Showing 21001 words to 24000 words out of 126765 words
Chapter 8 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf
house" Uncle Isma'il ya dinga jinjina kai yana tunanin abinda ya kai Majeederh wajan His
Excellency, mutum mai tsananin karamci da tausayin naƙasa da shi Al'ummar shi yana da
tabbacin ba zai taɓa cutar da Majeederh ba. Ya duba agogon hannunsa yaga lokacin ya ja,
gashi ance ma baya ƙasar yana Cameron. "dare ya riga da ya yi, gashi His Excellency ɗin ma
baya ƙasar da nayi masa waya ina so contact nasa kai tsaye ba shamaki"
"Liar, yana nan infact shi ya sa a kai ni prison, a gabansa Jee ta mareni" Uncle ya yi shiru yana
son fahimtar wani abu kafin ya ce "Me kayi mata?" Abraham ya ce
"Wai don na ce ni na bata ciki, am the father of her son, am the one who raped her, na rantse"
maganganun Abraham su kayiwa Uncle girma a kunne ya fahimci akwai buƙatar neman
Majeederh domin bai taɓa ji Abraham ya yi ƙarya ba, He is a man who stands by his words.
Uncle Isma'il ya ce "Amma me ya sa kayi haka Maminka ce fa?" Ya haɗe rai sosai yana ɓata
fuska ya ce "Ni yanzu ban son Mamin, she's my wife to be pls Uncle I need your help, Dadyna
baya understanding my feelings, Jee bata duba feelings nawa" ya faɗa cikin damuwa da murya
mai rauni.. "Ka aikata babban kuskure acikin tsarin addininmu na Islam, wanda ya sha bamban
da naku Addinin na Christianity mabiya Yesu, a tsarin dokokin Muslunci role and regulations ga
duk saurayin daya aikata Fyaɗe bulala ake masa, mai aure kuma jefe shi ake, wannan abin
ƙazanta ce ma fi muni, ba zan goyi bayan haka ba Abraham, Maminka?"
Uncle ya faɗa rai ɓace. Abraham was just looking into uncle's eye's ya kasa bambance fari da
baƙi, yana son fahimtar mene abin kuskure a tarayya da mace? Koda yake shi addinin
musulunci ya sha bamban da sauran, komai nasu sai sun kawo hujja, A strong argument.
Ya dubi Uncle a lokacin baka iya gane mai idanun Bad boy ke faɗa sbd launin da suka sauya a
taushashe ya ce.
".... I Just gave her i kissed, i Little kissed on her neck, duk abinda ya faru it was a mistake"
"Mistake?" Uncle asked.
"I.... I... I am sorry Uncle"
Was the first time daya bawa wani haƙuri saɓanin Jee, yana mata abu immediately yake cewa
"Sorry Malumana"
"Help" "Sai nayi bincike, idan ya tabbata dole ka amshi hukuncin Islama, bi ma'ana bulala, kuma
na kafa maka sharuɗa"
"Accepted alrdy"
Uncle ya ce "Tashi muje, zan kira Dr ya duba ka"
Sai a lokacin ƙarfi yazo masa, da ƙyar ya miƙe kansa na juyawa. Cikin gidan shiru kowa ya yi
barci Uncle ya nunawa Abraham wani bedroom, ya shiga ya haɗa masa warm water kana ya
ɗakko masa wata jallabiya tare da barin bedroom. A daren Uncle ya kira Dr, kana ya kira Uncle
Bello akan yana neman sa gobe by 11Am, daga nan ya turawa Abbu message akan umarni
yake bashi gobe yazo yana nemansa.
Daga nan zama ya yi tare da buɗe system nasa ya shiga Gmail ya turawa zuwa ga email ɗin
Governor Abu-turab Alƙasim na sirri akan yana buƙatar magana tare da full address da
muhimmacinsa wajan Malama Majeederh Abdul'aziz Khan.
Washegari Abraham na zaune watching TV daga shi sai 3gauter da Armless mara nauyi wacce
ta haska baƙar fatar jikinsa, gashin kansa sai ya yi kamar an gyara shi yadda ya cukurkuɗe
kamar indomie, duk wajan ciwon anyi dressing nasa, idanunsa wanda suke always a haka He is
so genius, and so romantic. Kana ganinsa kasan bashi da haƙuri zafin rai da taurin kansa,
musamman physquie. Ba komai yake ɗauka ya zuba a brain nasa ba, amma ƙwaƙwalwarsa ta
kasa mance ranar, komai ya faru cikin tsautsayi. Unconscious happenings, It is still fresh in his
mind, he remembers it every day.
