Showing 30001 words to 33000 words out of 85584 words
Chapter 11 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf
momma gani yadda girls d'inta suke tarairayarta, tsawa ta daka
musu kai miye haka?"
Dallah ku ja Teema ku koma d'aki.
Kuka Teema tasa tana bubbaga k'afa a k'asa tana cewa momma ke muguwa ce, ki barni na
ganta ina sonta tana da kyau.
Ran momma ya k'ara 6aci afusace ta mik'e ta finciko Teema daga jikin barrister A, taja ta kamar
kayan wanki ta kaita d'aki ra rufe tadawo ta kalle zee-zee da meena da ke tsaye wuk'i-wuk'i ta
daka masu tsawa, nace ku 6ace min da gani shasshashu yaran kawai kun zo za ku takurata.
"Da gudu suka nufi bedroom d'insu, duk abinda take ko ci kanki Aliyu bai ce da ita ba, za ka
ma dauka baya cikin sitting room d'in.
Hankalinshi kwance ya ce momma ga wifey ta zo yi muku bankwana, saboda na gayamata
gobe da safe za ku koma Abj.
"Yak'arasa magana cikin halin ko in kula d'inan.
Duk cikin zanceshi kalmar wifey ce tafi k'onawa momma rai, jin take kamar ya soka mata mashi
a k'ahon zuciya.
"zuciyarta kamar za ta fad'o k'asa tana murmushin dole ta ce, sannu daughter da fatan kina
kulamin da yarona?"
Kinsan ba son aure yake yi ba dole ne akayi masa, idan bakya bashi kulawa komai zai iya
faruwa, dole ki zage dantse ki bashi kulawa ta musanmman ko Allah zai sa kisami fili koda d'an
k'ank'ani ne a farfajiyar zuciyarshi.
"Duk sanyi da ke falon bai hanawa barrister A shar6ewa da gumi ba, atarihin rayuwarta ba'a
ta6a ci mata fuska a wulak'antata irin wannan ba, zuciyarta har tuk'uk'i take yi mata.
"Gani shirme da momma take yasa Aliyu ya yi sauri mik'ewa ya isa wurin barrister A ya rik'o
shoulder ta ya mik'arda ita tsaye, yana kallon cikin idanuwanta.
"Gani yadda suka canza kala tausayinta ya kamashi yasan momma ta wulak'antata ba kad'an
ba.
"Wifey mu je upstairs parlour ki gaisa da Daddy!
Har suka takala steps yana rik'e da ita momma tabi su da mugun kallo tana kintsa mugun nufi
akan barrister A.
Sosai Daddy ya tar6eta yasaki jiki sai janta da fira yake, yana tambayarta akan abinda ya shafi
aikinta, hakan yasa tasaki jikinta ita ma tana bashi amsa, nan take taji k'aunar dattijo ta cika ciki
da wajen zuciyarta.
Fuskar Daddy dauke da murmushi ya k'ara duban barrister A ya ce "Da fatan ba dai wata
matsala atsakaninku?"
"Cike da kunya ta girgiza kanta ta ce ba komai Daddy Alhamdulillah muna zaune lafiya.
"Masha Allah haka nakeso ji, ayi ta hak'uri da kuma biyayya don a cigaba da samun zaman
lafiya.
Insha Allah Daddy mun gode Allah yak'ara girma da nisan kwana.
Daddy yasaki murmushin jin dad'i zuciyarshi cike da farin ciki ganin d'anshi ya mallaki iyali
kamar kowa yanzu kam, hankalinshi ya kwanta sai kuma addu'a samun zuri'a dayyaba"
"A shagwa6e Aliyu ya turo baki ya ce uhm.....Daddy tun dazu da ita kadai ka ke fira ni ka
wareni, kamar ba kasani ba.
Dariya Daddy ya yi kafin ya ce kadai ba ka rabuwa da rigima gadanga, ba ka gani ita ce bakuwa
ko ba kasan bako rahama ne ba dole a girmamashi?"
"Sake turo baki ya yi ba wani nan Daddy nagano so ka ke ta kwace min fada awurinka.
Ba daddy kadai ba hatta barrister A saida ta dara.
Sosai sagarta Aliyu ya burgeta k'ato da shi yana shagwa6a, ta tuna yadda ita ma take yiwa
Abbanta, duk girman mutum a gaban iyayyenshi k'aramin yaro yake komawa.
"Amina kina ji na da wannan rigimame mijin naki ko?"
Sadda kanta k'asa tayi cikin sanyi murya ta ce rabuda shi kawai Daddy ai ya riga yaci
lokacinshi, a wurinka yanzu lokacina ne.
"Shigowar momma ya katsi musu nishadinsu, ko zaunawa bata yi ba ta ce kai Sultan tashi ku
tafi gida babu kyau mace tayi sallar magarib ba k'ofar d'akinta ba.
