Showing 63001 words to 66000 words out of 85584 words
Chapter 22 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf
dafe k'irji ni Yalla6ai....?
Ta tambaya da idanuwa a zare.
"Ehh...ke d'in.
Zaburo baki tayi tace gaskiya Yalla6ai kayi min sharri ni ba haka nake ba.
"Da gaske yafad'a yana kallonta.
Harararshi tayi har ta bud'e baki zata yi magana idanuwanta suka sauka k'asan dining table tayi
arba da Teema zaune ta lankwashe k'afafuwanta, gashin kanta awargaje.
Gabanta ya yi mummunar fad'uwa batasan lokaci da ta zabura ta tashi tsaye ba,tare da furta
wayyo...Allahna!
Da sauri ya baro wajen zamanshi ya rik'o shoulder ta sai faman tsandara ihu take, ya girgizata
da k'arfi yana fad'ar menene ya tsorata ki haka..?
Hey...look at me ta kalleshi numfashinta na fita da kyar saboda tsoro kumatunta ya d'an
bubbuga kad'an tare da cewa relax & breathe gani kusa da ke ba abinda zai sameki.
"Ta kalleshi a firgice tana fad'in Yalla6ai.....kalli Tee....teema k'ark'arshin table bansan yaushe
ta shigo ba ko kai kasan da shigowarta?"
Yayi ajiyar zuciya ya kai ganinshi inda take pointing da yatsanta, Teema na nan zaune kamar
yanda barrister taganta sai wasa take da 'yan yatsunta.
"Sosai Aliyu ya harzuk'a a fusace ya fizgo Teema ya cirota daga k'ark'ashin dining table har
ya d'aga hannu zai wanka mata mari barrister ta rik'e mishi hannu.
Haba.....Yalla6ai me tayi maka da za ka mareta?"
Cike da takaici yace narasani har sai yaushe Fateema zata daina wannan iskancin isakokan
nan nata.
Murmushi Barrister tayi tace Allah ya huci zuciyarka Yalla6ai amma ai ba ita ta dourawa kanta
ba addu'a za ku dinga yi mata har Allah ya rabata da su.
Girgiza kai ya yi yace Amina bakisan wacece Fateema ba banza bata kawo ta nan akwai laifin
da iskokan nata suka aikata ko kuma da akwai abinda takeso a wurinki.
Barrister ta zaro idanu a rud'e tace na shiga uku!
Gani yadda barrister take zarar idanuwa alamar ta tsorata yaba Aliyu dariya ga Teema sai k'ara
makalk'aleta take yi.
Ya matso daff...da ita yana dariya yace gaskiya Amina ke matsoranciya ce, don kawai nace
tana so wani abu a wurinki shine kike wannan zarar ido to ki kwatarda hankalinki.
To wai Yalla6ai ya akayi ka fahimce akwai abinda takeso a wurina?"
Murmushi ya yi tare da fad'in abinda yasa nace akwai abinda takeso wurinki saboda ni Allah
bai had'ani jinina da shirmeta ba, ko kusa bata kusanta inda nake.
Ki cire tsoron fateema ba mahaukaciya bace da hankalinta kawai dai tana d'abi'u kamar na
masu ta6in hankali, wasu lokuta za ki ganta ta dawo normal ko yanzu akwai abinda takeso
wurinki shiyasa kika ga tayi wannan kwanton bauna, tana samun abinda takeso za ki nemita
kirasa haka take da sannu za ki saba da al'amarinta mai ban mamaki. "Ajiyar zuciya mai k'arfin gaske barrister ta sauke tare da ciro Teema daga jikinta, ta zaunarda
ita akan d'ayan daga cikin kujerin dining table ta zuba mata abinci, ta ce Teema ki ci abincinki
idan kin gama za muyi magana ki gayamin abinda kike so kinji...?
Ta gyad'a kanta tare da daukar fork.
Aliyu yana murmushi ya rik'o hannun barrister yace zo ki rakani nayi kusan latti. tana dauke da
luggage dinshi suka fito adaidai k'ofar fita main parlour suka yi kicibuss....da zee-zee da meena.
