Showing 6001 words to 9000 words out of 85584 words

Chapter 3 - Gidan Rina latest New Book Complete by Hauwa Shehu Aliyu.pdf

27 Jul 2025

1514

da kai isa aure zai nemo
maka partner kuma, kuma cikin amincewa Allah sai ka ga sun zauna lafiya.
"Barrister Amina Abdallah Barkido tana d'aya daga cikin jikokinsh 'ya ce ga d'ansa Abdallah
Barkido.
Abdallah Barkido mutum ne mai tsautsura ra'ayi mafad'aci gaske mutum ne mai zafin rai,
matarshi ta aure d'aya Hindu shi da Hindu anyi musu aure had'i batare da su na son juna ba.
"Abdallah baya son Hindu ko kad'an duk da kasancewarta kyakyawa aji farko, kuma 'yar
uwarshi ta jini hakan bai sa ya so ta ba.
"Hindu mace ce mai hak'uri gaske duk wulak'anci da Abdallah yake mata shanyewa take, bata
kai k'ararsa ba Allah yabata cikinta na fari ta haifi Amina wacce suna mahaifiyar Abdallah ta ci
shiyasa suke kiranta da Minal.
"Zuwan Minal duniya ya chanza Abdallah har yafara nunawa Hindu k'auna.
Abdallah yana matuk'ar son Minal bai had'ata da komai ba, lokaci da tana yarinya idan tana
rashin lafiya har kuka yake yi.
Muddin kanaso ka ga 6acin ransa kata6a Minal.
"Shekarar Minal biyu a duniya Hindu tasake haihuwa 'yan biyu duka maza, Khalil da Khalid
sai Ahmad sai kuma auta Rahma wacce bata wuce 9yrs ba.
"Minal lawyer ce mai zaman kanta sau biyu Barkido yana za6a mata miji tana rejected, tare da
goyon bayan mahaifinta Abdallah wanda yasha al'washi ba zai ta6a bari ayiwa 'yarshi auren
dole ba.
"Wata rana Alhaji Muhammad Ardo yakawo ziyara a yola, ya je gaida Barkido kasancewar
Barkido abokin margayi Aliyu Ardo ne.
Anan yake tambayarshi Aliyu yaranshi nawa, sai ya ce har yanzu bai yi aure ba, sosai Barkido
yarufe Muhammad da fad'a daga k'arshe ya ce ya turoshi ya zo ya ga Amina su dai-daita.
*wannan kenan*
[7/26, 11:38 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBEN WANNAN NUMBER*
0813943903

*GIDAN RINA*

*Haske writers association*


Na Jeeddah Aliyu



*4*



*CIGABAN LABARI*


Barrister Amina tana tafiya tana tunanin maganganun da Barrister Zarah, ta gaya mata wanda
suka zama sanadin rage mata damuwa.
"Agajiye ta iso gida a parlour ta tararda mahaifiyarta Hindu wacce suke kira da Ummi suna
zaune da Rahma, da ke kallon cartoons.

Da sallama dauke da bakinta tashigo.

Sannu da zuwa Ya Minal.
Rahma tafad'a tana mai mik'ewa tsaye ta kar6i handbag din Minal
Yauwa Rahma kallo ake yi?"
Eh! Cewar Rahma tana mai nufar dak'in Minal takai mata bag d'in.
"Washhh! Barrister A tafad'a had'e da zama akan hannun kujerar da Ummi ta ke zaune.
"Sannu da gida ummi?"

''Yauwa Minal sannu da zuwa ya aiki da fatar anyi nasara?"

Alhamdulillah!
cikin yarda ubangiji mu yi winning case d'in.
masha Allah!
Ummi tafad'a cike da farin ciki nasara 'yarta ta.
Mik'ewa ta yi had'e da furta Ummi bara na watsa ruwa ko na d'an ji k'arfin jikina.
Toh! Afito lafiya
ummi tafad'a da murmushi akan fuskarta.
Da isar ta d'akinta ta cire kayan jikinta ta daura towel, ta fad'a bathroom ta sakewa kanta
shower bata dauki dogon lokaci ba tafito, ta zauna gaban mirror ta shiga shafe lallausar fatar
jikinta da lotion mai k'amshi gaske.
"Ta gyara fuskarta ta hanyar simple makeup, ta bud'e closet tafito da gown na atamfar Holland
tasaka had'e da fesa Arabia perfume ta jikinta dauki k'amshi.
"Rahma ta turo k'ofa dauke da sallama.

