Showing 18001 words to 21000 words out of 85584 words

Chapter 7 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf

27 Jul 2025

1490

RINA*

*11*


Ta kwalawa Asabe kira ta tayata had'a mishi abinci da drinks, ta dubi Asabe ta ce dauki ki kai
masa Asabe ki ce mishi ina zuwa.
"Bayan Asabe ta kai mishi abinci ta dawo ta lek'a d'akinta ta ce ta kai mishi saida iya juice ya
sha ya ce ya k'oshi da abinci, shikenan Asabe ki mayarda abincin kitchen.
Ta mik'e ta isa gaba dressing mirror ta gyara fuskarta, ta fesa Asrar alhub perfume sannan ta
fice cikin sanyayar muryarta tayi sallama ya amsa can k'asan mak'oshi, sai da ta zauna a sofa
da ke facing nashi sannan tasake gaidashi ya amsa a tsanake, shiru ya biyo baya kowanesu da
abinda yake sakawa a ranshi wayarshi tayi ringing hakan yasa ta d'ago ta sace kallonshi ya yi
receiving call d'in cikin tsadadd'en turancinshi yake magana, da business partner dinshi tsawo
30 minutes ya dauka yana waya kafin ya katse kiran ya d'an sace kallonta dai-dai ita ma ta
d'ago ta kalleshi karaf idanuwansu suka sark'e, wani irin kwarjini na musanmman kwayar
idanunshi tayi mata fiyye da farkon ganinta da shi, kamar daga sama taga yasake mata
k'ayatattace murmushi wani irin sanyi ya ratsa tun daga tsakiyar brain d'inta har zuwa tafin
k'afarta.
"Ita kanta batasan lokaci da ta mayar masa da martani murmushin na shi ba.

"Cikin salon maganarshi mai cike da yanga da aji ya ce Barrister da fatan za'ayi min afuwa
kasancewar kin gani daga sama ba sanarwa, wannan ya faru ne a dalilin rashin sanin phone
number dinki kiyi hak'uri da rashin ganina ayyuka ne suka sha min kai, yanzu dai bani digit dinki
gudu kar a koma 'yar gidan jiya. Yakarasa magana yana shafar geminshi.
Ta sadda kanta K'asa fuskarta dauke da yalwattace murmushi, ta shiga karanto masa numbers
dinta duka guda biyu da ta ke using da su.

"Ya shigar da digit din a wayarshi ya yi saving da Barrister 1 da kuma barrister 2 ya kira
numbers da wayoyinshi a lokaci d'aya phones d'inta guda biyu babban da k'arama suka yi
ringing ta kai dubanta ga wayoyi ni ne kiyi saving numbers d'in yafada kamar mai koyo magana.
"murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba, haka Kuma bata kalleshi ba.
Shiru ya biyo baya na tsawo wasu dak'ik'u, gani za su 6ata lokaci a banza shi kuma ba abinda
yafi ba muhimmanci irin lokacinshi saboda kowace dak'ik'a tana da matukar amfani a wurinshi,

a cewarshi idan lokaci yawuce shikenan ba zai ta6a dawowa ba shiyasa yake matuk'ar mutunta
lokaci.
"Don haka ya gyara zama duk da shi d'in ba gwani surutu bane, amma kuma ya zama dole ya
yi shi a gaban barrister sakamakon fahimtar da ya yi ita ma gwanace a fagge miskilanci, sosai
yake mamaki yadda zamansu zai kayya shi da ita.

Ya yi gyaran murya kamar mai shirin kiran salla, ya ce Barrister maganarki tsada ne da ita ko ya
ke ki ke presented case a court oho!"
Yadda ya k'arasa magana yana rik'e habbarshi yai masifar bata dariya, har batasan lokaci da
tasaki dariya mai k'aramin sauti ba har tana had'awa da rufe fuska da tafin hannunta.

