Showing 57001 words to 60000 words out of 85584 words

Chapter 20 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf

27 Jul 2025

1503

suka koma falo, tana
zaune akan three sitter yayin da ya yi pillow da cinyoyinta sai fira suke abinsu kaman ba d'azu

ya gama fushi da ita ba.
*****"""****"""****
*AFTER ONE WEEK [BAYAN SATI D'AYA*]



Tuni barrister A tafara aiki da Greatest Nigerian lawyer firm.
Team ne na kwararu lawyers the whole nigeria ake ji da su. kasancewarta kwarariya ta kuma
san makamar aikinta yasa cikin k'ank'alin lokaci sunanta ya yi fice.
"A hankali take tafiya tafito daga wuse zone magistrate court hannunta na dama rik'e da
jakkar laptop d'inta, ta nufi parking space ta shiga motarta tayi reverse tafice daga harabar
kotun, direct gida ta wuce tana gama parking tafito har ta nufi hanyar flat d'inta sai kuma tafasa
ta nufi hanyar na Maryama, tasha magiya kafin Baaba laraba ta bud'e mata k'ofa bayan ta shigo
saida tafara lek'awa d'akin Maryama, taga halin da take ciki sannan ta dawo falo wurin Baaba.
falon ya dauki shiru na wani d'an lokaci kafin Barrister A ta kawo k'arshen shiru ta hanyar cewa
Baaba ki yi hak'uri da ta k'urawa da nake miki wanda kusan kullum idan zan fita office ko na
dawo sai na biyo flat d'inan ina miki magiya ki budemin k'ofa ga alama yau dai kin gaji da naci
nawa, shiyasa kika bud'emin batare da korafi ba.
"Ajiyar zuciya Baaba tayi kafin ta ce ki yi hak'uri 'yar nan banida za6i da ya wuce na hanaki
zuwa sasshe nan, yau dinma na yanke shawara na bude miki ki shigo saboda akan idanuwana
Zaituna ta fita, yanzu ma ina shawartarki da ki yi gaggawa tambayata abinda kike so sani akan
rayuwar Maryama ni kuma ashirye nake da na ba ki amsa. "Murmushi barrister A tayi tare da gyara zamanta, ta ce "Baaba menene alak'arki da
maryama...?
Tsawon wane lokaci kika dauka tare da ita...?
Me kuma kika sani dangane da ciwonta....?
"Saida Baaba ta gyara daurin d'an kwalinta kafin ta ce "Alak'ata da maryama ta samo asali
tun shekara 32 da suka wuce abaya, na kasance 'yar aiki a wurin maryama.
Mijina ya mutu ya barni da marayu 'ya'ya har guda 4 mahaifina ya mutu mahaifiyata kuma
makauniya ce sai tayo bara muke samu abinda mu ka ci saboda ba wani dangi da zai iya
tallafawa rayuwarmu, saboda suma suna fama ne da nasu talauci.
"Asalina ni 'yar suru local government ce take cikin jahar kebbi, tsananin talauci ne ya kawo ni
aikatau a garin Abuja wanda anan Allah ya had'ani da Maryama had'uwata da ita shine silar da
rayuwarmu ta canza ni da zuri'ata, idan nace zan tsaya gayamiki irin dibin alkhairi maryama
agareni wannan makirar mata zata dawo ta tararda ke anan. "Haka ne Baaba sai ki hanzarta ni kaina banaso ta dawo ta tararda ni.
"Baaba tayi gyaran murya tare da cewa ciwon Maryama ya samu asaline alokaci da take dauke
da juna biyu har na watani 6 sai kawai muka waye gari da ita a haukace, alokaci Alhaji ya nema
mata magani daga bayane ya daina kulawa da ita kaman dai yadda muka waye gari da ita
ahaukace, haka muka waye gari ba wanda ke tada koda zancenta ne. "Tsananin tausayin rayuwar Maryama da d'inbin alkhairi da tayi min abaya yasa na za6e na
sadaukar da rayuwata agareta, shiyasa duk tsawon wad'annan shekaru nake zaune da ita duk
da a wasu lokuta Zaituna tana min barazana, ina da yak'ini tabarni na zauna da maryama ne

