Showing 39001 words to 42000 words out of 85584 words
Chapter 14 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf
safe sai dare nake dawowa, kuma ba kowane lokaci nakeci abincin
gidanan ba, saboda ina da k'yak'yami k'azantar chef Emma nake ji.
"Dariya tayi tana jinjina zance nashi tare da kallonshi ta ce "Gaskiya Yalla6ai kai hukuma ne.
uhmmm......koh?"
Girar idonta ta d'age alamar eh!
Ya yi murmushi kawai had'e da fara cin abincinshi, yana cikin ci ya d'ago ya dubeta ya ce yadai
naga ke bakyaci abinci sai faman kallona ki ke yi, ko kallon fuskar tawa ya k'ossar da ke?"
Sai da tayi dariya mai ban sha'awa kafin ta ce Yalla6ai kenan ina abun kallo a fuskarka wanda
har zai iya k'ossar da ni?"
Auu......kina nufi ba abun kallo afuskana?"
"Uhm.....ni dai ban ganshi ba.
Ashe ba iya snoring da kicking d'in d'uwawun mutane ba har da ciwo makata yana damunki.
Yak'arasa magana yana kallon cikin idanunta yana murmushi.
"Ta kauda fuskarta da sauri da barin kallonshi, tana ya motsa fuska had'e da turo baki.
Gaskiya Yalla6ai you kill me at all.....ni ce nake snoring?"
Ai ni ki ka kashe barrister can you imagine in my own room you kick me in the middle of the
night.
"Yadda ya k'arasa magana yana wani gesture ya yi masifar bata dariya, sosai da ke dariya har
tana dafe cikinta.
Ya k'ura mata idanuwanshi yana kallon yadda take dariya ba k'aramin burgeshi tayi ba,
musanmman yadda pink lips d'inta suke motsawa tsintar kanshi ya yi da kai hannunshi akan
upper lips d'inta ya rik'e shi yadda ba za ta ji zafi sosai ba, ya ce lalle.....yarinya nan kin reni
wato ma dariya ki ke mun?" Ai kuwa sai na cire miki lips in yaso naga da wanda za ki sake yi min dariya.
Soft hands d'inta ta doura akan nashi ta shiga kici-kici ture hannun nashi cikin sigar shagwa6a
ta ce auuch....Yalla6ai da zafi fa.
Da zafi ko?"
Yafad'a yana kallon tsakiyar idanunta.
Turo baki tayi had'e da furta ni ka sakeni ko na cije maka hannu.
"Dungure mata kai ya yi yana fad'ar kura kawai.
Ita ma tayi dariya tana cewa na dai ji.
Ta mik'e tsaye ta koma gefe ta zauna yaja plate d'in nama gabanshi, ya ci sosai ya kora da
ruwan juice yana gamawa ya tura plate yana cewa gashinan ki ci raguwana ko za ki sami
tabarakina kidaina snoring, yana gama magana ya mik'e ya haura upstairs.
Ta bishi da kallo cike da nishad'i ashe Aliyu yana da sauki kai sai in ka zauna da shi za ka
fahimci haka.
"Ita dai komai nashi burgeta yake yi ta tabbatarwa da kanta shi d'in cikkake namiji ne mai
kwarjini.
Tsarin zubinshi yayi mata kullum kwanan duniya soyayyarshi na dad'a shiga zuciyarta, alhali shi
kuma ba burbushin sonta a tashi zuciyar, ta d'an girgiza kanta cikin rashin jin dad'i sannan taja
naman gabanta taci har ta k'oshi ta sanya ragowa cikin fridge, ta dawo taci gaba da kallon
channel d'in girke-girke. Ta dauki dogon lokaci sosai ganin dare yayi sai ta mik'e ta had'a mashi coffee ta hau sama ta
tura k'ofar ahankali tunaninta yana cikin falon, sai taga ba kowa.
"Kaitsaye ta shiga master room d'inshi ta hango shi kwance akan tangameme gadonshi, yana
bacci sam bata yi mamaki ba tasan yana cikin gajiya.
