Showing 21001 words to 24000 words out of 85584 words

Chapter 8 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf

27 Jul 2025

1497

ya jefawa Aliyu gashinan
abinda ka kasa yi ne nayi invitation ne na dauri aure in ka ga dama ka ba wa friends da
business partners d'inka, tashi ka bani wuri. Salun-alun Aliyu ya mik'e ya fice zuciyarshi ba dad'i.




Jeeddah Aliyu[7/26, 11:54 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*

*13*

B'acin rai ya bayyana k'arara akan fuskarshi hakan yasa idanuwanshi ma'abota kyau da
kwarjini, suka canza launi daga farare zuwa ja.
picking lot yanufa da gudu direbanshi isah ya taso ya jawo mota ya bude masa k'ofa ya shiga.
Sai da suka dauki hanya kafin yace gidan Jamal za ka kaini kira shi a waya ka ji ko yana gida.
Okay....boss"
Cewar Isah direba yana ciro wayarshi daga gaban aljihu farar shirt da ke jikinshi, ya yi dialling
numbern Jamal.

Boss ya ce yana River plate park ka sami shi acan.
Omg! Uban me Jamal yake tsinta a park sai ya lura mutane na cikin damuwa yake tsira yawo
marar amfani "mtssss....ya ja tsaki cike da takaici ya umarce Isah ya kai shi can.

Suna isowa Isa ya bude masa k'ofa yafito ya kai hannu ya kar6i ledar da ke hannunshi, sai
lokaci Aliyu ya tuna da ledar.
"Please.....Isah sake kiranshi ka ji yana dai-dai ina.
kafin ya kai da kirar nashi suka hango shi, yana k'arasowa ya mik'awa Aliyu hannu suka gaisa
jerawa suka yi yayin da Isah ke bin bayansu.

Cikin wasu bukkoki da ke dauke da kujeri kamar na kaba had'e da table a tsakiyarsu, suka nufa
Jamal ne yafara jan d'aya daga cikin kujeri ya zauna, da sauri Isah yajawa Aliyu kujerar ya
zauna cike da damuwa ya dafe goshinshi waiter ne ya kawo musu menu ko da akwai abinda
suke buk'ata Jamal ne ya yi musu order. "A natse yake kallon abokin nashi kafin ya ce ya akayi ne king naga kamar da damuwa akan
fuskarka?"
Ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfin gaske ya ce ba kama bane Jamal, damuwa ce takeso yi min
yawa.
Subhnalillah......meke faruwa ne?"
Hannun ya mik'awa Isah batare da ya yi magana ba, ledar da ke hannunnshi ya mik'o mishi shi
kuma ya mikawa Jamal.
"Invited card ne na dauri aure koda na dawo daga Zurich har Daddy ya bugu su.
Ya k'arasa magana kamar zai yi kuka.
"Fito da cards din Jamal ya yi yana kallo yana murmushi saboda tsananin kyau da tsadarsu,
ya ce lalle Aliyu kai d'an hutu ne sam baka san wahala ba, gaba d'aya rayuwarka cikin gatanci
ka ke yi ta hatta aure ma baka san wahalar nemanshi ba, yi maka akayi.

"ka tsinci zankad'edd'iyar mace kyakyawa ajin farko a gidanka wallahi ka ji dad'inka.

"Yalwattace murmushi ya yi sannan ya jan tsaki mtsss.....ya ce ina gatanci ga aure da ba
soyayya a cikinshi, wasu lukuta inda na zauna ina nazari har misalta yadda zamana da Barrister
zai kasance, saboda ita kanta ba son nawa take yi ba dole ne akayi mata kamar yadda akayi
min.
Yanzu dai mu aje zance kana so ko baka so, tana so ko bataso muyi wanda ke gabanmu.
Ya raba card's d'in biyu ya mik'awa Aliyu kashe d'aya ka ba wa business partners dinka,
wannan zan ba wa friends d'inmu, sai abu na gaba ka shirya muje Yola domin muji nata
bangare me take shiryawa ka san dole ba za'a rasa events d'in da za suyi ba irin su dinner,
cocktail party. "Dallah ya isa ana zaune qalau za ka daukowa mutane bidi'a, ba da ni za'a yi wannan iskanci
ba.
yakarasa magana yana hura hanci.
Dariya Jamal ya yi ya ce ka ji da shi wai ciwon ajali a d'an yatsa aure ne dai ba fashi sai ayi.

