Showing 12001 words to 15000 words out of 85584 words
Chapter 5 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf
Suraj shi yake handled din
business d'insu na Yola.
Gidan uncle suka fara yadda zango bayan sun huta suka ci abinci had'e da sallar azhr, sannan
uncle ya had'a su da direbanshi yakai su gidan Alhaji Abdullah Barkido Misali k'arfe 2:52pm
direban da ya dauko Aliyu da Jamal ya Parker mota cikin gidan Abdullah Barkido, Khalid ne
yafito ya tarbe su had'e da yi musu jagaro zuwa falon bak'i. "Jamal ne yafara zaunawa yayin da Khalid ya fice.
Ahankali Aliyu yake nazarin falon kafin ya zauna yana shak'ar Air freshener & odour neutralizer
din da aka sanyawa, falon sosai ya yi masa dad'i sanyayyar ajiyar zuciya ya yi, sannan ya d'an
sosa gefen kuncinshi da yatsanshi, zuciyarshi ta afka tunanin saboda bai san yadda zai ga
yarinyar ba, ko yaya kamanunta suke bashi da mafita dole ya aureta domin ya farantawa Daddy
rai. 'Tunaninshi ya katse sakamakon sallamar da ta bugi dodon kunnenshi, alokaci d'aya shi da
Jamal suka dubi k'ofa Asabe mai aiki ce tare da Rahma suka shigo dauke da kayan abinci,
had'e da drinks Jamal ne ya amsa musu sallama, sai da suka ajiye kayan sannan suka gaida su
nan ma Jamal ne amsa saboda Aliyu bakinshi ne kadai ya motsa ko Jamal da ke zaune kusa da
shi ba lalle bane ya ji abinda ya ce ba.
"Bayan Asabe ta bar falon Rahma ta ja tai tsaye tana kallonsu, Jamal ya ce Baby ya
sunanki?"
kusa da shi ta nufa da yake Rahma akwai d'an banza surutu kamar parrot ta ce sunana Rahma
Abdallah Barkido, kaine za ka aure Ya Minal ko wannan da baya magana?"
Takarasa magana had'e da nuna Aliyu da baki.
"Aliyu ya d'ago fuskarshi dauke da lallausan murmushi, da yake sosai maganar Rahma ta
bashi dariya shiyasa ya murmusa, Jamal ya yi 'yar dariya ya ce bani bane wannan ne ya nuna
Aliyu da yatsa.
"hannunta Aliyu ya rik'o yana murmushi ya ce Rahma yakike ya karatu?"
Lafiya qalau....kaine za ka dauke mana Ya Minal?"
"Gyad'a mata kanshi ya yi yana cool smile ko ba za ki barni na dauke ta ba?"
Turo baki ta yi kafin ta ce zan bar ka saboda kana da kyau amma duk da haka saidai katafi da
mu duka gidanka.
Jamal ya kyalkyale da dariya yayin da Aliyu yak'ara fad'ad'a murmushinsa har kana iya jiyo
sautinsa ya ce na amince Baby Rahma, ya zura hannu cikin pocket dinshi ya fito da bundle na
'yan five hundred ya mik'a mata gashi Baby Rahma tasha ice cream.
"Girgiza kai ta yi ba zan kar6a ba Ya minal za ta dokeni, haka ranar abokin aikinta ya zo ya
bani kudi na kar6a bayan ya tafi ta zane ni.
"Kwatarda murya Aliyu ya yi ya ce kar6i kawai ba zan barta ta dokeki ba, kinmanta ni ne zan
aureta?"
Washe hak'ora Rahma ta yi tasaka hannu biyu ta kar6i kudi ta yi mishi godiya ta fice da gudu
tana murna.
"Bayan fitar Rahma Jamal ya dubi Aliyu ya ce duk da ak'oshe mu ke amma yakamata mu ci
koda snacks ne da drinks gudu kada su ji babu dad'i.
Uhmm.....Aliyu ya fad'a had'e da daukar samosa guda d'aya ya kuma tsiyaya Juice a handle
glass cup, yana kur6a juice d'in a hankali.
