Showing 81001 words to 84000 words out of 126765 words
Chapter 28 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf
kawai ta zauna ke kyaci tunda
kina zaune gida ke ba aure ba, ki je kiyi mata arba'in ɗan wanki da abincinta dana mijinta"
Majeederh ta kasa cewa komai ga biyya da take da ita bisa dole ta shirya ta nufi Badalawa....
Daddare Majeederh ta gama abinci tsaf tana zaune a parlour Amani ta ce "Allah sarki ashe
Alpha guduwa ya yi wai za a ƙaƙaba masa ke kuma baya so? Haka Raihana ta ce mini, ni dai
don Allah ba ruwanki da mijina daya dawo ki shige bedroom kawai haka kurum yadda mata
suke kwantai ki aure mini miji na shiga uku" Majeederh dai ta yi shiru Amani ta ce "Kema dai
ƙuruciya ke damunki ina ke ina Alpha? Yaran zamani kenan" Majeederh ta miƙe zuciyarta a ƙun
ta ce wai ƙanwar ƙanwarta take faɗa mata haka? Maybe ƴar cikinta da auren wuri ta
yi.....Majeederh ta fara koyarwa a B.u.k kuɗi take samu sosai ta zama feminist ɗin dole, a cikin
shekarar Abbu ya je makka arziƙi ya ci uban nada, tsakanin Majeederh da kuɗi siyan suttura
itama ba da yawa ba gudun kada Abbu ya ce ta kashe kuɗin....
*After 3yrs*
Lokacin Majeederh nada shekaru 31 cif a duniya a lokacin ta ƙara cin ta ƙara cin gasar Alkur'ani
ta duniya, Nigeria ta ƙara ɗaukan award, kuɗin data samu ba zai faɗo ba, wannan karan a
Saudiyya akai murmushi kwance a fuskarta ta tarawa Abbu dukiya tana tsaye riƙe da Award
idanunta ya sauka akan wani Matashin ko magidanci da yake ta kallonta Without blinking his
eyes sai ta ji ta tsargu ta shafa fuskarta ta jita a rufe ta sauke numfashi, tana ƙoƙarin barin hall
ɗin musabaƙar ta ji an ce "Tagawa lafiya Meke faruwa?" Ta sauri ta juya idanunta ya sauka
akan kyakkyawar fuskarsa sai ya motsata yake kamar yaro ga wata ilhama dake kwance a
kanta, ta ƙara ware idanu a ranta ta ce "Ƙhulud's husband, Ajlaal?" Gabaɗaya fadawa suka rufe
shi ruf ganin sai zufa ce ke yanko masa jikinsa na wani irin ɓari "Sannu Tagawa, Allah ya
ƙarawa sarki lafiya" A ranta take Mamakin yaushe Ajlaal ya zama sarki? Kuma ta san sarkin
Makka ai bai mutu ba, tana tsaye a wajan aka shigar dashi wata ƙaramar mota mai azabar kyau
aka nufi Palace da shi. Ta ɗan taɓe baki ta nufi mota zuwa masauki domin a gobe zata koma
ƙasarta Nigeria tabar Saudiyya ɗin, Majeederh ta zama kamar namiji sbd jajir cewa ƙoƙari da
neman na kai, sai dai ba ruwanta da kowa magana sai ya zame dole ga bala'in ji da take a
lokacin kuma gabaɗaya dangi kowa ya shiga yar bata da habaici babu aure sai gantali Anti ce
kawai ke bata baki Uncle Isma'il ma ganin laifinta yake aka juya mata baya ko taro ta daina
shiga......
Titin Government house cike yake da abun hawa an tara uban go-slow manyan mototci da
ƙanana, masu napep da barura hankalin kowa a tashe yake sbd ranar data ƙwalle, an kuma
rasa abinda ya haddasa go-slow ɗin... Abbu ya gyara zamansa a bayan mota yana jan tsaki ya
ce "Nigeria ba zata sauya ba" Driver ya ce "Wallahi Alhaji kamar faɗa ake a tsakiyar titin ma"
Abbu ya ƙara jan tsaki ya ce "Fita if there's any way sai ka bi" Driver ya fita, cikin sauri yake
kutsawa har ya ƙarasu tsakiyar titin. Wata baƙar mota ce lafiyayyiya daka gani ba a jima da
siyanta ba, ita ta tare kan titin, sai wasu ƴan matasa wajan su goma tsaye a wajan sun saka
wani a tsakiya wanda bakinsa ya fashe jini na zuba, sai a lokacin ya ƙara lura da sauran
motocin da sukai blocked hanyar.... "Fouk You" Wani ya furta daga cikin samarin daga shi sai
gajeren wando ko riga babu jikinsa kansa babu ko gashi sbd tabbatacce ne shi Ya nuna guy ɗin
da suke doka ya ce "Kai dan ubanka sa'an ubanka ne ni? How dare you talk to me like that?
