai faman yatsine fuska take yi shi kuma yana mata sannu.
Around 10:30pm tayi mishi sai da safe ta nufi bedroom d'inta bata jima da kwanciyar ba,
bacci ya yi awon gaba da ita.
Aliyu ya jima zaune har lokaci kwanciyarshi bacci ya yi, ya mik'e ya koma bedroom dinshi saidai
sam ya kasa bacci sai faman juyi yake yi, nan take tunanin ya fad'o mishi bai kamata ya barta
ita kadai ta kwana ba, dole ya kasance tare da ita karta falka tsakiyar dare ta buk'aci ruwa ko
wani abun daban. daga k'arshe ya tashi ya nufi d'akinta ya tasaki sa'a bata rufe da key ba. Yana murd'a handle k'ofar ta bud'e ya kutsa kai, duk da d'akin yana dauke da diff light hakan bai
hanashi gani kyakyawar fuskarta ma'a6ociya kwarjini ba.
"Sam bai yi tunanin kwanciya kusa da ita ba ya dauki two pillows ya jefa kan rugs carpet ya
kwanta, sai dai kuma ya kasa bacci domin wannan shine karo na farko da ya kwanta ad'akinta,
ya jima sosai kafin ya samu bacci ya dauke shi.
"Can tsakiyar dare ta falka don ta gyara kwanciyarta ta shak'i k'amshin turarenshi da ya
gauraye d'akin, ta tashi zaune ta hango shi kwance kan carpet da sauri ta yaye duvet da ke rufe
da jikinta ta zuro fararen k'afafunta k'asa, sannan ta mik'e tsaye ta isa wurinshi ta durk'usa
tashiga bubbuga hannunshi had'e da kiran sunanshi. A hankali ya bud'e idanuwanshi ganinta a durk'ushe yasa ya tashi zaune yana murtsuke
idanunshi asanyaye ta ce "Yalla6ai don Allah tashi ka koma kan gadon ka kwanta.
Ya girgiza kanshi ya ce "ki barni anan ya isa yana k'ok'arin komawa ya kwanta, Ta marairaice
murya kaman za ta fashe da kuka, tasake cewa don Allah yalla6ai ka tashi ba don ni ba.
Ko dai kana tsoro kar na dameka da snoring ne...?ni sai na kwanta k'asa sai kai ka hau gado.
"Murmushi ya yi batare da ya furta uffan ba ya mik'e ya hau gadon ya kwanta, yayin da tayi
tsaye tana kallonshi.

"Zo ki kwanta barrister banaso kallon nan naki mai kama da na tuhuma.
"Tayi murmushi batare da ta musa ba ta isa kusa da shi ta kwanta, yaja duvet ya rufa musu ya
shak'i k'amshin turarenta ya lumsashe idanuwanshi bayan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya.





Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:17 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*




*28*


Cikin kwanaki k'alilan shak'uwa ta ban mamaki ta shiga tsakaninsu, tun barrister A tana gani