saboda tasan ba wanda zai iya zama da ita sama da ni.
wannan shine kad'an daga cikin abinda nasani akan rayuwar maryama.
Baaba a labarinki kin ce Maryama tana da juna biyu shin ta haife shi idan kuma ta haifeshi ina
abinda ta haifa...?
"Maryama ta haifi cikin jikinta 'ya mace sai dai bata zo da rai ba kaman yadda nasamu labari
daga bakin Zaituna.
"Kina nufi lokaci da ta haihu ba ki tare da ita ne...?
Kwarai bana tare da ita saboda na tafi suru sakamakon rasuwar da mahaifiyata tayi.
"Numfashin Barrister A ta sauke kafin ta ce "Allah yajik'anta ya gafarta mata.
Amin!
Cewar Baaba.
"Barrister A ta Kalle Baaba ta ce "ki kwantarda hankalinki Baaba insha Allah maryama tayi
kusan samu lafiya, a cikin kwanaki nan Daddy zai fita da ita k'asar waje.
"Murmushin takaici Baaba tayi had'e da cewa idan har k'asar waje za'a fita da ita to kuwa har
abada ba zata samu lafiya ba. "Subhanalillah....!
Baaba meyasa kika fad'i haka?"
Saboda ciwonta bana asibiti bane balle har a fita da ita k'asar waje.
gyara zamanta barrister A tayi ta tattaro gaba d'aya natsuwarta, ta k'ure Baaba da idanuwa,
kafin ta ce "Ban fahimce ki ba Baaba warware min zare da abawa.
"Ciwon Maryama baida alak'a da asibiti saboda asiri ne aka yi mata, asibiti Kuma basuda
magani warware asiri.
"Wani shegen sweating ya zubuwa barrister a fuskarta, da sauri ta ciro handkerchief tayi
wiping muryata na rawa ta ce "asiri kuma Baaba...?
To waye ya yi mata asiri har ta haukace..?
Tabbas asiri aka yi mata 'yar nan kuma ba kowa bane face Hajiya Zaituna, kuma lokaci zuwa
lokaci tana sabunta asiri tare da saka wata likita marar imani irinta tana mata allura, duk lokaci
da akayi mata allura sai ta dauki kwanaki masu yawan gaske kafin ta bar ihu had'e da gurnani,
in tak'aita miki haukan sabo yake dawowa dal.... "Sosai barrister A ta tsorata ta kuma sha jinin jikinta tabbas momma ta cika cikkakiyar marar
imani, la'ananniyar mushirika.
"Da kyar Barrister ta bude baki ta ce Baaba nayi miki alk'awali koda zan rasa numfashina, sai
na cuto maryama daga hannun wannan makirar mata wannan alk'awalina ne.
Daga haka ta dauki jakkar laptop d'inta ta fice Baaba ta bi bayanta da kallo, sosai yarinyar ta
bata mamaki ta yaya zata ceto maryama wannan shine abinda ya daure mata kai.
Cike da mamakin da ya kasa sakinta ta mik'e ta rufo k'ofa.
"Barrister A ko baranda flat d'inta bata kai ba, motar momma ta shigo gidan da sauri ta k'arasa
isa flat d'in nata, batare da 6ata lokaci ba ta tura k'ofa ta shiga saboda tunda tafara zuwa aiki
Aliyu ya nemo mata 'yan aiki har guda biyu.
"Tana shigowa main parlour Salama ta fito daga kitchen ta kar6i jakkar hannunta, tana fad'in
"sannu da zuwa aunty!
"Yauwa...salama ina Bintu ta shiga ne?
Gani aunty!
Cewar Bintu tana fitowa daga kitchen d'in.