Ya akayi ne auta?"
Ummi ta ce in gaya miki in kin kammalla abinda ki ke tana son ganinki.
"Ta kalli k'anwarta ta anatse ta ce ki ce da ita gani nan zuwa.
Toh!
Rahma tafad'a tana ficewa daga d'akin.
Barrister A ta cigaba da daura d'an kwalinta tana kammalawa tafice rik'e da wayoyinta.
Tana isa parlour ta tararda ummi tana waya, ta samu wuri ta zauna, tana karantar yanayinta
koda wata damuwa sai taga sa6anin haka, sai ma fara'a takeyi.
"Ummi ta k'are wayar ta juyo ta kalli Barrister A fara'a tak'ara yalwanta akan fuskarta, ta ce
dama zan yi miki magana akan mutane da za su zo neman aurenki.
"Ummi ta yi shiru na wasu 'yan dak'ik'u kafin ta ce shine naga yadace mu yi magana.
Toh.....ummi ina saurarenki.
Cewar Barrister A tana mai gyara zamanta.
Yayin da Ummi ta cigaba da cewa Minal lokaci yana tafiya a kullum k'ara girma ki ke, shekaru ki
suna tafiya ak'allan yanzu kina da shekara 25 a duniya zuwa wannan lokaci ya kamata ace kina
d'akin mijinki.
"Amma a dalilin taurin kanki da na mahaifiki gashi har yanzu kina gida, Minal ki yi wa kanki
fad'a kada ki biyewa mahaifinki da ke cewa ba zai miki auren dole ba.
"Daga ni har shi aure zumunta akanyi mana gashinan muna zaune har aka haifeku.
Don haka ina gargad'inki a wannan karon ki amince da za6in da Barkido ya yi miki na tabbata
ba zai miki za6en tumu dare ba.
"Sassanyar ajiyar zuciya Barrister A ta yi jikinta ya yi sanyi magangganun Ummi suka ratsa ta
tabbas zance Ummi gaskiya ne shekarunta sun tafi, ita kanta tana yi so aure saidai sam
batason aurenan na Zumunta saidai a wannan karon tana jin za ta amince da za6in Barkido,
kasancewar za6i nasa ba daga family su bane. ''Minal kin yi shiru ba ki ce komai ba.
Ummi ta katse mata zance zuci.
murmushi ta yi ta rik'o hannun Ummi cikin nata ta ce Ummi please ki daina sanya damuwa
akaina shi aure lokaci ne da shi, auren zumunci ne banaso Ummi amma tun da wannan ba
daga Barkido family ya ke ba na amince zan aure shi.
"Alhamdullih!
Ummi tafad'a very excited ta rungumo Barrister A zuwa jikinta daga bisani ta ce in Abbanki ya
dawo ya tambaye ki, kin amince da Za6in Barkido ki fad'a masa kin amince za ki aure shi kinji
My dear?''
Dariya Barrister A ta yi had'e da cewa kai Ummi.
Shafa fuskarta Ummi ta yi tana tayata dariyar, ta ce kinsan halin botsarare mahaifinki sai da
haka akanki da kowa zai iya 6atawa banaso a dalilinki yasamu sa6ani da mahaifinshi,
musanmman da yanzu Barkido ya tsofa abu kad'an zai iya mayar da shi babba.
"Karki damu Ummi wallahi na amince da ko ma waye d'ari bisa d'ari.
Allah....ya yi miki albarka yasa biyayyar da ki ke mana ta zame miki alkhairi.
"Amin!
Ummi.
Daga haka su ka cigaba da fira duk dai akan zance auren nata ne.