"Shi din ma murmushi ya yi ya cigaba da cewa kodai har yanzu fushi ake da rashin zuwa na.
"Girgiza kanta tayi ta kalle shi da raguwar murmushi a fuskarta ta ce "A'a Allah ni ba fushi nake
ba duk abinda ka fad'a ina saurare kuma na fahimci bayaninka.
"To amma ai ba ki ce da ni komai ba duk da hak'uri da na bayar anyya kuwa barrister kin
hak'ura kodai na nemo paper da biro na rubuta miki I'm sorry ma'am sau dubu?"
"Zaro golden eye's d'inta ta yi had'e da furta rufa min asiri yalla6ai, ni asuwa da zan ba ka
wannan danye aiki.
Ke barrister mana masu murd'e gaskiya ta koma k'arya ku murd'e k'arya ta koma gaskiya.
"Turo baki tayi cikin shagwa6a da ita kanta batasan tayi ba, abinka da sangartattaciya ta ce ni
gaskiya ba haka nake ba ka je ka bincika sosai za'a gayamaka bana d'aya daga cikin masu
aikata wannan aiki saidai in kuma akasi aka samu, wannan kam ba zan maka musu ba saboda
d'an adam azaji ne. "D'an ta6e baki ya yi ya d'age girar ido yana kallonta wanda hakan ba k'aramin masifar k'ara
masa kyau ya yi ba, ya ce gashinan yanzu ina ba ki hak'uri kin k'i hak'ura.
"Ta d'ago ta dube shi da yalwatattacen murmushinta har sai da dimple d'inta duka biyu suka
lotsa, hakan yasa kyawun fuskarta ya k'aru cikin sanyinta had'e da tattausan lafazi ta ce "Don
Allah yalla6ai ka rufa min asiri kuma ai zance bani hak'uri bai ma taso ba saboda ba wani laifi
da aka yi min ba. "Murmushi ya yi ya ce shikenan tunda kin ce haka.
Daga haka ya yi shiru dama can ya gaji da surutu saboda har kanshi fara ciwo, shi kanshi yana
mamaki yadda ya barke baki yana zuba a gabanta.

"Gani yadda ya yi shiru ta gano fuel dinshi ya k'are saboda haka ta gyara zamanta, tana
wasa da bangles d'in hannunta ta ce yau ina ka baro Jamal?"
"Saida ya dauki lokaci kafin ya ce "lafiya qalau yake munyi waya da shi kafin na iso nan da
yake daga Lagos nake kaitsaye daga can nayo nan, shiyasa ba ki gan mu tare ba.
"Ayya!
Ta fad'a tana murmushi.
Sai kinyi hak'uri da ni Barrister saboda yana yin aikina ban cika zama ba sosai yanzu haka on
Monday zan tafi business trip a Zurich sai satin bikinmu zan dawo don haka duk abinda ki ke
buk'ata Jamal ko kamal P.A na za su kawo miki, amma zaki rik'a jin wayata duk lokaci da na
samu sarari.

"Ba dawuwa Allah ya taimaka!

"Amin ya fad'a yana mik'ewa tsaye zan wuce sai gobe in na shigo, ki gaida mommy in sun
dawo.
"Ita ma mik'ewa tayi had'e da cewa zasu ji an gode kwarai Allah ya tsare.
Ya gyad'a kai had'e da ficewa da sauri shiyasa bata sami damar raka sa ba ta koma cikin gida,
ko zama bata yi ba maigadi ya dinga shigowa da manya-manya shopping bags yana ajiye had'e
da wasu manyan kwalaye.
Ya kuma mik'a mata envelope mai dauke da kud'ad'e masu yawan gaske, ita kanta sai da ta
jinjina yawan kud'in.
"Ta zuge zip d'in handbag d'inta ta jefa envelope d'in ta kira Asabe ta shigarda kayan store.
Ta dauke jakkarta ta sake fitowa ta ja motarta ta nufi wajen saloon.
****"""*****"""****
*WASHE GARI*