Tsaki ya ja, babu abinda yake so a yanzu kamar barasa ita ce kawai zata ɗauke masa nauyin
zuciyarsa.
Jawaad ne ya shiga hannunsa zube cikin Aljihu sai Sona dake bayansa tana cewa "Yaya
Jawaad ka fiya ruwa, wallahi ko matarka sai tayi da gaske zata ci kuɗinka, ni mamakin ƴan
matan da suke nace maka nake tunda ba komai za su samu ba" Jawaad ya yi murmushi yana
zama kusa da Abraham ya ce "Yarinya ai mu akwai kalaman soyayya, mun san ta kan mace da
kalma ɗaya take nake sace zuciya, kuɗi kuma ai Abba na zuba miki acct" Sona ta ce "Ni dai ba
haka bros kewa sister's na su ba"
"A'a, ba zan goyi bayan ɓarnatar da kuɗi ba, bayan baku san ciwonsa ba" Was abinda ta ce.
"To don Allah ka bani, just 50k" "Yarinya ko ƙwandala, na aure nake haɗawa" Ta kumbura fuska
duk abinda suke Abraham na jin su..
"Yaa Abraham kai bani"
Ya buɗe idanunsa ya kalli Sona, kallon ɗaya kafin ya lumshe idanu ya ce
"Nawa?" "50k"
"Done" ta buga tsalle ta ce "Yes, thank you Yaa Abraham" Jawaad ya kalli Abraham sosai ya ce
"Ni ma Yaa Abraham ka bani na siyi new car"
Abraham ya watsa masa harara ya ce "Bana ƙarawa mai....."
Ya yi shiru yana zaro idanu alamar bai san ƙarshen karin maganar ba. Jawaad ya buga dariya
ya ce "Ba a ƙarawa mai ƙarfi, ƙarfi Anji Hausa fa, wai bayan kayi hijara garin Katsinawa ka je ka
koyo mana wasa"
"Mene ga hausa, Sometimes there is difficulty in pronouncing some words"
"Ni dai a bani kuɗin" ya juya ya kalleta ya yi shiru sai kuma ya miƙe yana riƙe kansa he's trying
to recovering something, kallonsa suke gabaɗaya ya yi ta zaga ɗakin ya haɗa zufa sosai
idanunsa sukai jajir da sauri ya ce
"Joshua" Ya ƙara yin shiru for some seconds kana ya ce "Call this phone" Sona ta ɗauki
wayarta ya shiga faɗa cikin sauri in a low voice.
Yana gama faɗa ta danna call, ringing ɗin farko Joshua ya ɗauka yana faɗin.
"Hey, who's on the line?"
Sona ta miƙawa Abraham waya ya amsa tare da sanya handsfree sbd yanayinsa ya fara
juyewa, Joshua ya yi ta magana shiru can Abraham ya ce "GANG"
"Bad boy" Joshua ya faɗa miƙewa da sauri yana cewa "Bad boy where are you? Gang team
need you"
"Ka haɗa mini Gang team, right now" ya fesar da numfashi cikin murya mai sanyi ya ce "I'll send
you a acct number, kayi dropping 500k ciki" daga nan yare suka sauya kana ya kashe wayar ya
ce Sona ta tura acct number. Daga nan kuma ya fara losing mind.
Uncle Isma'il ya kalli Abraham ya ce "Go and change your dress, before nan let's talk"
Abraham ya dai kalli Uncle bai fiya gane wasu kalaman ba ya ce.
"Faɗa mini duk abinda ya faru a can gidan His Excellency" ran Abraham ya ɓaci ya ji tamkar
yanzu abin ke faruwa in brief ya faɗawa Uncle Isma'il everything. Ya jinjina kai ya ce.
"Ina son ka saurara, ba zanwa Majeederh dole ta so ka kota aureka ba, kuma ina bayan tayi
maka hukunci daidai da laifukanka."