Sautin tafiyar takalminta ne yafara isa musu da sak'on zuwanta, kafin ta tura k'ofar falon ta
shigo k'amshinta ya mamaye k'ofufin hancinsu, cikin sanyayeyar muryarta mai matukar dad'i da
gard'i ta yi sallama.
[7/26, 11:47 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU...DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I
NE IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
08103943903
*SAI KA TURA SHAIDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KI IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYAN KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMIND'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA```
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELE*:-```RAYUWATA```
*SLIMZY*:-```IZZA TA```
*SAFIYA GALADANCHI*:-```TANA K'ASA TANA DABO```
*GIDAN RINA*
*8*
Cikin fara'a Jamal ya amsa mata sallama, sai da ta zauna sannan ta gaida su Jamal ne yasake
amsawa yayin da Aliyu yake k'are mata kallo ta k'asan ido.
Jamal ya gyara zamanshi ya ce sunana Jamaludeen Muhammad, tare muka taso da Aliyu tun
muna yara ko zan iya sanin sunan amaryar ta mu?
Sai da ta yi lallausan murmushi cikin sweetness voice d'inta ta ce sunana Barrister Amina
Abdallah.
Wow! masha Allah ashe amaryar ta mu lawyer ce?"
Uhmm.....tafad'a had'e da sadda kai k'asa.
Da fatar mun samu kar6uwa a wurin Barrister?"
Cewar Jamal yana mai kallonta.
Da kyar ta d'ago saboda kunya kunsan mu fulani da kunya duk wayewar mu da gogewar mu, za
ka sami wasu daga cikinmu da kunya....lol.
Ba k'aramin namijin k'ok'ari ta yi ba ta hanyar furta, insha Allahu daga gareni ba bu wata
matsala fatana anan Allah ya had'a kawunan mu.
Amin summa Amin Barrister.
Jamal ya fad'a cike da jin dad'i maganarta ya mik'e ya kalli gefen da Aliyu yake zaune ya ce
king bari na ba ku wuri ku fahimce juna.
Kafin Aliyu ya yi magana har Jamal ya fice, shiru suka yi na tsawon lokaci yayin da kowane su
da abinda yake sak'awa a zuciyarshi.
"Aliyu ya gyara zamanshi ya tattaro hankalinshi gareta sam bai dauka haka zai ganta ba, ya
yaba da irin shigar da tayi sai yaji ta burge shi, karo na farko a tarihin rayuwarshi da shigar wata
'ya mace ta burge shi ba ko shakka dole ya rubuta wannan a diary shi.
"Cikin husky voice d'inshi yayin da fuskarshi ke dauke da murmushi, ya ce Barrister Amina ya
gida?"
Ta cire kai da kyar ta kalle shi wani irin shock ta ji ya jata, a hankali ta bude baki ta ce "Lafiya
qalau, ya hanya da su mommy?"
'Alhamdullah!
Yafad'a yana kallonta suna had'a ido ta yi sauri sadda kai k'asa.
Daddy ya gayamin ke lawyer ce mai zaman kanta, kenan idan mu kayi aure anan za ki zauna
ko za ki bi ni Abuja?"
"Sai da ta yi murmushi kafin ta ce duk Inda ka za6a mana.
Ya fad'ad'a murmushinsa har lokaci idanuwanshi na kanta ya ce, gaskiya na fi zama a Abuja da
Lagos idan ki amince sai mu zauna a Abuja ko ya ki ka gani?"
"Ba laifi hakan ya yi.
Tafad'a Cikin sanyi murya.
Shikenan Allah ya nuna mana lokaci.
"Da kyar ta iya furta Amin.
Daga haka suka yi shiru.
Aliyu ya sauke ajiyar zuciya ya kalleta dai-dai ita ma ta d'ago ta sace kallon nashi, karaf....suka
had'a ido da sauri ya dauke kanshi, jimm....ta yi tana kallon gefen fuskarshi yana juyowa ta
kauda kanta.