Ina kwana Ya sultan?"
suka had'a baki suna gaidashi.
Harara ya galla musu yana fad'in wato ku bakuda aikin yi sai zuwa flat d'in mutane da sassafe
salon ku takura mana ko...?
"Zaro idanuwa suka yi suna kallonshi baki bud'e mamaki suke yaushe Aliyu yayi baki har haka.
Gani yanda suka tsareshi da idanuwansu baki sake suna kallonshi kamar ansaki sabon movie a
cinema, yasa sake walga musu harara a karo na biyu yace banaso iskanci wannan kallo da
kuka tsareni da shi na menene?
Barrister tayi dariya had'e da basu hanya tana fad'ar ku kyale wannan yayan naku, yau abokin
fad'a yake nema ku shiga ciki gani nan zuwa.
"Da sauri suka wuce ciki suna gulmar canji da suka gani a tare da yayan nasu.
Yana gani sun shige ya rungumeta yana kissing d'inta saida yayi mai isarshi sannan ya saketa,
har ya shiga mota tana d'aga mishi hannu saida taga fitarshi sannan ta juyo a dining area ta
hangosu tare da Teema suna breakfast har tanufi wurinsu sai taji wayarta na ringing
sai kawai ta nufi wayar da ke aje akan center table sunan barrister Z ke yawo a secreen d'in
wayar tayi receiving kiran had'e da k'arawa a kunnenta.
Gaisawa suka yi kafin barrister z ta ce "bebs nayi magana da malam ya ce sai kin kawo masa
Maryama dole sai ya yi mata ruk'iyya.
Ajiyar zuciya barrister A tayi ta yadda ganinta a dining area ta kalli su zee-zee taga hankalinsu
bai kanta ta haura upstairs ta shige bedroom dinta har da murd'a key, ta ce Bebs ta wacce
hanya zan fito da ita har na kawota Yola....?"
Ni ma nayi wannan tunani amma me zai hana gobe mu biyo jirgin safe ni da malam mu zo
abuja.
Shiru barrister tayi na mintuna k'alilan, kafin ta numfasa ta ce wannan shawara taki tayi, saidai
ko yanzu akwai matsala saboda muddin momma tasan manufarmu zata bi kowace irin hanya
domin ta hana malam aikinsa.
"To yanzu menene abin yi?"
Bani lokaci k'adan nayi tunanin mafita zan kiraki daga baya.
"shikenan ina jiranki.
Ta kashe waya had'e da folding hannayenta a k'irji tashiga kai da kawo a tsakiyar d'aki, wani
tunani ya fad'o mata take tayi na'am da shi ta bud'e k'ofa ta sauko k'asa, su zee-zee na ganinta
suka mik'e kowace ta dauki handbag d'inta meena ce tafara magana matar yaya za mu wuce
school ga Teema nan mu bar miki, ba musan laifi da tayi ma momma ba tun jiya ta rufeta a
d'aki. yanzu ma ta fita shiyasa muka bud'eta ta gudo nan don Allah matar yaya ki 6oyeta karki
bari momma taganta, zata iya bata magani nan da bataso sosai take wahala idan tasha shi.
"Murmushin k'arfin hali barrister tayi duk ta d'an k'adu bata bari meena tagano hakan ba, sai
kawai ta ce karki damu meena zan kulata da ita har ku dawo da yake yau ban zuwa office kinga
sai ta tayani fira.
"Shikenan matar yaya sai mun dawo.
Adawo lafiya!
Tafad'a had'e da zaunawa akan one sitter fitarsu ke da wuya Teema ta taso daga dining area, ta
zauna kusa da barrister ta sunkuya dai-dai kunnenta ta rad'a mata momma tafita zata had'u da
Jarumi ta kar6o poison da zata kashe maryama da Baaba laraba, saboda nace sai na tona
mata asiri shine ta rufeni a d'aki.
Kiyi sauri ki fita da Maryama daga gidanan idan kika bari ta dawo tabbas maryama zata mutu.