***----***----*****
Alhaji Muhammad Ardo ya na isowa garin Yola direct Ardo Family house ya wuce, anan ya
had'u da 'yan uwanshi suka dunguma zuwa gidan Barkido nemawa d'ansu Aliyu auren Barrister
Amina wanda nan take Barkido ya tsayar da lokaci nan da watani biyu masu zuwa.
"Sosai Alhaji Muhammad Ardo ya ji dad'i yadda Barkido ya karrama Su da kuma lokaci da ya
sanya na bikin.
Duk zance da ake alokaci Alhaji Abdallah kallonsu kawai yake, saboda ya sha al'awashi muddin
Barrister A ta ce bataso Aliyu yasan hanyoyin da dama da zai da bi ya hana auren.

*8:37pm*

Alhaji Abdallah yana zaune a parlounshi, ya aika Ummi ta kira shi mishi Barrister A.
Da sallama ta shigo dauke da bakinta.
"Alhaji Abdallah ya amsa mata yana murmushi.
Barka da hutawa Abba.
"Yauwa Minal.
Ta nemi bisa carpet kusa da k'afafunshi ta zauna
Cikin sanyi murya Alhaji Abdallah ya fara magana, Minal na kira ki ne domin na ba ki damar da
za mu tattauna akan zance aurenki.
Ya d'an numfasa daga bisani ya cigaba da cewa har ga Allah Minal naso ki fito da wanda ki ke
so za6in ranki, duk nasan zan sha matuk'ar wahala kafin Barkido ya amince.
"Amma hakan ya gagara daga gareki duk lokaci da na zo miki da zance, sai ki ce ba ki samu
wanda ki ke so ba.
Ba komai yasa nake miki gudun aure zumunta sai irin zaman da mu ka yi da mahaifiyarki, mun
sha bak'ar wahala da hak'uri ni da mahaifiyarki ba kad'an kafin mu fara k'aunar junanmu.
"Banaso ki fuskanci irin wannan rayuwar agidan aurenki.
shiyasa koda yaushe addu'a nake Allah ya kawo miki miji wanda ba daga zuri'ar Barkido ba.
Sai gashi Allah ya kar6i addu'a ta, Barkido da kanshi yai miki za6i ba daga zuri'arshi ba.
"Tun daga lokaci da ya gayamin mijin da ya za6a miki farin ciki ya lullu6e ni, saboda nasan
wanene Aliyu ba shi wata matsala ko kad'an yana da halaye masu kyau wanda kowane uba
nagari yakewa 'yarshi fatan samunshi amatsayin mijin aure.

"Yayin da Alhaji Abdallah ya cigaba da cewa, duk da Barkido ya gama zartarda hukunci har ya
kuma sanya lokaci bikinki nan da watani biyu masu zuwa kamar dai yadda ya fad'a tun kafin
zuwansu.
"Saboda haka banaso ki tashi hankalinki, nayi magana da mahaifin yaron, ya ce next week
zai zo ku gane ki kwatarda hankalinki idan bai miki ba, nasan ta hanyar da zan biyowa Barkido
ya hak'ura batare da rayuka sun 6aci ba

"Murmushi ta yi cike da jin kunya ta, sadda kai k'asa tana wasa da babban yatsar k'afarta.
Jin Shiru ta ya yi yawa yasa Abba ya d'ago ya kalleta,
shima ya yi murmushi ba ki ce komai ba Minal?"
Idan kuma ba ki da abin cewa za ki iya tafiya.

cikin sanyi murya ta ce Abba ya yi min duk ban ganshi ba, dama ni auren zumunci ne banaso.
"Good girl.....Allah shi yi miki albarka
Amin...Abba.
Tafad'a had'e da mik'ewa tsaye sai da safe Abba zan je na kwanta bacci nake ji.
Allah ya kai mu
cewar Abba.
"Kitchen tafara shiga ta had'a coffee ta wuce da shi zuwa d'akinta.
Gefen gado ta zauna ta yi crossing legs d'inta, ahankali take sipping coffee d'inta.
Yayin da wani gefen na zuciyarta ke nuna ma ta, tayi kuskure na saurin amincewa da mutume
da ko sunanshi sai yanzu ta ji.
Tana gama shanye coffee ta wuce bathroom ta wanke bakinta, ta dauko laptop d'inta ta duba
wani civil case da za ta yi presenting gobe.
Doguwar hamma ta yi had'e da shafa fuskarta hakan yasa ta rufe laptop d'in ta yi addu'a
kwanciya bacci, ta kashe wuta ta kwanta, ta rufe rabin jikinta da blanket.
****----****----***
*WASHE GARI*
*Abuja 11:08am*