Mun gode da ziyara ku gaida gida.
"Daddy ya daure fuska ya ce korarsu ki ke yi?"
Wai kin ma basu ruwan sha?"
Kafin ta bashi amsa Aliyu ya mik'e da sauri ya ce Daddy bari mu wuce Allah ya tsare hanya ya
kai ku lafiya sai mun zo.
"ita ma mik'ewa tayi tai musu sallama tafice Daddy ya dauko bundle na 'yan one thousand ya
mik'awa Aliyu gashi ka ba wa matarka, mun gode Allah ya ba ku zaman lafiya, Allah yak'are ku
da sharrin mahassada.
"Amin Daddy cewar Aliyu ya juyo wurin momma ya ce mun tafi.
Ku gaida gida.
Tafada kamar za tayi bindiga.
"Koda ya fito tuni har ta shiga mota shi ma ya shiga Isah ya ja motar suka tafi.
Akan hanyarsu ya doura mata kudin da daddy ya bata akan cinyarta, ya ce inji daddy ya ce
abaki.
Nagode Allah yasaka mishi da alkhairi
Amin!
Yafad'a yana kallonta kauda fuskarta tayi tana murmushi k'asa-k'asa.
Suna isowa gida ta wuce sashen tayi wanka had'e da alwala saida ta sallace sallar isha sannan
ta tashi, ta shirya cikin Indonesia straight silk gown ta yane kanta da scarf, ta sauko downstairs
parlour bata jima da zama ba ya shigo sanye da farar jallabiya mai gajeren hannu.
"Sannu da zuwa!
Tafad'a cikin cool voice.
Yauwa Yafad'a batare da ya kalleta ba ya cigaba da cewa idan kina jin yunwa akwai abinci akan
dining.
"Daga haka ya haura upstairs yabarta da kallon bayanshi, girgiza kai tayi taji koda yunwa za
ta kasheta ba za ta ci abinci ba gara ta kwana da yunwa.
"Kitchen ta wuce ta had'a coffee ta shige bedroom d'inta tana gama shan coffee, tayi brush
tabi lafiyar gado saidai da kyar tasami bacci sakamakon yadda tunanin momma ya rufeta ga
kuma na uban gayya, ita kam ta shiga uku wannan wane irin aure ne tayi?"
****"""****"""***
Washe gari sai misalin k'arfe 11:14am tafito downstairs parlour, waya take yi da wani client
d'inta ya shigo sanye da white sport wears k'afarshi sanye da sneakers farare, dawowarshi
kenan daga jogging.
"Ina kwana Yalla6ai?"
Ya tsaya cak....yana kallonta girar ido d'age daga bisani ya ce ya akayi jiya ba kiyi dinner ba?"
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDA NA KUD'I NE
IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*20*
Murmushi tayi kafin ta ce bana jin yunwa shiyasa ban ci ba, amma before in kwanta nasha
coffee.
"Ta6e baki ya yi had'e da mak'e kafad'a irin I don't care d'inan ya k'arasa haura steps.
Ta bi shi da kallo tana tausayin kanta yadda ta tsunduma soyayyar mutume da bai ma san tana
yi ba.
Ta rafka d'an uban tagumi, k'amshin turarenshi yadawo da ita natsuwarta ta bishi da kallo har
isa dining area bata dauke idanunta daga akashi ba, sosai dressing dinshi ya burgeta white long
sleeve had'e da white trouser yasaka. "Sumar kanshi tasha gyara ya yi masifar yi mata
kyau. "Saida ya zauna sannan ya waigo wurinta ya yafito da hannunshi, jikinta asanyaye ta mik'e ta
nufo wurinshi.
"Ya kalleta da girar ido d'age ya ce dai barrister ko yanzu dinma bakyaji yunwa?"
Murmusa had'e da zarar plate tayi serving dinshi, sannan ta zauna ta yi wa kanta serving.
"Suna cin abinci tana satar kallonshi afakace, yi ya yi kamar bai ganta ba.
"Yana gani za ta dame shi da kallo yasa ya ce Barrister ki ci abinci kada ya yi sanyi, ko abinci
ne bai miki dad'i ba?"
Sosai taji kunya ta rufeta, ta shiga cusa chips d'in tana taunawa kamar mai cin mad'aci, kafin ta
ankara ya mik'e yabar mata dining d'in.
Ajiye fork tayi ta talla6e kumatunta tayi zurfi atunani, taji sauti muryarshi yana cewa ni zan fita.
Da kyar iya furta adawo lafiya!
Yajuya abinsa ta bishi da kallo.
***"""***""****
Misali k'arfe 8:00 na dare bayan sun kammala dinner, ta tattara plates da suka yi using ta kai
kitchen ta wanke.
