Showing 72001 words to 75000 words out of 85584 words
Chapter 25 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf
uwansa M Ardo ya cika dama burinsa ya 6ata masa reputation shi da iyalinsa.
"Lokaci da barrister A ta iso k'ofar gidan Jamal tayi horn batare da mai gadi ya bud'e gate ba,
ya fito gefen goshinsa sanye da plaster ya gaidata tare da sanar da ita mutane gidan duka suna
asibiti.
"Sosai tasake shiga firgici cikin tsoro da fargaba ta ce "waye ba lafiya a gidan?"
Mai gidan da iyalinsa jiya daddare armed robbers suka shigo mana gida kalli goshina, dukan
bindiga ne suka yi wa maigida dukan tsiya suka yi awon gaba da bak'in da suka zo jiya gidanan.
Barrister A ta dafe saitin zuciyarta da ke hal6awa da k'arfi kana ta shiga furta
"Innalillahi wa'inna illaihim raji'um.....!
Da kyar ta iya tambayarsa wane asibiti Jamal yake, sannan an sanar da Jami'an tsaro.
Ehh.....an sanar da su ko d'azu sun zo sun sake bincike da yi min tambayoyi shi kuma maigidan
yana Nimzamia hospital.
"Cikin mugun tashin hankali ta tashi motarta, da zumar zuwa asibitin da Jamal yake kiran
Abbata ya shigo wayarta kaman ba zata dauka ba, sai kuma tayi tunani tana buk'atar wanda
zata yi magana da shi.
Tana picking ko gaisuwarta Abba bai tsaya amsawa ba ya ce "Minal wai meke faruwa ne a
family mijinki?"
saura kad'an tasaki steering mota, muryarta tana rawa ta ce "Abba wani ya sanar da kai wani
abu ya faru ne?"
Ba wanda ya sanarda ni gashinan yana yawo a kafaffen yad'a labarai da kafaffen sada
zumunta, abin ba kyau gani.
"Abba ni bansan komai ba wallahi.
Cike da takaici Abba ya ce "mother in law d'inki mijinta M Ardo ya kamata a waster dream hotel
she's having an affair abin takaici da k'aramin yaro, kuma wani kayan haushi Median ta shigo
cikin al'amari
sai yad'awa suke yi.
Kiyi gaggawa ki had'a kayanki ki zo Yola banaso press su yi wani rubutu akanki matsayinki na
daughter in law a gidan zai iya shafar career ki.
Idan babu flight ki nisanta daga gidan ki 6oye kanki zuwa gobe ki biyo jirgin safe.
Girgiza kai tayi har ta bud'e baki za tayi magana sai ta laura ga mirror mota da wani black van
tun daga fitowarta gidan Jamal yake biye da ita, tunaninta ya bata watakila hanya d'aya zasu bi
kuma gashi ta tare musu hanya saboda sannu-sannu take driving, gani haka sai ta d'an k'ara
gudu sai kawai mai motar ya dinga yi mata wani mahukacin horn. Kawai tayi decided ta gangara gefen hanya tayi parking saboda zata fi samun natsuwa ta
fahimtarda Abba ya fahimci ita ma a yanzu tana d'aya daga cikin alhalin duk abinda ya shafe su,
ya shafata ko ta gudu ko ta tsaya ba abinda zai canza hakan.
Tana gama parking sai kawai van d'in ta zo da matsiyacin gudu, tasha gaban motarta cikin
tsananin tsoro ta ce "Abba ga wata black van tasha gaban mo.....