Aliyu yafito daga apartment d'inshi jikinshi sanye da white suit, kamar yadda ya saba shigarshi
ta farare kaya, wannan yana d'aya daga cikin d'abi'unshi gaba d'aya tufafinshi farara ne.
Baya ta6a saka wani colour kaya idan ba white ba Hannunshi rik'e da brief case cikin yana yin
tafiyarshi ta k'asaita ya fito compound, da gudu direbanshi isah ya zo ya kar6i brief case d'in.
shi kuma ya nufi apartment d'in momma zaune ya tararda ita har k'asa ya durku'sa ya gaidata,
wannan yana d'aya daga cikin kyawawan d'abi'un Aliyu yana girmama iyayyenshi sosai.
"Momma ta amsa tana fara'a saida ta dube bakin k'ofa ta ga ba kowa, ta gyara zamanta
Sultan tun jiya mahaifinka ya dawo daga Yola.
"Uhm! Nasani momma naga lokaci da ya dawo ina tsaye a balcony.
Momma ta d'an yatsina fuska sannan ta ce, ya ce an tsayarda lokaci bikinka watani biyu masu
zuwa.
tak'arasa magana cikin murmushin yak'e.
"Ta6e baki ya yi had'e da mik'ewa tsaye momma ni zan wuce office.
Afakace ta galla masa harara, ina magana ka mik'e tsaye kuma ba ka ce da ni komai ba.
"Me Zan ce momma?
Auu.....ba ka da abin cewa?"
D'an bazawari murmushi ya yi momma sauri nake in nadawo za mu yi magana anatse, saidai
gaskiya idan har Daddy ya nace akan lalle sai nayi aure to ya barni na nemo wacce nakeso da
kaina.
in fact ban shirya yin aure a wannan shekara ba, balle nan da wata biyu ban so Daddy ya yi
sauri yanke lokaci biki ba
ahali ni da nake aure ban amince ba.
Rausayar da kai momma ta yi ta ce yanzu kan aikin ga ma ya rika ya gama, ni kaina ban zace
zai yanke iri wannan hukunci ba.
Amma ba komai ni ma nasan ta hanyar da zan bulluwa al'amarin.

"Kamar ya momma?"
Ya fad'a da alamar mamaki shinfid'e akan fuskarshi.
wayacewa ta yi ta hanya cewa je ki kawai kada na 6ata maka lokaci kamar yadda ka ce in ka
dawo za mu k'arasa
magana.
"Batare da yasake magana ba ya juya ya nufi sitting room d'in Daddy.

Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:42 PM] Jiddah Aliyu: *GIDAN RINA*

Na Jeeddah Aliyu

Free page

*Haske writers association*

*5*

Yana had'a ido da Daddy yafara murmushi yana sosa k'eya alamar rashin gaskiya, dariya
Daddy ya yi ya ce lale marhaban da bak'on Scotland barka da zuwa Gadanga k'usar yak'i.
"Dariya ce ta subucewa Aliyu ya rufe bakinshi da tafin hannu, Kallonshi Daddy yake yana
girgiza kai "Good morning Daddy Aliyu yafada yana shafar gemunshi, Morning Sultan idonka
kenan sometimes da sultan Daddy yake kiranshi kasancewar sunan mahaifinshi da yake da,
murmushi ya yi yace Daddy am sorry. "Ba komai sultan...Daddy ya fad'a but zo ka zauna mu yi magana ta fahimta.
zaunawa ya yi kusa Daddy kafin Daddy ya yi magana saida ya rik'o hannunshi d'aya, Sultan
dangane da zance aurenka ni da iyayyen yarinyar mu yi fixing din Date nan da watani biyu
masu zuwa, saboda muna so ku same isasshe lokaci da za ku fahimce junanku.
"This time around idan ka sake ka ruguza aurenan Sultan I won't forgive you....don haka make
sure ka shirya this weekend ka je Yola ku gana da yarinyar.
Ka ji ko?"
Daddy ya tambayeshi, yana kallon yadda ya 6ata fuska tamkar zai yi kuka ga wani uban gume
da yake ta faman shawagi akan face d'inshi, da kyar ya hadiye wasu yawu sakamako bakinshi
da ya bushe ya ce Daddy please.....idan har ya zama dole sai nayi aure ina neman alfarma ka
ba ni dama na nemo wacce nakeso, Saboda ba lalle bane kanemo min kalar mace da nakeso
ba...
Shut up....my friend!
Daddy ya daka mishi tsawa wallahi sultan ka shiga taitayinka da ni, muddin ka ga ba'a yi
aurenan ba k'addara hakan amatsayin bana numfashi tashi maza ka 6ace min da gani, shassha
banza da wofi.
K'asa da murya Aliyu ya yi ya ce Daddy am so sorry karka yi fushi da ni please.....duk abinda ka
ke so zan yi saboda ba zan iya jure fushinka ba.
"Dauke fuska Daddy ya yi da barin kallonshi, hakan yakara rud'a Aliyu ya durkusa agabanshi,