Barrister A da kanta ta shiga kitchen ta had'a mishi had'add'u dishes, sai misali k'arfe 4:20pm ya
iso lokaci da sak'on isowarshi ya riske ta tana zaune ta shirya cikin red colour din straight rubber
gown mai adon stones a jiki tai masifar fitowa da shape d'inta, ta yane kanta da scarf multi
colour jikinta na fitarda k'amshi Dima da Asrar ahub perfumes. "Ta dauki phones d'inta tafito kaitsaye ta nufi falon bak'i tayi sallama, ya amsa ciki zazzak'ar
muryarshi saida ta zauna sannan ta gaida shi, ya amsa fuskarshi sake.
"Sai lokaci ta kalli kayan da ke jikinshi farin material ne na maza transperent, saboda har ana
iya hango white vest dinshi sosai kayan suka k'ara fitowa da kyawunshi, ita kam tsawo
rayuwarta bata ta6a gani farar fata da farin kaya yake masa kyau irin Aliyu.
"Ba laifi yau ya ci abincin da aka kawo mishi saidai kad'an yaci, yau d'in ma ya yi k'ok'ari ba
kad'an ba wurin yi mata fira bai wuce 1 hour da zuwa ba ya ce zai wuce ta rako shi had'e da yi
mishi godiyar kayan jiya.
"Yana batun shiga mota direban Abba yadano kai dole ya jira fitowar Abba suka gaisa, saidai
babu wata walwala akan fuskar Abba ya tank'e fuska kamar maigadin mak'abarta sai ma wajen
'yarshi ya juya yana washe mata hak'ora, ta shige jikinshi tana cewa whats a pleasant surprise
Abba! "I'm sorry my princess I come without informing.
Yafad'a yana ciro ta daga jikinshi.
It's okay Abba...saidai gaskiya ba ka kyautawa Ummi ba duk dai ba wannnan ne first time da ka
fara yin haka ba.
Ta k'arasa magana kamar da fushi akan fuskarta.

Yayin da Aliyu ya zama d'an kallo sai sata kallonsu yake, saboda sun yi masifar burge shi da
alama akwai shak'uwa mai k'arfi atsakaninsu, kamar shi da nashi mahaifi ba san time d'in da ya
yi murmushi ba da ya tuna da yadda wani lokaci suke daro shi da Daddynshi.
"Abba ya ce ki je sallame bak'onki ki dawo naji laifina naga fuskar my cute princess ta nuna
fushi.
Murmushi tayi wanda bai wuce le6enta ba ta ce uhum!

Abba ya nufi cikin gida ta juyo wajen Aliyu tana murmushi ta ce sai anjima yalla6ai amma gobe
kafin ka wuce za ka biyo muyi sallama ko?"
"Insha Allah Abba's girl!
'Yar dariya tayi had'e da cewa ka ganka ko...
Batare da yasake cewa komai ba ya bude mota ya shiga direbanshi yaja suka fice daga gidan,
sannan ta juya zuwa cikin gida.


Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:52 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- RUYUWATA

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*

*12*

Washe gari bai samu damar biyawa wajenta kafin ya wuce Abuja ba, ya dai kirata a waya suka
yi sallama duk wannan abin yana yi ne don kawai ya farantawa Daddynshi rai ba wai don ya ji
yana sonta ko kuma ra'ayin aure ba.
***----***---****
*ABUJA*