"....No please Uncle, I'll die idan ba Malumana"
"Kasan mene matsalarka ta farko, kai ba musulmi ba, ga team na ƴan iska, ga shan barasa,
babu halarci a aurenka da Majeederh, amma I'll Adviser you duk da cewa akwai wahala ta
samun haɗin kanta, ka zama mutumin ƙwarai kuma ka zauna a gidana har sai lokacin dana
amince da gyaruwarka, Kai Kiristan ita Musulma, kuma babbar malama wacce ta girmemaka, ta
baka zatarar shekaru goma sha biyar Abraham,ta raineka ta ci kashi da fitsarinka akwai girma,
akwai nauyi ko da ace kai Musulmi ne Majeederh nasa izza da kame kai bata ɗaukan raini,
babu shakka ko auren akai zata rainaka".
Abraham ya ce "Raini? A sbd ba zan iya bata ciki ba? Ina da ishasshiyar lafiya inma yara 100
zan bata cikin dare ɗaya....,"
"Stop it, what noises ni wan mahaifin Majeederh ka ke faɗawa haka ba kunya? To ɗabi'ata data
Majeederh data Addinin musulunci tasha bamban da taku, akwai alkunya tsakanin surukai"
"Mene surukai Uncle?" Shi Abraham bai ɗauka laifi ya yi ba ya kuma kasa gane mene kuskuren
shi a cikin maganarsa. Ya suruna cikin raunatacciyar murya ya ce.
"I am sorry, amma mene ya sa zata raina ni wallahi kullum zan iya bata ciki.,,"
"Get out Abraham Denial David, out tunda ba zaka nutsu ba" "Ka yafe, forgive me please, zan
zama Muslunci ka taimaka" Uncle Isma'il ya ce "Mene ya ja ra'ayinka? Bayan iyayenka basa su"
"Shi ne first and simple way da zai mallaka mini Malumana" Uncle ya girgiza kai ya ce
"Ka fara tsarkake niyyarka, ba a taɓa musulunta sbd wani dalili ko neman yardar wani, ka
musulunta sbd ka yarda addinin Musulunci shi ne addinin na gaskiya, ka musulunta sbd ka
yarda da Allah da Manzonsa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ka yarda da su
babu abokin tarayya, ka mance littafin injila ka ɗauki Alqur'ani da hannu bibbiyu" "Ta zan yarda?" "Ka fara nutsuwa kasan mene ya sa ka ke son Musuluncin yanzu ka je ka
shirya, kuma babu kai babu yiwa Majeederh magana, balle uzzura mata ko kai hannu zuwa
jikinta yadda ta ce ka barta ta tsaneka to barta, ka ƙaura cewa ganinta, yanzu ne za ka yi faɗa,
fight for your love, ka je bata da bazata, bazata ta sabon sauyin da kayi ka zama tsarkake"
Abraham ya yi shiru yana tunanin ta ina zai iya all this, ba zai iya haɗa waje da Majeederh ba
tare daya taɓa ta ba. Ya miƙe tare da shigewa bedroom.
Babban parlourn a cike yake, Uncle Isma'il, Uncle Bello, Abbu, Mami. Gefe guda kuma Bar
Aliyu Sufyan Alhassan ne zaune cikin wani lallausan yadi, Sai Hajia da Papa iyayen Zaki. Daga
ɗaya barin Masu garin ne bakiɗaya, Governor Abu-turab Alƙasim da Mama sai Haseenatou
wacce ta ƙarasu. Abu-turab cikin wata dakakkiyar shadda fara tas sai ɗaukan Idanu take ɗinkin
jamper da babbar riga, he was so looking anger na jin meke faruwa. Daga tsakiya Malama
Majeederh ce zaune cikin wata blue black ɗin Abaya mai kyau tayi rolling kanta gefen fuskarta a
rufe hannunta riƙe da Khalil.
A inda take zaune take jiyo ƙamshin perfume ɗin da har abada ba zata mance ba. Abinda bata
sani ba dab da ita Oga Abraham Daniel David ne zaune cikin wani milk ɗin voyel mai manyan
zane ana iya hango faffaɗan ƙirjinsa mai ɗauke da zanan tattoo kansa kwance luff yana ƙyalli
sai sabga ƙamshin Boadicea The Victorious, idanunsa kafe a kanta babu ko ƙiftawa. Uncle
Isma'il ya yi sallama kana yasa aka yi addu'a. Ya gyara zama ya ce.
"Bincike da result ya tabbatar Khalil jinin Abraham ne" a kusan tare Governor Abu-turab da Bar
Aliyu suka ce..
"Ƙarya yake ɗana ne" Abraham ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Babu me zarar yi ma Jee
ciki kaf cikin ku, I'm lucky ni me sa a ne" duk suka kalli Abraham Abbu kuma ji ya yi kamar ya
shaƙe yaron.