Daddy nace na amince muddin zan sanyaka farin ciki koda mayya ce zan aureta.
Sai lokaci Daddy ya saki fuskarshi ya ce that's my boy.....saidai ba mayya ba ce jikar Barkido ce
sunanta Barrister Amina 'yar manyan mutane ce shiyasa banaso asame matsala, daga bangare
na.
''Zaro idanu Aliyu ya yi hade da Squeezing face.....Daddy kana nufi yarinya lawyer ce?"
Kwarai kuwa independent lawyer ce[lauya mai zaman kanta]
Whatever! Daddy ni ko lawyer government ce I don't care kawai dai kasan I hate liar's kuma
mostly lawyers mak'aryata ne, hararrashi Daddy ya yi had'e da furta banaso shirme Gadanga
don kawai tana lawyer shi zai sa ta zama mak'aryyarci?"
"Turo baki ya yi a sangarce ya ce ni dai Daddy I don't love her.
mak'e kafad'a Daddy ya yi irin I don't care dinan, kafin ya ce kai dai karka yi gaggawa ka jira
har ka ganta ido da ido.
Mik'ewa Aliyu ya yi Sai na dawo Daddy ina da meeting around 12 o'clock.
asauka lafiya....Daddy ya fada da murmurshi akan fuskarshi.
Ficewa ya yi yana fitowa isah direba ya jawo mota ya bud'e mishi back sit ya kame a owners
corner, isah ya ja motar cikin kwarewa da tuk'i ya fice daga gidan.
****--*****-----****
Sai around 2:20pm Aliyu ya fito daga conference hall, kaitsaye office d'inshi ya wuce ya ajiye
laptop dinshi da wasu files akan desk ya wuce ya bathroom ya dauro alwala, yana fitowa P.A shi
Kamal na shigowa rik'e da white coat d'in Aliyu yanufi wata hanger da ke ajiye a cikin office d'in
ya sarkafe rigar. "Aliyu yana fitowa daga bathroom da
sauri kamal ya shinfid'a mishi praymat
Batare da Aliyu ya kalle shi ba ya ce Kamal ka yi min order food a chicken republic restaurant,
yunwa nake ji cikina sai k'ugin yake.
"An gama Boss!
Har kamal ya juya ya sake cewa ba ka ji ba kamal.
Chak...kamal ya tsaya.
"please help me call Jamal tell him I wants to seen him urgently.
Yes boss!
Cewar kamal yana mai ficewa daga office din.
Aliyu yana gama sallah ya koma kan resting chair ya kwanta, ba abinda yake tunawa sai
babban k'alubali da yake tunk'aro shi, duk duniya ba abinda ya tsana irin aure duk yadda ka ke
da shi idan ka yi invited nashi daurin aure ba ya zuwa, ko a family su ake aure sai ya k'irk'iro
tafiya don kada ya je sosai abin yake ciwa Daddy tuwo a kwarya. "Mtsss....ya ja d'an siriri tsaki ya dafe goshinshi duk lokaci da ya tuna Daddy ya ce dole sai ya
je Yola wurin yarinyanan, sai ya ji fad'uwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login