Showing 9001 words to 12000 words out of 126765 words

Chapter 4 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf

ɓaci? Familyn bazan sunanka ɗin banza, da rayuwar mace kamar Majeederh
ta ɓaci ba gwara duka sunayenmu su ɓaci ba, wata rana dalilinta sunan namu ya samu
É—aukakar damu kanmu ba muyi zato ba, mai ya sanya mu iyaye idanunmu ya kan rufe idan
tsautsayi ya samu yaranmu? Yanzu Majeederh ko tana sane wannan abun ya faru ba zaka iya
yi mata uzurin akan rashin auren da take da shi ya ja mata wannan ƙadsarar ba? Ita ɗiya
macace duk runtsi duk jimawa dole ta ɓukaci ɗa namiji wata rana" Uncle Isma'il ya girgiza kai
sbd tsabar takaici ya ce "taya ƙasa zata gyaru bayan mu da kanmu bamu gyara zamantakewar
data yaranmu ba, fine ka kori Majeederh zan nemota na riƙeta a wajena....,"
"Yin hakan zai ja mana babban kuskure yaya, duk wanda zai so ta bayana yake bi, don haka a
barni kawai" Abbu ya tari numfashi Uncle Isma'il da faÉ—in hakan. Uncle Isma'il da ransa ya fara
ɓaci ya ce "Zan taimaketa kamar yadda take taimakon addinin Musulunci, bawai sbd data
kasance ƴarka ba Abdul'aziz Khan" Abbu rai ɓace shi ma ya ce "Kana iya yin haka amma daga
ranar babu ni ba kai, ka cire ni matsayin ƙaninka, ka yanke mu'amala ta dakai" murmushi sosai
Uncle Isma'il ya yi wanda ya fi kuka ciwo yana girgiza kai ya ce "In sha Allah, idan kero na yawo
zabo na yawo tabbas za a gamo Majeederh zata baka mamaki" Aaliyyah dake kuka sosai ta ce
"Abbu don Allah ka bawa Yaa Nura dama ya kawo kuÉ—in aurena, na ga ji da zaman gidan nan
na tsani komai dake cikinsa" kai tsaye Mami ta ce "Fitowa za kiyi ki ce kin tsanemu, aure kuma
dole sai kin kammala makaranta daman ke É—aya ki ka rage cikin gidan.." sai a lokacin Uncle
Bello ya ce "Aaliyyah aure ki ke so?" Duk kawaicin Aaliyyah ta shanye ta ce "Eh, Uncle"
"Ki faÉ—awa Nura ya zo ya saman a gida nan da sati mai zuwa In sha Allah zaki bar wannan
gidan" yana faɗin haka ya miƙe tsaye ya kalli Uncle Isma'il ya kalli Abbu ya ce "Yaya taso muje,
Allah ya bada ladan zumunci Sunan family kuma a rubuta a gaban ƙoshi ana yawo da shi"
Suka fice tare da barin gidan,Abbu ya nufi part É—in sa zuciya babu daÉ—i shi kam Majeederh ta
zame masa annoba, Aaliyyah ta shige nata bedroom É—in tana zuwa ta É—auki wayarta ta kunna
network ta shiga facebook inda labarin Majeederh da Bar Aliyu Sufyan Alhassan yake ta
trending a media. Ko photon Majeederh ta gani da gudu take skipping ta shige sbd tsaron zagi
da mugun alkaba'in da ake mata, tana cikin dubawa taci karo da wani posting photon
Majeederh ne sanye da abaya fara mai kyau fuskarta rufe hannunta riƙe da loudspeaker. An yi
rubutu a saman photon tare da saka.

*She's Innocent*
_Malama Majeederh Abdul'aziz Khan babbar malamar musulunci da muke da ita a wannan jiha,
wacce ta samu damar zama zaƙaƙura wajan lashe musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa, ita kuma ta
ƙara jawo kima da martabar jiharmu, wacce take taimakon marayu, marasa gata take nutsuwar
da matan aure akan darajar da aure yake da shi, duk da kasancewarta budurwa. Abin tambayar
shin ta cancanci haka kowa? Kai da ka ke zaginta ko ki ke zaginta kina da tabbaci akan abinda
ya faru, ko kina da hujja? Ko labarin ƙazan kurege aka baki har kike ɗorawa tare da aibatar ƴar
jama'a, ta haifi wasun ku da yawa, ta fiki ilimi tunani da sanin ya kamata, ta fika kusanci da
mahalicci amma kazo media ko sallar kirki a rana baka yi ka ɓuge da zagin babbar Malama?
Ashe muna rayuwa da dabbobi bamu sani ba? Ko masu aikata zina sai an same su turbi da

taɓarya tare da shaidu 4 sannan za a ɗauki mataki. MALAMA MAJEEDERH ABDUL'AZIZ
KHAN SHE'S INNOCENT I STAND BY HER SIDE._