"Sai kuyi tayi amma dai ba wanda isa ya sani zuwa party da ban yi niyya ba.
Ba wannan ba yanzu yaushe za mu tafi Yola?"
Mu bari koda zuwa ranar labara ne, duk da ranar ina da aiyyuka da yawa a gabana.
"Koma menene agogo sarki aiki jingine shi za kayi, har sai muje mun dawo, ka godewa Allah
abokina da yabaka zuk'ekk'iyar mace irin Barrister Amina wallahi kayi dace da mata.
Yarinya natstsiya mai kunya uwa-uba wayewa da gogewa na tsantsa ilimin zamani, kuma ga
dukan alamu har na addini tana da shi.
"Aliyu ya yi murmushi sannan ya ta6e baki ya ce nima ai tayi dacen miji santalele, business
tycoon irina wanda mata suke haukar so amma sai gashi ita tasamu a arha.....
"Jamal yaja tsaki....mtsss had'e da cewa kai dai anyi tsoho d'an iska wallahi, wato kana sane
da haukar da mata suke yi akanka, basarwa kawai ka ke yi.
"Ba gashi hakan ya yi wa barrister rana ba zata kwashi gara6asa.
Duka Jamal yakai mashi yana cewa ka shiga uku king ka dai anyi 6aud'add'e mutum, a lokaci
d'aya sukayi dariya har suna tafawa.

"Ka shirya kawai gobe muje sai mu dawo a ranar, ka ga ba za mu koma ba sai an sakata a
lalle alokaci ta dau k'amshi sai ka shinshshina kayanka a tsanake.

"Sosai maganar ta Jamal ta bashi dariya don haka ya shiga kyakyatawa abinshi, wanda hakan
ya janyo hankali Isah direba ya kura mishi idanu, a zuciyarshi ya ce lalle yau za'a yi ruwan sama
boss yana dariya.
"Shikenan ka shirya mu bi jirgi safe kamar yadda mu kayi a wancan lokacin.
****----*****---****
*YOLA*
*10:44am*

Barrister Amina tana zaune akan dining table ta sanya abinci agaba, tana kallo ta kasa ci gaba
d'aya tunanin Aliyu ya cakud'e mata zuciya, wani lokaci sai tayi yunkuri kirar numbernshi sai
zuciyarta ta haneta saboda aganinta kiranshi zai zama ta zubarda ajinta ne.
"muryar Barrister Z taji tana gaisawa da Ummi, hakan yasa ta saki nannauyar ajiyar zuciya ta
yi wulgi da folk d'in hannunta sannan ta mik'e tsaye dai-dai Barrister Z na isowa, amaryaaaa....
Cewar Barrister Z tana mai rungume Barr A murmushi Barr A tayi had'e da dan gajere tsaki, ke
zo muje room d'ina akwai abubuwa da yawa da za mu tattauna.

Gefen gadon d'akin sauka zauna barr Z ta ce ya dai bebs naganki wani irin ko dai har kin fara
shiga cikin fargaba aure ne?"
"Da yake muddin zakayi aure sai kayi ta faman da zullumi barin gidanku, amma karki damu
bebs na d'an lokaci ne za ki saba mu ma can takalminmu ya tsinke sai gashi yanzu mun manta
da gida sai dai mu kai ziyara.
"Barr A ta dalla mata harara tana mai jan dogon tsaki mtssss......
Barni da wannan zance bebs ni ai na jima da shiga wannan fargabar tun kafin zuwan lokaci
gaba d'aya komai ya cakud'e min, babban tashin hankalina bai wuce irin zaman aure da zanyi
ba.
"Tak'arasa magana kamar za tayi kuka.

"Dafa ta Barri Z tayi cikin tausassa harshe ta ce miye dalilinki na fad'i haka bebs?"

"Dalilina bai wuce har zuwa yanzu da ya rage sauran 'yan kwanaki k'alilan azarga min igiyoyin
aurenshi akaina, amma babu wata kyakyawar fahimtar juna atsakaninmu bana tunanin Aliyu
Ardo yana jin burbushin sona azuciyarshi, ni kuma gashi soyayyarshi ta mini mummunan kamu
shiyasa natsuwa da kwanciyar hankalina suka kaura. Damuwa tayi min katutu har cin abinci naso gagarata, ni narasa yadda zanyi da rayuwarta.

"Ba wata kulawa da nake samu daga gareshi, bai damu da ni ko kad'an ba ya yi halin ko oho
da al'amurina babban takaicina Ummi sai faman shirye-shirye take ba abinda ya dameta, na
tabbata da Abba yana da masaniyar da rashin fahimtar da ke tsakaninmu da tuni zai yi fatali da
zance aurenan, to abinda ni kaina bana fatan faruwarshi duba da yadda na tsunduma kogin soyayarshi.


_Just to manage_


Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:54 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830

*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*

*14*

murmusawa Barrister Z tayi tare da girgiza kanta sannan kuma ta, gyara zamanta ta fuskanci
Barrister A ta ce don ya nuna halin ko oho akanki, baya nufi bashida ra'ayinki,
Benbs kiyi la'akari da yanayin aikinshi ba na zama wuri d'aya bane.
ke da kanki kin sani don ya gayamiki, kuma duk da rashin kulawarshi ba'a fasa gudanarda
komai ba.
Don haka "don Allah ki kwatarda hankalinki kada ki haifarwa da kanki da wata matsala.
"Amma bebs ai yana da number wayana miyasa bai kirani ba?"