abin kaman al'mara har ta zo tafara sabawa.
"Gani yadda ya dauki komai nata da mahimmanci yasa tak'ara zage dantse wurin kyautata
mishi, duk da har yanzu ba abinda ya shiga tsakaninsu ko abisa kuskure bai ta6a gwada koda
sum6atar ta ne ba.
Tun bayan fitar Aliyu office take ji gidan so bore, sai kawai ta tsince kanta da son fita compound,
tasha fresh air mik'ewa tayi tasaka flip flops a k'afarta.
Jikinta sanye da palazzo trouser had'e da split flutter sleeve ta yane kanta da scarf shigarta ta,
tak'ara fitowa da ainihin kyauta.
Ta nufi k'ofar fita daga main parlour tana fitowa tayi tsaye a barranda flat d'inta, tana kallon
shige da fice na ma'aikatan gidan.
"Abinda ke daure mata kai ya k'ara jefata duhu, bai wuce flat d'inan mai dirty tsiya ba.
musanmman yanzu da take tsaye tana kallon yadda ma'aikanta gidan suke tsaftace harabar
gidan.
Hatta da ganye flowers da idan ya fado sai sun tsince shi, to amma meye dalilin da yasa suka
bar waccan flat d'in da dirty.....?"
Rashin sani amsar tambayarta yasa ta yanke shawarar yau dai sai taje wurin, koma menene
zata gani da idanuwanta.
"Har ta isa flat d'in ba wanda ya ganta da yake kowa aikin gabanshi yake yi, tana shiga
barrandar mamakinta ya k'aru sakamakon k'arar sautin television da taji, tayi shiru na wasu 'yan
seconds kafin ta nufi k'ofar ta shiga knocking....shiru ba'a bud'e ba kasa hak'ura tayi ta cigaba
da knocking da k'arfi tabbas yau sai taga abinda ke cikin wannan flat d'in. "Ta dauki dogon lokaci tana knocking batare da tagaji ba.
ba'a kuma bud'e mata k'ofar ba.
Har ta yanke hukunci ta zagaya backyard tunda akwai windows awurin ta lek'a koma menene
zata gani sai taji footsteps ana zuwa, da sauri taja da baya kad'an ta kuma k'ara ware
idanuwanta yadda zata ga me zuwa.
bud'e k'ofar akayi wata tsohuwa ce wacce ak'allan shekarunta na haihuwa zasu kai sittin a
duniya ta baiyana, kallon-kallo suka shiga yiwa junansu.
"Barrister A ce tayi k'arfin halin cewa sannu baaba.....!
Yauwa 'yar nan ko kece likita da Hajiya Zaituna ta turo?"
kafin barrister A ta bata amsa ta cigaba da cewa da yake ban wayeki ba waccan 'yar
k'armusasshiya nasani, mai siffar marasa imani amma ke da ganin fuskarki kina da burbushin
imani duk da abin ba'a fuska yake ba.
Shigo daga ciki ki dubata da yake kwana nan kamam tafara dawowa hankalinta.
Duk surutu da baaba laraba keyi barrister A tsaye kawai take tana kallonta.
"Gani ta ra6e ta bata hanya yasa tayi shahada ta kutsa kai, baaba kuma ta maida k'ofa ta rufe
da key had'e zare shi.
Ta wuce gaba barrister tana bin ta abaya, cikin d'an k'ank'ani lokaci ta k'arewa falon kallo gaba
d'aya cushion d'in da ke cikinshi sun tsofa irin sun zama old model muryar baaba laraba ce ta
karad'e mata kunne shigo likita ki ganta.
"Da sauri ta nufi d'akin da taga baaba laraba ta shiga, tana jefa k'afarta cikin d'akin gabanta ya
yi mashahurin fad'uwa har batasan lokaci da ta dafe k'irjinta da dukan hannayenta ba a k'asan
zuciyarta kuma ta furta....hasbunallahu waa'imaal wakil.....!

Sosai tadawo natsuwarta tasami damar k'arewa Maryama da ke daure da sark'a k'afafunta da
hannaye, abin gwanin ban tausayi.
"kanta na sunkuye tana rera kuka marar sauti, sai ka saurara sosai za ka iya jin sautin kukan
nata ba sai ka tambaya ba kasan na bakin ciki ne.
"Wani irin tausayinta ne ya yi ma barrister A dirar mikiya a gadon zuciya, cike da rashin tsoro
ta durk'usa gabanta sai lokaci Maryama ta d'ago da fuskarta wacce ta rine ta koma bak'a,
gurbin idanuwanta ya dusashe ya yi bak'i wulik.....yayin da lips d'inta suka bushe kaman
6a66ariyar fadama. "Ta k'urawa barrister A idanu ba ko kyaftawa kaman tanaso ta tuna idan ta ta6a ganin wannan
kyakyawar fuska saidai kash.....kwakwalwarta bazata bata had'in kai ba.
"Sai kawai tasoma k'ok'arin d'ago da hannunta mai daure da sark'a ta ta6a barrister, zaman
'yan bori barrister A tayi dabasss.....ta d'ago da ganinta ta kalli baaba laraba da ke tsaye tana
kallonsu ta bud'e bakinta da kyar ta ce "baaba tana duka ne....?"
"Baaba laraba ta girgiza kanta tana kya6e baki, ta ce ba ko d'aya tsabar mugunta ne da
zallunci irin na Hajiya Zaituna yasa tasaka akai mata irin wannan d'auri na k'ask'anci, amma don
Allah yarinya karki fad'a mata abinda nace.
"zazzafar ajiyar zuciya barrister A ta sauke kafin ta ce karki damu baaba ba zan gayamata ba,
asalima ni ba likita bace.
"Zare idanu baaba tayi cikin kad'uwa tace wacece ke 'yar nan....?
Mekika zo yi anan...?
Sunana Amina nice amaryar Aliyu baaba ki kwantarda hankalinki wallahi ban zo wurinan don in
cutarda ku ba.
"Baaba ina da tarin tambayoyi da nakeso ki bani amsoshi su, amma bansaniba ko zan sami
had'in kanki.
"Baza ki samu ba muguwa wato tanan Zaituna ta bullo, shine zata yi min ije ki zo ki bugi cikina
ko zan fallasa sirrinta to ba abinda zan fad'a rayuwata da ta Maryama tafi min komai, zo ki fita
tak'arasa magana had'e da finciko hannun barrister A ta nufi k'ofar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login