"Ba musu za kuyi nan ba, kuna son rusa mini ƴar fahimtar da nayi, His Excellency, Barrister,
Abraham na yarda duk kuna son Majeederh, shawara ɗaya zan baku Majeederh ba budurwa ba
ce ƙaddara ta faɗa mata" Zaki ya ce "Zan zauna da ita haka"
Uncle ya girgiza kai ya ce "Kuyi faɗa, faɗa na samun soyayyar Majeederh zan ga waye MIJIN
MALAMA, zanga mai zarrar sace zuciyarta, Ɗa dai na Abraham ne, ban san ya akayi aka samu
cikin ba wanda gabaɗaya yanzu Abraham zai bamu labari anan zamu tabbatar da gaskiyar shi".
"Idan tana da burin dawowa gidana to ta ɗauki shegen yaron nan mai gadon tsiya, wanda ya zo
da ƙazanta zuwa gidan marayu, kuma ki zaɓi Abu-turab matsayin mijinki shi ne ya dace dake"
lokacin guda Majeederh da Abraham da Aliyu suka kalli Abbu banda Abu-turab daya sauke
wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya.
"Abbu gidan marayu, ni na haifeshi ina raye kuma zan kai shi gidan marayu?" "Idan kin yarda ni
ne ubanki, ni ke da hakƙin zaɓa miki miji" ta runtse Idanunta zuciyarta na bugawa bata san
lokacin da ta ce. "Na amince, na amince Abbu albarkar ka nake nema" idanun Abraham kamar
za su faɗo. "You're liar, ki auri wani,ni kuma na ci gaba da tarayya dake kina haifar shegu, ba
zan barki ki zauna lafiya da wanda kika aura ba" tayi masa banza. Abbu ya kalli Abu-turab ya ce
"Idan ka shirya kawo sadaki yanzu a ɗaura auren ka tafi da matarka" Abu-turab ya ce "A shirye
nake Abbu" Majeederh na zaune ta ji an ɗagata cak tare da yin sama da ita har jaririn hannunta
kafin kowa ya yunƙura Abraham ya yi waje da Majeederh yana zuwa ya saka key ya buɗe ƙofar
mota ya cilla Majeederh ciki idanunsa rufe ƙwaƙwalwar taɓin hankalin na motsawa "Kai
Mahaukaci ne?" Ya dubeta yana sunkuyawa dab da ita ya zura mata seat blt ya ɗaurawa kansa.
A karo na biyu ta sake cewa "Kai Mahaukaci ne?" Ya buɗe ido ya ce "I don't know, amma yau
zan iya bamban cewa ni mahaukaci ne or not? Domin a yau zan ƙara baki wani cikin na kwanta
take a karo na biyu, daman wancan i have been drug ban san ya ki ke ba, wannan shi ne aikin
hankalina, wanda zan yi na hauka ya fi wannan,zan iya tsayawa tsakiyar titi babbar mota tabi ta
kanmu, me, you, and our son duk mu mutu" Majeederh ta runtse Idanunta tasan tabbas zai
aikata. Da gudu Bar ya fito Abu-turab na mara masa baya, suna fitowa motar Abraham Daniel
David na fice daga cikin gidan da gudu...
End of free pages
In sha Allah a nan na tsaya da free pages mu haɗu a paid grp. Yanzu zamu je asalin labari nan
tsakiya ne, book1 shi ne asalin tashin hankalin littafin duk wani abu daya faru a nan ya faru.
Book2 anan zamu ji yadda jaruman namu za su yi faɗa akan Majeederh.
Ɗan waye?
Ya akai sai bayan shekara biyu ta haihu?
Dashe akai mata?
Cikin Aljanu ne?
Ko Abraham, ko Abu-turab ko kuma Zakin Hajia? Wa zai ci riba.
Book1 500
Book2 500
Gabaɗaya har mu kammala littafin 1k ne. Zaka iya fara biyan kuɗin book1 kafin mu fara
book2.... 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank... Evidence of payment
08119237616. Zamu fara posting as soon as kun kammala payment. THANK YOU❤️
Kafin kammalawa Wannan page ɗin gabaɗaya sadaukarwa ne ga HASEENATOU AUTAR
MANYA. ELEGANT ONLINE WRITER'S, MIJIN MALAMA GRP 1,2. ALLAH YA SAKA MUKU
DA ALHERI☺️.