Kafin tak'arasa wasu mutane guda biyu suka fito daga van d'in d'aya daga cikinsu ya d'aki glass
d'in motarta ya tarwatsi da sauri ta duk'e gudu kada glass d'in yayi mata rauni a fuska, da k'arfi
ya fincikota daga cikin mota ya fito da ita waje sai ihu take, ta wayarta da tafad'i Abba yake jiyo
ihunta tana neman taimako, d'ayan ya duk'a ya dauki wayarta ta ya yi switch off d'inta tare da
jefawa aljihun black lather jacket d'in jikinsa, tana ji tana gani suka jefata cikin motar tare da
saka mata blindfold suka kuma rufe mata baki da salatif, ba ka ji komai sai gurnaninta doguwar
tafiya suka yi saida suka fita garin Abuja k'auyen madallah suka nufa sai da suka yi tafiya mai
nisa kafin su nufi wani poultry house suka yi horn mai gadi ya bud'e musu gate, bayan su yi
parking d'ayan daga cikinsu ya sa6o barrister A a kafad'arsa suka shiga da ita wani flat.
*****---****-----*****
Jamal da ke kwance akan gadon asibiti saboda yaran, Jarumi sun yi masa shegen duka har da
rauni aka matarsa Zulaiha ta shiga shafinta na Facebook sai kawai taci karo da sabon labari,
cikin mugun tsoro ta mik'awa Jamal wayarta. sosai shima ya firgita da ganin labarin jikinsa yana
rawa ya mik'e daga kan gado ya cire rigar asibiti Zulaiha ta taimaka masa ya saka jallabiya,
hannunta ya riko had'e da daukar handbag d'inta wacce yake da tabbacin makullin motarta
yana ciki, parking space suka nufa ya mik'a mata handbag d'inta tare da cewa Zulaiha yi sauri ki
ja mota mu tafi.
Ina za muje Jamal kai da baka lafiya?"
Nace ki ja mota mu tafi banso silly questions.
Yanda ya k'arashe magana cikin tsawa yasa babu gardama ta ja mota suka fice daga Nimzamia
hospital.
***--*----***-----*---***
*LAGOS NIGERIA*
Tun safe Aliyu yake conference hall yana meeting saboda wani contract na gina manya-manya
tituna da hanyoyin ruwa da kamfaninsu na contractual & building material company wanda
kowane kamfani irin nasu yake sa ran ya samu project d'in, daga k'arshe kamfanin su Aliyu ne
ya yi nasarar samun contract d'in. "Saboda haka cike da farin ciki Aliyu ya fito daga conference hall direbanshi ya bud'e masa
mota ya shiga, sai lokaci ya yi switch on d'in phones dinshi da zumar ya gira rabin ransa.
Da safe kafin ya shiga meeting da suka yi waya bai sake waya da ita ba gashi yanzu har
1:27pm, ya yi dialling digit d'inta saidai wayarta ta a kashe kafin ya yi yunk'urin kiran d'ayan
layinta call d'in k'anwarsa Zee-zee ya shigo wayarsa, ya yi picking tare da kara wayar a
kunnenshi cikin matsanancin kuka Zee-zee ta ce "Don Allah Ya Sultan duk inda kake duk
abinda kake yi ka jinginar ka zo Abj muna cikin tashin hankali wanda ba za mu iya jure shi mu
kadai ba, muna buk'atar taimakonka.
Ya lumshe idanuwanshi tare da fad'uwar gaba mai tsanani ya ce Zainab waye ya rasu?"
Ya Sultan ba wanda ya rasu amma wallahi gara ace rasuwa ce aka yi da wannan iftila'i da ya
fad'awa zuri'armu. Yaya Daddy ne ya kama momma a hotel tare da k'aramin yaro wanda a
shekaru ba zai wuce age mate din Meena ba they're having an affair kuma gaba d'aya duniya ta
dauka bansan ya aka yi median tasan abinda yake faruwa a hotel din ba yanzu haka sai
yad'awa ake yi musanmman a social median saboda Abba Yusuf, ya biya wasu daga gidanje
rediyo da talevision da su daina yad'awa shiyasa abin ya yi sauk'i a kaffafen yad'a labarai
ta k'arashe magana tare da rushewa da wani sabon kuka har tana shed'ewa.
Innalillahi wa'inna illaihim raji'um!