#Mrs No name

Wani murmushin jin daÉ—i Aaliyyah tayi 5 minutes da yin posting É—in amma comments wajan 1k
hakan ya tabbatar mata da Mrs no name yana da followers kuma babban mutum ne tunda har
ya iya ɓoye sunan shi, kai tsaye profile ta shiga ya rufe komai da komai ko message ba za a iya
yi masa ba, dole sai dai tayi magana ta comment section. Har aka kwana aka tashi Bar Aliyu Sufyan Alhassan bai farka daga suman da ya yi ba, hankalin
Hajia ya tashi tana da Papi tare da Almustapha, hatta korar da aka yi masa wajan aiki bai sani
ba.
Misalin 8 na dare wahala tayi wahala jikin jaririn ya yi zafi kamar wuta, a yanzu ji take ko jama'ar
gari za su kasheta babu abin da zai hanata fita ta nemi ruwan da zata bawa babyn nata, ta miƙe
da ƙyar kusan gabaɗaya kayan jikinta sun ɓaci tana bin gefen hanya harta isa wani wajan da
ake siyar da tsire kanta ƙasa tayi sallama, gabaɗaya mutanen da wajan suka dubeta wani ya ce
"Baiwar Allah lafiya?" Ta jima kafin ta ce "Ruwa nake nema, zan bawa yarona" wani saurayi ya
dinga kallonta kafin ya miƙe tsaye ya ce "Mene na rufe fuskar?" Ta ɗauke kai cikin sa a ya gano
rabin fuskarta da jaririn hannun da ƙarfi ya ce "Masiƙa la'ananniyya mazinaciyya ku je feta ita ce
Malama Majeederh" yana faɗin hakan ya sauke mata wani dutse a ƙoshinta ji ka ke tauu!! Nan
take ya fashe jini ya dinga zuba, kafin ka ce me mutane sun cika kowa ya É—akko duwatsu suka
fara jifanta ta ko'ina ta durƙoshe ta rungume jaririn da jikinta, jama'a sunfi ashirin idan wannan
ya jefa mata dutse aka sai Wannan ya jefa mata a baya...


Na'ima Sulaiman Shu'aibu
Nimcy sarauta
08119237616*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta
_*Follow my account👇🏾*_
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv

African Queen products
Sabulun matsi
Garin matsi
Humra
Turaren wuta
Maganin Infection
Ga number wayata...08130269641