"Ina fatan ba wani matsala ko?
Babu aunty.
Shikenan bari na watsa ruwa kafin na fito d'aya daga cikinku ta ciro Fish a freezer zan yi girki.
To aunty suka had'a baki salama ta bi bayanta rik'e da jakkarta suna zuwa k'ofar bedroom d'inta
ta kar6i jakkar, saboda bata yarda da 'yan aikin nata su shiga mata d'akin baccinta ko na Aliyu
ba.
ko falon sama bata bari su shiga iyakarsu, falon k'asa sai kuma kitchen.
Agurguje tayi wanka tafito ta zura blouson gown mai supghetti hands, tasaka winter hat akanta
tana sauka downstairs kaitsaye ta wuce kitchen da taimakon 'yan aikinta ta kammala
had'add'un girkinta, ta shirya table lokaci har an fara kiran sallar magarib.
"Wanka tayo had'e da alwala bayan ta gama sallah bata tashi ba sai da ta sallaci sallar isha'i,
tana gamawa ta shiga tsantsara makeup ta shirya cikin simple gown na shaking material,
fitinane k'amshinta na fitar hankali yana tashi a jikinta.
ta sauko k'asa ta kame a two sitter tana jiran dawowar king Ali Ardo.




Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:19 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO

*GIDAN RINA*



*32*


Misalin k'arfe 9:44pm na dare Aliyu ya dawo gida sosai yau ya d'ebo gajiya, yana shigowa main
parlour ya yi arba da ita tasha kyau na ban mamaki da sauri ta tashi ta nufeshi da sannu ta
kar6i kayan hannunshi sai kawai ya ware mata hannayenshi, batare da 6ata lokaci ba ta shige
k'irjinshi ya rungunmeta tsam....ajikinshi yana shafa gadon bayanta, ya rad'a mata akunnenta "I
miss you so much wifey!
"Cike da shauk'in sonshi ta mayar mishi da "I miss you too my king!
Ya cirota daga jikinshi ya kama hannunta suka nufi upstairs ruwan wanka ta had'a mishi koda
tafito ya cire kayanshi daga shi sai boxer, da sauri ta kauda kanta tana fad'i Yalla6ai na had'a
ruwan bari naje na had'a maka abinci kafin ka fito.
Ta juya da sauri zata fice daga d'akin cikin zafin nama ya finciko ta tayi baya kaman zata fad'i ya
tare da fad'add'e k'irjinshi, hugging ita ya yi tightly kaman zai shigar da ita k'irjinshi yayin da ya
shiga yawo da hannayenshi a sassan jikinta, harshenshi ya zura a kunnenta yana tsotsa tuni
jikinta ya dauki rawa romancing d'inta yake kaman wani sabon kamun hauka ta kasa motsawa,
jikinta ya mutu muruss...duk illahirin k'afafunta rawa suke yi suna neman kasa daukarta, jin
yanda tayi lakwass...yasa ya dauketa cak sai bisa gado ya yi connecting lips dinsu ya shiga
bata hot french kiss irin mai masifar shiga jiki, cikin sauri ya yi undressing d'inta gani haka tsoro
ya kamata, ta shiga tutture shi daga jikinta "tana cewa Don Allah ka daina banaso Yalla6ai,
nace kadaina banso...!
Ta k'arashe magana cikin shouting.
Cak...!ya tsaya da abinda ya keyi kamar anyi ruwan sama an dauke, ya tsareta da lulu eye's
dinshi da suka canza colour, ta kauda fuskarta ya hadiye yawu kafin asanyayye ya ce "menene
bakiso Amina ni ko kuma sunna da nake k'ok'arin mu raya...?
"Shiru tayi don batasan amsa da zata bashi ba.
ki amsa min mana Amina.
Ya katse mata shiru nata.
muryarta na rawa ta ce "Ba kaci abinci ba Yalla6ai.
Ce miki nayi inajin yunwa ne...?
Yafad'a yana zare mata jajaye idanuwanshi.
Ah'a!
Tafad'a cike da wani sabon tsoro.
To.....kingani tunda ban fad'a ba ki barni nayi abinda nakeso please!
"Ah'a....Yalla6ai ba zan iya ba kaje kayi wanka.
Da sauri ya kalleta tasake kauda fuskarta hadda runtse idanuwa.
"Amina ko ina body odour
ne...?