Aliyu ya shiga maimaitawa har wani duhu-duhu yake gani da yana da d'abi'ar saurin kuka da
yau ba abinda zai hana shi rushewa da kuka, cikin wani yana yi na k'onar zuci ya ce "Zainab ki
daina kuka saboda ba abinda zai canza faruwar wannan al'amari, ba'a fata sai ma ya haifar
miki da wata matsala muyi hak'uri mu kuma doshe kunneyenmu mu dauki wannan al'amari a
matsayin k'addararmu, ke ce babba ki rarrashi k'anneki kafin na zo kinji?"
"To Yaya tafad'a tare da share hawaye.
Ina Amina in tana kusa da ke ki bata waya nayi magana da ita.
Yaya batanan tun lokaci da al'amari ya faru na shiga apartment d'inta, masu aikinta suka ce
tafita kuma har yanzu bata dawo ba, duk da muna hospital na bar ma Daniel sak'o idan tadawo
ya sanar da ita muna asibiti.
"Shikenan Zainab ki kula da Daddy kafin na zo ki kuma kira uncle Suraj ki sanar da shi
abinda ya faru, ya sameki a hospital ba za ki iya hidimar asibiti ke kadai ba.
"Yaya na kira shi yafi a kirga wayarshi switch off.
Aliyu ya dafe goshinsa damuwarsa ta k'ara k'aruwa.
"Ba damuwa ki cigaba da zama wajen Daddy ita kuma Meena da Fateema su zauna wajen
momma kafin in iso.
To....Yaya ta k'arashe magana had'e da hanging up.
Aliyu ya kira number wani friend dinshi da ke aiki a Airport ya ji ko akwai jirgin da zai tafi Abj da
rana, cikin sa'a ya ce akwai 2:30pm zai tashi ya ce ya siya mishi ticket gashinan zuwa a cikin
Airport din ya samu ya yi sallar azhar, yana gama sallah saida ya sake gwada kiran number
barrister still tana rufe hakan ya k'ara jefa shi a damuwa saboda yasan bata da hearing a court,
da kanta ta sanar da shi lokaci da ya kira ta da safe ta ce yau tana gida ba zata fita ba.
"Oh.....ya rabbi ka taimake ni kasa ita ma ba wani mummunan abu ne ya sameta ba.
har ya shiga jirgi bai fasa tunani da zance zuci ba yana cikin tunane-tunane jirginsu ya d'aga.
***----**----***----**
Jarumi uncle Suraj yana hakince akan royal chair wacce ta k'awata masa falonsa, da ke poultry
house d'inshi ya yi crossing legs dinshi jikinshi sanye da farar shadda hannunshi na dama rik'e
da pistol yaranshi suka shigo d'aya sabe da barrister A a kafad'arsa, ya direta gaban Jarumi
tare da furta "mai girma Jarumi mun cika aiki. Da pistol d'in hannunshi ya yi masa ishara da ya ja baya, ya tsare barrister A da shegu
idanuwansa kafin ya saki wani shegiyar murmushi ta gefen baki.
Ya kalli d'aya daga cikin yaransa ya yi masa alama da ya cire mata salatif d'in bakinta, nan take
ya cika aiki tana jin an bud'e mata bakinta ta dagargaje iya k'arfinta ta kurma ihu
wayyyo........don Allah ataimake ni wasu la'ananun Allah sun satoni wayyo Allah....ataimakeni.
"Jarumi ya mik'e daga mazauninsa ya nufi wurinta ya shiga zagayata, jikinta ya bata akwai
mutum a kusa da ita ta juya da k'arfi ta shiga ja da baya tana kuma kici-kici kwance igiyar da
suka daure mata hannaye, tuntube tayi da center table tayi baya za ta fad'a kanshi cikin sauri
Jarumi ya rik'o hannunta ya daura bakinsa dai-dai k'ofar kunnenta ya ce "welcome to my palace
sarauniyata.
"Un.....cle....sur..raj!