Gaban barrister A yayi mummunar fad'uwa ta zazzaro idanuwanta, cikin kad'uwa take kallon
fuskar Teema mai kama da ta momma Murmushi Teema tasaki mata tare da fad'in ki tashi
matar yaya kada lokaci ya k'ure miki.
Gaba d'aya ta zama speechless sai kawai ta tattaro raguwar natsuwarta tayi amfani da ita ta
hanyar mik'ewa tsaye, da gudu ta haura sama ta canza kayan jikinta ta dauko makullin mota.
Ta tarik'e hannun Teema gudu-gudu suka isa flat d'in maryama wani heavy knocking tashiga yi,
har tana had'awa da kiran sunan Baaba.
Ta window baaba ta lek'o wacce fuskarta ta kumbure saboda maruka da tasha, hannun momma
ta bud'e kumburaren bakinta ta ce 'yar nan daina wahalar da kanki da bugun k'ofa tun jiya
Zaituna ta kar6e makullin hannuna.
"Barrister A ta zaro idanuwa ta ce Baaba ki kwantar da hankalinki, yanzu nan zan nemo
hanyar da zan fito da ku.
Girgiza kai Baaba tayi tana fad'in babu wata hanya 'yar nan dama nasan zuwanki sasshe nan
sai ya haifar mana da gagarumar matsala.
"Batare da barrister ta tanka mata ba tanufi backyard Teema ta bita a baya, windows d'in wuri
tashiga dubawa taga babu yanda za'a yi mutum ya iya fita ta cikinsu.
"Iya tunaninta ta rasa lala6o mafita, juyawa da zata yi tayi ma Teema magana sai taga
wayam...bata wajen da sauri ta dawo gaban barandar flat d'in tana kallon k'ofar.
"ji tayi an dafa kafad'arta ta waigo atsorace Teema tagani tana mik'a mata wasu tulin keys,
matar yaya ki gwada wad'annan kila adace ki samu key da zai bude k'ofar.
Jikin barrister yana rawa ta kar6i keys d'in daga hannun Teema, tashiga gwadawa duk wanda
tasaka bashi bane, sai wani shegen sweating take yi kaman wacce aka watsawa ruwa.
"Daga can gate Sa'eed ya hangota ya nufo wajenta, sam bata lura da ya iso wajen ba sai
kawai taji sautin muryarshi yana cewa ma'am ko zan iya taimaka miki...?
Da mugun tsoro ta waigo suka had'a idanu muryarta na rawa ta ce Sa'eed wallahi ka tsorota ni
banga lokaci da ka iso wurinan ba.
"Murmushi ya yi tare da fad'ar ai kin shagala da gwada keys ne shiyasa baki lura da ni ba.
Kawo na taimaka miki ta mik'a masa keys d'in ta koma gefen teema tayi tsaye zugun.....
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:21 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
_ina ma'abotan so k'amshin ga dama tasame ku idan kina son ki kasance cikin k'amshin a koda
yaushe tamkar barrister A, ki tuntube ni ina siyarda Arabian perfumes masu k'amshin gaske da
saurin siye zuciyar maigida k'amshi shine mace duk mace da ta bari mijinta yaji odour a jikinta
taci baya saboda haka ki garzayu ki kwashi gara6asa ina siyarda Arzaan, Armani, Burhan,
Al-maleka, mufaddal, Dima, Asarar Alhub perfumes da dai sauransu Bangare body spray akwai
Nada, Bushra, thaljee kuma akwai Air freshener domin k'amsasa d'akin uwargida da na maigida
ina da turaren garwashi mai shegen k'amshi akwai hand&body lotion skin dinki ya yi smooth ki
dinga glowing, palm dinki ya yi soft kaman auduga ga mai ra'ayi siya sai a tuntubeni a wannan
number 07032566172 don Allah serious buyers only_
*GIDAN RINA*
*35*
Momma tana zaune gefen gado a hotel d'in suka saba had'uwa da Jarumi gaba d'aya shirinsu
na daff...da lalacewa tun jiya da ta dawo daga unguwa kamar ace ta shiga flat d'in maryama
ashe zata yi karo ne da sabon tashin hankali, tun daga shigarta Falon ta cin karo da abinda
bata ta6a tunani faruwarshi ba. Maryama na zaune a falo cikin tufafinta masu kyau, ga jikinta ba datti tsaf-tsaf da ita kaman ba
mai ta6in hankali ba.