"Koda tadawo downstairs parlor ya fice, shiru tayi tana nazarin wayar da ta yi da barrister Z
d'azu da safe.
_Inda take cewa Bebs ki cire kunya da miskilanci ki nemi kusanci da mijinki, shi namiji ne ko a
yanzu yana da damar auro mace har uku, sa6ani ke kinga kenan kece a wahala ki yi wa kanki
fad'a bebs tun kafin lokaci ya k'ure miki, karki mata ke mace ce Allah ya yi miki ni'imomi da
yawa da za ki janye hankalin d'a namiji da su karki yi wasa da damarki, kafin ku wuce Abuja ki
yi k'ok'ari ki nemi kusanci da shi_
Ajiyar zuciya tayi had'e da dafe k'irjinta, daga bisani ta nufi bedroom d'inta ta sauya kayan jikinta
zuwa Indonesia gown mai santsi gaske talafe a jikinta, ita kanta da ta kalle kanta da mirror
saida ta firgita sakamakon yadda gown d'in ta baiyana surorin jikinta.
"Arabian perfumes tayi amfani da su saboda sun fi k'arfi da jan hankali, tasaki gashinta ya
sauko har gadon bayanta ta yanne kanta da d'an siriri mayafi.
"Tasaka wasu slippers masu taushin gaske a k'afarta
Kai tsaye ta wuce kitchen ta had'a mishi coffee sannan ta nufi falonshi da ke upstairs, tun kafin
takarasa take jin sautin muryarshi, tasan waya ne yake yi.
"Da sallama tashigo ya juyo ya kalleta ita ma kallonshi, tayi kafin ta kauda kanta ya yafito ta
da hannunshi ya yi, alamar da ta k'araso.
Ta ajiye mug din coffee akan center table da ke gabanshi, ta nemi sofa ta zauna bai wani jima
yana waya ba ya ajiye.
"Ya dauki coffee yana sha ahankali yayin da ta sadda kanta k'asa tana wasa da gefen
gyaleta, shiru ya biyo baya karar TV kawai ka ke ji sai kuma zuciyar barrister A da ke bugawa
very fast.
Ya canza channel zuwa idan ake haska movie na horror, satar kallonshi tayi anan ta ga
hankalinshi na kan movie d'in hakan yasa ita ma ta maida hankalinta ga Tv.
"Tuni hanta cikinta yafara kad'awa gani yadda zombies ke wasa da jinin bil-adama, ta runtse
idanunta gam....
Ita kam sam bataso irin movies dinan tsorata ta suke yi.
"Kallonta ya yi ya ta6e baki ya cigaba da kallonshi, can yasake kai dubanshi wurinta still
idanunta a rufe ruff....ya yatsine fuska kafin ya ce barrister tashi ki koma bedroom dinki kada ki
yi bacci anan.
Sai lokaci ta bud'e idanunta ta girgiza kanta muryarta, asanyaye ta ce ba bacci nake ji ba.
"Bai ce da ita uffan ba ya cigaba da kallonshi sai around 11:20pm aka gama film d'in yana
k'ok'arin tashi ta kalle shi ta ce sai da safe Yalla6ai.
Batare da ya kalleta ba ya ce "sai da safe.
kafin ta k'ara wata magana sai ya mik'e yabar mata falon ya nufi bedroom, ta bishi da kallo tana
sanyaye murmushi.
Ita da ta zo mashi fira ya tafi ya barta da gadin falonshi, ta d'an jima zaune tana zance zuci
daga bisani ta mik'e ta koma nata sasshe, da kyar bacci ya yi nasarar dauke ta.
"Tabbas akwai jan aiki agabanta ba kad'an ba.
"Shi ma ta6angareshi yana kwance zuciyarshi cike, da tunani abinda yafi tsaya masa arai duk
yadda barrister A tayi kwaliyya sai ta burgeshi, zai dauki dogon lokaci kafin ya manta da
kwaliyyar ta ta.
Uwa-uba mayyen turarenta da ke addabarshi muddin ya shak'i k'amshinta sai ya tsince kanshi a
wani yanayi wanda shi kanshi ya rasa gane na menene.
"Washe gari da safe suna zaune a dining table tana serving d'inshi, ya d'ago ya dubeta
afakace ba shiri ya dauke kanshi zuciyarshi na bugawa da k'arfin gaske, sakamakon yadda tayi
mishi kyau kamar wata aljana.
"Ya sadda kanshi k'asa yana cin abinci ba don yana jin dad'inshi ba, adaddafe yaci abinci
yana kammalawa yabar dining area ta bishi da kallo har ya haura steps idanunta na kanshi.
"""****"""****""""
A kwana atashi asarar mai rai gashi yau kusan sati biyu kenan da auren Aliyu da barrister
Amina.