*5.......*
Ta ko'ina suke jifa mata duwatsun jikin ƙaramin lokacin suka farfasa mata jiki. Wani saurayi
wanda kana ganinsa kasan criminal ne yana da dakakkiyar zuciya ya É—auki wani dutse tare da
faɗin. "Fasiƙa, mazinaciyya, duk yadda akai kema ba ƴar halak ba ce, shi yasa tsayin shekaru
talatin da biyar ki ka sa yin aure kina bin mazan aure da samari" yana faÉ—in haka ya sakar mata
dutse a goshinta nan take ya fashe jini ya wanke mata fuska,ta fara gani dishi. Sunayen Allah
take kira da neman É—aukinsa, tsoro ya kamata jin babyn nata ya daina motsi da kukan da yake
fatan É—aya Allah ya sanya jifan bai same shi ba, balle ya yi sanadin mutuwarsa.
"To, wai me muke jira ne? daga ita jar jaririn mu sanya musu fetur a ƙona mazinaciyya mai ci da
musulunci, a kuma ƙone mugun iri!"
Wani wanda yake da É—an hankali ya ce "Amma kana ganin ba muyi kuskure ba? Ai ba jifeta ya
dace ayi ba, tunda ba matar aure ba ce, budurwa ce bulala ne ya dace da ita" cewarsa.
Saurayin ya ce "A to mene martabarta da matar aure? Ai auren ne ba tayi niyya ba shi ya sa
take ta gantali ta shiga rigar addinin musulunci ta ci zarafin Musulunci da musulmai, ita fa
yankata ya dace ayi"
Kafin kowa ya sake magana hasken wata dalleliyyar mota ya haske wajan duk da irin fitilar da
suke kan hanya.
Gabaɗaya suka kalla motar mai ƙirar Mercedes-AMG G63 Ash colour, slowly yake driving har
ya ƙara su wajan, ta cikin motar yake ƙare mata kallo ganinta durƙoshe har yanzu ko motsi ba
tayi, ya ja idanunsa ya lumshe wani abu ya daki zuciyarsa zafi da raÉ—aÉ—i yake ji sosai abinda
yake ji tsayin shekaru ya ƙara yawa a ƙirjinsa. Ya fesar da numfashi tare da sanya hannu ya ɗan
danne gefen zuciyarsa, gently ya gyara Bluetooth na kunnenshi speaking calmly ya ce.
"Meet me at my house right now" Yana faÉ—a ya É—auki face mars ya sanya tare da É—aukan
Glasses ya saka a idanunsa, cikin tarin nutsuwarsa da kamewarshi wacce ta riga ta zauna a
jikinsa musamman yanzu da izzar mulki ke É—awainiyya da shi. Ya fito daga motar fuskarsa haÉ—e
duk da babu wanda ya san waye, bai kula kowa ba ya nufeta tare da sanya hannu zai kama
nata a firgice ta É—ago idanunta tare da girgiza kai cikin wata murya mai rauni da tausayi ta ce
"Kuyi mini komai, ban taɓa jikina" "ji banza shashasha, uwar mene ya yi saura a jikin banda
najasa...,"
Marin da aka sauke masa ne ya sanya ya yi shiru da bakinsa domin har tsakiyar kansa ya ji
marin shatin yatsun His Excellency ya fito raÉ—au a fuskar.
Ya ƙara kai hannu zai riƙe nata hannun domin taimaka mata tayi saurin ɗauke hannu kamar bai
son magana murya can ƙasa ya ce "Please Hawwa'u, akwai jama'a"
Ta girgiza kai numfashinta na fita da ƙyar ya ƙara rusunawa shi kansa kamar wanda ya yi jinya
ya ce "Haba Jiddo" ganin da gaske take ya sanya ya tattara ƙarfinsa waje guda tare da sunkutar
ta gabaÉ—aya har jaririn sai cikin mota, ya kwantar da ita a baya ya sanya hannu ya zare jaririn
tare da ɗaukarsa ya nufi ɓangaren diver. Yana shiga ya yi wa motar key da hannu ɗaya ya fara
driving cikin sauri ɗaya hannun kuma ya rungume jaririn, keɓantaccen gidansa ya nufa da ita
direct.
Wani tsohuwo ya ce
"To ba ga irinta ba, É—aya daga cikin kwarton abokin alfashar nata ya zo ya É—auketa, ai ni duk
wani É—an shege na daina tausyainsa tunda ana sane ake haifarsa"
Haka suka dinga surutu, suna faÉ—in duk wata mace mai irin shekarun Majeederh wacce ba tayi