"Saura kirisss.....zuciyar momma ta buga tunda take a rayuwarta bata ta6a riskar tashin
hankali irin wannan ba, shiyasa tun farko ta shawarce Jarumi su kawarda Maryama kada zuwa
gaba ta zame musu matsala tsabar taurin kanshi yasa yak'i amincewa da shawararta to ai ga
irinta nan. "A fusace ta fizgo wuyan Baaba ta shek'eta sosai kamar zata rabata da ranta, sam bata yi
la'akari da tsofanta ba ta shiga dukanta ba ji ba gani saida ta gaji tasake ta ta koma kan
Maryama ita ma duka taci, ta farfasa mata baki daga bisani taja ta kaman kayan wanki ta
watsata d'aki ta rufe ta kuma kar6e keys d'in hannun Baaba, shine tana fitowa ta kira Jarumi a
waya ta sanarda shi halin da ake ciki da yake yana cikin abuja ya ce da ita gobe da safe zai zo
ya kawo mata poison ta zubawa maryama da Baaba a abinci su duka biyu su mutu, alokaci da
take waya da shi ashe Teema tana la6e momma na gama waya Teema tafito daga ma6oyarta
tana kyakyatar dariya tare da fad'in sai na fad'awa Daddyna. shine momma ta rufeta a d'aki
saboda toshewar kwakwalwa da gajin hak'uri irin nata ta fita tabar Teema a gida.
Jarumi kuwa sai kai da kawo yake tsakanin wannan bango zuwa wannan bango, gaba d'aya
jijjiyoyin kanshi sun tashi sun yi radau-radau idanuwanshi sun yi jajir kallo d'aya za ka yi mishi
ka gano irin 6acin ran da yake ciki, sai huci tare da k'yarma yake yi.
sai da ya furzar da zazzafan iska daga bakinshi kafin ya ce Har yanzu ina mamakin Zaituna
ta yanda k'aramar yarinya irin barrister Amina tafi ki wayo in banda kina dabba ko a ciki dabbobi
Zaituna ke jaka ce, uban me yakika zo yi anan shin ba ni nace da ke zan zo har gida na kawo
miki poison d'in ba...? Ko don kutumar b***ubanka gidan bak'o na ne?
Banza jahila mai kwakwalwar dabbobi.
ya k'arashe magana yana zabga mata uwar harara.
Momma ta gyad'a kanta a tsorace sai zarar idanuwa take.
Ya sake watsa mata harara a karo na biyu ya ce shine don kina sha'awar mahaukaciya 'yarki ta
fallasa min sirri kika barta gida ita kadai, kika fito?" idan har haka ta kasance ki fara kirga sauran
kwanakinku a duniya don wallahi sai na kashe ku.
"Cikin kad'uwa Momma ta zaro idanuwa, jikinta yana rawa ta bud'e bakinta da kyar ta ce ban
yi tsanmani rashin imaninka Jarumi ya kai har da za ka iya kashe 'yarka jinin jikinka ba.
idan har ni ba ka had'a alak'ar komai da ni Kaman yanda ka ke a koda ayaushe, to....karka
manta da fateema 'yarka ce..
Shut up Zaituna nagaji da saurare maganganu ki marasa amfani, don fateema tana 'yarta ce
miki nayi ina buk'atarta ban k'ula alak'a da ke ba face sai da na hango zan samu biyan buk'atar
raina a duk lokaci da na cima burina, yada kwallon mangwaro na huta da kuda ba zai zame min
wahala ba. "Hanta cikin momma ta murd'a saboda duk lokaci da Jarumi ya ce zai kasheta ta kan dauki
zancen nashi a matsayin barazana, sa6ani yau da ta hango zahirin hakan a cikin idanuwanshi
sakamakon ya cire face mask d'in fuskarshi.