Kema ai kina da numbernshi miyasa ba kira shi ba?"

Saida ta galla mata harara kafin tace haka kawai zan kira shi salon ya daukeni marar aji.
Oh! Haka ne ashe ba shi kadai bane mai laifi, kema kina da naki saboda haka ki jingine wannan
k'orafin naki bai samu kar6uwa ba.
Muyi magana da ke gabanmu.
Dole barrister A ta share zance duk da yana nuk'urk'usar zuciyata ta dauki invited cards suka
fice wurin rabawa 'yan uwa da abokan arziki.
A washe gari mai gyara jiki ta musanmman da Ummi ta kira daga Sudan ta iso, tun daga ranar
ta shiga gyara Barrister A.
***---***---***---****

*ABUJA*
*10:37am*

Aliyu yafito cikin shirin shi na farar shadda daga flat d'inshi yanufo na iyayyenshi, a sitting room
ya tararda Daddy da momma zaune.
Tun kafin ya k'arasa yake jin tashin muryoyinsu, tsinta kanshi ya yi da jin 6acin rai saboda
yasan duk saboda zance aurenshi ne yake saka su hayaniya.
Jikinshi asanyayye
ya nemi kujera can gefe ya zauna ya talla6e ha66arshi yana kallonsu, batare da ya tanka musu
ba.
Daddy ne ya yi k'arfin halin cewa Sultan ina zuwa da sanyi safiyanan?"
uhmm....saida ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce Yola...
Daddy ya fad'adda murmushinshi ya ce da kyau my fav boy, shigowar nan taka maganarka ce
muke yi ni da mahaifiyarka, bisa wani tunani da nayi na yanke hukunci a gidanka da ke Yola za
ka fara zama kai da matarka, na wani d'an lokaci kafin ta tare anan Abuja duk wani abu da
gidan yake buk'ata an zuba maka. Idan akwai abinda bai maka ba in ka je sai kayi min magana kaji ko?"
Dafe goshi Aliyu ya yi ya shiga nazarin maganar Daddy tsawon some minutes kafin yad'ago
wearing a killer smile on his face "ya ce thank you Daddy Allah yak'ara lafiya da nisan kwana ni
zan wuce.
Yak'arasa magana had'e da mik'ewa Allah shi yi maka albarka Gadangan Daddy Allah ya tsare
min kai, yakare ka daga sharri mutum da na aljan, yadda ka ke min biyayya kaima Allah yabaka
masu yi maka.
Cak...Aliyu ya tsaya saboda sosai addu'ar Daddy ta ratsa k'ashi da 6argon jikinshi, saida ya
juyo sannan ya amsa da Amin summa Amin Daddy.
Momma ta tur6une fuska ta ce zo nan Sultan nima a matsyina na wacce ta haifeka ina da
magana.
Har Aliyu ya juyo Daddy ya ce je ka abinka Gadanga za ta 6ata maka lokaci ne a banza, shiru
Aliyu ya yi shi bai tafi ba kuma shi bai dawo ya zauna ba.
Sosai ran momma ya 6aci tasaki tsaki ta kuma shan alwashin sai ta raba Barrister A da
numfashinta, gashi tun kafin ta shigo ta fara raba mata kan iyali.
Ta cije le66enta na k'asa ta yi kyaci ta mik'e fuuuu...tafice daga sitting room.
Daddy ya dubeshi yana murmushi cikin sigar kwantarda hankali ya ce yi tafiyarka Allah ya
kiyayye hanya barni da ita zan rarrashe ta.
Cike da gansuwa Aliyu ya gyad'a kai ya fice.
***--****----*****
Daga Airport Aliyu ya wuce gidanshi shi kanshi gidan ya burge shi sosai, bai kuma ci karo da
wani abinda bai mishi ba saida suka huta shi da Jamal kafin su nufo gidansu Barrister A lokaci
da sak'o ya riske Barrister A Aliyu ya iso ana mata gyara jiki tsakanin jiya da yau fatar jikinta
tak'ara glowing, sai fitarda k'amshi mai jan hankali take.
Scrub d'in da ke jikinta ta nufi bathroom a gurguje ta wanke tafito daure da towel, ta dube
k'awarta Fadila wacce cousin d'inta ce 'yar wurin Aunty Khadija ce.

Tq ce Fadila please ki je wurinsu kafin na shirya, saida Fadila ta tsokaneta kafin ta fice tanufi
falon bak'i.