Da yake jirgin safe Aliyu ya shigo yana isowa direbanshi Isah ya yi picking d'inshi daga Airport,
lokaci da ya iso Ardo mansion ba nemi kowa ba ya wuce flat dinshi dama wannan yana d'aya
daga cikin d'abi'unshi, za ka san tafiyarshi amma ba lalle bane kasan dawowarshi.
"Freshen up ya yi gani lokaci sallar azhar ya yi yasa yasaka farar jallabiya mai gajeren hannu,
ya nufi masjid da ke gidan ya yi sallah yana dawowa ya cire jallabiyar ya jefa akan sofa ya nufi
master bedroom dinshi ya haye tangameme gadonshi, ya k'ara gudu Air con ya lumshe
shanyayun idanuwanshi masu cike da bacci bai dauki dogon lokaci ba bacci ya yi awon gaba da
shi.
sai misali k'arfe 5:17pm ya farka a gurguje ya yi wanka saboda jikinshi ya sake bayan ya yi
sallah la'asar ya canza jallabiya jikinshi zuwa fari three quieter da white colour hoodie armless,
wacce ta fito da muscles d'inshi farare slippers masu taushin gaske yasaka, ya kwashi
wayoyinshi ya nufi flat d'in momma. A falo ya tararda ita da girls d'inta sai faman zazzagawa Tima fad'a take akan tak'i shan
maganinta.
Ya yi sallama can k'asan mak'oshi Minat ta amsa mishi sannan ta gaidashi, ya amsa mata
kamar yadda ya yi sallama.
"Zee-zee ma ta gaidashi ya yi banza da ita, Tima da ke shasshek'ar kuka ya dakawa tsawa
ke!
A firgice ta d'ago ta dubi shi rufewa mutane baki tun kafin na take miki wuya, me akayi miki da
za ki tsirawa mutane kuka duk kin cika min kunne?"
sadda kanta k'asa tayi tana sharar hawaye, ke Zainab me take yi ma kuka?"
Magani ne momma ta bata tak'i sha shine momma take mata fad'a.

"Yatsine fuska ya yi ya ce momma please....ki dinga hak'uri da yarinyar nan mana, tunda ta
ce bataso magani ba sai ki kyalleta ba in fact wannan magani mai wari tsiya ko waye dole ya yi
kuka shan shi, ni narasa ina ki ka samo shi.
"Kafira harara momma ta zanga masa kafin ta ce gidan ubanka na samo shi, wallahi Sultan
ka shiga taitayinka da ni.
Dama ina cike da kai zaman jiran zuwanka nake.
"Kallo da yakewa su Zee-zee yasa suka gano me yake nufi da sauri suka mik'e Minat ta
kamo hannun Tima suka nufi upstairs parlor.
"Ya tsare momma da idanuwanshi da suka nuna zallan 6acin rai, duk duniya ba abinda ya
tsana irin fad'a tun yana yaro da ka yi mishi fad'a gara ka rufe shi da duka.

Gani yadda ya tsareta da idanu yasa tagano ya hasala, dama haka takeso saboda duk lokaci
da ya harzuk'a tafi sauri aiwatarda shirinta akanshi.
"Don haka ta cigaba da cewa wai har da kai sultan za'a had'a kai a munafuce ni, wato shine
za'a kai kayan lefen aurenka Yola ina matsayin mahaifiyarka ba d'an banza da ya gayamin sai
da naji a bakin shannu talla, hakan da ku ka yi kai da mahaifinka kun kyauta?"
Tak'arasa magana tana share hawayen kissa.

Ta gefen ido take satar kallonshi.

Sosai jikinshi ya yi Sanyi gani yadda take kuka kuma duk a dalilinshi, ya sausauta muryarshi
cikin tattausan lafazi yafara magana ki yi hak'uri momma bansan cewa Daddy bai gayamiki
zance lefen ba, ni kaina ba sanarda ni ya yi ba sai ana gobe za'a kai kayan Aunty Salma ta
kirani a waya take sanarda ni. Kada wannan abin ya dameki momma Daddy ya yi haka ne duba da banaso aure, ya kuma san
duk abinda banaso ba lalle bane ki so shi, ki kwatarda hankalinki momma aure ma ba sonshi
nake ba balle wacce aka kai ma kayan lefe.
"Gyara zama momma tayi ranta fari tasss.......ta ce ni na dauka ko had'uwarka da yarinyar
kafara sonta, musanmman da naji ance kyakyawa ce ajin farko.
"Uhm....yafada had'e da dafe goshi ya ce kema momma kina da wani zance sai kace kin
manta da waye Aliyu, ko kayan sawa nace banaso to ta tabbata banaso su kuma har abada ba
zan so su ba, balle mace wacce kiyayyata darsu azuciyata.
"Hamdallah momma tayi ta cika fuskarta taff da murmushi, ta ce ka bi hankali sultan kada
Daddynka ya yi sauri hal6o jirginka ka ko san ba za ku kwasheta da kyau ba.
"Insha Allah bama zai gane ba saboda ko cikin kuskure banta6a fad'a mishi bana sonta ba.
Madallah d'an albarka bari nasa Laure ta kawo ma abinci.
Da sauri ya ce no am okay"
Sama-sama suka cigaba da fira yawanci firar tasu duk tambayoyi ne momma take mishi, akan
barrister wani ya bata amsa wani kuma ya ta6e baki ko ya yi shiru.
***----****----****
*™YOLA*