He?" Taj ya saki dariya ya ce.
"You're just wasting your time, ka ci uban ɗan Shegiya muga waye ya tsaya masa a Nigeria,
Legas ma babu wanda ya isa damu balle Kano"
"Exlty, We are Nigerians, we will decide, we will say whether it is heard or not, there is no one
behind us..... Tell them" John Ya faɗa yana murza gun ɗin hannunsa. Taj ya ƙara sakin dariya ya
ce ya ce "Speak louder John, ba wani shege" Joshua ya ce "Mahaukata ne ku, wallahi kun saɓa
ba haka bad boy ya ce ba, a karya masa ƙafar daba da hannun hango a zubar titi" Driver ya
zare idanu. A na kana wani police ya zo ya ce "who are you? Waye uban a garin nan? Dalla ku
matsa akan titi.....,"
"What if we refuse?heeee?" Gabaɗaya Gang team ɗin suka juya idanunsa ya sauka akan shi,
fitowarsa kenan daga cikin mota, Matashin saurayi mai ji da ƙuruciya. Police ɗin ya ce "I'll
report, za ku yi prison for life" Guy ɗin daya fito daga motar yana wata iriyar tafiya majestic har
ya ƙarasa gaban police ɗin a taƙaice ya ce. "Ohhh" Ya faɗa yana hura masa yahaƙin
Cigarettes... Police ransa ya ɓaci ya ɗaga hannu zai nuna shi da yatsa cikin zafin nama guy ɗin
ya kama hannu tare da murɗewa nan take hannun ya kare.......Kuka Abbu yake wiwi hannunsa
dafe da Alkur'ani ya ce "Wallahi wallahi Majeederh ni ne ubanki, mahaifinki ni na haifeka jinina
ke yawo a jijiyoyin jikinki, Majeederh ina tunanin ke aka sauya mini kin tuzartani kin ɓata mini
suna a dangin kina roƙan Soyayyar namiji? Ni na cancanci haka?" Majeederh ta ce "Ka yafe
mini, zan yi aikin ba zan ƙara ba kuma ba ai bai aurenin ba he left me"...... Shekarunta 31 cif tun
ranar ba wanda ya ƙara cewa yana sonta balle aure, a haka ta ƙara zama Gwarzuwar Alkur'ani
wacce aka gabatar a Saudiyya.....
Sun cike titi babu wajan da mota zata shige, sun haddasa go-slow na ban mamaki wasu ne da
basu da maraba da ƴan fashi wajan su goma a tsakiyar titin sun saka wani a tsakiya suna duka.
" Kai dan ubanka sa'an ubanka ne ni? How dare you talk to me like that? He?" " Wanda suke
doka ya ce "Me nayi muku?" Taj ya ce "You're just wasting your time, ka ci uban ɗan Shegiya
muga waye ya tsaya masa a Nigeria Bama kano ba, Lagos ma babu wanda ya isa damu balle
Kano"
Joshua ya ce "Mahaukata ne ku, wallahi kun saɓa ba haka bad boy ya ce ba, a karya masa
ƙafar daba da hannun hango a zubar titi" Wani police ne ya ce "Ku titin iyayenke ne? Zaku jawa
kanku dilla ko kwashe motocin ku, ku bawa jama'a waje.
Daga bayansa aka ce "What if we refuse?heeee?" Gabaɗaya Gang team suka kalli Bad boy
wanda ya fito daga mota, police ɗin ya ɗaga hannu zai nuna Bad boy kafin ya yi pointing ɗinsa
ya kama hannu tare da karya shi nan take....
https://arewabooks.com/chapter?id=64ac50ef324ef73a495e70b9"This is the first and last da za
ki yi pointing nawa da finger, Dog!" Guy ɗin ya furta hakan a tsawa ce, mai da police ɗin ma ce
ta hanyar faɗin “Za Ki yi” Saboda rashin cikakkiyar hausa maganar ta shi ma a gurɓace take.