Cikin abinda bai wuce 10-12 minutes ba Barrister A ta shirya ciki atamfar exclusive d'inki riga da
skirt ya zauna dass....a jikinta d'an siriri veil kalar atamfarta ta yane kanta da shi, ita kanta lokaci
da tayi arba da dressing mirror saida tasaki k'ayatattace murmushi, sakamakon kyau da tayi ta
fice daga d'akin cikin yanayin tafiyarta mai matukar daukar hankali. "Tun kafin ta k'arasa shiga falon iska ya kai musu fitinanne k'amshinta, ta tura k'ofa bakinta
dauke da sallama ta shigo.
Jamal da Fadila suka amsa mata sa6ani gogan naku da lips dinshi ne kawai suka motsa, saida
ta zauna kafin ta gaida su a lokaci d'aya dukansu suka kalle ta, sosai kyawota ya rud'asu da
sauri Aliyu ya dauke fuska.
Jamal ya yi murmushi yana mai cigaba da kallonta ya ce amarya da fatan za'a yi mana afuwa,
kasancewar kin ganmu kwatsan ba sanarwa, muyi ta neman layinki baya shiga kinsan dai
yadda lamari network yake.
Sadda kanta k'asa tayi tana wasa da yatsun hannunta, tasan duk abinda Jamal ya fad'a ba
gaskiya bane yana dai neman ya kare abokinshi ne.
"Da kyar ta d'ago tayi murumushi, batare da tace komai ba Jamal ya dubi Fadila ya ce
malama Fadila zubamin lemo muje daga waje, naji shirye-shiryenku kafin ango da amaryar nan
su gama zantawa dariya Fadila tayi tana mai cewa lalle kam gara mu basu wurin naga sai
fik'i-fik'i da idanuwa suke yi. "Murmushi Aliyu ya yi cikin husky voice d'inshi ya d'ago yana lumshe lulu eyes dinshi, ya ce
Fadila daina biyewa Jamal kinsan nace ke ce ta hannun dama na.

Dariya Fadila da Jamal suka yi yayin da Fadila ta tsiyayawa Jamal juice a handle cup, sannan
ta kalli Aliyu ta ce na daina ranka ya dade Jamal ne yakeso ya had'amu, ba kuma zai yi nasara
ba.
"Karka dai manta da alk'awalinmu.

Tafad'a had'e da nufar k'ofar fita Jamal ya biyo bayanta yana cewa ai bai isa ya manta da
wannan alk'awalin ba.
Bayan fitar Jamal da fadila suka yi shiru na some minutes shine ya fara d'agowa cike da isa da
tak'ama ya kalle ta ya ce Barrister ya gida ya kuma shirye-shirye biki?"
Ita ma ta d'ago da murmushi akan fuskarta wacce sai glowing take, ta ce Alhmdulilah!
Yalla6ai ina neman alfarma wurinka da, ka kirani da ainihim sunana Amina ko ka ce Minal.
"D'an gajere murmushi ya yi kafin ya ce nima sunana Aliyu ko ki ce Sultan ba yalla6ai ba, don
haka sai kindaina kirana da Yalla6ai zan daina kiranki da barrister.
Turo d'an k'aramin bakinta tayi mai kama da gidan tsuntsu, tana gunguni k'asa-k'asa.
"mekika ce ne?"
Ni ba da kai nake ba.
Tafad'a cikin sigar shagwa6a.
Ta6e baki ya yi ya dauke fuskarshi da barin kallonta.
Shiru suka sake yi na tsawon lokaci daga bisani Aliyu ya ce taimaka kiyi min text din account

numbernki.
Tayi rau da idanu ta ce me za kayi da shi?"
Cikin daure fuska ya ce ina ruwanki da abinda zan yi ke dai ki turomin kawai, batare da ta furta
uffan ba tayi mishi sending.
yana jin shigowar text a wayarshi ya duba ya ga ita ce, sannan ya d'ago ya sake cewa
dame-dame za ku yi na shagalin biki?"

Ta d'an kad'an idanunta ta ce za muyi Fulani night sai mother night sai kuma dinner da abokan
aikina suka had'a mana.




Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:55 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*

*15*

Ya d'an yi rolling lulu eyes d'inshi ya ce kai duk ku kadai, lalle barrister kina so bidi'a.
Ta d'ago ta zuba mishi idanu tsananin kyau da kwarjininshi suka cika mata idanu.
Ta kasa dauke idanuwanta daga kanshi, gani yadda tai mishi kurrr.....da idanu yasa ya dafe
goshi "Omg barrister daina yi min kallon tuhuma ai gaskiya na fad'a ya k'arasa magana yana
d'age girarshi.
Sosai hakan ya k'ara mishi kyau.
lumshe idanu tayi eyelashes d'inta suka kwanta kamar ta k'ara da na katti, daga bisani ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login