Tafad'a cikin rawar murya. "Yesss.....sweetheart ashe ina da matsayi a wurinki har haka bansani
ba duk da kin kasance, a cikin wannan hali kika iya sheda muryata ina godiya rabin raina
kai....oska zo maza ka kwance ma sarauniyata hannayenta, za mu fi jin dad'in gaisawa da sauri
wanda ya kira da Oska ya zo ya kwance mata hannaye. Ita ma ciki sauri ta cire blindfold d'in idanuwanta ta yada ganinta cikin parlor, tana kallon
gumaka yaran Jarumi saboda yadda suka yi tsaye k'ame sun fi kama da gumaka har ta gangaro
kan Jarumi wanda ke tsaye gefe yana zabga murmushin mugunta.
Wani mugun kallo ta watsa masa shi kuma ya washe mata hak'ora tare da nufar mazuninsa na
tun farko ya zauna ya yi crossing legs dinshi, ya d'aga pistol d'in hannunshi yana sosa gefen
fuskarsa a fusace barrister ta nufi wurinsa ta nuna shi da yatsa tare da fad'in "kai.....uncle kayi
hauka ne me yake damun kanka, ka ne shin kuwa ka san hukunci kidnapping a kund'in
shari'a?"
Uhm..uhm....Ya za'a yi nasani my beautiful daughter in law wannan sai ku manyan lawyers.
Ta girgiza kanta cike da takaici take kallonshi saboda ta fahimci yana so ya raina mata hankali,
cikin fushi ta ce "to.....uban me zan maka da kasa aka yi kidnapping d'ina zuwa nan...?"
Ta6e baki ya yi kafin ya ce ki natsu barrister muyi magana cikin mutunci da lumana.
"Harara ta zabga masa tare da fad'in babu zance natsuwa ko mutunci atsakaninmu uncle, idan
har kana so mutunci da lumana ka sa banzaye gumaka yaranka su maidani inda suka satoni, ni
kuma zan rufa maka asiri na dauke wannan al'amari a matsayin sharrin zuciya.
"Idan kuma nak'i fa my beautiful daughter in law?
Za kayi nadama mafi muni a rayuwarka, ni kwata-kwata kaina ya daure nasa gane menene
manufarka na satoni?"
To....ta ya za'a yi ki sani baya baki bani damar da zan sanar da ke ba.
ya k'arashe magana yana murmushi abinsa.
Ya cigaba da cewa Ki nemi kujera ki zauna ki bud'e kunnenki da kyau ki saurare manufofin da
suka sa na tura gumaka yarana suka yi kidnapping d'inki, saboda haka ki nemi wuri ki zauna tun
kafin ki kaini bango nasa a zaunar da ke dole.
"Rau-rau tayi da idanuwa tare da furta amma kasan hakan bai dace ba, ko?"
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:28 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
_SECOND TO THE LAST PAGE_
*39*
*NATIONAL HOSPITAL ABUJA*
Daddy kwance akan gadon asibiti anyi masa fixing d'in drip a hannunshi na dama, sai sharar
bacci yake yi Zee-zee wacce ta gama waya da Aliyu ta mik'e daga kan kujerar da ta ke zaune,
ta nufi wajen gadon Daddy ta zauna kusa da shi.
"Ahankali ta rik'o hannunshi na dama cikin tsananin tausayi take kallon fuskar mahaifin nata,
yayin da bangare zuciyarta guda take ji tsanar mahaifiyarta tana huda sasssa jikinta.
Ta lumshe idanuwanta hawaye masu zafin gaske suka zubo mata, bata damu da ta goge su ba
ta ce "Daddy sam ba kayi dace da mata tagari ba, ba ka samar mana da uwa tagari ba.
Daddy a yau ina nadamar kasancewar 'yar da Zaituna ta haifa momma ta cucemu Daddy ta
zubar mana da daraja da k'ima a idon duniya.
Ahalin yanzu ba wanda zai auremu saboda mu kasance 'ya'ya matar da ta aikata Zina da
igiyoyin aureta. "Shikenan yanzu ba mu da damar shiga Jama'a sai an goranta mana.
ta k'arashe magana had'e da rushewa da kuka mai tsananin gaske ta kifa kanta akan k'irjin
Daddy, tana cigaba da kukanta.