aure ba to kawai iskanci take tana aikata zina.
Lokacin da His Excellency Abu-turab ya isa gidansa P.a É—insa na tsaye yana jiran zuwansa,
Hammad ya nufi Abu-turab wanda yake ɗauke da jaririn yana zuwa ya miƙawa Hammad jaririn
shi kuma ya koma wajan motar, lokacin Majeederh ta gama sumewa jikinta ya É—auki zafi sosai a
ransa yake istigifari kafin ya tattara ya É—auketa cak, sanin halin Abu-turab yasa tuni Hammad ya
shige ciki da jaririn wani ɓangare ya nufa da ita ya kwantar kan bed, bai tsaya jan aji ba ya
samu ruwan zafi da showel ya danna duk inda aka fasa mata tare da yi mata allurar kashe zafi
data barci, ya yi mata dressing yana yi yana É—auke kansa, raunin jikinta bai hana shi ganin
asalin kyanta ba, asalin kyawun Fulanin Usul. Zuciyarsa kamar tayi tsalle ta fito ya razana da
kyanta sosai shi ya sa ko Hammad bai bawa damar shigowa ba sai da ya gama komai ya sanya
mata driving tana ta barcin wahala.
After ya gama ya duba babyn. A hankali ya fito yana dafe kansa sbd ciwon da yake masa yana
zuwa ya faÉ—a saman kujera idanunsa rufe. "Amma yana da kyau ka huta Your Excellency" ya
ware Idanu tare da tsiyaya black tea a cup sai da ya shanye ya ce
"P.a, kana tsaya iya aikin ka" "Am sorry sir, bayan p.a you're my best friend hakƙina ne na faɗa
gaskiya kuma na kula da kai, idan kana son hakƙin Majeederh tana bawan Allan nan kada ya
kama mu yana da kyau a bata wasiƙar ta karanta" ɓacin rai wanda Hammad bai taɓa gani ba ya
bayyana kan fuskar Abu-turab, idanunsa da suke a ri ne ya ware akan P.a cikin kakkausar
murya ya ce
"Kasan me hakan ke nufi?" Ya shiga kaɗa ƙafa a duk sanda ransa ya ɓaci kafin can ya ce
"She never choice me, ba zata taɓa zaɓata a matsayin miji ba, she most go back to him ba zata
gane shekarun da nayu ina jiranta ba" ya miƙe yana kai kawo
"Sunanta na sanya jinina, sunanta na sakawa Æ´ata Jiddo, ko sunan mahaifiyata ban sanya ba
sai nata, shi kaÉ—ai ya isa yasa ka gane, zan iya adalci a mulkina al'ummata, amma ba zan iya
adalci akan soyayyar Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ba, duk hanyar da zan bi na raba ta
da kowa zan yi" Hammad zai magana Abu-turab ya daka masa tsawa ya ce
"Get out" dole ya fita amma shi a ransa ya san babban kuskure ne su riƙe wasiƙar nan.
"Ya Allah!" Abu-turab ya furta yana É—aukan gorar ruwa mai sanyi, sai da ya shanye tas kafin ya
yi cilli da Robber.
Babyn daman yana wajan wata maid yana ta barci ya ji ruwan zafi da kaya masu kyau ga
madara da aka bashi sai numfashi yake saukewa.
Yadda Majeederh ta kwana kan gado haka ya kwana a parlour, lokaci zuwa lokaci yana zuwa a
cikin daren sai da ya sanya mata drip uku kansa cewar ruwan na tafiya da sauri. Kiran sallar
Subhi ya sa ya nufi bedroom É—insa farar singlet É—in jikinsa ya cire ya sakarwa kansa shower
ruwa na saukar masa, alwala ya yi ya shirya cikin ash É—in jallabiya masallacin dake gefen
gidansa ya shiga lokacin ana kuraye kirayen Assalatu....
Assalatun ya yi daidai da farkawar Bar Aliyu Sufyan Alhassan a gadon asibiti ya motsa a
hankali yana dafe kansa dake masa ciwo kamar ya rabe gida biyu, dishi dishi ya fara gani kafin
ganinsa ya daidaita idanunsa ya sauka akan Hajia ta ce "Zakina, sannu ka ji" ya yi ta kallonta
kafin ya juya ya kalli Papa shi ma ya ce "Sannu Haydar, ya jikin?" "Ba sauƙi Papa" Papa ya ce "Meke maka ciwo?"
Ya mutsa fuska ya yi yana rufe Idanu "Meke damunka? Almustapha kira Dr"