Ta doura coffee akan d'an k'aramin center table, idanunta suka hango wasu documents zube a
k'asa ta shiga tattara mishi, tana waigowa ta ganshi zaune ta kalleshi tana fad'in "Allah yasa ba
motsi na bane ya tasheka ba?"
"Ya girgiza kanshi ya ce "Ah'ah dama baccin nawa bai yi nisa sosai ba.
Ta yi murmushi kafin ta ce akwai abinda ka ke buk'ata bayan coffee nima nafara jin bacci.
"Ki je ki kwanta sai da safe.
Allah ya tashe mu lafiya.
Amin yafad'a can k'asan mak'oshi.
***"""****"""****
Washe gari da wuri ta tashi duk tasan basuda foodstuffs ta shiga gyaran gida, tana cikin
mopping d'in downstairs falo Aliyu ya shigo ta runsuna har k'asa ta gaidashi ya amsa da
murmushi akan fuskarshi.
"Ki shiga daga ciki tare da nake da maza zasu shigo da kayan abinci store.
Toh.....
Tafada had'e da daukar mopping bucket ta fice daga falo, dama already tagama mopping d'in
tana dai d'an k'ara goge wuri ne.
"Tana zaune a falonta ya tura k'ofa ya shigo, batare da ya bari sun had'a ido ba ya ce ki tashi
ga foodstuffs an shigo da su ki had'a mana breakfast.
Saidai karki yi amfani da gas yanzu nan aka jona cylinder d'in, ki yi amfani da stove akwai
kerosene aciki.
"Bai jira jin ta bakinta ba ya yi tafiyarshi, ta bishi da kallo cike da sonshi.
Murmushi tayi a k'asan zuciyarta ta ce Aliyu hukuma zama da kai sai mai dogon hak'uri,
dubeshi don Allah kamar ba shi bane daren jiya muke nishad'i tare ba.
Koda misalin k'arfe 10:00am tayi har ta kammala girki ta yi arranging table, agurguje tashiga
wanka tafito bataso ya yi latti saboda lokaci da tana kitchen yana downstairs falo taji yana waya
yana da meeting around 11 o'clock.
"Simple makeup tayi tasaka material d'inki doguwar riga, ta yane kanta da veil ta bi lungu da
sak'o na jikinta da perfumes jikinta da d'akin suka dauki k'amshi ta kalli mirror ta d'an saki
murmushi, ita dai atsarinta tana masifar son turare shiyasa bata rabuwa da shi hakan yasa take
cikin dadd'add'e k'amshi mai tsawa a rai. Flip flops slippers tasaka a k'afafunta ta sauko k'asa, tana tsaye a dining area taji footsteps
d'inshi ta maida ganinta akanshi yasha farare suit hannunshi rik'e da briefcase, tana kallonshi
har ya k'araso cikin falon ya ajiye briefcase d'in akan center table sannan ya nufo wurinta taja
mishi kujera ya zauna tayi serving dinshi. Suna kammala breakfast ya dubeta ya ce mu je ki gaida Daddy jiya da dare ya dawo daga
Lagos.
"Yana gaba tana binshi a baya suna zuwa compound idanuwanta suka sauka a apartment
d'in Maryam, kamar yadda tayi jiya hakan ne yafaru tayi tsaye tana kallon wurin.
Sosai taji tsigar jikinta ya tashi, ta tsince kanta da son sani miyasa duk cika da girman gidan iya
apartment d'in ne kawai keda k'ura da k'azanta.
"Mu je mana!
Sautin muryarshi ya dawo da ita duniyar tunani.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:02 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*24*
A dining area suka iske ahalin gidan suna breakfast.
Daddy yana ganinsu fuskarshi ta cika da farin ciki, wanda ya kasa 6oyewa sai zabga murmushi
yake yana fad'i barka ku da zuwa yaran albarka.
"Barrister A ta durk'usa har k'asa ta gaida daddy da momma yayin da su Zee-zee suka
gaidata ita da Aliyu.
Ku zauna ku yi breakfast tashi Zaituna ki yi musu serving.
Cewar Daddy yana washe baki yana kallon momma.