Teema ta Kalle Meena wacce idanuwanta suka yi luhu-luhu saboda tsabar kuka, ta ce " Ya
Meena na rok'e ki da ki daina kukan nan ni fa ya dace nayi ta rusa kuka ba ku ba, saboda ko ba
komai ku ta hanyar ha.....
Da sauri momma ta zabura daga bacci k'arya da take yi, ta dannawa Teema ashar tare da fad'in
"Teema wane sharri ne aljanunki suke shirin k'ula min?
Da ba zasu bar ni naji da wanda aka riga aka doura min ba.
"Meena ta taso da sauri ta nufi wajenta gabanta na fad'uwa ta ce "momma kina nufi abinda
ake yad'awa a kafaffen labarai akanki sharri ne ba gaskiya bane?"
"Kuka momma ta fashe da shi tana girgiza kanta kaman k'adangarwa "sharri ne da gadar
zare da magauta suka shirya min Meena, saboda an ga mahaifinku zai fito takarar kujerar
Governor.
"Meena ta share siriran hawaye da suka zubu mata da bayan hannu, ta ce "to.....amma
momma me ya ki ka je yi a hotel kuma ba kaya a jikinki sai wani d'an munafukin bathrobe ne
sanye ga jikinki...?
Gaba d'aya momma ta didice da ji wannan tambayar ta Meena, nan da nan tayi tunani k'aryar
da zata yanka mata sai kawai ta karkace bakinta ta ce "na fito daga gida da zumar zan je gidan
k'awata Hajiya Dijama, har na kusa isa gidan wata bak'ar mota tasha gaban motata wasu katti
majiya k'arfi nagani sun nufo motata kafin ki ce kwabo sun fesa min wani abu ga fuska shikenan
ban sake sani idan kaina yake ba sai falkawa nayi nagani akan gadon hotel tsinane yaronan da
ban san uwar da ta haife shi kwance kusa da ni, na yunk'ura da k'arfi na nufi k'ofa ina bud'ewa
sai kawai naci karo da Daddynku a tsaye kafin nayi wani yunk'uri kare kaina sai kawai
wad'annan la'antattu 'yan jarida suka kewaye mu.
Cike da fushi Meena ta ce "tabbas....ko waye ya shirya miki wannan abu momma sai Allah
yasaka mana ya bi mana hakki 6ata mana suna.....
Mtssss......Dogon tsaki Teema ta ja tare da fad'in kaichonki.......momma wai kam har sai
yaushe za ki daina daukawa kanki zunubai?"
Shin ke bakisan hukunci k'arya bane a addinance?"
Kiji tsoron mahalincinki momma ki tuna komai dare dadd'ewa za ki mutu kuma tilasss.....za ki
riske abinda kika shuka yana jiranki a kabarinki.
Momma ki sani duniya k'ararriya ce lahira kuma a can za mu dauwama......iya aikinka nagari
shine zai ceceka, tun tashe ni nayi wayo momma banta6a gani kin yi aiki nagari ba shin ke ba ki
tsoron azabar Allah ne?"
Teema ta k'arashe magana tana mai tsare momma da firgitattu idanuwanta.
"Momma ta rushe da kuka tare da fad'in Teema me nayi ma aljannunki ne me na tsare
musu ne da akoda yaushe suke bi na da mugun alkaba'i?"
"Har Teema ta bud'e baki zai tayi magana Meena ta dakatar da ita ta hanyar rik'o mata hannu
tashi mu tafi d'akin Daddy mu bar momma tana buk'atar hutu.
Batare da Teema ta furta uffan ba ta mik'e yayin da Meena da tana janye da hannunta, saida
suka kai bakin k'ofar fita Teema ta juyo ta kalli momma cikin sa'a idanuwan momma su na
kansu, tasaki mata mushirinki murmushi had'e da karkad'a mata babban yatsanta ta nota shi
k'asa