Sosai Police yake jin azaba nan take hannun ya kumbura zufa na yanko masa ya ce "This is not
fair, su waye ku? You came and blocked the road and prevented the vehicles from
entering"....“Your Father” Guy ɗin ya faɗa. Yana ware kuma dara-daren idanunsa akan Ɗan
sandan, Kyakkyawan saurayi ne mai ƙarancin shekaru domin baifi 16yrs ba, kulawa da
kwanciyar da jin daɗin rayuwa haɗi da samun duk wani abun da yake so ya sanya jikinsa wani
irin mahaukacin buɗewa, domin gabaɗaya cikin Gang team ɗin yafi kowa girman jiki, tsayi da
kauri jikinsa a murɗe yake ga wasu six-pack da suka bayyana musamman saman ƙirjinsa, baƙi
ne shi sosai irin baƙin ƴan America ɗin kana ganinsa kaga Ba'amurke baƙar fatarshi mai kyau
da sheƙi irin baƙin da yafi farar fata kyau da ɗan kan idanu. Gabaɗaya jikinsa zanen tattoo ne
daga wuya har zuwa ƙirjinsa da hannaye ga wata ƙatuwar sarƙa mai tabon Cross a jiki. Sumar
kansa a murmurɗe kamar indomie wacce ta ƙara fito da kayan fuskarsa da jajeyen laɓɓansa....
he is outstandingly handsome and robust, very masculine. Cikakken namiji mai iko da tsayawa
akan ra'ayinsa. Police ɗin ya nuna kansa ya ce "Ni ka ke zagi?"
"An zage ka titin na ubanka ne?" Taj ya faɗa yana nufar kan Police ɗin ganin haka yasa ya yi
saurin yin baya tare da barin wajan. Taj ya ja tsaki ya juya ya kalli Guy ɗin daya karyawa police
ɗin Hannu ya ce
"Abraham let's go" Da wani irin kallo wanda aka kira da Abraham ɗin yake bin Taj da shi cikin
warning ya ce "Sai na ci Babarka, duk sanda ka sake ce mini Abraham" Ya faɗa cikin harshen
turanci. Da sauri drivern Abbu ya juya zuwa wajan mota yana isa jiki na rawa ya ce "Yallaɓai
wallahi ƴan fashi ne, mun shiga uku" Abbu ya ɗago kai ya dubi driver a hankali ya ce "No! Ba
ƴan fashi ne, ƴan fashi da rana??" Driver ya ce "Kwarankwatsa su ne, hadda bindiga irin ta film
na gani fa? Innalillahi mun shiga uku" Abbu ya ajjiye Jaridar hannunsa domin meeting ne da shi
na gaggawa akan wata contract da zai yi signing akan papers ɗin. Ganin haka ya sa Driver
buɗewa Abbu ƙofa ya fito yana tattare babbar riga cikin sauri kana ganinsa kaga manyan
Alhazawan nan masu tashe da kuɗi, ya dinga ratsa mototci yana shigewa har ya isa tsakiyar
Gang team ɗin. Abraham na tsaye hannunsa riƙe da Cigarette yana busawa tare fitar da yaƙinta
zuwa sama. Taj ya ce
"Guy's let's go, go go" Abraham na ƙoƙarin shiga mota ya ji an damƙi wuyansa ta baya, abinda
tunda uwarsa da haife shi ba a taɓa yi masa ba, kasa juyawa ya yi saboda tsananin mamaki
kafin a ankare ya ji an fizgoshi tare da sauke masa wasu tagwayen maruka. Gabaɗaya Gang
team ɗin, Taj, Joshua, John... Da sauran sukai kan Abbu kowa yana fito da bindiga Jikin
Abraham har wani tsuma yake naman wajan na wata kakkarwa idanunsa sukai jajur Yatsun
Abbu suka fito raɗau a saman kyakkyawar fatarsa. Da wata murya ya daka musu tsawa ya ce
"Noo!!!!! Don't shoot him" John ya ce "But why? Marinka ya yi, He slapped you, waye shi a
Kano? Ubansa ma ubansa zamu ci dan kaza kazanshi" Abraham dai kallon Abbu yake without
blinking his eyes. "Ni ne zan hukunta shi, Ba a taɓa mini haka ba in my whole life" Abraham ya