Sosai ran momma ya 6aci da jin furuncinshi duk da haka sai tashiga murmushi yak'e wanda yafi
kuka ciwo.
Kafin tayi magana Aliyu ya rigata ta hanyar cewa Daddy a k'oshi muke.
Daddy ya ce shikenan mu je sitting room dina zan yi magana da ku.
Har momma ta mik'e tsaye ya ce A'ha'h!.....Zaituna koma ki zauna da yarana kadi nakeso
magana mu je sultan.
momma tana kallo suka haura steps suka barta tsaye da baki galala, me Daddy yake nufi da
yaranshi kawai yake so magana?"
Tabbas.....akwai abinda yake nufi tasanshi farin sani bai cika fad'ar magana marar manufa ba.
Jikinta ya yi sanyi tashiga wasi-wasi shin ko yafara hal6o 6oyayye sirrita ne?"
Idan haka ta kasance kashinta ya boshe awurin Jarumi ba ko shakka sai ya yi
gunduwa-gunduwa da naman jikinta.
Wani shegen fitsari taji yana k'ok'arin kuce mata, da sauri-sauri gudu-gudu take haura steps.
"Duk magana da girls d'inta suke babu wacce taji, tana shiga bedroom kaitsaye ta zarce
bathroom, tsabar rud'ewa ko bathroom slippers bata saka ba.
"Ta ware k'afafunta a tsakiyar tiles ta tattare doguwar rigar leshi da ke jikinta, tasaki fitsari
daga tsaye ji ka ke sharrrrrr.......saida ta gama fitsarin ta ankara da inda tasake shi, ruwa ta
debo ta tsaftace jikinta da wuri sannan tafito ta zauna gefen gado ta rafka tagumi, sai kuma ta
mik'e zubur....ta dauki wayarta tayi dialling contacts d'in Jarumi, rufi asirinta ta kira shi tun kafin
zarginta ya tabbata.
Yana dauka ko gaisawa bata bari suka yi ba muryarta na rawa ta shiga fad'ar
Ja.....ru.....mi.....akwai matsaloli domin ba guda d'aya bace suna da yawa ta farko dai sultan ya
sadu da matarshi, na biyu kuma kaman Alhaji yafara gano plans d'inmu don Allah duk abinda ka
ke yi ka ajiye ka zo Abuja mu had'u. "Kittt.....taji an datse layin duk da haka ta cigaba da fad'ar hello....hello...Jarumi kana ji na?"
Sororo tayi rik'e da waya a hannu tasake afkawa sabon tunani me kuma wannan d'an iskan
Jarumi yake nufi da ita....?"
"Ta zube akan gado kamar kayan wanki yayin da wani mashahuri tsoro ya k'ara shigarta.
****"""****""""****
A sitting room d'in Daddy kuma suna zama daddy ya kallesu ya ce dama dangane da aikin
matarka ne, akwai wani team na independence lawyers shugabansu childhood friend dina ne
na yi magana da shi next coming Monday za ta fara aiki da su sai ki zama ready.
"Nagode Daddy Allah yak'ara girma da nisan kwana.
Amin!
Daddy Yafad'a yana k'ara fad'add'a murmushinshi.
"Shima Aliyu godiya ya yi mishi had'e da sallama tare suka dawo apartment d'insu, ya dauki
briefcase da sauri ta kar6a tayi mishi rakiya har zuwa parking lot.
"Tana dawowa ta shiga tattara plates d'in da suka yi amfani da shi ta wanke.
Bata jima da zama a falo ba, su Zee-zee suka shigo cikin shirin tafiya school da yake kowacce
su lectures d'in safe take da, Teema ce kawai bata zuwa makaranta saboda lalurarta.
"Fira suka ta6a sama-sama barrister A ta dubensu ta ce har kun fito?"?
Meena ce ta bata amsa eh....matar yaya yau lectures d'in safe mu ke da, Teema muka rako ta
tayaki fira.
"Ita bata da lectures d'in ne?"