Kafin tadawo daga duniyar tunani ya fizgota da k'arfi yana fad'in fita ki bani wuri ba wani
poison da zan ba ki, ki je ki baje basirarki kada numfashin maryama ya kai gobe inaso sak'on
mutuwar maryama ya riskeni idan har hakan bata kasance ba, ki sani sai na dinga yanka
naman jikinki har sai kin mutu.
Ya karashe magana had'e da hankad'ata waje ya rufo k'ofa.
****-----*****---****
Luckily Sa'eed na gwada d'aya daga cikin keys d'in k'ofar ta bud'e, Baaba na tsaye sai
wuk'i-wuk'i take da idanuwa da taimakon Sa'eed barrister A tafito da Maryama suka sakata a
mota, kasancewar da sanyi safiya ne sauran ma'aikatan gidan suna cikin d'akunansu ba su fito
ba, gateman ne kawai a tsaye yana kallonsu. Barrister ta mik'awa Sa'eed key mota ta ce kayi driving dinmu Sa'eed ni ba zan iya ba.
"Har suka fito daga gidan batasan ina suka nufa ba, har saida Sa'eed ya tambayeta.
Ma'am ina muka nufa naga sai tafiya muke ba ki fad'amin in da za muje ba?
Ban saniba Sa'eed amma kai kana gani ina zan samu safe place da zan kai su, kafin zuwa
gobe?
Abinda ban fahimta ba ma'am meyasa kika fito da su...?
Ajiyar zuciya barrister tayi tare da fad'in saboda ana farautar rayukansu
iya abinda zan iya sanarda kai ahalin yanzu saboda haka sa'eed ka nemo muna mafita kawai,
saboda kai ma yanzu ta shafe ka kuma kaga daga Daddy har Aliyu sun yi tafiya dole muna
buk'atar taimakon wani kafin nasamu hujja da zan dogara da ita na kama momma da laifi
dumu-dumu, saboda yanzu banida wani kwakwaran evidence a hannu. "Gaskiya ne ma'am amma me zai hana mu nemi taimakon Uncle Suraj shi kadai nake saka
ran zai iya basu kariya....?"
Uncle suraj?
Ta maimaita sunan.
Ehh....ma'am shi kadai nake gani zai iya wani abu akai saboda wannan matsala ce da ta shafi
iyali bai kamata mu dauko bare mu saka a ciki ba.
"Idan kuma ba ki amince da wannan shawara ba ki kira M Ardo kawai ki fad'a mishi abinda ke
faruwa ko kuma ki fad'awa Yalla6ai Aliyu.
"Barrister A ta girgiza kanta tare da fad'in ba zaka gane ba Sa'eed duk laifi da akace babu
evidence akanshi k'irk'iraren labari ne, dole sai da hujjar da zata tabbatarda momma mai laifi ce.
Kira uncle suraj d'in in kana da contact dinshi mu ji ko yana gari.
Sa'eed ya ciro wayarshi daga gaban aljihun shirt d'in jikinshi, ya yi dialling number uncle suraj
sai dai kashhh...wayarshi a rufe take.
Ma'am wayarshi arufe take ko na kira oga Jamal shima zai iya taimakawa.
"Cikin sauri baerister ta ce Kwarai kuwa kira Jamal zuciyata tafi kwantawa da shi.
"Ringing d'aya zuwa biyu Jamal yayi picking Sa'eed ya mik'o mata wayar agurguje tayi mishi
bayani, yace su iske shi gidanshi da ke zone two Sa'eed yasan gidan.
Abinda bai wuce mintuna biyar ba suka iso gidan koda suka shigo compound Jamal yana tsaye
yana jiran isowarsu ya yi musu iso a guests room d'in gidan. barrister A tayi ma Baaba sallama
da zumar zata dawo gobe.
Parking lot ta tararda Jamal yana jiranta, anatse ta fayyace masa abinda yake faruwa sosai ya
kad'u ya kuma shiga firgici daga bisani ya yi k'arfaffiyar ajiyar zuciya tare da fad'in gaskiya
barrister A bai kamata kiyi