TALLAH
Shin kuna bibiyar littafin *DAUƊAR GORA!* Wanda *HAWA__B__KUMO (REAL-SMASHER)*
ke kawo maku? Wai³ this is an emotional story ever,idan ba kya bi maza ki nema ki fara kada
ayi babu ke,*DAUƊAR GORA!* Labari ne dake ƙunshe da sarƙaƙiya akan ƙaddarar wata baiwar
Allah *AYSHATOU AYATULLAH* wacce tayi fama da matsalar yoyon fitsari at a very young
age,she really went through tsananin rayuwa,ƙiyayyar Family'n uba,kowa yana ƙyamar zama da
ita,saboda larurar data sameta lokaci ɗaya,ba kuma wai dan haifeta da shi ba,ku nema ku
karanta kada ayi babu ku..
*DANƊANO*
Kallon ƙyama Inna Tabawa matar ƙanin Babanta data kama baki kamar an yi pausing ɗinta
ta bita da shi dawani murya take cewa "toh! Yau muke ganin tsiya da wasali.. Ke yanzu da
girmanki gotai² sai ki saki fitsari a jikin kayanki? O'ohh! Ikon Allah.. Ni Tabawa na ga abunda ya
isheni bai ishi Allah ba" ta riƙe haɓa tana sake jinjina al'amarin,kamar an cillota kuma kamar me
jiran ayi da ita,Inna Larai tai wuff ta fito daga ɗaki jin maganganun da Tabawa ke faɗa ta ɗora da
faɗin "ai Tabawa in faɗa maki iskanci ne da kuma ganin ta samu masu ɗaure mata,amma babu
wani rashin lafiyar dake damun yarinyar nan,samun guri ne kawai.. Allah na tuba yau aka fara
yin ciki? Kou a kanta aka fara haihuwa da za'a raina ma mutane hankali ace ta gamu da wani
larurar dake hanata riƙe fitsari.. Zallar taɓara ce dai ke damunta,tou kuma kin san abunki da
goyon kaka,babu abunda baza tayi ba da sunan larura" hawayen da suka ciko idonta tai saurin
sa hannu ta goge,da sauri ta wuce za ta bar gurin,Inna Larai ta kalli yara²n gidan tace "Kaiii! Kui
mata ihu kou za ta ji haushi ta dena abunda take,kui mata waƙar me fitsarin kwance ni na
saku,duk wanda yayi kuma zan bashi Nera 5-5,manya kuma zan baku 20-20" ihu da tafi suka
hau yi,kafin kace me ƙananan yaran gidan sun ɗauko murafen languna da ƙananun gallon suka
fara kiɗa. Kamar cikin watan ramadhan lokacin tashe,haka muryoyin yara da manyan gidan
masu jin haushinta babu gaira ba dalili suke tashi cikin waƙe suna faɗin "me fitsarin
kwance,amalaala! Wace ce? Me fitsarin kwance.. Amalala.. Me fitsarin zaune.. Amalala.. Me
fitsarin kwance!" Inna Larai tace "baku kama sunanta ba,ku faɗa ku ɗaga murya kowa yaji,idan
tai zuciya gobe ta daina" kamar Inna Larai ta zugasu kuwa suka ci gaba da kiɗa suna waƙa
"wace ce? Aya me fitsarin kwance,amalaala! Aya me fitsarin kwance.. Amalala.. Aya me fitsarin
zaune.. Amalala.. Aya me fitsarin kwance!!" Ba waƙar da suke yi ne yafi taɓa mata zuciya
ba,yanda wasu ciki ke zagayeta har suna kama mata zani suna janta,wasu na dungure mata kai
shi ne abunda yafi komai sawa taji ta muzanta a idanun duniya,da wani irin sauri ta durƙushe
bakin ƙofar ɗakinta,banda kuka babu abunda take kamar ranta zai fita,bata taɓa jin ta yi loosing
hope ba irin yau,zuwa yanzu kam gaba ɗaya rayuwar ma ya fice mata a rai,musamman irin
tozarci da wulaƙancin da take kan fuskanta daga danginta,abun yai mata yawan da ciwon
zuciya yake neman kamata nan take,daga jiya zuwa yau sosai take cikin barazana/walaƙanci
da tsokanarsu,har tunanin fita take kou wani uzuri ya kamata da dole zaisa ta haɗuwa da wani
cikin mutanen gidan ba Baba Wada kou su Inna Asama'u ba,wani