Murmushi Meena tayi kafin ta ce, bata zuwa school saboda yanayi na rashin lafiyarta,
secondary school d'in adaddafe aka samu tagama.
"Shiru barrister A tayi tana kallon fuskar Teema wacce bata ma san me suke yi ba, saboda ta
shagaltu da wasa da yatsun hannunta.
"Ajiyar zuciya barrister A tayi kafin ta ce Ayya......Allah ya bata lafiya.
Amin!
Suka had'a baki sai mun dawo matar yaya.
Allah yatsare sai kun dawo.
kayan kallo ta kunna suka fara kallo ita da Teema, suna cikin kallo bacci ya dauke Teema akan
kujerar da take kwance.
Innocent face d'inta barrister A take kallo, can ita ma tafara hamma pillow kujera ta dauko ta
kwanta akan rugs carpet a haka bacci ya dauketa.
"Can cikin bacci taji kamar inuwar mutum tsaye akanta, kasancewar baccin nata bai yi nisa
ba.
Ta falka atsorace tana mik'ewa zaune taga Teema, tsaye gashin kanta ya wargaje ya rufe mata
fuska wanda koda tayi bacci yana gyare tsaf.......sa6ani yanzu da ya yi wani cirko-cirko.
"Inna lillahi wa'inna illahim raji'um!
Barrister A tafad'a cikin sark'ewar lafazi.
"Sosai ta tsorata da ganin Teema a cikin wannan yana yi, ta had'iye yawun tsoro ta ce
Tee...ma...menene haka?"
"Ba Teema bace ki tashi ki je ki ceto rayuka mutane guda uku daga ciki har da mijinki, kada ki
bari su cutar da shi kamar yadda suka cutarda mutane guda biyu.
Ba mu da k'arfi taimakonsu saboda su fi mu k'arfi amma ke kina da k'arfi ceto rayuwarsu
tsawon shekaru 28 muna jiran zuwanki.....domin ki bankad'o ma'adanan sirrika da ke 6oye
Amina......kada ki kyalle su ki daukar mana fansar abinda suka yi ma godiyarmu.
"Teema na gama magana ta koma kan kujerar da tashi ta kwanta, ta cigaba da bacci abinta.
Cabdijam!
Barrister A tafad'a tana squeezing fuskarta, tabbas tashiga sark'akk'iya.
Shin meke faruwa da Aliyu, shin wani irin sirri ne da zata bankad'o wanda a tsawon shekaru 28
aka rasa wanda zai bankad'o shi sai ita?"
"Rashin sani wanda zai bata amsoshi tambayoyinta masu matuk'ar rud'a d'an Adam su
hartsuna masa tunani.
"Yasa tayi K'ok'ari yakice tsoro da ya lullu6eta ta waiga ta kalli Teema wacce har yanzu take
sharar bacci.
Kujera ta nema ta zauna, tsawon 20 minutes Teema ta dauka tana bacci kafin ta falka, sosai
hanta cikin barrister A ta motsa sakamakon falkawarta daga bacci.
"Abin mamaki Teema ta mik'e ta nufo ta, zubur.....barrister A ta mik'e ta shiga ja da baya
anufinta da tayi tazara kad'an da ita, ta 6alla da gudu ta haura upstairs tayi locking k'ofa.
"Karaf......Teema ta rik'o hannunta batare da tace ita komai ba tashiga jan ta duk da barrister
A ta tsorata matuk'a haka ta cigaba da bin ta.
Ta backyard suka bi har izuwa garden sannan tasake mata hannu tayi mata ishara da hannunta
cike da wani sabon tsoro barrister A tabi hannunta da kallo, a jikin bishiyar mangwaro taga wani
tulin k'asa kamar gidan tururuwa.
"Dawo da ganinta akan Teema tayi cikin wani irin tsoro mai barazanar tafiya da numfashinta,
ta ce k'asa ce Teema mai zan yi da ita?"
"Teema wacce ke wasa da yatsunta kamar yadda take yi a koda yaushe, bata ce komai ba sai
cigaba da wasanta take yi.