basu amsa. Cikin sauri kuma ya ƙwaci bindiga a hannun Taj zai bugawa Abbu kan bindigar ya ji
Abbu ya ce "Wato kune irin gagararrun da muke da su a kano ko? Haihuwar kan titi wanda baku
san girma da darajar kowa ba? Shegu gayyar tsiya, gayyar na ayya" Cak Abraham ya tsayar da
hannunsa dab da fuskar Abbu ya runtse rinannun idanunsa. Ganin ya tsaya Gang team ɗin
suka haɗa baki wajan faɗin "Bad boy Shoot, Shoottt him" Ko motsawa bai yi ba balle ya yi
ƙoƙarin harbin Abbu, murmushi Abbu ya yi ya ce "Idan kai ɗan halak ne harbeni, ɗan daba
masu kwacan wayoyi sisi babu a aljihu maimakonsa ku nemi aikin yi kun bige da sata da bashi
da makami, me ake da talauci shi yake saku irin wannan Allah wadaran naka ya lalace" Wani
acikin jama'ar wajan ya ce "A'a Alhaji ɗa ai na kowa ne, ka yi musu fatan shirya idan da rabo
watarana sai kaga sun zama wasu a Nigeria bana jihar nan ba" Abbu ya girgiza kai ya ce
"Goodness! Ai basu da rabon shiriya irinsu da haihuwar su gwara ɓarin su, basu da wani
muhimmaci talakawan banza, maybe na shan wiwi da sigari basu da shi" Yadda jikin Abraham
ke ɓari kaɗai zai bawa mutum tabbacin maganganun sun shige su, duk da ba komai yake
fahimta ba cikin yaren Hausar.
"Useless" Abbu ya ƙara furtawa yana tofar da yawu. Kafin su Taj su lura Abraham ya shigo
dukan kansa da ƙasan bindigar nan nan da nan jini ya fara zubar masa. Ganin hakan ya sa
John nufar Abbu Gadan-gadan zai harbe shi kafin ya ƙarasa Abraham ya cimmasa yana zuwa
ya dunƙule ya naushi John a ciki yana huci kamar zaki ko kumurcin maciji cikin ƙara ji ya ce "I
said no!"
"Bad boy akan wannan tsohon ka ke cutar da kan ka?" A fusace ya sake juyawa kan Taj ya ce
"Abu ɗaya ka ƙara cewa zan kashe ka, I'll kill you Taj" Yana faɗin haka ya ƙwaci key ɗin motar
shi hannun Joshua motar da tafi ko wacce mugun kyau ya nufa yana zuwa ya buɗe tare da
shiga ya jata da wani irin sauri kamar zai tashi sama haka yabar wajan, ganin irin gudun da
yake saka Gang team ɗin suka shiga mota tare da marawa Bad boy baya, Abbu ya ja tsaki tare
komawa a hankali masu tsaron kan hanyar suka dinga bawa mutane hannu suna shigewa "Ƴan
iskan yara gantalallu" Abbu ya faɗa bayan driver ya shige da shi zuwa hanyar su da Murtala
Muhd way.... Gudu kawai Abraham yake idanunsa yana zuwa kan corner da zai You-turn danja
ta tsayar da shi, a hankali ya ɗora kansa akan string motar zuciyarsa kamar tayi tsalle ta fito sbd
wani irin baƙin ciki da takaici da yake ji, This is the second time he finds himself in this situation,
bai damu da jinin da yake zuba daga kansa ba burinsa kawai ya tuna inda ya taɓa jin muryar,
tabbas ya san muryar Abbu but where? Ba a taɓa riƙe wuyan rigarsa ba balle wani ya yi
attempting marinsa, bai kuma san dalilin daya sanya ya kasa yin komai akan Dattijon ba, da
alama he's special da wani da wallahi sai ya kuntile hannu idanunsa har wani ruwa ne ke
kwanciya sbd tsabar zuciya da taurin rai.... Knocking Glasses ɗin motarshi ya ji ana yi a fusace
ya ɗago zai zabga ashar idanunsa ya sauka akan wata yarinyar wacce take duƙun-duƙun ya ja