Yana magana had'e da shinshina jikinshi.
Ta girgiza kanta.
To idan ba haka bane Amina menene...?
"Ni gaskiya I'm not ready kuma yunwa nake ji.
You're not ready....?
Ya maimaita magana nata wanda ke nuna tsintsa mamakinshi, ya saki d'an siririn tsaki ya tureta
daga jikinshi wani mugun haushinta ya lullu6eshi.
"Afusace ya nuna mata k'ofar fita dallah tashi ki fita banaso ganinki bakida wani amfani
awajena, matuk'ar ba za ki iya mallaka min kanki ba ko a mafalki karki sake zuwa wajena tashi
ki 6acemin da gani.
"Jikinta ya dauki k'yarma ta bud'e muryarta a raunane ta ce "I'm sorry Yalla6ai I don't mean to
hurt yo....
Cikin fushi ya katseta ta hanyar cewa shut up please I don want your fucking...apologies just
leave my room right now.
Yadda ya k'arashe magana cikin hargowa kamar zai kai mata duka yasa ta mik'e ta dauki rigarta
jikinta na rawa tasaka batare da tasake furta uffan ba, ta fita daga d'akin.
"Ya nemi gefen gado ya zauna dafe kanshi wani irin takaicin barrister yake ji, ai ita ba
k'aramar yarinya bace da zata nemi ta wahalarda shi kuma a wannan shekaru nata ba zata ce
batasan menene aure ba.
"Tsabar ta tsaneni ne kawai da tana sona ba zata k'i mallaka min abinda yake halak d'ina ba.
D'ayan bangare zuciya Aliyu ya ce da shi haka.
Ba shakka hakane.
Yafad'a abaiyane
Ya mayarda ganinshi akan erection d'inshi, ya matse k'afafunshi yana sauke numfashi tsawon
rayuwarshi bai ta6a jin feeling irin wannan ba, mik'ewa ya yi ya bud'e bathroom ya shiga ya yi
wanka ya fito ya saka boxer ya sauka k'asa, har zuwa lokaci mararshi yana mishi ciwo.
"Yana saukowa ya hangota zaune a dining area tayi wuk'i-wuk'i kaman kazar da aka tsamo
daga ruwa, ya tabe baki yana k'arasowa ta mik'e jikinta na 6ari taja mishi kujera buge mata
hannu ya yi before ya juyo ya galla mata harara yana cewa ba nace ki rabuda ni ba...?
"Sadda kanta k'asa tayi idanuwanta suka yi rau-rau, tana kallo ya zari plate ya yi serving har
ya kammala cin abinci tana tsaye tana kallonshi, yayin da shi ko kallon nashi da take yi haushi
yake ba shi.
Ya ra6ata ya wuce bedroom d'inshi.
Kasa cin abinci tayi duk da tana jin yunwa coffee kawai ta iya sha, ta wuce d'akinta ta rafka
tagume meyasa Aliyu ba zai fahimce ta bata ta6a ke6ewa da wani d'a namiji ba sai shi, wannan
shine first time d'inta to meyasa da ba zata tsorota ba. in fact ita ba ta kawo wannan abin anan
kusa ba. "Ta mik'e jikinta sanyi lak'ass...ta sanya sleeping dress d'inta ta kashe bulbs ta bi lafiyar gado,
har tafara bacci taji an murd'a handle ta bud'e idanuwanta da sauri ta koma mayarda su ta rufe,
gabanta na cigaba da faduwa.
"Tana jin lokaci da ya iso ya zauna kusa da ita yana kallon innocent face d'inta da ke
haskawa acikin diff light d'in da ke haskaka d'akin.
"Ya nemi gefenta ya kwanta ya saka hannayenshi ya rungume bayanta, ya tura hancinshi