"D'an gajere tunani tayi cikin sauri ta nufi wurin ta zube gwiwayoyinta duka biyu a k'asa
tasaka hannayeta tashiga tonu wuri, gani zata wahala abanza hannayenta ba za su iya hak'o
wurin ba.
"Ta mik'e da sauri tashiga dube-dube can idanunta ya kyallo mata k'arfen rodi, da gudu ta
dauko ta shiga hak'o wurin sai da tayi gina mai zurfi gaske kafin ta ciro wasu 'yan uban layoyi
birjik....masu ban tsoro da firgici.
Babu shiri tayi cilli da su ta mik'e tsaye jikinta yana rawa kamar mazari, ta zaro manyan
idanunta tana kallo layoyin kafin tadawo da ganinta akan Teema wacce har yanzu tana cigaba
da wasa da yatsunta.
"Na shiga uku!
wad'annan layoyi na menene Teema ki ka sani na hakk'o?"
Batare da Teema ta bata amsa ba ta kwashe layoyi, sannan ta dubeta sai lokaci tayi magana yi
hak'uri matar yaya yanzu ba lokaci tambaya da amsa bane, mu hanzarta bari wurinan tun kafin
wani ido ya ganmu.
Ta ko ina jikin barrister Amina rawa ya keyi, tsawon rayuwarta bata6a gani irin wannan al'amarin
ba.
"Suna shigowa main parlour ta ruga kitchen ta dauko ruwan masu sanyi gaske tasha, sai
lokaci tasami 'yar natsuwa.
Koda ta dawo falo Teema bata nan sai 'yan uban layoyi da ta zube mata akan center table, cikin
kad'uwa ta d'ebesu ta nufi upstairs bedroom.
"Ta kasa zama ta kasa tsaye takai gwaro takai mari, shin ya za ta yi wad'annan kayan
tsinbace-tsinbace?"
Oh!......ya rabbi ka kawo min mafita.
Cikin sauri ta ciro wayarta daga charging mutum na farko da ya fara zuwa mata arai ta kira ko
za ta samu mafita.
Agaugauce take dialling digit d'in Barrister Zarah, wayar har tayi ringing ta tsinke Zarah bata yi
picking ba.
"Ta yada ganinta akan wall o'clock ta tabbata a irin wannan lokaci barrister Z tana cikin
courtroom, dole wayarta zai kasance a silent.
"Zarah ce kadai take iya tunkara da wannan murd'add'en labari, rashin samunta a waya ba
k'aramin cikasss......ya kawo mata ba.
"Ta koma gefen gado ta zauna talla6e da kumatu, sai sak'a da warwara take yi.
Gani lokaci na ta tafiya bata tsinana komai ba, sai d'an banzan tunani da fargaba da suka taru
suka hanata shakattt.
"Cikin wani yana yi mai wuyar fassarawa ta tashi saida tafara adana layoyi, kafin ta sauko
k'asa ta nufi kitchen domin daura launch.
****"""****""""*****
Tana kammala girki ta juye a warmers ta shirya table, sannan ta nufi bedroom da nufi yin wanka
tana shigowa wayarta na ringing da azama tayi picking.
Hannunta har rawa yake yi musanmman da taga Barrister Z ce, batare da ta bari suka yi
doguwar gaisuwa ba ta shiga bata labarin abinda yafaru da kuma neman mafita.
"Ita kanta Barrister Z ta kad'u da jin wannan labari.
Amma don ta k'arfafawa k'awarta k'arfin gwiwa duk tasan cewa tashiga *GIDAN RINA* mai
cetonta sai Allah.
"Da farko shawarar da zan ba ki, ki fara bincike akan Teema shin da gaske ne tana da lalura
ta shafar aljanu?"
Sai abu na gaba dole sai kin cire tsoro kiyi fitsari ki zubawa layoyin kowane irin sihiri ne zai
karye, ki kuma tsananta bincike ki gano waye ya yi wannan asiri, sannan kuma suwaye mutane
nan guda biyu?"
Kuma suna ina?
menene alak'ar Aliyu da wanda ya yi asirin?"
"Lokaci da barrister Z ta zo k'arshe a zancenta,