siririn tsaki ganin yadda fuskar yarinyar take duk majina, idanunsa ya ɗauke tare da rufe shi
yana jin komai ya duniyar ya fice masa a rai, ya yi dana sanin dawowa ƙasar bakiɗaya. Ci-gaba
da knocking kawai tayi ya zuge Glasses ɗin zuwa ƙasa da sauri ta ce "Ka taimaka mini dana
abinci saboda Allah Yallaɓai" Bai san meta ce ba, amma ya ji sunan Allah sarai sai ya ci gaba
da kallonta, nan da nan zuciyar tausayin sa ta motsa musamman akan ɗiya mace yana da
tausayin mata ƙwarai tashin hankalinsa yaga mace na kuka, ya ɗauke yana kwaso kuɗi ya
watsa mata ta ƙofa da sauri kuma ya ja motar ya yi gaba... Tun daga ƙofar gate ɗin gidan yake
danna horn kafin gatekeeper ya fito ya yi saurin fitowa kansa a ƙasa domin baya jira bai yarda
kuma a jira shi ba, ya nufi ƙaramar ƙofar shiga tare barin motar a buɗe a waje, cikin sassarfa
cike da kuzari duk da jiri na ɗaukarsa haka ya nufi cikin gidan ya tsaya a ƙofar farko yana danna
password ƙofar ya buɗe, a Main parlour ya tsaya cikin zafin nama kamar Mahaukaci ya shiga
ɗaukan duk abinda hannunsa ya je kai yana doka shi da ƙasa... Daga saman upstairs aka ce
"Grandson!" Abraham bai tsaya daga abinda yake ba, ganin zai jiwa kansa ciwo ya sa David ya
shiga sakkowa daga steps ɗin benen da sauri yana zuwa ya kama hannun Abraham ya ce
"Waye? Kai da wa?" Yaƙi cewa komai sai huci da yake jikinsa na rawa David ya san Abraham
ba zai taɓa magana ba, hakan yasa ya ja hannunsa zuwa saman kujera ya damƙa masa wani
cup ya ce "Drink"
Bai tsaya tantance mene ba ya amsa tare da kafawa a baki ya shanye tas, David ya ƙara zuba
masa wata ya shanye daga nan ya miƙe ya nufi wani part not too ya dawo hannunsa riƙe da
first-aid box ya gyara masa wajan.
"Who is he?" David ya tambaya, cikin mayen daya fara ɗaukar shi ya ce "I don't know, but i knw
him na san muryar" David ya ce "Where?" Ya yi shiru... Ganin yana cikin maye kuma zai fi
ɗaukar magana ya sa ya ce "Look Grandson, na ce ko da wasa bana son ganin jini a jikinka
gwara ka fitarwa da wani jini da a fitar maka, ka ci mutuncin wanda ya ci naka, ka taka wanda
ka ke so, kai ɗaya nake da shi a gefena You're my grandson exit? Babanka yabarka, baka da
Mother baka da kowa a duniya sai ni, ni ne Grandfather naka, idan kuɗi na maganin komai a
duniya to duk irin bala'in daka ɗauko zan ji da shi, ni ne shugaban church ni ne Pasto bayan
haka kafi kowa sanin matsayina a ƙasar nan bana country ba, ina da kuɗi mai kuɗi shi ke da
magana, a top 5 na masu kuɗin Nigeria zan shiga ciki, Mahaifinka Daniel zai shiga.....," "Stop
calling his name, i hate him he's not my father" Abraham ya faɗi hakan idanunsa na lumshewa
ya shiga surutan maye yana faɗin
"She left me, Mamina Grandpa, Mamina Mamina" Sai kuma jikinsa ya shiga jijjiga. Grandpa ya
yi shiru kafin ya ce "Mamin nan taka maybe she's no more bata ra....," Tasss! Ya ji saukar
Glasses ya miƙe da sauri yana riƙe Abraham ya ce "Am so sorry Dear, Maminka na nan I'll find
out where she's hiding to" Da ƙyar bacci ya ɗauke Abraham bakinsa ɗauke da sunan “Mamin,
JEENA" Ganin ya yi bacci yasa Grandpa kiran Taj a waya ta prvt line nasa yana ɗagawa ya