Ya duba agogon da ke daure a tsintsiyar hannunshi sai ya mik'e tsaye yana cewa mu je ki
rakani mu gaisa da Mama.
Ta mik'e tsaye ta wuce gaba yana bin ta, a farfajiyar gidan suka hango Jamal tsaye yana waya,
alama Aliyu ya yi mishi da hannunshi.
"Hakan yasa Jamal ya katse wayar ya kuma nufo su, har Falon Ummi ta shigar da su ta ce ku
zauna bara na kirata bayan ta kira Ummi suka gaisa sannan suka yi mata sallama har
compound ta raka su idan direban uncle ke zaman jiransu.
"Tsaye suka yi suna facing junansu, kafin ya yi magana wayarshi ta yi ringing ya fito da waya
gani momma ce mai kiran nashi yasa ya kalli Amina ya ce please 2 minutes.
Uhmm.....Tafad'a tana mai wasa da zoben hannunta.
Nesa da ita ya yi ya amsa wayar, yana receiving ya kara wayar a kunnenshi hello....momma!
Ya hanya yaron momma?"
"Alhamdulillah....momma mun iso lafiya har muna shiri wucewa sai ga kiranki.
"Uhmm!
Da fatar yarinyar ta yi maka?"
Murmushi ya yi mai sautin gaske had'e da shafar sumar kanshi, ya ce momma za mu yi
magana idan na dawo gida lokaci yana k'urewa kada mu yi missing flight d'inmu.
"Daga haka ya katse kira saboda yasan halinta sarai sai tasake, watsu masa wata tambaya.
Daga chan gefe kuma Barrister Amina ta k'ura masa ido tana nazarinsa daga sama har k'asa,
tabbas ya amsa sunanshi cikkake namiji domin ya mallaki komai na cikar halitta, ta d'an namiji
wanda kowace lafiyayyar mace za ta yi burin mallakarshi a matsayin life partner.
"Ganin ya juyo gareta yasa ta yi gaggawar kauda kanta, ya k'araso daf da ita shi ma kallonta
ya yi sosai sannan ya yi gyaran murya tare da kiran sunanta Aminaaa......!
Yadda ya ja sunanta yasa tsigar jikinta tashi yarrrr.....
Ta d'ago ta kalleshi ya ce mu za mu wuce saboda yau za mu koma Abuja, gashi ban yo miki
tsarabar komai ba, sai wani lokaci idan Allah yasake had'a mu.
"Murmushi ta yi wanda yak'ara mata kyau ta ce ba komai, nagode da ziyara Allah yakai ku
lafiya, ka gaidamin da su mommy.
"Amin...
Ya furta chan k'asan mak'oshi.
Ta juya wajen Jamal ta ce malam Jamal nagode Allah ya kiyayye hanya ka gaida iyali.
"Mu ke da godiya barrister.
Cewar Jamal.
Daga haka ta juya ta nufi cikin gida.
Yayin da Aliyu da Jamal suka shiga mota direba ya ja aka bude musu gate direct Airports ya kai
su, ko gidan Uncle Suraj ba su koma ba.
****---****----****
*ABUJA*
Momma zaune akan sofa abin duniya ya taro ya yi mata yawa, tun jiya da Aliyu ya dawo daga
Yola har zuwa yau bai bari ta had'u da shi ba.
Yau tun da sassafe ya fice kuma har yanzu yamma lis bai dawo gida ba, ta kira phone d'inshi
yafi a kirga saidai ta ji P.A shi ya dauka ya ce yana meeting.
"Mtss...ta ja tsaki daga bisani ta dauki wayarta ta yi dialling, d'aya daga cikin contacts d'inta
sunanshi ya bayyana akan wayarta, kamar haka Jarumi!"
Wayar ta shiga ringing kamar ba za'a dauka ba saboda saida ta yi kusan tsikewa, ya yi picking
Hello....
Yafad'a ahankali.
"Cikin rawar murya momma ta ce Jarumi akwai gaggarumar matsala da ke shirin tunk'aro mu,
idan har mu ka yi sake ta afku shikenan mafalkinmu ya zo karshe.