Tafiya Abba ya shiryawa ummi da Barrister Amina zuwa Dubai, siyayyar kayan aurenta
milliyoyin kudi ya basu ita kanta Ummi sai da ta zare kud'ad'e masu dibin yawa a account d'inta
da za tayi tafiyar da su Barrister A ita ce 'yarsu ta fari kuma 'ya mace daga kanta za suyi
shekaru kafin su aurarda Rahma don haka duk wani tanadinsu akanta suke yi. Ana sauran kwana biyu tafiyar Barrister ta zauna tayi nazarin irin makud'an kud'in da take da a
account d'inta tarawa kawai take batare da tana amfani da su ba, don haka yanzu amfaninsu
yazo, zarar abinta tayi za tayi tafiyar da su.
"Kwanansu tara a Dubai suka juyo Nigeria duk tsawon lokaci nan Aliyu bai nemi ta ba, kamar
yadda ita ma bata nemi shi ba duk da koda yaushe cikin tunaninshi take, amma ba za ta iya
karya bulleta ba ta nemi shi.
****''''****'''''***
*ABUJA*

Aliyu zaune a sitting room d'in Daddy suna tattauna nasarar da ya yi a business trip d'in da
yadawo, Daddy ya gyara zamanshi ya dubi Aliyu da kyau kafin yace wane irin shiri ka ke yi
dangane da aurenka?"
Yatsine fuska ya yi ya ce babu.
meaning?"
cewar Daddy a fusace.
Daddy babu duka fa jiya-jiyanan nadawo ko hutawa banyi ba, yanzu haka gajiya bata gama
sakeni ba.

"Sosai ran Daddy ya 6acin sai kallon Aliyu yake kamar ya rufe shi da duka.
Ya ce wannan zance banza ne yau duka saura kwanaki tara a daurama aure, amma ba ka
shirya komai ba.
Kai kenan duk lokaci da akayi maka magana akan aurenan sai kasan yadda za ka kare kanka,
ka sani sultan ina nema maka alkhairi ne ba sharri ba domin duk uba nagari yana fatan d'anshi
ko 'yarshi suyi dace da abokanan rayuwa masu nagarta da mutunci.
Abinda nake so ka gane Sultan shi ne wannan auren umarnina ne, ba wai ina shawartaka ba
don haka ka kasance a shirye ka kuma yi abinda kowane ango yake yi yayin aurenshi, saboda
ba abinda za'a fasa sai in dai mutuwa ce ta dauke ni kafin lokaci, shi ne ka ke da damar fatali da
umarnina, shiyasa da na fahimci mahaifiyarka tana min zagon k'asa a zance aurenka na tsigeta
a tafiyar domin banaso abinda za kawo min tangard'a saboda haka ka kiyayye.

Sosai jikin Aliyu ya yi sanyi ya kalli inda Daddy yake zaune, ya ce Daddy kayi hak'uri wallahi
abubuwa ne sukayi min yawa har narasa ina zan sa kaina.
"Takaici ne yak'ara kama Daddy batare da yace da shi komai ba, ya mik'e ya shiga bedroom
bai dauki dogon lokaci ba yadawo hannunshi dauke da led'a fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login