"Da Yammacin ranar talata barrister A tana tsaye a kitchen tana gyaran fruits za ta had'a fruits
salad, taji shigowarshi saida ta kammala had'awa ta zuba mishi nashi a bowl tasaka ice cubes
sannan ta nufi falonshi.
Zaune ta sameshi yana operating waya jin motsinta da kuma k'amshin fittinane turarenta, da
ya bigi k'ofufin hancinshi ya haddasa masa d'agowa da kanshi, ya kalleta ya kauda fuska ya
cigaba da dannar wayarshi, ga alama chat ne yake yi.
Ta ajiye bowel d'in hannunta akan center table.
Sannan ta isa ga kujerar da ke facing dinshi ta zauna tana mishi sannu da dawowa.
Ya amsa batare da ya d'ago da kanshi ba ya kalleta.
Ta kalleshi sosai kafin ta ce "Yalla6ai ga fruits salad na kawo maka bansani ba ko kana da
sha'awarshi.
Asanyayye yai murmushi ya d'ago suka had'a ido cikin tsadaddiyar muryarshi ya furta nagode!
Daga haka suka yi shiru shi yana dannar wayarshi ita kuma tana aikin kallonshi, can dai ya
d'ago tai sauri kauda kanta.
Ya yi murmushi saboda ya ganota sarai....kallonshi take yi ya dauki fruits salad d'in yana sha
yana kad'a kai alamar ya yi mishi dad'i.
"Yana gama sha ya mik'e ya shige shi bedroom ya barta zaune.
Da tagaji da zama ita kadai ta koma nata falo.
**"""***"""****
Misali k'arfe 10:00 na dare fitowarta daga wanka kenan, tana daure da towel wanda ko
cinyoyinta bai gama rufewa ba. Barrister Z ta kira ta ta duba email d'inta akwai sak'o da ta turo.
"Laptop d'inta ta dauko da ke aje akan bedside drawer, ta nemi gefen gado ta zauna ta shiga
duba email d'in ta shagala sosai har rabin towel d'in ya zame daga k'irjinta rabin boobs d'inta a
fili.
"Jin an murd'a k'ofar d'akinta yasa ta tsorata da sauri ta juya Aliyu tagani tsaye ya yi folding
hannayenshi a k'irji, mayyun idanuwanshi ya zuba mata masu kama da na mai jin bacci, kamar
mai koyo magana ya ce coffee za'a bani.
"Ta gyad'a kai alama amsawa sai dai kuma tana matuk'ar jin kunyar yadda za ta, tashi da
wannan d'an towel a gabanshi.
A tunaninta ficewa zai yi sai ta tashi sai taga sa6anin hakan.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:01 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
Not edited!
*21*
Ya gyara tsayuwarshi ya kuma rik'e handle d'in k'ofar, ya cigaba da kallonta ta gefen ido.
Ta waiga gefenta ba wani abin da za ta rufe jikinta da shi.
Can Allah ya taimaketa ta hango hijabinta na sallah akan praymat, ta d'an sosa tsakiyar kanta,
cikin tsananin jin kunya yadda za ta tashi gashi ya tsareta da brown eye's dinshi.
Gani bata da niyar tashi yasa ya ce I'm waiting barrister!
Ta d'an kalle shi cikin jin kunya ta ce "Yalla6ai ka tsaya a bakin k'ofa ban san yadda zan yi in fita
ba, ina jiran ka janye sai in tashi"
"Dama idanuwanshi na kanta ya dan murmusa sannan ya juya ya fice, daga d'akin.
Gani haka yasa ta mik'e cikin sauri ta isa wajen praymat, ta dauki hijabinta ta sanya ya sauka
mata har k'asa, sannan ta fice.
"Ta had'a coffee a mug ta nufi falonshi a tunaninta yana nan falo, sai taga sa6anin hakan.
"Dole ta wuce bedroom d'inshi zaune ta sameshi akan resting chair, asanyaye cikin
girmamawa ta runsuna ta mik'a masa coffee.
"Garin amsa by mistake ya had'a da hannunta, wani irin shock ya ja su, sai kace electric
shock jikinta ya dauki rawa cikin zafin nama ya rik'e mug d'in da coffee ya zube mishi a jiki.
kallon k'asan ido ya yi mata ta kauda fuskarta, had'e da furta "I'm sorry!.
Ki zauna mana ki yi tsaye!
Yafad'a yana kallon gefen face d'inta.
Girgiza kai tayi had'e da cewa bacci nakeji idan akwai wani abu da ka ke buk'ata, ka fad'a nayi
maka kafin na kwanta.
"Ya kai mug d'in coffee abakinshi ya d'an kur6a ya kalleta a tsanake, ya ce ki je ki gyaran min
bed tunda komai sai na rok'e ki.
Sosai ta dube shi kamar ba za ta