"Har ta dasa aya a zance ta Jarumi yana saurareta, huce ya yi ya fesar da iska mai zafi daga
bakinshi, cike da tafarfasar zuciya ya ce duk abinda yake faruwa nasani kema kuma kin san
nasani, yanzu haka ina cikin garin Abuja domin mu nemowa kanmu mafita.
"Ki zo Ina westerns dreams hotel room 402, saboda wannan magana ba ta waya bace
gudun kada wani ya jiyo ki lokaci da mu ke magana.
Yana gama magana ya katsi kiran.
A gurguje momma ta nufi bedroom d'inta ta shirya key motarta ta dauka had'e da handbag, ta
nufi k'ofar fita kicibuss....ta yi da Tima zaune a k'ofar fita daga main parlour ta wargaje gashi
kanta, ya rufe mata fuska.
"Gaban momma ya fad'i....rass!
Cikin sark'ewar halshe momma ta ce Ti....Ti...ma me ki ke yi anan?"
Tashi maza ki koma bedroom d'inki.
"Wata mushirika dariya Tima ta yi mai amon gaske ta ce ba Tima ba ce, rijiya ce mai dauke
da kunamu da macizai sun lullu6e wata 'yar jakka mai dauke da kundin sirri.
"kafin kyaftawa ido har Tima ta mik'e kamar walk'iya, ta kai k'ofar d'akinta.
Da mugun tsoro momma ta bi ta da kallo, da kyar ta hadiye yawu sakamakon yadda
mak'oshinta ya bushe.
"Har Tima ta kama handle d'in k'ofa ta juyo tasake
Kyalkyalewa da dariya ta ce je ki momma je ki maza kada jirgi ya tashi ya barki ba lalle bane ya
dawo daukarki.
"Kafin momma ta yi yunk'uri furta wani abu har Tima ta shige d'akinta.
Mtsss.....!
Momma ta ja tsaki ta girgiza kai tai ficewarta hankali kwance.
Abinda zai ba ka mamaki momma na isa Hotel d'in ta ciro bak'ar jallabiya daga k'asan seat din
motarta ta sanya had'e da yane kusan rabin fuskarta, da mayafin rigar, ta ciro wani k'ato black
shade ta lullu6e kwayar idonta duk sani da kayi mata ba za ka gane ta ba nan take ba.
"Kaitsaye ta wuce receptionist ta yi magana da ba za ta wuce ta 60 seconds da wanda yake
kula da dakunan hotel din.
Sannan ta nufi upstairs ba ta yi wata doguwar tafiya ba ta iso wani dogon corridor, rooms ne
birjik.....suna facing juna ahankali take duba d'an k'aramin allo da ke dauke da rooms numbers,
har ta yi nasarar gani room 402 hankali kwance ta yi knocking, wani mutum mai matsakanci
tsawo fuskarshi lullu6e da face masks kwayar idanuwanshi kawai ka ke iya hangowa ya bude
mata k'ofa ta shiga d'akin.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:50 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*9*
Rigar jikinta ta fara cirewa ta jefa bisa gado, ta nemi gefen gadon ta zauna yayin da Jarumi ke
safawa da marwa daga farkon bangon gabas zuwa bangon yamma, ya nad'e hannaye a
bayanshi.
"Zai kyau ka nemi wuri ka zauna mu yi magana da ke gabanmu.
Cewar Momma tana nuna masa kusa da ita da d'an yatsanta.
Cikin kaukkausar muryarsa mai cike da ban tsoro ya ce ba zan zauna ba Zaituna har sai kin
fad'a min ta ya ki ka yi sakaci har asiri da ke jikin Muhammad ya karye, har yake da gwari
gwiwar nemowa Aliyu aure?"
"Karka yi min wannan tambayar banza Jarumi saboda banida amsarta, kawai ka nemo mafita
ba wai ka tsaya kana dawo da hannun agogo baya ba.
Kukan kura ya yi ya chafke mak'oshinta, ya shek'eta kamar zai rabata da ranta tsananin
azaba yasa momma kwantawa ya bi ta ya haye ruwan cikinta, sai da ya ga ta kusa daina motsi
sannan yasake ta ya sauka daga kanta.