cikin neck d'inta yana shak'ar k'amshinta, ya rad'a mata idan ke za ki iya bacci ina fushi da ke ni
ba zan iya bacci mala'ikun rahama suna tsine miki ba.
kiyi hak'uri wifey ba zan sake ba tunda bakiso zan jiraki har zuwa sanda kika yi ra'ayi.
"Ajiyar zuciya tasauke ta bud'e baki da zumar bashi hak'uri, shhh....ya fad'a yana d'ora
yatsanshi akan soft lips d'inta yace "please Wifey ban hak'uri nan ya isa haka nifa ba zai rage
min rad'ad'in desire da nake ji ba.
"Murmushi tayi mai cike da zallan tausayinshi da zata iya da ta bashi abinda yake so.
Ya gyara mata kwanciya akan k'irjinshi ya ce kiyi baccinki my wifey ba abinda zan miki kinji!
Ta gyad'a kanta tana k'ara shigewa jikinshi, ya rungumeta tsam...yana shafa bayanta ahankali
tashiga lumsashe idanuwanta, ya yi holding nose d'inta yana fad'i sai shegen son jiki kaman
magge amma ki ce ba ki so....
D'an k'aramim duka ta kai mishi a chest tana 'yar siririyar dariya.
Yaja musu duvet.
***"""****""""****
*Washe gari*

Tsaye take a kitchen tana had'a breakfast 'yan aikinta na taimaka mata, Aliyu ya shigo kitchen
d'in da sauri 'yan aikin nata suka fice, saboda barrister A ta sabar musu da sun ga Aliyu zai su
bar wurin, yana k'arasowa daf...da ita ya rungumeta ta baya ya ce "Good morning my lovely
wifey! Murmushi tayi had'e da cewa morning how was your night!
Kunnenta ya rik'e ya d'an murd'e shi ya ce "Bansaniba.
Kyalkyalewa da dariya tayi kafin ta ce "uhmm...!Yalla6ai daga tambaya sai cibi ya zama k'ari.
Ya kashe mata ido ya ce "Ehh...d'in.
cikin dariya ta ce to Allah ya baka hak'uri muje na baka abinci naga kanaso kasani nayi latti
kuma yau ina da hearing a court.
Suna kammala breakfast suka fito atare direbanshi yaja shi ita kuma taja motarta kaitsaye,
chamber d'inta ta nufa kafin lokaci shiga court ya yi barrister z ta kira ta bata labari da Baaba
laraba tabata, ajiyar zuciya Barrister z tayi ta ce "Abinda za'a yi yanzu wannan al'amari baza mu
iya solving dinshi mu kadai ba dole sai mu nemi taimakon malam[tana nufi kakanta]. "Nima nayi tunanin hakan saboda Baaba ta ce asiri ne kinga dole sai an warwareshi.
Ba matsala da na baro office ko gida ba zan je ba sai na biya ta gidanshi, duk yanda mu kayi zai
nemiki a waya.
"Shikenan nagode bebs Allah yasaka miki da alkhairi.
Amin summa Amin!
Amma ki daina yi min godiya bebs saboda kin fi k'arfin hakan daga gareni.
"Kafin barrister A ta furta uffan har tayi hanging up.


_Just to manage....!_

Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:19 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO



*GIDAN RINA*




*33*


K'arfe 5:30pm tadawo daga office kaitsaye ta wuce flat d'in Maryama cikin sa'a Baaba laraba ta
bud'e mata k'ofa ta shigo, bayan sun gaisa ta shiga d'akin da maryama takecoat d'in jikinta
tafara cirewa ta ajiye sannan ta durk'asa gabanta cikin rashin tsoro ta kwance mata sark'a da ke
daure da k'afafuwanta da hannayenta, atsorace Baaba ta ce mekike shirin aikatawa 'yar nan...? "Kwance ta nayi Baaba wanka za muyi mata.
Zaro idanuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login