"Babu abinda zai iya"
Almustapha ya ja tsaki ya ce "To ai kun ji, shi fa sam baya tausyain kansa ina can gidana tare
da matata ku kirani wai jikinsa ya tashi kamar shi kaÉ—ai kuka haifa? Mene abin so a wajan wata
Majeederh tsohuwar ko me?" Aliyu kamar zai kuka ya kalli Hajia ya ce
"Kin ganshi ko?" Hajiya ta ce "Ka fita idanuna Almustapha, kabar mini yaro ya ji da abinda ke
damunsa" "I love her"
Cewar Aliyu. "Kayi haƙuri zaka sameta idan rabonka ce" Almustapha kamar ya shaƙe Aliyu
haka yake ji ya ƙara yin tsaki ya ce
"Gashi nan an sallame ka daga court É—in da ka ke aiki, sai ka zauna zaman kashe wando kana
jiran wata" Zaki ya kwaɓe fuska ya ce "In sha Allah sai Allah ya ɗora maka son wacce bata son
ka" Dariya sosai Almustapha ya yi kafin ya ce
"Ai matata Æ´ar Aljanna ce ta wada tani da komai na kwanciyar hankali to me zai sanya na fara
tunanin yi mata kishiya?"
Sai a lokacin Papa ya shiga dramar ya ce
"Shi ma tashi matar ai Æ´ar Aljanna ce" "Barshi Papa idan ya cika ya zo ya dauki Latifa ya sata a
wuta, matar taka duk raguwar mai"
Yana faÉ—in haka ya juya zuwa ga Hajiya tare da É—ora kansa a cinyarta ya ce "Hajia zuciyata
babu daÉ—i ki taimaka mini" ta shiga lallashinsa ta ce "Yanzu yana da kyau ka shaidawa duniya
baka da haÉ—i da É—an gidan Majeederh, after that sai ka fara shirin nemanta ko?" Ya kalli
mahaifiyar tasa sosai sai bai ce komai ba. Misalin 12 na rana lokacin an sallami Aliyu zuwa gida
yana zaune ya faÉ—a sosai kamar wanda ya yi jinyar shekara kamar daga sama ta faÉ—o bai
kalleta ba, ƙamshin turarenta kawai ya ji ya fahimta "Ya jikin?" A gajarce ya ce "lfy" ta zauna ta
ce
"Amma ka fasa aurenta?" Ya dubeta ya ce "Ita wa?" Kai tsaye ta ce "Waccar Mazinaciyyar
mana" ya yi murmushin kawai bai ce komai ba ta ce "Magana nake kayi shiru" ya juya
gabaɗaya tare da saka hannu ya riƙe fuskarta ya ce "Kina son rabauta ko Wife? Me ya sa ki
kewa mijinki haka?" Ta ce "Idan har zaka ƙara aure zaka iya ganin fiye da haka" ya sake ta
yana kwanciya jikin kujera ya ce
"Sai dai idan bana raye, Latifa Omar ke baki tausayina ne? Sai fa Majeederh zata zo gidanki ki
ke gyarawa, tsafta zero, kwalliyya zero, girki zero, mu'amalar aure zero, aikin ki kawai ki sani,
yanzu mene ribarki don ki aibata mijinki? yaran da zaki haifa sune abin zai zamewa tabo not me
or Majeederh" ta miƙe tsaye ta ce "Divorce me" "Never, ki jira zama tare da sweetheart" baƙin ciki ya cika mata zuciya ya zari key car tabar
gidan ya bita da kallo.
Tunda ta farka daga nauyayyen barcin ko tari ba tayi ba, tsoran ta buÉ—e idanu taga su waye
akanta take, bata so ta samu É—auki ba ta so ace mutuwa ce ta risketa.
Mama dake zaune ta zabga tagumi ta ce "Baiwar Allah kenan, Allah ya saka miki" ta goge
hawayen Idanunta Hammad ya ce
"Kamar ta farka ai" Mama ta ce "Ato gwara ta tashi ai, ga É—an yana ta kuka gwanin tausayi" a
hankali ta buÉ—e Idanunta ba tare data kalli kowa ba sai gefe guda, yadda take ji zaka É—auka
kuka za tai ta rusawa amma idanunta a ƙafe komai na tunaninta ya sabunta hanyar da zata bi ta
zama cikakkiyar karuwa kawai take nema. "Sannu Malama, Sannu kin ji" sai a lokacin ta juya ta kalli Mama tana jinjina kai. Gently ta mayar

da Idanunta ta rufe daidai shigowarsa yana gyara zama babbar rigar jikinsa, nutsuwa da haiba
tattare da shi.
"Barka da zuwa Your Excellency" Abu-turab ya jinjina kai tare da neman kujera ya zauna
idanunsa kwance a kanta,daga nan Mama miƙewa tayi. Jin shirun ya yi yawa yasa ta juya cikin
sa a suka haÉ—a idanu tayi saurin É—aukewa. A ransa ya ce "Ma sha Allah, Tubarkallah" a fili
kuma ya furta "Jiddo ya jiki?" Ta haÉ—e rai sosai "akwai ciwo?" Nan ma shiru tayi gani take yanzu kowa ya tsaneta. Sosai ya
gane bata san waye a gabanta ba domin ƙwayar idanunsa kawai ta kalla. Yana ƙoƙarin magana
ya ji ƙarar bindiga na tashi ta karaɗe gabaɗaya gidan, ya buɗe idanu da mamaki yasan akwai
securities amma harbin na mene? Hammad ya fice da sauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login