Yayin da tari ya turnuk'e ta, da kyar ta iya tashi zaune robar ruwan Faro ya dauko a fridge ya
jefa mata.
Jikinta na rawa ta balle murfi ta kafa baki tasha rabin ruwan duk ya zube mata a jiki.
Cikin angry Voice ya ce ki shiga taitayinki da ni kinsani sarai banida mutunci, bana d'aya daga
cikin mutane da ke jure rainin hankalin tsohuwar kilaki irinki, don haka ki natsu ki saurari irin
hasara da ki ka janyo mana.
Ajiyar zuciya mai k'arfin gaske momma tayi, had'e da shafar wuyanta da ke ji tamkar an daure
mata shi da igiya, yayin da idanuwanta sun kad'a sun yi jajir.
Afusace Jarumi ya cigaba da cewa duk wurin malamin da na je magana d'aya ce, tabbas sai
Aliyu ya yi aure don haka ba mu da za6i illa mu kashe yarinyar bayan aure.
Sai abu na gaba muddin kina so hakkar mu ta cima ruwa, dole sai kin hana Aliyu kusantar
yarinyanan malam ya gayamin muddin suka yi tarayya, komai na mu ya rushe duk wani wahala
na tsawon shekaru 28 ya rushe.
Hannunshi yasaka a pocket d'in rigar shaddar da ke jikinshi, ya ciro wasu bak'ak'en layu ko
kallonsu ka yi sai gabanka ya fad'i ya mik'awa Momma, ki binne su dai-dai wurin da ki ka san
Aliyu zai taka.
Hannunta na rawa ta kar6a ta shiga jujjuya su.
Sake dauko wata batta ya yi wacce aka lullu6e da fatar damisa, wannan kuma ki turare shi idan
ki ka san Aliyu zai shak'i k'amshinsa karki sake wani ya ji k'amshinsa fa ce Aliyu, kinji ko?"
Gyad'a kai ta yi kafin ta gyara zama muryarta bata fita wtsosai saboda shak'ar da ya yi mata, ta
ce ba ka yi min gamsasshe bayani magani na menene?"
"Shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba daga bisani ya zauna kusa da ita, ya dafa kafad'arta
ya yi kasa da murya tamkar mai rad'a ya ce amfanin wannan magani shine mazakuta Aliyu zai
mutum mutusss, koda tsirara ya ga mace ba zai ji sha'awarta ba.
Karki manta sihiri da ke jikinsa na tsanar aure ne da tsanar mata ba na sha'awarsu ba, ki sani
kasancewar Aliyu da wannan yarinya a waje d'aya dole wata rana zai ji sha'awarta, idan har ya
had'a shinfid'a da ita daga ni har ke kashinmu ya bushe don haka ki kiyayye.
"Shikenan idan wannan ne Jarumi bakada matsala.
Da kyau 'yar gari sai ki tashi ki tafi, na gama magana Sai dai idan wani emergency ya taso zai
nemi ki.
Mik'ewa tayi tasaka rigarta da black shade d'inta, ta kuma zuba guzirin shed'an d'in da yabata a
handbag.
***---****----****
Da misali k'arfe 5 na yammaci Aliyu yana zaune a office d'inshi, ya duk'ufa akan system dinshi
aiki yake sosai.
Aka yi knocking k'ofa yes!
Yafad'a batare da ya kalli me shigowa ba,
Sakatariyarshi ce Ester.
Cikin girmamawa ta ce Sir Jamal ne ya zo kasan da zuwanshi a shigo da shi.
"Sai a lokaci ya d'ago darara idanuwanshi, masu masifar tafiya da imani 'ya mace ya ce ki
shigo da shi mana.
Okay sir!
Tafad'a had'e da juyawa.
Bata jima da fita ba Jamal ya shigo hannu ya mik'awa Aliyu suka yi musabaha kafin ya ja kujera
ya zauna, ya ake ciki abokina tun jiya yakamata mu